Free chapter · Read without an account
Chapter 04
ASHRAF: Beauty meets Ugly
04
Duk abinda aka ce ƙaddaranka ne to fa ba zai taɓa wuce ka ba.
Da Asuba da Qayyisah ta tashi ta buɗe datar wayarta sai ga shigowar email.
Dan kada ma hankalinta ya tashi tun bata yi sallah ba ta ajiye wayar ta shiga banɗaki, amma kam zuciyarta cike da taraddadin ina aka turata.
Ta idar da sallah tayi azkar tareda addu'ar Allah yasa koma ina ne dai Allah yasa Baba ya amince da wajen.
Ta ja dogon numfashi sannan ta ɗauki wayarta da Bismillah. Tana buɗe gmail ɗinta ta fara bin layi da layi tana karanta call-up letter ɗin da aka turo.
Ta shiga ƙyafƴyafta ido dan bata yarda da abinda take gani ba.
Ta kifa wayar akan gado tana tunanin anya ba idonta ne ke ganin abinda zuciyarta ke son gani ba.
Chan ta ɗau wayar ta kira numbar Zaidu. Gara shima ya zo ya gani dan ta tabbatar da ko dai gaskiya Abujan aka turata ko kuma idonta ke mata gizau.
"Chaɓ! Kice bakin Anty Fa'iza ya kama ki" Zaidu ya faɗa lokacin da ya karanta call-up letter ɗin.
"Zaidu da gaske Abuja ne ?"
"Kin ɗauka wasa ne. Ai ki haɗa kayanki kawai za ki Asorock"
Qayyisah ta maki kafaɗarsa " it's not funny Zaidu. Ka san Baba ba zai amince ba"
"To ina ruwan NYSC da abinda Baba yake so. Inba Baba bama ai ba lallai ma cikin Abujan za a posting ɗinki ba"
"Idan ma cikin Abujan ne ai ba abinda zai haɗa ki da gidan Abba"
Qayyisah ta yi Hmmm.
Ita ba wai dan zuwa gidansu Abba yasa take son zuwa Abuja ba. Saboda Nura ne.
Ta sani babu abinda ganin Nura zai yi mata. Amma deep down tana son sanin ko Nura ya taɓa tunawa da ita. Ko yayi dana sanin abinda yai.
Daɗin daɗawa tana son yi masa tambayoyin da bata samu daman yinsu ba a wancan lokacin.
Tana son sanin ko ya taɓa sonta ko kuma dama tun asali yaudararta yai.
A lokacin uzurin daya faɗa yasa ta manta da maganar yaudara.
A lokacin gani take tunda akan aƙidar Baba ne gara ta haƙura da shi dan kar hankalin Baba ya tashi.
Lokacin da suke soyayya ba abinda bai sani akanta ko akan Baba ba.
Hatta yadda mahaifiyarta ta rasu sai da ta gaya masa.
Ta gaya masa abinda bayan iyayenta babu wanda ya sani babu wanda ta taɓa faɗawa wannan labarin.
Ta gaya masa cewa ita ce sanadin ɓatan Humairah ko kuma tace kisan Humairah.
Duk da dai Baba yace gawan data gani bana Humairah bane. Amma har yanzu tana ji a ranta cewa baƙin gawan data gani na Humairah ne.
Shima Nuran ce mata yai ba gawar Humairah bane. Wai ta ɗauka cewa Humairah ko ɓata tayi ko mutuwa ta yi ba laifinta bane, haka Allah ya tsara.
Mutane dayawa sun rasa danginsu a rikicin Jos.
Dama ai koma bayan kowanni faɗa ko yaƙi tashin hankali ne da kuma asaran rayuka da dukiyoyi.
Nura ya san komai nata. Ya san komai daya kamata ya sani kafin ya turo iyayensa.
Wai ma idan ba munafurci ba mutanensa basu yi bincike bane kafin su zo.
Wai sai da aure ya zo gab. Sai da aka printing invitation cards, aka yi kusan kaso 80% na aure zasu fito su soki aƙidar mahaifinta.
Abin haushinma Nura bai iya gaya mata baki da baki ba sai turo mata mummunan text yayi.
*I'm sorry My Zee* tsabar ƙarfin hali sai da ya haɗa da MY ZEE dan ya ƙunsa mata baƙin cikin da kyau.
*wallahi Abbanmu yace ba za mu yi aure ba. Wai an faɗa masa Baba ɗan Ɗariƙa ne...*
"Ai ki fito kawai ki faɗawa Baba Abuja aka tura ki ayita ta ƙare kafinma ya fita shago"
Zaidu ya katseta daga tunanin da take.
"Zaidu taya zan faɗa masa"
"Ni ina na sani, ke ce 'yar gaban goshinsa kin san ya kika saba yi masa magana ai"
Ta girgiza kai.
Bata faɗawa Baba ba har aka karya suka wuce shago. Jira take sai suna cikin aiki tayi kaman a lokacin aka turo email ɗin.
Hakan kuwa suka yi.
Wayan na hannun Zaidu ya shigo kawo mata wayan yace Zee an turo miki call-up letter fa, an cillaki chan ƙasar Igbo.
Baba dake zaune a kujera yace "ƙasar Inyamurai kuma"
"Baba Enugu fa aka turata. Zata je tai ta cin doya, kafin ta gama service zata zama wata ɗimemiya"
"Zaidu ban son wasa, ka bani wayana"
Dake abin nasu coded ne shima Zaidun sai ya ɗaga wayar sama yana faɗin ir ta karɓa idan zata iya.
Idan ka kalli tsayin Zaidu ka kalli Zainab ba zaka taɓa yarda cewa su ɗin 'yanbiyu bane.
"Zaidu ka bata wayarta" Baba ya daka matsa tsawa.
Itama Zainab ɗin ta wani daddage a dole sai ta karɓi wayan har abinma yana son zama faɗa.
Zaidu ya bata wayar yana dariya. Ita kuwa ta watsa masa harara.
"Zainab duba mana ko ƙarya yake yi"
Qayyisah ta buɗe email ɗin tayi kamar a lokacin take ganin call-up letter ɗin.
Ta na karantawa ta saka Innalillahi har da kama baki.
Baba yace "Enugun ne ?"
Zaidu ya karɓi wayan yace " Baba bafa Enugu bane Abuja ne"
"Abuja?"
"Iyi, amma ana iya chanjawa idan aka fito daga Camp"
Baba yai shiru.
Har aka tashi a shago bai ce komai ba.
Da dare Baba ya kirata yace ta je tayi lissafin abubuwan da zata siya ta gaya masa total ɗin kuɗin.
Qayyisah tace zata rubuta.
Sai washegari ne ma Anty Fa'iza take jin wai Abuja aka tura Qayyisah. Ta fara tsiyar wai Qayyisah ta bata kuɗin addu'a dan addu'arta ne ya karɓu.
Qayyisah ta shareta ta cigaba da shirinta.
Kamar miracle sai gashi har ranan tafiyarta Baba bai yi ƙorafin tafiyarta Abuja ba.
Dama kullum addu'arta kenan Allah yasa Baba ya amince ta yi service ɗinta a Abujan ba tareda yace ta chanja ba.
***
Ashraf tun ranan daya je gida yai wa Mom masifa bai sake komawa ba.
Zaman hotel ya koma yana cigaba da tunanin yadda zai ɓullowa Dad.
Idan yace ta rikici zai biyowa Dad ba zai taɓa samun abinda yake so ba.
Daga ƙarshe ma sai dai ya rasa komai.
Hajiya tace ya je ya sameta amma bai je ba.
Yau da ya gaji da komai ya shirya ya wuce gidan Hajiya Halima ƙanwar Dad.
Yana shiga compound ɗinsu ya haɗu da Abba shima zai fita, suka gaisa. Abban ya fara masa ƙorafin baya zuwa ziyara
"Yaushe rabon da na saka ka a ido Ashraf. A dinga zumunci kaji ko"
Ashraf ya gyaɗa kai, suka yi musabaha da Abba ya wuce ciki.
A zuciyarsa yana faɗin Abba kenan. Wani zumunci ma zai yi duk yaran Abba ba tsarinsa bane. Shifa idan ya zo gidan nan ya zo dan Aunt ɗinsa ne ita ɗinma yana zuwa ne dan su haɗu su zauna su dinga magana akan Dad.
Yana jin daɗin yadda Hajiya ke sukan duk abinda Dad yake mishi. Har zagin Dad tana yi a gabansa.
Har ta dinga cewa hatsarin da Dad yai ne ya taɓa masa ƙwaƙwalwa.
Sai daya shiga falo ya zauna sannan ya kira numbar Hajiya yace mata yana falon ƙasa.
"Wai wai Son kaine a gida..." kafin ta ƙarisa ya katse kiran.
Ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna wayarsa.
"Ya Ashraf sannu da zuwa"
Maryama ce tsaye a kansa tana kallonsa fiskarta ɗauke da murmushi.
Sai da ta sake gaishe shi kafin ya ɗago ya kalleta.
Woow! Wannan ba yarinyar nan bace. Step daughtern Hajiya.
Yaushe ta girma haka.
"Ya Ashraf mi za a kawo maka"
Tana maganan yana assessing ɗinta.
Tana da abubuwan daya ke so sai dai kuma ita ɗin irin matan da baya son harka da su ne.
Sai an ɗan sha wahala ake samunsu amma da an samu kuma sai su maƙale wa mutum da zimmar sai ya auresu.
Shiyasa yake son harka da wayayyu. Dama kin san abinda ya kawo shi wajenki ba wani ɓoye-ɓoye.
"Just water"
"Ruwa kuma Ashraf." Hajiya dake saukowa ta faɗa.
"Je ki kawo masa abinda zai ci"
Maryama ta bar wajen tana murmushi.
Ta jima tana crushing ɗin Ashraf.
Hajiya ta zauna tana faɗin "sai yau kaga daman zuwa. Tun yaushe na ce kazo. Jinka dan ka bar gida zai sa Yaya ya chanja ra'ayinsa ne. Ka san halinsa sarai."
"Hajiya Dad ya ruining komai. It was just a minor issue fa amma yabi ya ɗaga hankalinsa. Jinsa Umar ko Tahir zasu riƙe masa Company kamar yadda zan yi ne.
"Tahir ƙwace kamfanin Dad yake son yi. Shi kuma Umar ba wani cigaba da zai kawo, he's too outdated"
Hajiya tace " ka cire maganar ɗan Direban nan ba wanda zai bashi kamfani. Shi kuma mijin Zulfa ba zamu bashi damar daya ke so ba"
"Kaima Ashraf ka san halin Dad ɗinka sarai. Yana so a dinga bin komai a natse"
"Hajiya nifa ba faɗa zaki min ba. Ki yiwa Dad magana ko kuma in bar masa ƙasar in koma inda ya ɗaukoni"
"Ashraf waƙa zaka koma! Allah ya sawwaƙe"
"Kaga ka je ka.."
"Wai a cinyarsa zaki ɗaura masa ne!"
Hajiya ta dakawa Maryama tsawa
"Ajiye a nan ki tafi. Haba!"
Har zata tafi Hajiyar ta sake kiran sunanta "Maryama zo nan"
A tsaye zaki amsa min ne.
Maryama tayi saurin zaunawa tana faɗin "gani"
"Ki je ki warming pepper soup ɗin nan ki kawo min. Ki haɗo min da kunun Aya guda ɗaya"
"Hajiya kunun ayan fa ya ƙare jiya"
"Uban wa ya shanye"
"Hajiya Ya Khalifah ne ya ɗau sauran"
"Dan ubanki jira kike nayi magana kafin ki haɗa wani"
"Babu ayan ne a gida"
"Ki san yadda zaki yi ki kawo min kunun aya da pepper soup yanzun nan"
Tana tafiya Ashraf ya kalli Hajiya yace " Hajiya Maid ɗinki ta gudu kenan"
"Bana son iskanci Ashraf"
Ashraf yai murmushi.
Da wuya mai aiki ta kai shekara guda a gidan Hajiya bata gudu ba.
Akwai wata daya sani da. Ita ce ta jima sosai kusan 3yrs kafin halin Hajiya ya isheta ta tattara ta gudu...
Bisa shawaran Hajiya Halima Ashraf ya koma gida da zimmar zai bawa Dad haƙuri.
Hajiya tace masa idan ta kama ma yasa gwiwowinsa a ƙasa ya bashi haƙuri.
Kai cewa ma tayi har kuka yayiwa Dad saboda zuciyar sa ya motsa...
***
Ko Dad zai yarda?