Free chapter · Read without an account
Page 8
*MUNƊO*
(MAI HAKURI)
Na Zee Yabour
Da
Ayusher Muhd🤸🏻♂️
*Dandano...*✍️
008
Kano......
Araab ya shirya tsaf dan fita aiki sanye yake da suit baka sai shirts ɗin ciki light blue ya masa kyau sosai, fuskar nan tashi tana nan yanda take babu fara'a balle murmushi.
Sallama yai sai data bashi izini ya shiga, kamshin ɗakin kaɗai ya isa yasaka lumshe ido, tana zaune a ƙasa akan lallausan carpet ɗinta.
Tana zaune akan sallaya tana jan carbi. Ya tsugunna ya gaisheta ta amsa fuskarta haryanzu bata gama sakewa ba.
Mik'ewa yai ya d'auki Qur'anin dake gabanta ya maidashi inda take ajiyewa, sannan ya fito.
Ikram da Ilham sun gama shirya mai breakfast akan dinning dan shi dama ba wani abincin kirki yake ci ba in zai tafi gun aiki.
Madara yasha mai dumi yaci chicken susage sannan ya mike ya kalli Ilham yace "
"In kin gyara dinning ɗin ki kawowa Ummy tea ɗaki."
Da sauri tace "To Ya Araab."
D'akin Ummy ya koma yanzu kuma tana tsaye tana duba wasu kaya dake gefen gadanta, kusa da ita yaje ya d'an zauna a saman hannun kujerar d'akin yace "Ummy please ki saki ranki akan maganar nan, maybe ba matata bace shiyasa."
Jakar kwallin dake gefenta ta ɗakko ta ajiye a gabansa tace "Sakon Meenal ne ta fito school ka ajiye mata kafin ka wuce gun aiki."
Da sauri ya ɗago ya kalleta yace "Ummy??"
Fuskarta babu alamun wasa tace "Inkaje ka tsaya akwai sakona nima a gunta ka amsomin."
Yawun bakinsa ya haɗiiya tare da shafa sajensa da alama Ummy bata bashi damar yin magana ba. Hannu yasa ya ɗauka yace. "Naji Ummy amma dan Allah ki saki ranki. Kinjj?"
Kallansa tai ita kad'ai tasan meke ranta tace "Allah ya taimaka, sai ka dawo."
Mik'ewa yai a hankali ya fito daga d'akin dan babu alamar ma tana san jin magana daga gareshi, itakam har yabar d'akin idanunta na kanshi tausayinsa takeji ya sadaukar da komai dan yaga cigabansu shiyasa itama dole zata dage dan ganin ta samar mai matar da zata kula dashi.
Ikram ce ta taho da ɗan sauri ta mikamai wata ƙaramar roba wanda aka yanka lemon tsami (lime) a ciki, amsa yai yana neman wucewa tace "Yaya sai ka dawo." Kai ya d'aga sannan yace "Ku tabbatar Ummy taci abinci in kuma bataci ba amin waya a sanar min." Da to suka amsa shikuma ya fita.
Ajiyar zuciya yai ya furzar da iska, zuciyarsa na sake tafasa saboda mutanen can sun jawomai Ummy tayi fishi dashi, robar ya buɗe ya ɗakko lime ɗin guda ɗaya ya matsa a bakinsa sannan ya kunna motar.
Cikin ɗan zafin rai ya fita da motarsa, cikin sauri da ɗan karfi ya taka birki wanda kansa sai da ya bugi sityarin motar, ledar pure water ya ɗaga a hankali ya kalli ledar pure water ɗin data sauka akan glass ɗin motarsa sannan ya kalli motar data taho da karfi an kure disco, ta glass ya kalleshi ya wani ɗaga mai hannu wai alamar sorry, ajiyar zuciya yai yana neman kwantar da hankalinsa sai dai jiyai bazai iya ba, a fusace ya fizgi motarsa yabi motar nan da gudu, ya gaji da iskanci mutanen nan sun fara kaishi bango.
Bilal da abokinsa Khalil daga glass ɗin motar suka hangoshi. Khalil wanda ya dawo da mota da safen nan suka sake fita yawo ya kalleshi cikin dariyar mugunta yace "Kai wallahi baka da kirki ka san daidai saitinsa ka buga ruwan nan?" Yasa dariya sannan ya cigaba "Allah ba ruwana yau ka taɓo wanda yafi karfinka." Ya karasa maganar yana kallan yanda Araab Hassan ya kusa kamosu.
Bilal yai tsaki ta glass ɗin motar yace "Yau Allah yayi ya kulani, hahaha dama neman hanyar da zan ɗan bugamai mota nake bansamu ba sai yau, wallahi Khalil na tsani naga motar guy ɗin can nine ya kamata na mallaki gida da mota amma kalleni." Ya sake jan tsaki ya bigi saman sityarin yacigaba "Wai ni kasan motoci nawa yake dasu? Ga tsinanen girman kai ko fa ganinshi ba'ayi....."
Kafin ya sake magana yaji an buga motarsa ta baya wanda yasashi taka birki da karfin gaske. Jikinsu ne ya fara rawa suka kalli juna idanunsu yayi jaa, Khalil ya kalleshi bayan ya juya yace "Wallahi mutum nan ne, Bilal mubar nan da alama yaran nan bashida kirki zai iya mana abinda......" Jin haka yasashi fusata ya buɗe kofar mota cikin kunar rai, ya nufi motar da Araab Hassan ɗin yake. Samari da almajiran dake kan titin suka ɗan tsaya kallo.
Nan Bilal ya sake fusata yana ganin an zubar mai da kima dole yai rashin mutunci.
Glass ɗin motar ya buga yana hucci kamar wani tsohon kumurci, Araab sai da yai minti biyu sannan ya zuge glass ɗin, kallan Bilal yai wanda yake magana irinta wanda suka riku a shaye-shaye yace "Bakada hankali ne? Ko bakaga abinda kai ma bayan motar mu ba."
Kansa ya ɗan karkatar kaɗan alamun ya kalla sannan ya kalli Bilal hannu yasa ya buɗe sif ɗin motar ya ɗakko kudi bandir ɗin ƴan ɗari biyu ya ɗan sauke ajiyar zuciya ya samai a saman kirjinsa ba tare da ya kulashi ba ya maida glass ɗin motar ya zuge yai reverse yabar gun.
Bilal mutuwar tsaye yai riƙe da kuɗi zuciyarsa na san kuɗi sai dai mamakin kamaninsa da zatinsa da kuma yanda ya ki kulashi suyi rigima duk sun sa ya kasa tunanin komai.
Har Araab Hassan yabar gun yana nan a tsaye, Khalil ne ya ƙaraso ganin kuɗi yasa shi ya amshi kuɗin yace "Kai wai baka yai? Ai wallahi rabawa zamuyi baka isa ba."
Bilal jiyai gaba ɗaya wani takaici da ɓacin ran da baisan dalili ba yazo wuya ya tokare shi, naushi ya kaiwa Khalil wanda yai sauri ya kauce yace "BG menene hakan kuma? Me nayi maka?"
Fizgar kuɗin yai yace "Na fasa zuwa gida zan koma ina da abin yi."
Bai tsaya takan Khalil ba ya shiga motarsa ya juya zuwa gida, haka kawai ya rasa me ya kamata ya ɓata mai rai dan komai ma haushi yake bashi. Yana gama parking ɗin motar a waje yasa ƙafa ya daki tayar motar da karfi. Jin kafarsa ta ɗauki zafi yasashi ɗan yin shishitu yana yarfe hannu.
*******
A ɓangaren Araab kuwa BUK ya isa new site, yanayi yana kallan agoggon hannunsa, text ya mata ya sanar da ita inda yake sannan ya kwantar da kansa a saman kujera ya ɗan lumshe ido yana tunani ko Ummy yanzu ta huce? Me zaiyi ya shawo kanta?
Alamun ana neman buɗe kofa ne yasashi buɗe ido, kallanta yai ta glass tasha uban kwalliya kamar ba makaranta tazo ba.
Glass ɗin inda take tsaye ɗaya bangaren driver ya zuge, Meenal ta d'au gayu sanye take da riga ƴar kanti baƙa bata kamata sosai ba, ta ɗan kusa gwiwowinta sai wando baki data saka irin pencil ɗin nan, tai rolling da mayafi baki sai ta ɗauko abaya mai buɗewa gabaki ɗaya ta saka ta bar ta a buɗen.
Kanta ta zuro cikin motar ta sa a saman hannayenta tace "Yayana bazaka barni na shigo na ganka sosai ba?"
Hannu yakai bayan motar ya ɗauko jakar nan ya mika mata yace "Ina sakon Ummyn?"
Ajiyar zuciya tai tace "Ka buɗe min please na shiga sai na baka." Ta ƙarasa maganar tana kai hannu gun buɗe motar.
"Gun aiki zani sannan I don't think akwai abinda zaki yi a cikin motar nan da har sai kin shigo." Kwantar da kanta tai tace "Yayana please kar mutane su fara wucewa sosai."
Kai ya kauda hakan yasata ta buɗe ta shiga ga mamakinsa gani yai tana neman sa seat belt, ido kawai ya zuba mata harta gama tana ɗagowa ta sauke idanunta akanshi ta ɗan hadiyi yawun bakinta tace "Allah bani da lectures kuma Ummy ta sanar da secretary ɗin ka akan bazakazo da wuri ba tace muyi magana ta fahimta tunda muna san ju......"
Yanda ya kalleta ne yasata yin shiru tana tsuke baki...
*******
Danejo ce ta zubawa ɓangaren Munɗo ido gashi sun sa mutene su dinga kula akan kar a kuskura a barta ta fito, jiki a sanyaye ta mika mata abincinta sannan ta faɗa mata halin da Maccido ke ciki, tana hawaye tace "Ba komai Danejo kila rayuwa tace tazo karshe indai har Baffana ya samu sauki koma menene zan yi.
Haka ta taso zuciyarta duk babu daɗi ta nufi ɓangaren Maccido.
Ba kowa sai shi dake kwance kamar mai bacci, kwaryar data damo mai fura ta ajiye a kusa dashi sannan ta zauna tana kallansa cike da tausayi.
A hankali ya buɗe idanunsa ya kalli mahaifiyar tasa cikin dashashiyar murya yai magana yace "Danejo!"
A firgice ta kalleshi hawayen da suka zubo tai saurin gogewa ta mike a rikice tace "Maccido? Bari na kirawo Ardo."
A hankali ya girgiza kai cikin sanyin magana wanda kana gani kasan dakyar yakeyi yace "Danejo ki taimakeni."
Kallan mamaki tamai nan danan taji jikinta yayi sanyi, ya lumshe ido sannan ya buɗe yace "Dan Allah karki faɗawa kowa ina magana, ki taimaka kisa Salau ya nemo min Kawu Jauro."
Cikin sauri tace "Jauro kuma?"
Ɗan ajiyar zuciya yai sau kusan uku a tare kafin yace "So nake na bashi amanar Munɗo da dukiyarta bazan bari ajalina yazo min ba tare da na samo mata makafa ba, in har mutuwa tazo min ke kanki kinsan kudinta zasu sa a gaba su cinye sannan su kasheta."
Kallansa take duk kanta ya kulle tama rasa abin cewa, a hankali ya sake cewa "Na sani sarai baki yarda da Jauro ba tunda ya kwashe gadonku ya gudu amma shi kaɗai nake dashi da zai nisantata daga cikin rugar nan, ni yanzu kafafuna banaji zasu iya taka ƙasa ma balle na iya fita na kaita, duk abinda zai faru Kawu nasan ko darajar kudin ta zai kula da ita."
Tasan Jauro ba ruwansa matarsa ce ke zugashi sai dai tabbas tasan zaman Munɗo anan daidai yake da mutuwarta.
Yawun bakinta ta had'iya tace "To shi Salau ina yasan inda Jauro yake?"
"Ni da shi Salau ɗin mun san inda gidansa yake, kwanaki da muka je birni har kofar gidan muka je sai mukai rashin sa'a matar ta fita ta kulle gidan ashe shi kuma kawun ya manta da nashi makulin."
Shiru tai alamun tunani tace "Yanzu kana nufin duka dukiyar nan zaka kwace ka bashi? Na tabbatar daga sanda ka bashi kaima mutanen rigar nan bazasu barka ba." Hawaye ne ya gangaro gefen fuskarshi ya sake maida numfashi yace "Danejo ya zanyi in na mutu yarinyar nan......"
Da sauri tace "Maccido me kake cewa haka ne?"
A hankali ya ɗan girgiza kai kaɗan sannan ya lumshe ido yace "Ni in nine sumin duk abinda sukaga dama, amma ita fa? A dalilinta bamu taɓa neman kuɗi ba, dukansu da arzikinta suke ci suke sha amma ita kenan cikin bala'i na rayuwa? An min sharadi na ɗau alkawari akan bazan faɗa ba a dalilin haka suka yadda da ita sai dai menene amfanin yardar tasu? Yanda take rayuwa ko me?"
Danejo kam ta fahimceshi sosai sai dai ita Jauro ne hankalinta bai kwanta da matarshi ba amma in ta duba koma menene gwara su da nan.
Muryarshi ce ta katseta yace "Danejo dan Allah ki taimakeni."
Kai ta jiniina tace "Shikenan zan tura Salau yanzu zai wuce Kano in yaso sai su taho da motar kwasar dabobbi daga can?"
Kai ya ɗaga alamar eh sannan yace "Akwai ɗankunaye da sarka da mamanta ta bada suma a bashi."
Kai Danejo ta girgiza da sauri tace "Wannan suna gurina zan ajiyesu har sai auranta."
Bai musa ba yace "To kicewa Salau in sunzo da Jauro su zauna a bayan gari da motar har sai wajen biyu na dare sannan zaki musu magana. Ita kuma Mund'o kice ta haɗa kayanta karki ce mata komai banda haka na tabbatar bazata je ko ina ba in ba dani ba."
Ta jinjina kai cikin gamsuwa sannan ta mike ta fito cikin sand'a ta nufi bangarenta tasa aka kira Salau ta kunce gefen zaninta ta bashi kuɗi ta sanar dashi sakon Maccido.
ƳAN TAGWAYE BIYAR 2023
ƘASAITATTUN LABARAI MASU DAƊI DA SANYA NISHAƊI, SABON SALO MAI ƊAUKE DA DARRUSA NA RAYUWA UWA UBA ƘASAITATTUN SOYAYYA MAI HUDA JIJIYA.
IYALINA (A'ILATY)🔥
RAFEEQ🔥
MUNƊO🔥
ZAMANIN MU AYAU🔥
FATHIYYA.🔥
DOMIN SIYAN GUDA BIYAR N1500.
DOMIN SIYAR ƊAYA N400.
Account Details
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
Ga MUTANEN MU NA NIGER 🇳🇪
Tura ta Nita da sunan
Asma'u Buhari Aliyu
***
SAI KI/KA ISAR DA SHAIDAR BIYA TA ƊAYA DAGA CIKIN NUMBOBIN NAN.
***
***
***
***
#Munɗo
#Araab Hassan
#Bilal BB
#One love 💕
Ayusher Ce🤸🏻♂️
Da Zee Yabour