Free chapter · Read without an account
NUFIN ALLAH! Chapter 2
📱 *NUFIN ALLAH....!* 🤲🏻
_*Arewabooks@ayshadansabo*_
*Paid book:500*
*Chapter 2*
_Free page._
Kafin ruwan ya tafasa tuwan ya ɗumamu Najma ta kammala sharan ɗakinsu, wanda ba wani girma bane da shi. Bayan ta haɗa musu shayi ruwan bunu(ruwan lipton), ta juye ɗumamen a kula ta nufo ɗakin Inna Mairo da shi. A falo ta aje komi ta nufi bedroom ɗin wajen Inna Mairo, ta sameta a kwance har lokacin tayi lamo akan katifarta tana faman zurfafa tunani. Cikin sanyin murya Najma ta zauna daga bakin bed ɗin tana faɗin, "Inna na kammala, ga ɗumamen da ruwan lipton can a falo. Inna Mairo ta muskuta ta tashi zaune tana sauke manyan idanunta da Najma ta gada a kanta, ta sauke numfashi a hankali ta ce, "Sannu Najma da ƙoƙari, Allah ya yi albarka ya zaɓa muku mazajen aure na gari." Najma da tuni ta gane jam'u da Inna Mairo tayi tana nufin ita da su Luban gidan hakimi take wa addu'ar, sai ta kauda kai tana amsawa a zuci. Inna Mairo ta cigaba da cewa, "Da zaran mun kammala karin kumallon sai ki bani ruwan wanka, watakila idan nayi naji ɗan ƙarfin jikina." Najma ta murmusa ta ce, "To Inna!" Daga haka suka fito zuwa falon da Najma ta shareshi tsaf, ta goge yagaggen ledar tsakar ɗakin. Suna cin abincin suna taɓa hira akan ciwon Inna Mairo da irin yadda ake samun kuɗin sayen magungunan da ƙyar.Ba don Hakimi ba da tuni watakila Innar ta mutu,sabida rashin gata da wanda zai tsayawa lamuransu har ya ɗauki nauyinsu. Ba kuma don Innar ta rasa Ƴan uwa ba, sai don Ƴan uwan nata sun gujeta sun juya mata baya shekaru kusan bakwai kenan rabonta dasu.Tsakaninta dasu sai dai aiken kayan abinci da zanin sallah da suke mata duk shekara, amma baya ga haka babu mai takowa inda take domin sunyi arziƙin da suke ganin tamkar ci bayane su tako ƙauyen garin giwa su ce suna da ƙanwa bare har su ga halinda take ciki su tallafa mata. Wani irin abu mai ɗaci ya tsayawa Inna Mairo a maƙoshinta, lokacin da ta tuno zuwan Gwaggo na ƙarshe garin giwa, bayan rasuwar marigayi Malam Mahmuda. Najma ta kwashe komi ta kai kicin ta aje, ta ɗauki bokiti ta ɗebowa Inna ruwan zafi ta surka, ta kai mata banɗaki don tayi wanka ko zata ji daɗin jikinta kafin Baba Hakimi ya aiko da magungunan da zata sha.
Ɗakinta da ke kusa dana Inna ta shiga ta share tare da gyara shinfiɗar lafaffiyar katifarta, wacce tun ta makarantar kwanan da suka yi ne ta dawo da abin ta tana kwanciya akai. Gefen katifar ta samu ta zauna ta sauke numfashin a hankali, zuciyarta na kwaɗaita mata son jin asalin tarihin Innarta da yadda aka yi ta auri Mahaifinta Malam Mahmuda. Tana matuƙar son sanin musabbabin da Gwaggon kaduna take nuna wa Inna ƙiyayyar da har ta kai ta rabata da Ƴan uwanta, ta hana su raɓeta ko ita Innar ta rabesu. Tana nan zaune tana zurfafa tunani har ta ji shigowar Inna ɗaki alamun ta dawo daga banɗaki yin wanka, tayi saurin tashi ta fito tana faɗin, "Inna har kin fito?" Inna Mairo ta dubi tilon Ƴarta da take duba ta ji sanyi a ranta ta bata amsa da faɗin, "Na fito Najma, ke ma sai ki je ki yo wankan kafin asan abin yi zuwa rana ko?" Najma ta jinjina kai tana faɗin, "To Inna, amma ina ga da rana ɗinnan da wuya mu samu abin girkawa domin babu sauran kayan abinci sun ƙare." Inna Mairo tayi shiru, kafin daga bisani ta dubi Najma tana faɗin, "To shikenan Najma, Allah zai rufa asiri. Ina ga Hakimi ya shafa'a ne ba a kawo kayan abincin wannan satin ba.Ki yo wankan ki fito akwai ɗari biyar sai ki je ki auno mana garin kwaki muyi kwaɗonsa da ƙuli muci kawai." Najma ta jinjina kai cike da gamsuwa da maganar Inna ta ce, "To shikenan Inna, bari in je in yo wankan." Ta nufi ƙofar fita daga ɗakin ta bar Inna Mairo da bin bayanta da kallo, tana mai jin matuƙar tausayin Najmar na danne zuciyarta.A kullum ta tuna cewa Najma ita kaɗaice a gareta, kuma bata da sauran dangin uba a raye da zasu tallafeta sai ta ji hankalinta ya sake tashi. Domin ita kanta ya ta ƙare da nata Ƴan uwan bare har ta sanya ran watarana zasu tallafesu ita tilon Ƴar nata Najma. Ta ɗanɗana zafin rashin Ƴan uwa ko Ƴar uwa shaƙiƙai da bata da su, ta san zafi da illar hakan ga duk wanda ya taso cikin tsangwaman Ƴan uban da kansu ba a haɗe yake ba. Ta san illar ƙiyayyar matar uba, domin shi ne silar shigarta duk wani halin ƙuncin da take ciki a yanzu, bayan ƙasa ya rufe idanun Abbah da gwarzon mijinta Malam Mahmuda. Domin a lokacin Abbah na raye duk irin ƙiyayya da jin zafinta da Gwaggo ke yi, bata iya nuna mata wani abun sabida shakkar idanunsa. Amma tun daga randa ya kwanta dama, ta sake gane irin ƙiyayyarta da ke zuciyar Gwaggo, wanda bakomi ya sake assasa ƙiyayyar ba sai mugun riƙo da Gwaggon ke da shi.
Inna Mairo ta faɗa ɗakinta don shafa mai ta sanya kaya, tana yi zuciyarta na sake tariyo mata da irin rayuwar da tayi a garin giwa ,tun daga zuwanta tana amarya, har kawo yau da wanda ya yi silar zuwanta garin bashi a raye. Ya tafi ya barta da tarin kewa da ƙuncin zuciya, Ya barsu a lokacin da ita da tilon Ƴarsa ke matuƙar buƙatar kulawarsa. Hawaye masu tsananin zafi da sam bata iya riƙesu a duk lokacin da tunaninsa ya bijiro mata suka silalo daga idanunta,ta kai hannu ta sharesu tana jin ƙunci mai yawa na sake mamaye zuciyarta. Cikin sanyin jiki ta kammala kintsa kanta ta sanya riga da zani na wata atamfar chiganvy, wanda ke ɗaya daga cikin irin zannuwan da ake aiko mata dasu daga hannun Ƴan uwanta su Yaya Kabeeru.
Najma wanka tayo ta shirya kanta cikin wata doguwar rigar atamfar roba, kalar atamfar ja ce da ta haska baƙar fatarta mai laushi.Fuskarta ya yi fayau babu ɗigon kwalliya illa tozali da ta zizarawa fararen idanunta, waɗanda ke da wani irin haske da ƙyalli tamkar ruwan hawaye na taruwa a cikinsu. Gashin kanta sassalka irin na asalin fulanin da ta gado wajen Inna, ta ɗaureshi a tsakiyar kanta kafin ta ɗaura ɗankwalin kayan nata. Lokacin da ta fito daga ɗakin ta samu Inna Mairo zaune a falo, ta nema waje ta zauna daga ƙasan ledar tsakar ɗakin ta ce, "Inna na kammala shirin, bani kuɗin siyan garin kwakin in je in dawo kafin rana tayi." Inna Mairo ta dubi Najma tana yaba kyawunta, wanda ta gado a wajenta. Baƙar fatarta ce kawai na Malam Mahmuda, amma kyawun fuskar da surar jikin duk nata ne, domin babu inda Najma ta barota a kamanni sai bambamcin kalar fata kawai. Ita Inna farace tas! Wacce a kallo ɗaya zaka gane cewa jinin fulanice sosai. Ta miƙa hannu ta ɗakko naira ɗari biyar ɗin da shi kaɗai ya rage musu a gidan ta miƙawa Najma, ita kuma ta sanya hannu ta amsa tana miƙewa tsaye ta tashi ta nufi ɗaki don ɗakko hijab.
Lokacin da Najma ta dawo ta samu Auwalu ya kawo ma Inna magungunanta, sai dai ba a samu guda ɗaya ba sabida tsadarsa. Ta dubi Inna a lokacin da take mata bayanin ta ce, "Yanzu Inna to ya za a yi kenan?" Inna Mairo tayi murmushin ƙarfafa guiwa ta ce, "Allah zai kawo yadda za a yi Najma, ni burina ma mu sake samun jarin da zaki cigaba da toya ƙosannan tunda sana'ar ya amshemu dashi muke samun na rufin asiri." Ta kai ƙarshen maganar da sanyin murya. Najma ta jinjina kai ta ce, "To Inna ina zamu sama jarin? sai dai idan za a sake ɗaga wani abin a siyar ko?" Inna ta ɗanyi jim...Kamar ba zata tanka ba, sai daga bisani ta bai wa Najma amsa da faɗin, "Najma na yanke shawaran mu sai da katifar ɗakin Malam tunda babbace zata yi daraja." Najma da zuciyarta ke sake raunana ta dubi Inna ta ce, "Hakan ya yi Inna, Allah sa tayi darajar da za a samu jarin mai ɗan kauri."
Inna Mairo ta amsa da cewa, "Ameen Najma, idan kin kammala ayyukan zuwa anjima sai ki je gidan Adama dillaliya ki yi mata maganar katifar." Najma ta ce, "To Inna!" Daga haka ta zare hijab ɗin jikinta ta nufi kicin don haɗo musu kwaɗon garin kwakin. Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala yin kwaɗon wanda yaji ƙuli dasu tumatir da albasa da ta yankasu gunin sha'awa a ciki, ta juyosa cikin baban faranti ta nufi ɗakin Inna dashi. Ta samu Inna ta shige ɗaki don yin sallar azuhur, hakan yasa ita ma ta fito ta ɗauki buta ta nufi bayi don kama ruwa da ɗauro alwala.
Bayan sun idar da sallar ne suka haɗu suka ci kwaɗon cikin kwanciyar hankali. Najma ta ɗebo musu ruwan rijiyarsu mai daɗi suka sha suka yi hamdala,sannan ta ɗakko ma Inna magungunanta ta sha.
Suna zaune suna ɗan taɓa hira Najma ta dubi Inna Mairo ta ce, "Inna don Allah ki sanar dani tarihinki dana aurenki da Babana, ina son sanin dalilin ƙiyayyar da Gwaggon kaduna ke miki." Ta dakata da maganar tana duban fuskar Inna Mairo don ganin yadda ta amshi maganarta. Inna da idanunta ke kan Najma tuni ta haɗe fuska, tana mata wani duba na mai yasa kike son sani? Kafin ta buɗe baki ta ce, "Najma sau nawa zan sanar dake babu ruwanki da sai kin san abinda ya faru? Ki rufe wannan maganar bana sonta." Najma da zuciyarta ke matuƙar son sanin cikakken tarihin Innarta da yadda aka yi aure ya wanzu tsakaninta da mahaifinta, sai ta narke murya tana matso hawaye ta ce, "Don girman Allah Inna karki gwaleni a wannan karon, wallahi ina matuƙar son sanin cikakken asalina da tarin yadda aka yi kika auri Babana? Ki taimaka ki sanar dani tarihin rayuwarki ko na ƙaru da wani abin." Inna Mairo ta jinjina kai cike da jin tausayin Najma, don ta san tana son jin tarihin baya ne ko zata gano ita ce mai laifi ko Ƴan uwanta su Yaya Kabeeru da suka wofintar da rayuwarta. Ta dubi Najma tana bata tabbacin zata sanar da ita tarihin rayuwarta baki ɗaya, da yadda aka yi Malam Mahmuda ya yi nasarar aurenta, har ya ɗakkota daga birni ya kawota ƙauyen garin giwa. Ta muskuta tana gyara zamanta sosai, ta fuskanci Najma da tayi zuru tana sauraren jin cikakken tarihin rayuwar Inna Mairo da Mahaifinta Malam Mahmuda...........✍🏻
🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*
*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA *** DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻
#Najma#
#Luvstory#
Ayshat Ɗansabo lemu😘