Free chapter · Read without an account
BABI NA UKU
by Fatima Eshak · FATHIYYA
Page__3.
*FATHIYYA*
Na
*BILLY S FARI*
Da
*UMM ASGHAR*
*YAN TAGWAYE.....*✍️
*PAID BOOK....*#400
GA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA DAYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
________________________________
Mahmoud kuwa ya jima a wajen zaune har cook ɗin dake haɗa abinci a gidan ya fito tare da russunawa a gaban shi yace "Sir! Breakfast is ready".
Mahmoud daya buɗe idanuwanshi a hankali tare da sauke ajiyar zuciya yana tashi zaune daidai ya ce "ok". Sannan ya miƙe ya koma sama, yana shiga ya tadda wayarshi na haske, ko daya duba kiran babban aminin shi ne da basa rabuwa wato Farouq kusan missed calls biyar, yana ƙoƙarin kiranshi message ɗinshi ya shigo
_"We need to talk abokina, a ina zamu haɗu?"_
_"In my Office, let's say by three o'clock"_
Ya tura mishi amsa tare da ajiye wayar gefen gadon, yana ƙoƙarin miƙewa kiran Zinnira dake gab da shiga kamfanin nasu ya shigo wayarshi tana son faɗa mishi cewa kada ya manta ya fito da wuri saboda ana buƙatarshi shima a wajen meeting ɗin, yana ganin ita ce ya yi tsaki tare da kashe wayarshi gaba ɗaya ya mayar ya ajiye, toilet ya shiga yayi wanka ya shirya cikin wani haɗaɗɗen voile kalar Royal blue ɗinkin half jumper, ya taje kanannaɗaɗiyar sumar kanshi baƙa siɗik irinta fulanin asali haɗe da sajenshi dake ƙara fito da cikar kyawun fuskar shi da kwarjinin shi na cikakken namijin da ya amsa sunan shi ya shafa mai sai kyalli suke yi, hula ya ɗauko kalar royal blue itama ya ɗora akai yana kallon kanshi ta madubi haɗe da murza ƴan madaidaitan laɓɓansa da suke pink colour tamkar ya shafa jambaki sannan ya ɗauki turarukan savage(dior) da kuma eros(versace) ya fesa tare da ɗaura silver agogonshi na pierre cardin a tsintsiyar hannunshi, baƙaƙen eye glasses ɗinshi da suka kasance na ƙara ƙarfin gani ya saka, abun tubarkallah masha ALLAH don Mahmoud kam badai kyau ba, gwargwado shima ALLAH ya kyautata surarshi don mutane har kasa banbancewa suke yi tsakanin shi da amininshi Farouq wanda yafi kyau, amma yadda mata ke matowa a kanshi yasa wasu ke ganin ya ɗara Farouq kyau nesa ba kusa ba, duk da kuwa rashin fara'ar da yake fama da ita in ba can baka rasa ba, shima ɗin hakan tafi faruwa idan yana tare da abokanan kasuwancinshi ko kuma mai girma Zinnira.
A hankali yake saukowa daga upstairs ɗin har ya ƙaraso ƙasa ya nufi wajen dining, kaɗan ya tsakuri breakfast ɗin ya mike don sam ba tayi mishi daɗi a baki, cike da girmamawa ya shiga amsa gaisuwar masu aikin dake harabar gidan da yake faman ratsowa ta wajensu yana wucewa, wasu bayin ruwa suke yiwa fulawoyi, wasu kuma share-share, wasu wankin motoci wasu kuma masu yin cefane ne da sauran masu kulawa da aikace-aikacen gidan.
Sai daya tambayi kowannen su idan yana da wata matsala suka amsa mishi da babu haɗe da yi mishi fatan ALLAH ya kiyaye sannan ya shiga motarshi da kanshi ya tayar ya bar gidan, kai tsaye office ɗin shi ya nufa dake ɓangaren kamfanin da yake kula dashi ba tare daya damu da zuwa wajen meeting ɗin da za a gudanar a can ɗayan kamfanin ba wato head office ɗin su yana jiran isowar abokinshi Farouq don yau ya sha alwashin sai ya baƙanta ran Zinnira kamar yadda ta baƙanta mishi shi yasa ba zai tafi wajen taron ba, duk da ya san cewa zuwan nashi a wajen nada matukar muhimmanci sosai don shi suka fi sani ba ita ba...
*****. *****. *****.
A ɓangaren Faruq kuwa sai da suka yi sallar azahar ya samu ya lallaɓata ta sha tea rabin mug ya ɓallo paracetamol ya bata ta sha sai faman narkewa take yi tana zuba mishi shagwaba, kukan da ta yini tana yi ne ya saukar mata da zazzaɓi, kwanciya ya sata tayi, cikin lokaci ƙalilan kuwa bacci ya ɗauketa yana zaune yana riritata kamar wata jaririya.
Sai da ya lura baccin nata yayi nisa sosai kafin ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka a gurguje ya fito ya shirya yana kallon ɗan karamin agogon dake ajiye akan bedside drawer, bai da buri yanzu irin ya ganshi wajen Mahmoud daya ce mishi su haɗu a Office ɗinshi, ya tabbata bazai rasa samun mafita ba a wurin shi don shi a daidai wannan lokacin ya rasa abun yi gaba ɗaya.
Shiryawa yayi cikin ƙananun kaya wandon jeans kalar faded blue da baƙar polo shirt duka na kamfanin Ralph Lauren sai baƙaƙen loafers da ya sanya a kafarshi, turaren Chanel(Bleu) da ya zama signature perfume ɗin shi don baya amfani da kowanne irin turare idan ba shi ba ya ɗauka ya feshe dukkan jikin shi kafin ya ɗauki makullin mota dake ajiye akan dressing mirror ɗin ya fice bayan yayi pecking Fathiyya dake bacci hankali kwance a goshinta.
Har ya fice ya bar gidan zuciyar shi na saƙa mishi ta yadda zai yi ya zille wa wannan auren da Mami ke neman ƙaƙaba mishi ya rasa mafita, dukkan wacce ya kama sai yaga ba mai ɓullewa bace shine ma yasa zai fita wajen Mahmoud yasan idan har ya faɗa mishi damuwar shi ba zai kasa sama mishi mafita ba.
Kusan mintuna goma sha biyar suka ɗauka a haka babu wanda ya iya cewa uffan kafin nan a turo ƙofa, sakatariyar Mahmoud ce ta turo ƙofa cikin girmamawa ta gaishe su sannan ta nufi wajen fridge ɗin dake ajiye daga can gefe a cikin office ɗin ta buɗe ta ɗauko gorar ruwa guda biyu da cups biyu ta ɗora a saman ɗaya daga cikin trays ɗin da aka tanada anan gefen fridge ɗin don tarbon baƙi haka idan sun zo.
Bayan ta ajiye ta fara ƙoƙarin buɗe wa ta tsiyaya masu Mahmoud ya dakatar da ita haɗe da bata umurni kawai ta fita, da kanshi ya tsiyayawa Farouq ruwan a cup ya tura mishi a gabanshi shima ya tsiyaya nashi, har zai kai cup ɗin a baki sai kuma ya fasa tare da kallon Farouq da har lokacin fuskarshi na tallabe da hannayen shi ya ce "have some water, zaka samu relief a cikin zuciyarka" ya ƙare zancen tare da miƙa hannu ya ɗauki cup ɗin ya miƙa mishi.
Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya tare da dire cups ɗin suna kallon juna, yayin da Mahmoud ya haɗa hannayen shi waje ɗaya ya tokaresu da ƙaton Table ɗin dake gabanshi haɗe da tallabe fuskarshi dasu yana sauke ajiyar zuciya "Menene problem ɗin? Me yake faruwa ne Dude?"
Sai da shima ya yi ajiyar zuciyar sannan ya ce "Kamar dai kullum Mami ce problem ɗin, na rasa dalilin ta na cewa dole sai na ƙara aure, haihuwa ba nufin Allah bace, shikenan don Fathiyya bata haihu ba sai ace dole sai nayi aure bayan babu buƙatar hakan ko kaɗan a tare da ni saboda Allah".
Ɗan murmushi Mahmoud yayi yana mai jingina da bayan kujerar da yake zaune a kai yana jujjuyawa kafin yace "kai naka ma mai sauƙi ne ashe don banga abun tashin hankali a cikin wannan al'amarin ba, Mami ai ba zata saka ka yin wani abu da zai kasance cutarwa ga rayuwarka ba, aure da tace kayi ba laifi bane tunda kana da halin yin hakan koda kuwa ace mata uku ta nemi kayi ka haɗa da Fathiyya su zama huɗu, kamata yayi kayi focusing wajen ganin ka kwantar wa da Fathiyya hankali don kasan su mata basu da babba basu da ƙarami in dai akan kishi ne, kada ka kuskura kayi jayayya da hukuncin Mami domin kuwa duk abinda take yi to tana yi ne domin farin cikin ka, kowa ya aurar da ɗanshi to fa burinshi na gaba shine ganin zuri'arshi don haka Mami bata da laifi don ta nemi da ka ƙara aure ko Allah yasa ka dace da abinda ake nema sai dai kuma ka tabbata kafin kayi auren nan kun ziyarci likita a duba ku gaba ɗaya don a tabbatar da a ina matsalar take a kuma san matakin ɗauka, ni na rasa dalilin da yasa kaƙi kuje asibiti tuntuni kamar ba wayayyen mutum kuma ɗan boko ba, kodayake laifin Fathiyya ne data biye maka ta kasa tankwara ka kuje asibiti tuntuni".
Ruwan ya ƙara tsiyaya a cup ya ɗauka ya shanye kafin yace "ba zaka gane ba Mahmoud, nifa nasan lafiyata ƙalau banga abinda zai sa na kai kaina asibti gaban likita ba suna yi mini jaye-jayen ciwo haka kurum, Fathiyya kuma nayi-nayi da ita ta shirya taje don su bata treatment ɗin da ya kamata tace ba zata je ba idan har ba tare dani bane to Saboda Allah ya kake so nayi mata, infertility ai matsalar mata ce ba ta namiji ba".
"A ina kaji ance matsalar infertility daga mace ake samu Farouq? A ina? Please kada ka ƙara faɗar haka har wani ma yaji yayi maka kallon marar ilimi, kayi ƙoƙari kuje asibiti a bincike ku gaba ɗaya ko don samun kwanciyar hankalin ku, sannan kada ka kuskura ka saɓawa Mami akan abinda bai fi ƙarfin ka ba, girma da matsayin Mami yafi gaban tayi maka umurni ka tsallake, nasan damuwarka bata wuce akan Fathiyya ba to kayi ƙoƙari ka nuna mata muhimmancin yin biyayya ga umurnin Mami kada ka manta Uwa gaba take da kowa idan har son gaskiya take yi maka dole ta taimaka maka wajen kaucewa saɓa mata.
A yadda ma nasan Fathiyya bana jin zaka samu wata matsala daga gareta tunda kai kake faɗa mini irin haƙuri da kamewarta tare da hangen nesanta, da dai ace irin halin Nira gareta na rashin ganin girman miji da ɗaukarshi ba komai ba da sai nace anan matsalar take". Yayi maganar yana mai tunowa da wulaƙancin da Zinnira tayi mishi ɗazu da safe, wani irin ƙunci yaji ya ziyarci zuciyarshi kamar a wannan lokacin abun yake faruwa.
Kallon tausayi Farouq ɗin yayi mishi don yasan wasu daga cikin problems ɗin shi da Zinnira.
"Wai har yanzu kuna nan dai da matsalarku bata canja ba?"
"Mts" yayi tsaki. "Ai bana jin Nira zata sake hali nan kurkusa dai don abubuwan nata kullum ƙara gaba suke yi, wai ace yanzu har ta kai haƙƙina na aure ma ba zata bani ba idan nayi magana tace na isheta da jaraba ko tace tana da abun yi don haka bata da lokacin saurara ta da buƙatuna, to Saboda Allah ina da wani wuri da zan je na sauke larurata ne bayan wurinta, ɗazu fa da safe akan zata fita ta hanani haƙƙina nayi magana tace zata shiga cikin mutane don haka sai dai nayi haƙuri saboda a wajenta mutanen waje sun fi ni".
Girgiza kai Farouq yayi yace "to amma mutumina haka zaka cigaba da zama da ita tana gara ka kamar gare-garen wasan yara? Baka ga ya kamata ka ɗauki wani mataki akan hakan ba".
"Wane irin mataki zan ɗauka Farouq, ai babu wani mataki da zan ɗauka da ya wuce na cigaba da haƙuri har zuwa lokacin da zata gane gaskiya ta canja halayenta".
"ALLAH ya kyauta, abinda kenan ko a mafarki Fathiyya bata taɓa gwada yi mini ba, wallahi ko ciwo Fathiyya keyi na nemi haƙƙina ba zata hana ni ba, kuma zata bani haɗin kai ɗari bisa ɗari sai na samu cikar gamsuwa sosai, kai ina faɗa ma har nuna mini take yi ta fini buƙatar hakan saboda kawai ta faranta mini alhalin a zuciyarta bata buƙatar hakan.
"Ikon ALLAH, ubangiji ka shirya mini Nira haka nima, da na bata dukkanin farin ciki a duniya, ciki kuwa har da duka rayuwata".
Dariya Farouq ya kwashe da ita haɗe da bashi hannu suka tafa, a zuciyarshi yana ganin ai ba wani abu bane don matarka ta sunna ta baka kanta, abu ne da ya zame mata dole ko tana so ko bata so amma tsabar sakarci irin na Mahmoud yake ganin don anyi mishi hakan sai ya bi da wata kyauta ko wani abu makamancin hakan kamar yadda ya faɗa, wai ciki ma har da rayuwarshi, wannan wane irin shirme ne.
Da haka suka ci gaba da hirarsu har aka kira sallar la'asar suka tashi tare suka je suka yi Sallah, daga nan suka yi sallama da juna shi ya wuce abin shi Mahmoud kuma ya koma office.
Ko mintuna biyar bai yi da zama ba Nira ta turo ƙofar office ɗin ta shigo, ƙamshin turarenta daya damar mishi hanci ya saka shi ɗagowa ya kalleta tare da maida kanshi ga computer ɗin dake gabanshi daya kunna.
Ganin bai da niyyar kula ta ya sata ƙarasowa gaban ƙaton table ɗin dake gaban shi ta ajiye handbag ɗinta tana faɗin "Wai meye haka Mahmoud? Wane irin wulaƙanci ne kake ƙoƙarin yi mini haka?" ...
#Fathiyya
#Tagwaye
#Billy s Fari
#Umm Asghar.