Free chapter · Read without an account

Page 7

by Ayusher Muhd · MUNƊO (Mai Hakuri)

*MUNƊO*

(MAI HAKURI)


Na Zee Yabour 

 Da

Ayusher Muhd🤸🏻‍♂️


*TEAM ƳAN TAGWAYE NOVEL*✍️




Page 007.........


Tun daga yanayin yanda Ardo yai magana yasa Dadda ta fito daga cikin ɗakin zuciyarta duk ba daɗi. Kai tsaye ta nufi ɓangaren da Munɗo take daga yanda take tafiya kaɗai zakasan cikin fishi take dan fuskar nan babu wargi.


Ai mutanen cikin gidan suna ganin haka daɗi ya kara kamasu, sufa yau take sallah dan babban burinsu suji ance za'a wahalar da Munɗo su a san samunsu ne a konata kowa ya huta yadda kwallan mangwaro ko sa huta da kudan dake damunsu. Hannu tasa ta zare sandar da aka rufeta dashi, tana shiga ta sa kafa ta hankaɗata tayi baya kanta ya bugu da bango, da faɗa take cewa "Tashi ki faɗamin uban wa yace ki fita bayan aiki na sakaki? Sannan da kika turo maciji ya sari ubanki kin ɗauka bazamu gane kece kika shirya hakan ba? Kungurmar munafuka."

 Ganin ba alamun motsi yasa ta wuce inda take ta cakumo wuyanta zata zabga mata mari, sai dai yanda taganta ne yasa ta jijjigata tace "Ke Munɗo meye hakan?"

Tana sakinta taga jikinta ya saki ta zube gabaki ɗayanta. Dadda zatai magana sai ga Danejo wacce tazo dan taga halin da Munɗo ke ciki. Hankali a tashe ta karasa gurin ganinta kwance a kasa, Dadda ta mike tana kade hannu kafin ta ɗan kauda kai tace "Toh da alama tana nufun itama dafin karyar ciwon yana jikinta dan kar a zargi itace ta ke neman kashe ubanta."

Danejo ta kalli Dadda idanunta sun canza launi tace "Dadda dan Allah yiwa Ardo magana yazo ya duba yarinyar nan ni kamar ma bata numfashi." Tai maganar duk a rikice. Ga mamakinta gani tai Dadda ta juya kai tace "Alhakin mutane ne ya fara kamata, dama kaci kuruwar mahaifinka ka kwana lafiya ne? Ai dama kasan abinda ka jawowa kanka, ni kinga ina da abin yi." Hankalinta a kwance ta fita daga ɗakin. Danejo ta ɗagota da kyar ta iya sakata a bayanta dan girma ya fara kamata ta fito da ita mutanen ciki gidan na kallon su, dukansu daɗi ne ya kamasu dan su kiris suke jira suji ance ta mutu su huta.

Ɓangaren Ardo tai da ita yana zaune yana duba maganin da aka kawo wanda za'a haɗawa Macciɗo. Ganin Danejo yasa ya ɗan maida hankali kanta, a hankali ta sauke Munɗo ta sa mayafi ta rufe gefen fuskarta kaɗan dan fulani akwai jin kunya, tace "Ardo ka taimaka ka duba yarinyar nan, kamar fa bata numfashi." 

Kusa da Munɗo ya dawo ya dubata kafin ya ɗago ya kalli Danejo yace "Tana numfashi sai dai baya fita sosai. Ina ganin dafin daya ciji Maccido ya ɗan shiga jikinta ne kaɗan." Nan ya ware magani daga cikin na Maccido ya mika mata yace "Gashi ki tafasa yanzu ki bata, ni zan wuce gun shi dan jikin nashi ya ban tsoro."

Amsa tai ta sadda kai ƙasa tanaso ta tambaya ya jikin Maccidon sai dai bazata iya ba, kallanta yai bayan ya kwashi maganin yace "Maccido na shan wahala dan baya gane wanene a kansa, sai dai muna fatan samun sauki in yasha magungunan nan." Yana kaiwa nan ya fita, hannu tasa ta share hawayen da suka zubo mata, shikenan mutanen da take dasu a duniya guda biyu neman halaka suke su barta.

A d'akin Ardo ta bar Munɗo ta nufi waje ta tafasa maganin ta dawo ta ɗagata ta bata wanda rabin maganin zubewa yai a ƙasa. Hannunta kawai ta kamo ta matse a cikin tafin hannunta tanaji duk rayuwar ta isheta. Dama itace a kwance su suna nan lafiya da ta huta da ganin wannan tashin hankalin.


*******


 KANON DABO.......


 Har ya kwanta zai fara bacci yaji ana kwankwasa mai kofa, a hankali ya mike ya jawo rigar dake gefen gadansa ya saka, gefen gado yakai hannu ya d'auko lime ya d'an matsa a bakinsa sannan ya taso ya nufi ƙofar tare da cewa "Wanene?"

Ummy daga waje tace "Araab nice."

Jin muryar Ummy yasa ya ƙarasa bakin ƙofar cikin sauri ya buɗe ƙofar tare da kallanta yace "Ummy maimakon ki sa a kirani ko kimin waya nazo? Kidena wahalar da, kanki Ummy."

Cikin ɗakin ta shiga wanda girmansa da kyansa kaɗai abin kallo ne, anyi kwalliyar ɗakin ne da ash colour light da dark.

Gefe ta nufa inda akasa kujeru guda biyu da ɗan ƙaramin table a tsakiya. Zama tai shi kuma ya matsa ya zauna a ƙasa tare da lanƙwashe ƙafafunsa. Charbin hannunta ta ɗan murza tana kallan ɗakin tace

"Araab munyi waya da Meenal na kuma ji abinda ya faru, sai dai menene laifinta akan abinda iyayenta sukai? Sannan dan sun faɗi hakan suma menene laifinsu? sai me?"

Kansa dake kasa ya ɗago ya kalli Ummy da idanunsa, fuskarsa a ɗaure yanda a koda yaushe take yace "Sai me fa kika ce Ummy? Taya zasu faɗi haka a kanki?" Sai kuma yai shiru tare da shafar bayan sumar kansa ya ɗan dunkule hannunsa yana neman sake matsa lime din hannunsa.

Ajiyar zuciya tai cikin sanyin murya tace "Araab ni ɗin wacece da baza'a faɗi haka a kaina ba? Sannan naji sunyi laifi ita menene laifinta? Kafi kowa sanin yanda ta ke sanka duk abinda ake cewa ka taɓa ji ta sa baki?"

"Bata sa ba sai dai ni bazan iya haɗa zuri'a da mutanen da zasu faɗi haka akanki ba."

Ya zatai da kafiyar Araab Hassan? Zatai magana taji yace "Ummy dan Allah kije ki kwanta ki huta banasan wannan ƙaramin abin ya hanaki bacci, uwata ce basaso nima 'yarsu ce banaso shikenan magana ta kare."

A hankali take kallansa ta sani a gunsa itace rayuwa a kanta kuma zai iya rabuwa da kowa, sai dai ita a koda yaushe burinta taga yayi aure ya samu wacce zata kula dashi wannan shi kaɗai ne burin daya rage mata a duniya, ta sani in har yana raya kanensa bazasu tozarta ba. Hannunta ya kamo ya ɗauraa saman kansa yace "Ummy dan Allah ki ajiye maganar mutanen can please!"

Kai ta ɗaga a hankali tace "Allah yai ma albarka ya baka mace ta gari."

Ameen yace sannan ta miƙe ta fito daga ɗakin, maimakon ya koma gado ya kwanta sai kuma ya tashi ya buɗe window yana kallan harabar gidan, hannunsa yasa a aljihu....


*******


 Cikin baccinsa yaji alamun hannun mutum a cikin aljihunsa, a zabure ya damke hannun tare da cewa "Salame yi maza ki haskamin nan wallahi ɓarawo ne ya ke neman yi min sata." Hankaɗashi baya tai cikin takaici tace. 

"Dalla ni sakar min hannu nice nan ba wani ɓarawo ba."

Sake ta yai tare da haska fitilarsa dake gefen gado, ta zake zabgamai harara tace "Fito da abinda ke aljihunka mu gani."

Ya sake haskata da fitila yace "Wai nikam Salame meke damunki ne? Haka kawai ina kwance kice na fito da abinda ke aljihu na? Ajiya kika bani ko me?"

Hannu ta sake kaiwa inda aljihunsa yake ya mike cikin sauri ya matsa daga kan gadan yace "Salame baki da hankali ne?" Ɗankwalinta ta cire ta ɗaurashi a kugunta tace "Kasan Allah fito da duk wani abu dake ciki, tab! harni zaka munafurta kanaji ina neman kuɗi shine zaka raina min hankali kaƙi gaya min?" Ajiyar zuciya yai yace, 

"Ina kika ganni da kudi? Sannan in kuɗi ne ke kanki kinsan bazan cinye ba tare da na baki ba?" Ta sa hannu ta cakumoshi ta rike kugu tare da mika mai hannu tace "Fito dashi? Ai Bilal indai ganin kudi ne kasan duk duniya bayashi tunda yace yaga kudi a aljihunka wallahi ya gani."

Kai ya kawar yanaji zuciyarsa na wani irin soya wannan wace irin rayuwa yakeyi? Tabbas alhakin Yayarsa Danejo shine yake binsa.


RUGAR JIJI


A hankali ta buɗe idanunta ta sauke shi a kan saman ɗakin nan da nan duk abinda ya faru ya sake dawo mata, kuka kawai ta fashe dashi sannan ta fara ƙoƙarin mikewa. Ji tai gaba ɗaya jikinfa babu karfi, kallan magungunan dake kasa tai sannan ta sauke idanunta akan Danejo dake kwance akan tabarmar ɗakin. 

Dakyar ta samu ta mike tana dafa bango ta fito, rugar tayi tsit sai karar tsintsaye da beraye dake ɗan tashi sama-sama tana tafe tana tangaɗi ta nufi ɓangaren mahaifinta. Tayi sa'a duk babu kowa a wajen.

 Hannu ta kai a hankali zata buɗe ƙofar ɗakin ta bayanta taji an fizgota da karfin gaske wanda ya sata zubewa a kasa hanunta ya bugi da kujerar tsugunun dake gun.

 Muryar Dadda taji cikin fishi tace "Uban me kikazo yi nan?"

Bakinta ne ya hau rawa ta kasa cewa komai.

"Munafuka wato kinga bai mutu ba ke kuma kin kwanta ciwo shine zaki dawo ki lamushe shi ki gudu ko?"

Altine jin faɗa a kasa ta ɓangarenta yasa ta fito, idanunta na sauka akan Munɗo ta ja baya tana girgiza kai tana cewa "Dadda ki taimaka ki hana yarinyar nan aikata abinda take shirin yi banasan zama bazawara dan Allah...."

Munɗo ji tai kalamanta sun daki zuciyarta, ta kalleta tace "Taya zanso wani abu ya samu mutumin da ya ragemin shi kaɗai a rayuwa?"

Da karfi Dadda ta riko wuyan rigarta ta fara janta a ƙasa, batada karfi dan har yanzu ba lafiya gareta ba hakan yasa ko shure-shure kasawa tai balle ta gwada kwatar kanta.

Bata tsaya ba sai a ɓangaren da take zama, hankaɗata ciki tai ta faɗi kasa tana hawaye. Dadda ta kalli Danejo dake bacci takaici ya ƙara kamata "Danejo!" Ta kira sunanta cikin kakkausar murya.

 Nan Danejo ta mike ta kalleta cike da mamaki kafin tai magana tacigaba da cewa "Fito daga ɗakin nan umarni Ardo ya bada a kulle yarinyar nan kuma kar a sake bari ta fita."

Zatai magana ta katseta da cewa "In bayan gida takeji ta sa a kirani zanzo na kaita tai na dawo da ita." Mamaki ne ya hana Danejo magana, "meya faru tana bacci?" Haka ta fito suka kulle Munɗo a ɗaki, banda kuka da kiran sunan babanta ba abinda take yi.


 A can ɓangaren Maccido kuwa washe gari Allah ya nufeshi da buɗe idanunsa, sai dai iya kacinsa buɗe ido dan ko magana ya kasa yi. Ya rasa yanda zai yi yace su kira mai Munɗo dan tunda ya kwanta halin da take ciki kawai yake tunani. Su sun ɗauka magana ce gaba d'aya ba yayi shi kuma kawai ji yai zuciyarsa na zafi bayasan cewa komai, 'ƴarsa kawai yake san gani kuma yasan ba barinta zasuyi ba, dan yana kwance yana jin sanda suke dariyar mugunta suna tsinewa Munɗo da shirin tozartata in har wani abu ya sameshi.

 Yau yana kwance idanunsa a rufe dan takaicin duk ya isheshi ya gwada mikewa yakai sau nawa amma ya kasa. Ji yai kanwar Altine ta shigo da alama ganin yana bacci yasa ta cewa "Altine yanzu nazo wucewa naga Dadda ta fito da mayyarcan zata zaga bayan gida, kinga yanda ta koma?" Ta ɗan fara dariya Altine ma dariya tasa suka toshe baki alamar kar yaji kafin tace "Ni aradun Allah har Allah-Allah nake a ce min ta mutu hankalina ya kwanta, kinsan saboda haka na daure nake wannan auren? Hmm ai daga sanda ta mutu ni kuma kasuwa da mulki ya bud'emin."

Suka sake sa dariya ƙanwar tace "In ta mutu ai ke kinfi kowa riba."

Hawaye ne suka gangaro gefen idan Maccido lalai dole ya samu ya kwashe dukiyarsu da ƴarsa subar rugar nan dole ne ya sanar da Danejo halin da ake ciki dan ta taimaka mai ya kwashe komai ya kuma ɗauke ƴarsa ko mutuwa zaiyi ko ita kad'ai ce sai ya nemawa gata. Jauro ne ya fad'omai a rai nan danan ya shiga dogon tunani.....


#Munɗo

#Araab Hassan

#Bilal BB


GA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500

GUDA HUDU 1300

GUDA UKU 1000

GUDA BIYU 700

GUDA ƊAYA 400

_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)

_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour) 

_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)

_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)

_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)


ACCOUNT NUMBER 

2083371244

Zenith Bank

Aisha m salis


KATIN WAYA

***



Ayusher Ce🤸🏻‍♂️

Da 

Zee Yabour


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.