Free chapter · Read without an account

VVF! (End of book 1)

by Hawwa__B__Kumo · DAUƊAR GORA!

💠💠💠💠💠

©®AS-2023.







         *♡DAUƊAR GORA¸.•💥*

           (Cɪᴋɪ ᴋᴀ sʜᴀ ᴛᴀ)  







Nᴀ

  *HAWWA__B__KUMO.*

    (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕

*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:REALSMASHER.*

••••••••••


*It's all about:#Vesicovarginalfistula,#VVF,#Desined,#Stepmom,#Family-Saga,#Rural-Urban,#Nigerians,#Halfcast,#Arabian-Fulbe,#Arrogance,#Hated & #Romance..*




              21 




#VVF! 


*FROM THE WRITER OF:*

-ƘADDARA KO SAKACI?

-RAYUWAR WANI

-ƳAR GARUWA

-BAMBANCIN AL'ADU

-INA MAFITA

-ZAƁIN WA ZAN BI?

-WANI AL'AMARIN

-ALƘAWARIN JINI

-ƊAN MACE

- IFZAA

-MAKTOUB

-MANAR

-IN-LAWS 

-KALLO YA KOMA SAMA!

-CIWO A JIKIN WANI!

    AND NOW

-DAUƊAR GORA!

😘


              Yau kwana biyu kenan da Aya ta fara jin ciwon mara wanda ya haɗa har bayanta,kasancewar sama² take jin ciwon,sannan da yake ba wai ta san ciwon haihuwa ba,iya karta duk wata ciwon mara me tsanani idan za tayi period,wannan ma sai take ganin kamar bai wuce haka ba,ganin yanda Amado yai mata rashin mutunci kafin ya wuce Kano ya barta akan maganar zuwa gidan Iyami da tayi masa,yasa kou da take jin ciwon take ta daurewa,duk saboda gudun kada ta tadawa kakarta hankali,underneath kuwa sam ba ta jin daɗin zaman gidan saboda rashin abokin zama da hira,ga kaɗaici da kewar wani makusanci a kusa da ita,kullum ta kwana ta tashi da ƙyar take iya fita tai sallah,tunanin Tayyibah fal ranta da kewar taimakonta gareta,sam ita ba ta ma ta batunsa shi kam,domin tunda ya kama hanya tafi bai kira wani daga ƴan gidan ya ce a bata yaji yanda take ba,a haka har tai kwana huɗu ta kama hanyar shiga kwana 5 tana ciwon a tsaitsaye,zuwa ranar kam babu yanda take,Iyami kuma itama cikin kwanakin kamar wanda akaiwa asirin ƙin zuwa ta dubata,tun wata ranan da tazo taga take²n ƴan gidan,har ana yar mata habaici da hannunka me sandan tana zarya za ta kashewa Aya aure,ta fi son ta saka ƴa da jika a gaba babu me aure cikinsu,kou da ba'a fito fili an kama sunayensu ba cikin maganar,amma ta fahimci da ita ake,wannan dalilin yasa ta kama mutuncinta ta daina zuwa kwana biyu,sanin yanda tayi fama lokacin da ƴarta take gidan,wannan kuwa taga suma danginta ne kou da dai suna nuna ba sa sonta,amma tana da yaƙini akan baza su barta ta mutu ba,wannan dalilin yasa ta bar saƙon idan Ayan ta fara ciwo a aika mata da wuri dan Allah. Da yake Iya bata gari ta yi tafiya can Maraɗin Niger,gaishe²n mutuwa da Allah ya sanya alkhairi,bukukuwa na dangi duk da bata samu ta je ba sai yanzu,kuma zata ɗan kwana biyu can ta zaga dangi,sai yasa sam babu wanda hankalinsa ya kai kan Aya,bare kou da Iyamin ce a kira ta kula da ita,tunda ta fara ciwon haka take wuni ba ta cin komai,sai ƴar fura kawai da take daurewa ta sha,shima gudun kada ta mutu ne,haka kou sallah ma idan lokaci ya yi,tunda ba wai ta fita daga hayyacinta bane a daddafe take yinta a zaune,dan tsaiwa tana gagararta. Yau tunda ta wayi gari ciwon da take ji ya ninku,tamkar mara gatan dangin Uwa da Uba,ita kaɗai take fafutuka tsakanin ƙarya da gaskiya,sallah kuwa ba'a maganarta yau,kasancewar lokacin da akai kiran zhuhur ba ta da nutsuwar yi yasa ta haƙura,banda ajiyar zuciya da addu'o'i gami da numfarfashi babu abunda take,a wannan ranar ta tabbatar yin kuka hawaye su sauko daga cikin idanunta ma rahama ne,dan yanda ta nemi hawaye ta rasa gaba ɗaya,daga inda take tana jiyo hayaniyar mutanen gidan,kowa na harkokin gabansa suna waƙe² da aiki,da yake duka gidan babu wanda take gabansa yasa babu wanda ya damu da rashin fitowarta,haka nan babu wanda ya damu da rashin yin girkinta,tunda kusan tunda ta dawo garin bata taɓa ɗaura sanwa ba,so kou da take fitowa kwana biyu ma kafin yau,babu wanda ya damu da condition ɗinta bare ayi tunanin kou wani abu ya faru da ita da suka jita shiru,tamkar ba'a garin musulmi ba haka suke wani irin zama da ita,kou da yake mahaifiyarta ma haka tai fama a gidan for the past years,har Allah ya ƙaddara abunda ya zana mata cikin littafin ƙaddararta,tun ana lissafin awanni da wayar gari har yamma ta kawo jiki dare ya shiga,a gefen Aya kam tun furar da Baba Wada yasa yaro ya kawo mata da rana bata sake sa komai cikinta ba,ga ciwo da take fama gadan² sai dai haihuwar har lokacin ba'a maganarsa,akan kanta tana jin wani irin azababben yunwa dake cinta,sai dai bata iya cin komai idan ba abu me ruwa² ba,tun ranar farko da Amado ya dawo da ita gida,Baba Wada ya sanar da Inna Larai a dunga sa sanwa da ita,rashin tausayi irin na uwar mijinta yasa tai tsalle ta dire tace ai itace a haƙƙu ta huta a yanzu ba Aya ba,tunda al'adar ƙauyika idan ɗanka yai aure kullum matarka za tai abinci ta aikawa suruka,ita kuwa tunda har Aya bata yi ta bata ba,itama bata ga dalilin da zaisa tai mata aiki ba,wannan dalilin yasa Baba Wada bai sake mata magana ba,ya koma siyawa Ayan abunda za taci,tou kusan kwanakin da suka wuce data fara rashin lafiya sai ta sanar masa ba ta iya cin abinci,wannan yasa yake aiko mata fura,sai ɗan abunda baza'a rasa ba wanda zai ɗan riƙe ta,sanda ciwon yai ciwo itace kwanciya,idan taji bai mata ba ta tashi ta zauna,kou taita zagaye ɗakin,idan shima ta gaji ta tsuguna,sam ta rasa meke damunta a duniya,har sanda tsaiwar ma yazo ya gagareta,tana nan durƙushe ta rasa makama,tana jin sanda yaran gidan suke shigowa su fita,sai dai sanin ba mutunci ne da su ba,haka za tai ta kallon ƙofar ɗakin kou wani zai shigo,amma har ta mayar da kanta babu wanda za ta gani,yaran da suke kawo mata fura ma inji Baba Wada duk ƴan gidan ne,idan tace suje kirawo mata Iyami kuma in sun fita bata sake ganinsu,dan yanda suka rainata tun can da lokacin da take zuwa ta tafi,kaf ɗinsu iyayensu mata sun sake masu damar yi mata rashin kunya,dama² idan Baba Wada na nan takan ɗan ji sanyi,a hankali ta ɗago a jigace tana sauke ajiyar zuciya,lips ɗinta da suka bushe sun yi fari tas sun tsattsage ta lasa,tana me jinjina girman Allah a zuci da fili,dan idan ba shi da ikon juya al'amura suke hannunsa ba,ta tabbatar da bata kawo yanzu ba,a haka har dare ya shiga ta daina jin motsin kowa,tana so kou da kwanciya ne tayu kou za ta ji daɗi,amma hakan ma ya gagareta,bare kuma azo maganar idanunta su runtsa,zuwa yanzu kam hatta da ɗan cikinta da take jin yana motsi,yau tun safe bata jin yana motsawa,sanda ciwon yafi ƙarfinta ta koma ta zauna sosai,tana ci gaba da kiran sunayen Allah tsarkaka da neman taimakonsa,yau kam sosai ta tabbata mara gata,Iyami ce kawai duk duniya take da a yanzu,itama kuma ƙiri² an hanata zuwa gurinta,yau da ace tsakanin mahaifinta kou mahaifiyarta suna nan tare da ita,duk da bata ga wulaƙanci da tozarci akan cikin da ba ita taiwa kanta ba,shi kansa kuma wanda ya haɗata da wahalar,tunda yai tafiyarshi yau kimanin kwanaki biyar kenan babu shi kuma babu dalilinsa,ta mutu kou tai rai dama ta san wannan bazai zama asararsa kou ta danginsa ba,tana jin sanda wani ruwa da bata san na mene ne ba suke biyo jikinta ga wani irin abu da take ji kamar za tayi fitsari,sai dai tsananin ciwo yasa ta ma kasa bambance takamaiman me yake mata daɗi,rayuwar kanta zuwa yanzu ta gaji da ita har tana fatan da ace mutuwa za tazo mata,gefe ɗaya kuma sosai daren yai mugun tsayi,addu'ah kawai take gari ya waye ta jiyo alamun fitowar Baba Wada ta samu yasa a kira mata Iyami,idan kuma ta mutu kafin lokacin shi kenan,ita dai kou me zai faru da ita yau a sanadiyyar zuwan Iyami,tana ji a ranta ya jima bai faru ba,domin ta san idan ma mutuwa tayi daga Ummiinta sai Iyami ne za su ji ciwon rashinta. Can cikin dare Baba Wada ya fito zai je bayan gida,alamun hasken da ya gani a ɗakinta da ƙofarta da take buɗe suka sa gabansa faɗuwa,dama duk gidan shi kaɗai yake damuwa da ita har ya tsaya su gaisa kafin ya fita,da darene dai bai cika dubata ba saboda lokacin da yake shigowa yana zaton tai bacci,butar hannunsa ya ajiye ya taho da sauri har kamar zai faɗi yana kiran sunanta "Ayatullah! Lafiya kike?" Kou idanunta da ƙyar take iya buɗesu saboda wahala,tana numfasawa da ƙyar,maganarta a can ƙarshen wuyanta saboda muryarta bai fita da kyau tace "Baba dan Allah.." Sai ta kasa ƙarasawa ta runtse ido tana girgiza kai tare da dafe ƙasan cikinta,abunda bai taɓa yi ba tunda akai aurenta da ɗansa,da sauri ya ɗaga labulen tare da shigowa jin yanayin muryarta,sai dai abunda ya tarar sosai ya ɗaga masa hankali,yana kallonta a wani irin tsorace yace "Ayatullah! Me yake faruwa? Me yake damunki Ƴata?" Cikin yanayin fita a hayyaci ta girgiza masa kai tana watsa hannuwa tace "ban sani ba nima,amma ji nake kamar zan mutu Baba,dan Allah a kiramin Iyami,ace masu su yafe min.. Ina jin mutuwa zan yi.." Yanda take magana tana hakki maganar na rarrabewa,shi kansa sai da ya shiga ruɗani,yana girgiza kansa yace "subhanallah! Bari na kirawo ƴan uwanki mata su taimaka maki,sannu kin ji Allah ya sauwaƙe,in sha Allahu baza ki mutu ba" ya juya ya fita da ɗan sauri,Inna Larai ya shiga ƙwalawa kira tun kafin ya ƙarasa ƙofarta,tana jinshi cikin masifa tace "yoo! Malam me zan yi maka ne da daren nan kake rafka min kira haka? Kou ma mene ne ina laifin ka jira har gari ya waye" Baba Wada cikin tashin hankali yace "Larai! Don Allah fito kije ki duba yarinyar nan,ina jin haihuwar za tayi,na tambayeta ta ce min bata san me yake damunta ba" tsaki Inna Larai tayi tace "yo! Allah na tuba idan ma haihuwa za tayi ni me zan mata? Nawa duk da na haifa wani shege ya tayani naƙudarsu,da zaka ce naje na duba ta? Ta mutu ma mana me zai dameni?" Girgiza kansa Baba Wada yayi,sanin rashin mutuncinta wannan kaɗan ne daga ciki,gudun kada su raba hali duk gari a jisu tunda dare ne,tsaf idan mutane suka ji hayaniya za su firfito,bai sake bi ta kanta ba ya juya ya shiga kiran sauran matan ƴan uwanshi su Asabe,a nan ɗinma dai da ƙyar ya samu mutum biyu suka fito suna faɗin "ashsha! Ai bamu sani ba wallahi" a cikin wannan daren Baba Wada ya shiga azalzalarsu suka wuce zuwa ɗakin Aya,tunda suka shiga Inna Asma'u ta kalli Aya bayan sun kwantar da ita,ta kalli Inna Asabe tace "gaskiya yarinyar nan ba na jin za ta iya haihuwa da kanta Asabe,ina ga me zai hana baza mu sanar da Malam ɗin a nemo Ungozoma ba,tunda baza'a samu likitoci yanzu ba,kin san abunki da zamani kuma suma ƴaƴan zamani,idan wani abu ya faru sai azo ana wallahi tallahi" Inna Asabe tana kyaɓe baki da yake dama gulma ce ta fito da ita tace "tou yanzu waye zai fita a wannan daren kiran Ungozoma Yaya? Ai kawai mu yi mata taimakon da za mu iya kafin a kira assalatu kou?" Inna Asama'u tace "a'a Asabe gara dai a sanar masa gudun afkuwar matsala" yanda Inna Asama'u ta dage ne yasa Inna Asabe amsawa ba don ta so ba,ta fito tare da sanar da Baba Wada halin da ake ciki,yace kada su damu bari shi ya fita,cikin hanzarinsa ya koma ɗakinsa ya ɗauko touchlight sannan ya fita domin zuwa kiran Uwani,saboda kaf garin a masu karɓan haihuwa babu kamarta,sai dai wani ikon Allah kou da yaje a rufe ya tarar da gidan,wasu maƙotanta da suka ji bugun ƙofa suka fito suke sanar masa bata nan anyi mata rasuwa a can Gwarzo,hakan yasa Baba Wada dawowa jikinsa a sanyaye ya sanar da su abunda ake ciki kamar yanda ya samu labari,wata sabuwar Ungozoma dake aiki primary health care ɗin garin Inna Asabe tace kou za'a kira,ganin wai aikinta ne kamar dai matsalar da take gudu ɗin idan an yi haka an tsira,haka Baba Wada ya sake fita yaje ya buga mata gida ya tado ta,ta fito cikin daren suka taho,tunda Nurse Ikilima ta shigo ɗakin Aya taga yanda take tace su Inna Asabe fita su basu guri,Inna Asama'u tace "yarinyar nan fa ba na tunanin za ta iya haihuwa da kanta Dr" Nurse Ikilima tana hura hanci ita nan ana ce mata Dr ana hura mata kai tace "dan Allah Hjy ku fita ku bamu guri,ni da aikina kada kice za ki koya min yanda zan yi" Inna Asama'u ta kalleta kawai tace "tou ai shi kenan Allah ya bada sa'a" daga haka suka fito dukansu suka barta,suna tsaye tsakar gida sun yi cirko²,yayin da suke jiyo maganarta tana cewa Aya tayi nishi amma sam ta kasa,saboda galabaitar da tayi ma har gabannin ketowar alfijir bata haihu ba,zuwa lokacin nan kam Aya har suma tayi ta farfaɗo da kanta,Inna Asabe da al'amarin yasa ta yin shiru ta rasa bakin magana,duk ita da ƴan tseguminta yau kam ta tausayawa Aya matuƙa,can tana girgiza kai tace "hum! A gaskiya Yaya ina ganin fa maganarki ne yake neman tabbata,idan ba haka ba Yarinyar nan tun yushe take fama,amma ace abu yaƙi ci ya ƙi cinyewa,ita kuma Dr ɗin dan dai ta gwada mana taurin kai taƙi yarda tabi ta taki" Inna Asama'u tace "tou gane min hanya dai Asabe.. Amma tunda ta ce kada mu koya mata aiki,ai dole mu zuba masu idanu muga ƙoƙarin da za ta iya" Inna Asabe ta kyaɓe baki tace "uhmn! Barta dai ƴar iya,in ba don haka ba Allah na tuba,kou Uwani da take Ungozomar da ai ta san abunda ya kamata,kuma ni tunda nake jin labari banda wanda na gani,a duka karɓar haihuwar da tayi wallahi banji inda taje haihuwa tai mata gardama ba" Inna Asama'u tace "uhmn tou! Allah dai ya raba yarinyar nan da wahala.." Inna Asabe tace "ameen.. Gaskiya ina tausayin yarinyar nan matuƙa.." Haka sukai zaune suna ta jinjina al'amarin Aya,abu tun ana lissafin lokaci har aka kira assalatu,Baba Wada ya fita masallaci yai sallah ya dawo,lokacin gari har ya fara haske,Nurse Ikilima da taƙi jin shawararsu ta leƙo duk ta haɗa zufa tace da Baba Wada a siyo mata reza,Baba Wada ya fita ya sayo ya dawo,jikinsa na mazari ya bawa Inna Asama'u ta bata sannan ta sake fita,duka abunda ya faru bai fi minti biyar ba,da kawowa da kuma fitowar jaririn duniyar,sai dai tunda Nurse Ikilima ta yanke masa cibiya ta ɗaure har ta naɗeshi cikin zani sam bai yi kuka ba,duk dabarar da za tayi kuma shima ta yi amma abunda alamu suka nuna mata shi ne,Baby'n ya jima da rasuwa tun a ciki,Aya kuwa lokacin nan sam bata ma san me yake faruwa da ita ba,dan tana samu kan Baby'n ya fito ta sake suma,nurse Ikilima ta taimaka ta ƙarasa zaroshi daga jikinta. Fitowa Nurse Ikilima tayi dake irin matan nan ne masu ƙiba,tana takawa da ƙyar ta fito fuskar nan a ɗaure,tamkar bata taɓa dariya ba tunda Allah ya halicceta,tana ta tsaya kallon inda Wada yake tace "Baba dan Allah ɗan ƙaraso nan ina son magana da kai" Baba Wada da saurinshi yace "tou!" Ya taso daga kan benchinsa ya ƙaraso,Inna Asama'u dake lazumi tana jan casbaha ta kalleta kawai tare da ɗauke kanta,da yake tunda taje tai sallah ta sake fitowa ta tsaya cikin zullumi,domin ta tabbatar idan akace Aya ta rasu a yau,tou fa dukansu da suke cikin gidan Allah zai kamasu da laifin ƙin taimaka mata,Nurse Ikilima tana yin ƙasa da muryarta kada aji tace "Baba! Sai dai haƙuri gaskiya,domin abunda ke cikinta bai zo da rai ba,ita kuma she's unconscious yanzu haka,so a samu a shiryata sai a kaita asibiti,saboda a ɗinke ƙarin da akai mata" Baba Wada sai amsawa yake da "tou!" Shi dai bai gane ma'anar unconscious data faɗa ba,tace "zanje nayi sallah sannan na shirya naje asibitin,sai ai saurin kawota" yace "in sha Allahu za'a kawota" sallama tai masa sannan ta fita gidan ba tare da ta kalli gefen da Inna Asama'u take ba,Baba Wada ne ya juya gurin da take zaune fuskarshi na bayyanar da alhini yace "Asama'u don Allah a shiga a gyara mata jikin,sai ai maza a kaita asibiti,likitar ta ce za'ayi mata ɗinki.. Sai kuma batun abunda ta haifa ta ce bai zo da rai ba" salati Inna Asama'u ta ɗauka tana jin kamar za tayi kuka,saboda tausayin Aya da ya sake ninkuwa a zuciyarta,Baba Wada yace "yanzu in sha Allahu zanje na sanar da Kakarta halin da ake ciki,sai ki sanar da sauran mutanen gidan kafin na dawo,mu samu a yiwa jaririn jana'iza" Inna Asama'u ta amsa masa sannan ta juya cikin sauri,shima ya kama hanyar fita gidan. Inna Larai ta fara shiga ta sanarwa abunda ke faruwa a matsayinta na uwar mijin Aya ɗin,sanda ta gama surutunta ta fita ba tare da Inna Larai ta ce mata ci kanki ba,daga nan ta shiga sauran ɗakuna duka ta sanar masu,sai dai daga masu cewa Allah ya mayar da na aike,sai masu cewa Allah ya bata lafiya,amma batun zuwa kanta a dubata babu wanda yai niyya saboda mugun hali,daga ƙarshe haka Inna Asama'u ta fito gwuiwoyinta sun yi sanyi ta nufi ɗakin Aya,sanda ta shiga a kwance ta samu Aya babu inda yake motsi a jikinta,nan take hankalinta yai mummunan tashi ta shiga salati da salallami tana ƙwalawa Inna Larai kira,jin bata amsa ba yasa ta fitowa da gudu tana fashewa da kuka tace "matan gidan nan ku fito don Allah,ina ga itama uwar Allah ya karɓi abarsa" kafin kace me duk sai ga su suna fitowa,nan dukansu sukai cirko² aka rasa me bakin magana sai salati suke. A can gidan Iyami kuwa sanda Baba Wada ya iso,da kansa ya shiga zauren gidan yai sallama,Iyami dake shirin zuwa gurin Aya,dan yau tun dare take mafarki da ita,da asuba kou da ta tashi tai sallah sai ta hau shiri,ta gama dafa abinci ta dama mata kunun gyaɗa saboda shi ne abunda tafi so,tai mata awara kuma da kanta,jiyo sallama a daf da tsakar gida yasa ta fitowa daga ɗaki tana amsawa,sai taga Baba Wada har ya shigo ciki,ta ɗan saki fuskarta gabanta na faɗuwa saboda yanayin fuskarsa tace "a'a Wada.. Sannu da zuwa" yace "yawwa Iyami.. Ina kwananmu?" Iyami ta amsa tana jin hankalinta na sake tashi,ɗan shiru suka yi dukansu,kafin Baba Wada yace "Iyami dama zuwa nayi na sanar maki maganar haihuwar Ayatullah!" Cikin sakin fuska Iyami tace "Alhamdulillah! Ta sauka lafiya? Me muka samu?" Ɗan jim Baba Wada yayi kafin yace "an samu ɗa namiji.. Sai dai bai zo da rai ba" duk da jikin Iyami yai sanyi amma hakan bai hana ta sake tambayarsa ba "yaya Ayan take?" Baba Wada yana sunnar da kanshi yace "tou! Gaskiya dai Iyami bazan iya cewa komai ba a yanzu,amma likitar data karɓi haihuwar ta ce sai an kaita asibiti sun mata ɗinki,kuma wannan shi ne dalilin zuwana domin na sanar dake" zuwa lokacin nan kam sosai Iyami taji hankalinta ya mugun tashi,zuciyarta taita saƙa mata kou dai itama Ayan ta mutu ne ake son ɓoye mata,ganin tunani bazai kai mata ba tai saurin cewa "tou Wada bari na bika mu tafi,tunda dama shirin zuwan nake sai kuma kazo" Baba Wada yace "tou Iyami babu komai,Allah ya bamu haƙurin rashi ya tashi kafaɗun Uwar" Iyami ta amsa sannan ta koma ta ɗauko kwanukan abincinta ta fito tare da rufe ƙofar parlonta,Baba Wada ya isa inda ta ajiye ya ɗauka tare da wucewa gaba ta biyoshi a baya,sanda ta tsaya ta kulle gidan kafin suka kama hanya,kafin su ƙarasa ƙofar gida Baba Wada ya tura yaro gidan su Aminu abokin Amado yace ace masa yazo gida yana son ganinsa yanzu,su kuma suka ƙarasa gidan shi da Iyami. Kou da suka shigo tun daga yanayin fuskokin ƴan gidan,ya sake sawa jikin Iyami ya ƙarasa yin sanyi,lokaci ɗaya jikinta ya kama rawa musamman ganin irin kallon da suke mata,Allah ya taimaka ba'a samu wanda yai hanzarin yai mata magana ba har suka gaisa sukai mata gaisuwa,a zahiri kuma su a gurinsu suna yi mata gaisuwar Aya ne da Inna Asama'u ta sanar masu ta rasu,yayin da ita kuma Iyami ta ɗauka suna mata gaisuwar jaririn wajen Aya ne,bayan sun gama gaisawa ta wuce ta isa ɗakin Ayan,duka suka bita da kallo an rasa mutum ɗaya da zai yi ƙarfin halin binta gudun kada ace da sa hannunsau a mutuwarta,sallama Iyami tayi kafin ta ɗaga labulen ta shiga,abunda idanunta suka gano mata yasa take taji zuciyarta na rawa,cike da ƙarfin hali dana zuciya ta dunga tafiya har ta isa inda Ayan take tana kiran sunanta,dan ita kanta batai zaton haka za tazo ta sameta ba,jin shiru yasa ta sauke mayafinta ta ajiye sannan ta tafi ta kamata tana ƙoƙarin zaunar da ita,sai taga wuyanta ya karye kamar ba ta da rai,kiranta ta sake yi nan ma taji shiru,a hankali ta mayar da ita ta kwantar,sannan ta nemi guri ta zauna tare da zuba mata ido na wani lokaci,hankalinta da nutsuwarta suna son barin jikinta amma ta daure tana kiran sunan Allah,ta jima tana kallonta kafin Allah ya bata ikon fahimtar Aya na da sauran rai,cikin azama ta tashi ta duba cikin robar ruwanta ta ɗebo,tana zuwa bata tsaya ba ta kwara mata,nan take Aya tai jan zuciya kafin ta shiga sauke numfashi da ƙyar,Iyami tayi hamdala kafin ta nufota tana kamata tana cewa "sannu Shalele.. Sannu kin ji,Allah ya baki lafiya" Aya da idanunta har sannan suke rufe ta gane muryar Iyami,a wani irin hankali ta shiga ƙoƙarin buɗe gajiyayyun idanunta,ɗagata Iyami ta sake yi tana ƙoƙarin zaunar da ita,Aya ta saki wani irin kuka mai ƙaramin sauti tana girgiza kanta,da dasasshen muryarta cikin wani irin yanayi me ban tausayi tace "Iyami ki barni na kwanta,ina jin ciwo sosai a jikina idan kina taɓa ni" Iyami data fahimci kamar ba ta jin daɗin motsatan da tayi ta ɗan mayar da ita a hankali ta kwantar,tana mata sannu kafin tace "ehh Wada ya faɗa min sai anyi maki ɗinki,nima mantawa nayi na ɗagaki,amma bari naje naji yanda za'ayi a kaiki asibitin" Aya bata iya cewa komai ba kou buɗe idonta har Iyami ta fita tsakar gidan da sauri tana cewa "ina Wada yake?" Inna Asama'u tace "yanzun nan ya fita waje" Iyami bata jira har ta koma ta ɗauko mayafinta ba tai hanyar ƙofar gida da gudu tana zancen zuci da fili,a ƙofar gidan ta hango Baba Wada tsaye shi da ƴan uwansa sai Aminu abokin Amado yana masu bayanin abunda ya faru,suna kuma shawarar yanda za'ayi a sanar da Amado,wasu daga ciki suna cewa kada a sanar masa a bari har yazo,shi kuma Baba Wada yana faɗa da cewa gara a sanar masa saboda sakancinshi ne ya janyo komai ya faru,ƙwala masa kira Iyami ta shiga yi tun kafin ta ƙaraso inda suke tana cewa "Wada ya za'ayi da yarinyar nan ne? Ni kaɗai bazan iya shiryata ba tunda da ciwo a jikinta,idan nai ƙoƙarin ɗagata tana nuna alamun ba ta so" Baba Wada ya taho da saurinshi yace "Iyami! Duk ina matan gidan suke da aka rasa me zuwa? Dama ita uwarshi ba na ta ita,mugun halinta ya ƙi bari ta taimaka,tun dare nake fama da ita,dake ba matar arziki bace haka tai biris da ni" kusan tare suka shigo gidan,ya kalli tarin matan gidan da sukai cirko² yace "yanzu ku wane irin mugun hali ne yasa aka rasa wanda za ta iya taimakawa a shirya yarinyar nan a kaita asibiti fisabilillahi?" Nan ya rufesu da faɗa sosai,Inna Asama'u dake cikin tsoro tai ƙarfin hali tace "ayi haƙuri Malam,ɗazu na shiga na tarar da ita kamar ta mutu,shi yasa naji tsoron sake komawa wallahi,amma bari naje mu shiryata" Iyami ta kalli Inna Asama'u dake jan sharhin maganar,kafin ta juya ta koma ɗakin,Inna Asama'u da Inna Asabe suka bi bayanta,su biyun nan suka haɗu da Iyami suka ɗaga Aya,duk yanda take kuka saboda jikinta da babu daɗi,a haka suka wanke mata jiki a cikin ɗakin,sannan aka sauya mata kaya,daga Iyami har su kansu yanda suka ga gabanta ya kumbura sannan ga ƙarin da akai mata na rashin mutunci,dan babu yanda ma za'ayi ace wai wanda yai mata yana cikin hayyacinsa kou kuma ya san aikinsa,tsakanin Iyami da su sai aka rasa wanda zai rarrashi wani,domin duk rashin tausayin mutum yaga yanda gurin yai angle,dole ya zubar mata hawaye,da ƙyar suna kuka suka daure suka gama shiryata sannan suka fita ɗakin,Iyami kam tunda ta share ruwan da sukai mata wanka waje,ta nemi gurii ta zauna take kuka sosai,tsantsar tunani da tausayin Aya gaba ɗaya ya dagula mata lissafi,ita sam ba ta jaririn da ya mutu take ba a yanzu,Aya dake nan da uban ciwo a jiki kawai ce a ranta,sai tunanin Ummii kuma da ba ta ƙasar,yau ta tabbatar da Maryama na nan bata san ya zata ji ba,sai dai tabbas ta san rigima dai babu mai hanata yinta da dangin Aya,zuciyarta ce ta shiga mata waswasin ina ma da bata barta ta yi tafiyar nan ba,though ma dai saboda su ne da kuma zaman garin da yake neman sa mata ciwon zuciya,yasa dole ta barta saboda gudun su rasata,badon haka ba ita kanta bata ga dalilin da zaisa ta amince mata ta tafi ba. Baba Wada ne yai sallama ƙofar ɗakin,Iyami data sauke dogon ajiyar zuciya ta amsa,ba tare da ta damu ta share hawayen da suke fuskarta ba tace "shigo Wada" Baba Wada yace "babu matsala Iyami?" Iyami tace "shigo kawai babu komai ai mun gama" Baba Wada ya sake yin sallama sannan ya shigo,Iyami ta ɗan kautar da kai gefe tana share fuskarta,Baba Wada ya ɗan raɓe gefe yace "Iyami za mu tafi da jaririn ayi masa jana'iza ne.. Ita kuma Ayatullah za'a kawo mota da zai ɗaukeku zuwa asibitin yanzu in sha Allah,na yi magana da Aminu abokin Ahmadu,zai kula da komai idan kun je" Iyami ta ɗan gyaɗa kanta tace "tou! Babu komai" ƙarasawa yayi da niyyar ɗaukan jaririn dake naɗe cikin zani,kyakkyawan gaske da shi idan ka kalleshi za kace bacci yake,kamanninsa kuwa babu inda ya baro Aya kamar itace lokacin tana jaririya,duk da halin da Aya take ciki bai hana ta jin maganarsu ba,jin wai jaririnta za'a yiwa jana'iza,a hankali wasu irin hawaye suka sauko gefen idonta,tabbas ita uwa ce dole ne taji kewa da soyayyar ɗanta,watanni 9-10 da yayi a kwance cikin mahaifarta sun yi shaƙuwa da juna na sosai² wanda baki bazai iya faɗa ba,a hankali ta ɗan buɗe kumburarru kuma gajiyayyun idanunta ta juyo tana kallon Baby'n wasu hawayen na sake saukowa fuskarta,tana kallon sanda Baba Wada ya ɗaukeshi ya fita da shi,a hankali ta sake mayar da idanunta ta lumshe dan ba sosai ma ake gane idanunta a buɗe suke ba saboda kumburi,ba'a jima da fita da shi ba Aminu abokin Amado ya iso tare da mai mota,ya shigo har cikin gidan ya sanar da Baba Wada dake ƙoƙarin wucewa yaiwa jikanshi wanka,Baba Wada yace "tou yi masu magana su fito da ita kuje kada a ɓata lokaci" Aminu ya amsa tare da ƙarasowa inda Baba Wada yake tsaye,yara da manya na gidan duk sun zagayeshi suna kallon Baby'n suna faɗan kyaunshi,ɗan murmushi Aminu yai me ciwo yana kallon Baby'n,da yake duk Baba Wada yai masa bayanin abunda ya faru da ita,sosai tausayin Aya ya cika masa zuciya,wayarshi ya fitar daga aljihu yaiwa Baby'n pics sannan ya juya da sauri ganin su Iyami har sun fito da Aya,yanda take yamutsa fuska kawai ya isa yasa ka fahimci ba ta jin daɗin motsatan da suke,da ɗan saurinshi ya isa tare da cewa "Iyami ku bari na fita da ita,na ga kamar tana jin jiki motsa tan da ake" Iyami da Inna Asama'u suka ce "tou shi kenan.. Ai dama rashin namiji ne da zai iya fita da ita yasa muka ɗaukota" shi ya karɓeta yai hanyar fita,Iyami da Inna Asama'u suka biyosu,while Baba Wada kuma ya fita cikin taron ƴan gidan ya wuce inda zai yiwa jaririn wanka. Lokacin da su Iyami suka iso asibiti,a nan suka samu Nurse Ikilima sai feleƙe take da yiwa mutane masifa kamar ta haifesu,tana ganin su Iyami ta taho tana takawa da ƙyar cikin faɗa tace "sai yanzu za ku kawota? Ku koma da ita gida kawai tunda lafiyarta bai dameku ba" Iyami za ta bata haƙuri,Aminu da ya fito motar ya tsaya sallamar driver,ya iso fuskarsa babu alamun wasa yace "akan me za'a mayar da ita?" Nurse Ikilima ta juyo da sauri jin muryarsa,dariya ta ɗan yi wanda sam bai mata kyau ba tana faɗin "Dr tare kuke ashe?" Yace "ai da yake kin san ƙanwata ce dole ki ganni" Nurse Ikilima tace "Allah sarki,ai ban sani ba" wasu metrons ta shiga kira tana cewa "ku kawo wheelchair maza a ɗauketa" sanin masifaffa ce a gurin ba kowa take ɗagawa ƙafa ba,duk wanda suke ƙasanta takasu take duk girmansu,shi yasa jiki na rawa suke yin abu,kafin akai ga ta tsinkasu a cikin mutane,kafin su fito tuni Aminu ya ɗaukota ya wuce cikin ɗan sassarfa ya shige da ita,sauran ma'aikata sai barka da zuwa suke mashi da marasa lafiya saboda yanda yake mu'amalantarsu da mutunci tare da kulawa,yana tafiya yake faɗan abubuwan da za'a kawo na kayan aiki,Nurse Ikilima data biyoshi tana neman yi masa bayani,cikin saurin yace ta bashi guri ya san me zai yi mata,duka asibitin ba wani babba bane dan duk wanda yasan primary health care,ya san komai na ciki sai addu'ah,daga likitoci har kayan aikin,musamman a ƙauyuka irin wannan da ba'a cika samun ƙwararrun likitoci da sukai zurfi a karatun ba,biyoshi akai da komai da ya nema zuwa wani room da babu kowa ciki,Iyami da Inna Asama'u suna biye da su har ƙofar ɗakin sannan suka tsaya,duk da Aminu bai da zurfin karatu,amma nacinsa akan duk abunda yake so,yasa ya zama kamar shi ne incharged na asibitin duka,domin shi yai karatu sosai akan sauran ma'aikatan asibitin,duk da shima ɗin iyakar karatun nasa diploma,tunda ya fara duba Aya zai mata ɗinki,yaga irin ƙarin rashin mutunci da akai mata ransa yai mugun ɓaci,ya juya ya kalli Nurse ɗin da ta kawo masa kayan aikin tare da karɓan allurar anesthesia dai² potion da bai wuce ƙa'ida ba yaiwa Aya,sannan ya ɗauki allura da zaren tsirgiya ya shiga aikinsa,duk yanda muryarta bai fita sannan da allurar da yai mata ya ci ace bata ji zafi ba,amma yanda take kuka me cike da azaba da ban tausayi,su Iyami kansu da suke waje suna jiyota,nan ma tausayinta yasa suka dunga share hawaye suna girgiza kai. Almost good 2 hours Aminu ya ɗauka akanta kafin ya gama ɗinkin ciki da waje,zuwa lokacin kam Aya ta ma gaji da kukan ta koma sauke wani irin ajiyar zuciya me ban tausayi,yana gamawa yai mata sannu yana jinjina al'amarinta a ransa dan bai san da me zai kwatanta ba,ya zare hand gloves da suke hannunsa sannan ya fita,su Iyami suna ganin fitowarsa suka fara yi masa sannu shima yana yi masu,cikin sanyin jiki Iyami tace "Dr ya jikin nata?" Yai ɗan ajiyar zuciya kafin a hankali yace "yanzu dai alhmdllh,za ta zauna nan ta huta zuwa yamma kafin mu tashi daga aiki" Iyami tace "tou! Babu wani abu da ake nema?" Yace "ehh yanzu dai babu,sai zuwa anjima idan za mu wuce gida,zan maki bayanin yanda za'a kula da gurin" Iyami ta amsa da "tou! Sannu Dr Allah ya bada lada" ya amsawa Iyami tare da wucewa bayan ya basu izinin shiga gurinta. Nurse Ikilima dake ta feleƙe a waje ya fara kira cikin wani irin sauti,ta taho jiki na ɓari tana cewa "Dr ga ni" ya kalleta da wani irin yanayi yace "waye ya karɓi haihuwar Aya?" Nurse Ikilima tace "ni ce Dr" bai damu da cewar akwai majinyata a gurin ba,kuma dama shima ya shirya yai mata wankin babban bargo a gaban mutanen da take wa tsawa,yace "ke yanzu dan Allah baki ji kunyar kanki ba da kika amsa min cewar ke ce? Shin kina cikin hankalinki kika karɓi haihuwar nan? Haka aka koya maki ake yin aiki? Idan baki iya abu ba me yasa baza kice a nemi wani ba? Kin kama kin yanka ƴar mutane kai tsaye saboda gidadanci da wauta,yanzu idan wani abu ya sameta me za kice da ƴan uwanta da mijinta?" Yanda yake faɗa cikin ɗaga murya gaba ɗaya yai calling attention duk wanda suke kusa da su,ai kuwa mutane duk suka yo yuya suka tsaya suna kallonsu,da yawa idan ka kallesu kou ka tona zuciyoyinsu cike taf yake da murnar ganin yau Nurse Ikilima ta samu dai² da ita a iskanci da tozarci,tatas yai mata kafin ya juya fuuu a zuciye ya fice hospital ɗin saboda ya samu ayi jana'iza da shi,yana fitowa premises na asibitin ya nufi gurin da ake parking vehicles tare da ɗaukan machine ɗinsa da yasa ƙaninsa ya kawo masa hospital ɗin tun ɗazu ya fice daga hospital ɗin,sanda ya iso rumfar ƙofar gida few mutane ya tarar,yana niyyar ya isa cikin gidan sai ga Baba Wada ya fito da jaririn a cikin buzu,Aminu ya ɗan dakata yana tunanin ba dai ace har yanzu Amado bai iso ba,sai ga shi shima ya fito gidan fuskarsa babu fara'a sam,jira yayi har suka ƙaraso ya miƙawa Amado hannu suka gaisa,a lokaci guda yai masa ta'aziyya tare da jaje,Amado ya amsa masa cikin sanyin jiki sannan suka bi Baba Wada,daga liman sai few mutane suka sallaci gawar then aka wuce da shi maƙabarta,daga can kou da suka fito Aminu da Amado basu dawo gidan ba,asibiti suka wuce duba jikin Aya,a hanya Aminu yaiwa Amado bayanin komai,shi dai jinsa kawai yake domin ƙwaƙwalwarsa tana can gurin tunanin ɗansa da ya rasa,a duniya idan akwai abunda ya ƙwallafa ransa akansa tou wannan cikin ne,sai kuma ga shi Allah ya saukar da ikonsa ta hanyar ɗauke abunsa,har suka iso hospital ɗin Amado bai iya buɗe baki yai magana ba,Aminu ya kaishi har ɗakin da Aya take,lokacin kou da suka shiga ɗakin Aya tana bacci,da yake sai lokacin allurar ya gama bugar da ita,hannunta kuma da drip da ake ƙara mata,Amado ya daure ya gaishe da su Iyami sannan ya tambayi me jiki,Iyami ta amsa a lokaci guda tana masa ta'aziyya,ya amsa kafin su sake fita tare da Aminu,daga nan suka koma gurin jana'iza domin tun kafin tafiyarsu aka fito da manyan tabarmi aka shimfiɗa rumfar da su Baba Wada suke zama. A ɓangaren Aya kuwa sanda ta samu good 3 hours tana bacci,sanda ta farka alhmdllh jikin ya ɗan yi sauƙi,dan har ta samu ta buɗe idanunta,sai dai maganarta da ya gama dashewa saboda ihun kukan da ta sha,magana take so ta yiwa Iyami amma da ta buɗe baki ta yi magana sai taji sam sautin bai fita,gashi tunda ta farka take jinta cikin lema,jikinta kuma duk yai mata nauyi,sai da ƙyar ta samu ta iya ɗago hannunta me lafiyar ta ɗan bubbuga gadon,Inna Asama'u ta fara kula ta taɓo Iyami tana cewa "alhmdllh! Ta farka Iyami,inaga kamar wani abu take so" Iyami tai saurin kallon Ayan sai ta tashi fuskarta yana nuna jin daɗinta tace "sannu Shalele! Allah ya baki lafiya ya tashi kafaɗunki,sannu kin ji Allah ya mayar maku,Ubangiji ya kawo na aike" Aya dai duk ba ta wannan take ba,magana kawai take son yi mata,fuskantar hakan yasa Iyami sake matsowa tana cewa "kina son wani abu ne?" Aya ta gyaɗa mata kai tace "ina son zanje nayi fitsari" iya kalmar ƙarshe na fitsari kawai Iyami ta gane,ta gyaɗa mata kai tace "tou bari na kira Dr a cire ruwan,idan kinyi sai a mayar" lumshe ido Aya tayi alamun tou,Iyami ta juya tana cewa Inna Asama'u "Asama'u bari na kira Aminu" Inna Asama'u tace "tou Iyami" cikin hanzari Iyami ta fita kiransa,dai² lokacin shi kuma shigowarsa asibitin kenan daga can gurin makoki,tana ganinsa "tace "Dr Aya ta farka ta ce min tana son zuwa tayi fitsari,sai dai ruwan da kasa mata bai ƙare ba" yace "tou Iyami! Ai babu matsala za'a iya cirewa taje tayi" tare suka shigo ɗakin da sallama,Inna Asama'u ta amsa masu,ya isa gadon yana faɗin "kin tashi?" Aya ta amsa masa da kai,yace "sannu! Ya jikin?" Bakinta ta motsa tace "da sauƙi" ya gyaɗa kansa tare da cewa "Allah ya ƙara lafiya" ta sake amsawa da "ameen" ruwan ya cire mata sannan ya kalli Iyami yace "Iyami ku taimaka mata taje tayi,amma saboda ɗinkin a samu ruwan ɗumi ba me zafi ba sai ta kama ruwa da shi" Iyami tace "tou Dr,sannu Allah yayi albarka" ya amsa mata yana cewa "idan ta gama sai a sanar min,zan duba wasu patients yanzu" Iyami ta sake amsa masa,shi kuma ya fita yana mata addu'ar Allah ya ƙara lafiya,Iyami da Inna Asama'u ne suka kamata za su kaita banɗaki,ta tashi zaune a hankali tana cizon lips ɗinta tare da girgiza kai tana runtse idanunta saboda azabar da take ji ba kaɗan bane,sanda suka barta ta huta kafin suyi ƙoƙarin sauko da ita daga saman gadon,tana tashi tsaye fitsari ya fara zubowa kamar an koroshi,Iyami ta kalleta tace "subhanallahi! Haba Shalele me yasa za kiyi haka? Bayan yanzu za mu kaiki kiyi sai kuma kiyi a nan? Fitsarin ya matseki dama har haka?" Kuka Aya ta fashe da shi tace "Iyami wallahi ba ina sane nayi ba,da kansa yake zubowa" da yake suna kusa da ita duk sun ji me tace,Iyami ta girgiza kai tace "ikon Allah.. Me yake faruwa kuma?" Ɗan juyar da kanta Aya tayi tana ci gaba da kuka,alamun lemar da taji a jikinta tun data farka yasa ta kallon saman gadon,abunda bata taɓa yi ba a tarihin rayuwarta fitsarin kwance tun tana yarinya,amma yau sai ga shi ta gani da idonta,cikin wani irin damuwa da tarin kunya ta dunga kuka,Iyami tace "tou kuma mene ne na kukan Shalele? Kiyi shiru don Allah kada ki ƙarama kanki wani ciwon" tayi maganar tana goge mata fuskarta,da ƙyar Aya tayi shiru shima saboda Inna Asama'u ta sa baki ne gurin bata haƙuri,tare da yi mata maganganu masu sanyaya rai,Iyami tace "kin gama fitsarin tou?" Ta gyaɗa mata kai a hankali cike da kunya,Iyami tace "tou muje banɗakin sai ki kama ruwa" a hankali suka dunga tafiya da ita suka shiga ciki,Iyami ta dawo ta haɗa ruwan tare da ɗauko mata wasu kayan sannan ta dawo tare da kai mata,da taimakonta Aya tai tsarki aka wanke mata jiki sannan suka fito da ita suna tai mata sannu,kou da suka dawo alamun danshin dake kan gadon kamar an kwara ruwa yasa Iyami faɗuwar gaba,ta daure dai suka ƙarasa sannan ta cire zanin da aka shimfiɗa tasa ruwa ta goge katifar sannan aka shimfiɗa wani suka zaunar da ita,zannuwan da suka ɓaci Iyami ta haɗa cikin leda kafin ta kalli Inna Asama'u tana cewa "bari na kira Aminun ya mayar mata da ruwan" Inna Asama'u ta amsa,ba'a jima ba Iyami suka sake shigowa ya ƙarasa yana mata sannu ya mayar mata da ruwan,da zai kuma fita Iyami ta tambayeshi kou za'a iya bata abinci taci? Ya ɗan tsaya yana gyaɗa mata kai yace "ehh za'a iya bata,sai dai saboda ɗinkin baza'a so taci abu me nauyi da zaisa idan za tayi bayan gida yai tauri ba,nishin da za tayi zai iya bawa gurin matsala,and zai ma iya janyowa ɗinkin ya farke,idan za ta ci abinci a bata ba da yawa ba,sannan a dunga haɗa mata da fruits tana sha,za su taimaka sosai wajen hana a samu matsala" Iyami ta amsa masa tana ta sake yi masa godiya da addu'o'i kafin ya fita. Abincin da Iyami tai mata da suka taho da shi nan asibitin ta ɗan ɗebar mata kunun gyaɗan da awara ta bata,sannan tace za taje ta siyo mata kayan marmari da za ta sha,Inna Asama'u tace "babu komai Iyami,kije ina nan tare da ita har zuwa sanda za mu tafi gida" Iyami tai mata godiya kafin ta fita ta barsu,daga nan asibitin gida ta fara zuwa ta ɗebo ƴan kuɗaɗe da za ta riƙe a hannunta kou da za'a nemi wani abu kuma,sannan ta wuce kasuwarsu ta siyo kayan marmari cikin leda me yellow da baƙi biyu,sanda ta dawo sukai mata sannu ta zauna ta shiga gyarawa Ayan wanda za ta ci,Iyami na ƙoƙarin bata plate ɗin data yanka mata,sai ga ruwa yana zubowa daga saman gadon,Aya data san daga ina yake fitowa,kunyar duniya ya cikata dan ita kanta ba da saninta hakan ke faruwa ba,abune da bata taɓa jin ya faru da wani a garin ba,kuma bata san dalilin da yasa ta kasa riƙe fitsarin ba,Iyami kam poster tayi ta kasa magana musamman da taga Aya ta sunkuyar da kai,cikin damuwa tace "haba Shalele! Haba Ayatullah!! Me yasa za kiyi haka kuma? Yanzu baza ki iya cewa za kiyi fitsari ba a kaiki bayan gidan,sai dai kawai kiyi shi kina zaune,idanunki biyu ba bacci kike ba? Mmmm?" Kunya da damuwa su suka hana Aya ɗagowa ta kalli su Iyami,Inna Asama'u kam al'amarin nan sosai ya ɗaure mata kai dan itama bata kawo komai a ranta ba,cikin shagwaɓa kamar Aya za ta kece da kuka saboda kunyarsu tace "wallahi Allah Iyami ba ina sane nake yi ba,fitsarin ne da kansa yake zubowa,na kasa riƙesa.. Kuma ai ban taɓa yin fitsarin kwance ba da can,me yasa yanzu zanyi ina zaune?" Shiru Iyami tayi tana kallon yanda Ayan ke matsar ƙwalla,sosai al'amarin ya tsorata ta,ta dunga jinjina kanta kafin tace "tou! Bari na kira Aminu na sanar masa,kada muje wani matsalar ne mukai shiru duka tun ɗazu" daga haka ta juya ta fita jikinta a sanyaye,Inna Asama'u kuma ta taso ta fara ƙoƙarin gyarawa Ayan jiki kafin su shigo,tare Iyami suka dawo tana yi masa bayanin abunda yake faruwa,shi kansa ya mugun kaɗu sosai,yayin da zuciyarsa ta shiga waswasi take yana kuma tambayar kansa kada dai ace Aya ta gamu da matsalar Yoyon fitsari ne a dalilin haihuwar nan? Kou da suka shigo tuni Inna Asama'u ta canja mata zanin jikinta,tambayoyi yaiwa Aya ta amsa masa kanta a ƙasa ta kasa kallon kowa cikinsu,daga yanda ta bashi details ɗin komai ya fahimci inda aka dosa,cikin tashin hankali da damuwa ya dunga jinjina kansa ya kasa daina kallonta,lokaci ɗaya ya juya yana cewa Iyami yana zuwa,bayan ya fito waje layin Amado ya kira,sai da wayan ya kusan katsewa kafin ya amsa,Aminu yace "Malam kazo asibiti yanzu ina son ganinka akwai damuwa" daga haka bai jira Amado ya amsa ba,ya katse wayar ya ci gaba da zagaye gurin ya kasa komawa ɗakin,ba'a ɗauki dogon lokaci ba Amado ya iso,Aminu yana hangoshi ya ɗan sauke ajiyar zuciya sannan yace "biyoni muje" babu musu ya biyoshi har zuwa ɗakin,tunda suka shigo yake kallon Aya dake zaune a ɗan goce saboda ɗinkinta,suka sake gaisawa da su Iyami kafin yaiwa Ayan ya jiki,ta amsa masa da kai tunda muryarta ba ta fita sosai,and gara ma yanzu akan ɗazu,wani lokaci sautin yakan yi seizing aji wani abun,Aminu yace "assalamu alaikum.." Suka amsa masa dukansu,kafin yace "game da matsalar da kuka sanar min ne Iyami nake son maku jawabi duka.. Na tabbatar idan ma na ɓoye ban sanar daku ba a yanzu dole za ku damu,kuma wata rana za kuzo kusan gaskiya,saboda abunda yake faruwa ba me ƙarewa bane nan kusa.." Iyami ta gyaɗa kanta tace "haka ne" Aminu yace "tou! Alal haƙiƙa matsalar da Aya take ciki a yanzu idan ban sanar maku ba,zai zama kamar na ci amana ne,tunda Aya matsayin Ƙanwa nake kallonta,kou da ma ace ba Ahmad take aure ba,mutunci da zaman lafiyan da akayi tsakanin iyayenmu wannan yasa zance ita ƙanwata ce ako ina.. Tou a zahirin gaskiya abunda yake faruwa yanzu shi ne,Aya ta gamu da wata matsala ce da ake cema Yoyon fitsari,wanda a turance kou gurinmu likitoci muke cema *VESICOVAGINAL FISTULA (VVF).."* Daga Iyami har Inna Asama'u salati suka ɗauka,dan kou da yake basu taɓa ganin wanda ya gamu da matsalar a garin ba,amma suna yawan ji a redio ana faɗanta,nan duka hankulansu ya ƙara tashi fiye da zato,ɗakin da duka occupants ɗin ciki sukai shiru aka rasa me bakin sake magana...



      *#TURƘASHI!* ```Masoya shin me kuke tsammanin zai faru ga Aya a dai² wannan gaɓar? Anya kuna ganin Amado zai yarda ta koma gidansa bayan ta gamu da wannan larurar? Yaya iyayen Amado da danginsu za su ɗauki wannan al'amari? Shin kuna ganin Aya za ta warke kou kuma daga nan rayuwarta ya zo ƙarshe kenan? Me kuke zaton zai faru idan Ummii taji wannan mummunan labarin ga ƴarta? Shin kou ina Bukar mahaifin Aya ya shiga duk tsayin wannan lokaci? Kuna ganin nan gaba zai iya bayyana? Mene ne makomar auren Aya da Amado? Kuna tunanin nan gaba Amado zai gyara ɗabi'unshi har yaso Aya da gaske? Uhmn! Koma dai me zai biyo baya,sai nace da ku mu haɗu a littafi na 2 dana 3 domin jin yanda za ta kaya,na gode da goyon baya tare da bibiyarku masoya,mu haɗu cikin littafi na gaba wanda zai zo maku a matsayin na kuɗi kamar yanda kuka sani..```



    _#Ga wanda suka shirya koma nace suka fara tambayar kuɗin book kafin yanzu,za ku samu Book 2 & 3 akan farashi me sauƙi,Normal group za ku biya ₦500,SP 1K,all via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then sai a turo evidence of payment ta wannan number ***. Ga ƴan uwa ƴan Niger kuma za ku iya tuntuɓata domin jin yanda za ku biya naku,na gode._





#Follow

#Vote

#Comment

#Share

#Asli Smasher.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.