Free chapter · Read without an account

Chapter 06

by Azizat Hamza · ASHRAF: beauty meets ugly

ASHRAF: Beauty meets Ugly


06




Yanayin garin akwai hadari sosai za a iya fara ruwa a kowanni lokaci.

Zaidu da Aliyu ne suka rakota tasha.

Aliyu sai teasing ɗinta yake da Abuja Kopa Abuja Kopa.

Ta dena kula shi ma ta fita harkarsa.

Ta yiwa tafiyar camp ɗin nan shiri na musamman.

Ance mata abincin camp babu daɗi dan haka tayi shirin wannan. Cornflakes ne, cerelac ne, madara ne, Hollandia, biscuit, ga kuma chinchin ɗin da Baba ya sa Anty Fa'iza ta soya mata.

Irin kayan data shirga a jakarta zaka ɗauka ba sati uku kawai ake a camp ɗin ba.

A cikin motar tasu kusan su biyar duka camp ɗin zasu wuce.

Ba ta fi minti shabiyar ba motarsu ta cika.

Su Zaidu suka yi ta waving mata har motarsu ta bar tasha.

Gayen dake gefenta ya tambayeta ko itama camp ɗin zata je ta gyaɗa masa kai.

"But you look young oo. You sure say you graduate" ya ƙarisa maganar yana dariya.

Zainab ta haɗe rai. Tun yanzu ta fara haɗuwa da 'yan rainin hankali.

"I'm Paul by the way"

Ta juyar da kanta gefe tana kallon titi.

Ta ja siririn tsaki. Da wani ƙaton bakinsa a wajen. Ga uwa uba warin hammata da yake.

Wai har yanzu akwai wanda basa amfani da roll on ko body spray?

Sauran 'yan tafiyar tasu tuni suka buge da taɗi kowa na faɗin irin shirin da yai wa rayuwar camp. Mazan na cewa zasu samu kyawawan 'yanmata. Matan kuma na cewa zasu ci kuɗin samari a Maami market.

Chan ta matse musu. Qayyisah kam saka earpiece tayi a kunnenta tana sauraron audio book ɗin littafin Micheal Obama my suna *Becoming*

A haka dai motar tasu ta cigaba da tsalala gudu...

Rana na farko a Camp Qayyisah ta tsani komai a wajen. Kasancewar bata yi boarding school ba. Bata saba da haɗakar mata a waje ɗaya daga gari mabanbanta ba.

A wajen registration ta sake haɗuwa da Paul. Wanda suka shigo mota tare.

Wannan karan ta ɗan amsa masa da ya gaisheta.

Dake ita ɗaya ke tafiyarta wannan Paul ɗin ya maƙale mata har suka gama registration tare. Aka sake haɗa su a Platoon ɗaya wannan yasa ta ɗan sake da shi har ta iya gaya masa sunanta.

Bai iya kiran Qayyisan ba aka bar shi a Zainab kawai.

A rana ta huɗu suna tsaye a filin parade wani ya taɓa kafaɗarta.

Ita fa an sa mata ido a Platoon ɗinsu. Kowa ya tashi sai ya mata magana. Smallie kamar yadda sojojin ke kiranta duk da kuwa ba ita kaɗai bace guntuwa a wajen.

Ta juyo a fusace.

"Yi haƙuri. Kin yi min kama da wata 'yar'uwarmu ce. Tun jiya da na ganki nake tunanin kaman na san ki a wani waje"

Itama ɗin sai da yai maganar ta ƙare masa kallo. Tabbas ta gane shi. Ai yaran Abba basa ɓuya a ko'ina ka gansu. Goshin nan dai na gado shi ke bayyana su.

Ta manta sunan shi, kaman shine Salim ko kuma Khalifah, tsakanin biyun nan dai.

"Kin min kama da wata cousin ɗina da suke Jos. Aisha Qayyisah"

"Zainab Qayyisah" ta yi saurin amsa masa saboda bata so ya kawo maganar Humairah.

"I knew it. Dama tun jiya nake ta tunanin kece ko ba ke bace. Ikon Allah Qayyis ke ce a nan. Gaskiya what a small world. Yaushe kika shigo camp? Ina twin ɗin ki?"

Kai!

Wani soja ya daka masa tsawa.

"Sorry Officer" ya faɗa yana sara wa Sojan.

Sojan ya mishi warning akan ya dena surutu.

Ita Zainab gani take kamar rayuwa take a mafarki. Tabbas akwai babban al'amari da zai faru a Abujan nan.

Idan tayi addu'a akan wani abu kuma alamomi suka bayyana fiye da biyu to tabbas akwai alkhairi a abun. Amma idan ba ta ga sign ko ɗaya ba ko kuma ta ga alama guda ɗaya to abin zai zo da matsala.

Ba coincidence bane yasa ta haɗu da ɗan Abba a camp ɗin nan. Tabbas akwai wani abu mai girma da zai faru.

Ƙila kuwa ƙarshen gabar dake tsakanin Abba da Baba ne ya zo.

Da aka tashi daga parade ita da Khalifa da Paul suka wuce Maami cin abinci. Shi Paul sai wani ɓaɓɓata rai yake yana hararan Khalifa a fakaice...


***

Alhaji Sani Muƙaddas yana zaune a ɗaya daga cikin kujerun falonsa yana hutawa kiran ɗansa ya shigo.

Khalifah kenan ɗan autansa a cikin maza. Daga shi dama sai Sabira da kuma Maryama.

Tunda ya gama degree ya dawo Nigeria ya faɗa harkar kasuwancin mahaifinsa. Yana yi tana attending masters na shi a Jami'ar Abuja. Yanzu da ya gama masters ɗin yai register dan yayi bautar ƙasa.

Duk cikin yaran nasa maza babu wanda Abba yake alfahari da shi kamar Khalifah. Khalifah ɗan Albarka ne.

Shiru Abba ya yi yana jin bayanin ɗan nasa kan cewa ya haɗu da Zainab a camp. Zainab dai 'yar marigayiya Hawwah.

Har yau yana dana sanin abinda ya faru a wancan lokacin amma kuma kunya da kuma mantuwa ya hana shi waiwayan 'ya'yan da ƙanwarsa ta bari.

Ko yanzu ya tabbata dai Aminu ba dan dukiya ya auri Hawwah ba sannan gashi duk da ya rasa komai a wancan lokacin bai gaza ba ya tashi kansa har ya iya kula da 'ya'yansa.

Tabbas shi da sauran ƙannensa sun ti kuskure a lamarin Hawwah. Dukkansu sun gane kuskurensu amma an rasa wanda zai cire girman kai ya je ya bawa Malam Aminu haƙuri.

"Na yafe gadon Hawwah. Gadon 'ya'yana kuma ni bana buƙatarsu yanzu, duk ranan da kuka yi niyya ku kawo musu abun su. Idan kuma kun ga basu cancanci gadon ba Allah yasa mu gama da duniya lafiya"

Kalaman Malam Aminu kenan haɗuwar da suka yi na ƙarshe.

Abba ya sauke ajiyar zuciya. Tabbas sun zalunci Malam Aminu da 'ya'yansa.

Kada Allah ya kama shi da alhakin yaran nan. Shifa dama niyyarsa idan an kwana biyu zai dawo ya basu gadon su, amma Hajiya tace a bari sai Babansu ya zo ya nema da kansa. Gashi bai zo ba gashi shi kuma ya manta da zancensu ya cigaba da harkokin rayuwa.

Tabbas wannan dama ce ta zo masa da zai gyara abinda shi da 'yan'uwansa suka ɓata.

Zai samu lokaci ya je kano su tattauna a san yadda za a yi a bawa magada gadonsu. Dama juya musu aka ce za a yi zuwa lokacin da zasu girma.

Ya cewa Khalifah ya kula da Zainab sosai sannan ya tura masa numbarta.

"Numbar wa za a tura maka?" Hajiya Halima ta faɗa tana saka hannunta biyu duka a ƙugu.

"Zainab ce"

"Wace Zainab"

" 'yar marigayiya Hawwah"

Ta ɗan yi shiru tana so ta tuno wace marigayiya Hawwar yake nufi.

"Ohooo! kace Hawwah rikici kenan"

Abba ya buga mata wani kallo.

"To Allah dai ya jiƙanta. Mijin nata ya fara gane kuransa ne. Ai wallahi kun yiwa kanku da kuka bari ya kashe muku ƙanwa baku tura shi kurkuku ba"

"Halima!"

" au! Allah ya baka haƙuri, na yi shiru"

Abba ya kau da kai ya kalli wayarsa dake haske. Numbar Zainab ne da Khalifah ya turo...


***

"Ni ne na yi kuskure dana ɗaukoka daga rayuwar sheɗanci na baka shugabancin kamfanina. Ashraf cikin shekara biyu babu abinda ka tsinana min a wannan kamfani. Idan da babu Umar a kusa da kai da babu makawa ba zamu kai war haka ba tareda komai ya lalace ba"

"Dad zaka iya ba shi kamfanin ai. Just give him the damn company. Infact ka adopting ɗinshi kawai ya zama legal son ɗinka"

"Ashraf!" Mom ta daka masa tsawa

Ashraf ya cizi leɓensa da ƙarfi kamar zai ɓula shi. Hannunsa rawa yake saboda tsabar masifar da ke cinsa.

Ya gaji da haɗa shi da Umar da Dad yake yi. Umar kaza Umar kaza.

Ko lokacin da yake yaro duk dukan da Dad zai masa akan Umar ya fishi ne.

Abu kaɗan Umar ya je Islamiyya kai ka gudu, Umar yana karatu a gida kai kana wajen buga ball. Umar yana fita sallah a masallaci kai kuma sai dai ka rufe ɗaki kayi ta kallo.

"Dad i resign. Zan kai resignation letter ɗina gobe"

"Ashraf!"

Ya dangwalar da fork ɗinsa ya miƙe zai bar dining ɗin

"Muhammad!"

Yana jin haka ya tsaya cak. Ya san ma'anar kiran sunan nan.

A hankali ya tako ya zo zauna.

"Kada ka sake tashi a gabana ina magana" Dad yai maganar idanunsa sun kaɗa jawur

"Sss sorry Dad"

Shiru ya biyo bayan hakan.

Kusan minti biyar kafin Dad ya iya shanye duk wani ɓacin rai daya zo masa ya fara magana.

"Ajiye aiki ba shine mafita a gareka ba, dan kuwa kana ajiye aiki kamfani zata maka ka a ƙotu saboda kuɗin kamfani daka ci"

Ashraf ya zaro ido.

"Ka dena kallona. Lokacin da ka cire maƙudan kuɗin kamfani ba tareda committee sun amince ba ina wajen ne?"

"Na ce ina wajen?"

"No Sir" Ashraf ya faɗa yana tura baki.

"Idan ka shirya zuwa kurkuku Bismillah ka je ka ajiye aiki"

"Sayyidi Dan Allah ka dena faɗin mummunan abu haka. Allah ya tsare min ɗa da zuwa prison"

"To ki gaya masa" ya nuna Ashraf da yatsa.

"Ki gaya masa ya je ya ɗauki takardar appointment a wajen Sakatariya gobe. Ki gaya masa daya amshi takarda ya fara aiki ranan monday"

"Sayyidi wa zaka bawa CEO" Mom ta tambaya cike da jin haushin abinda Dad ɗin ke shirin yi.

Maimakon ya amsa mata sai ya kalli Ashraf yace

"Zan baka wata shida, zaka yi aiki babu albashi. Zan baka allowance na kuɗin man mota daga aljihuna. Idan ka gyara halayenka kanka zaka yiwa. Idan ma sheɗancin da ka saba zaka cigaba da yi. Bismillah ina daidai da kai"

Ashraf yai shiru. Dad ya riga ya ƙulle shi ne ta ko ina.

"Ka amince da hakan ko kuma ajiye aikin zaka yi?"...

***

©AzizatHamza2023


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.