Free chapter · Read without an account

Page:7

by Ramlat Abdulrahman Manga · SANIN GAIBU....

SANIN GAIBU...!!

   _Sai Allah_

ͲϴᏢ-ΝϴͲᏟᎻ 2023

    *Mai_Dambu*

Fatan Alkhairi Autar Manya ❣️😻😍

    Page:07

"Don Allah Malam meye haka kake kamar yaro karami? Taya zaka shure ta kamar ka samu jaki?" Inna Laminde ta fada a fusace. "Yo ai tafi kama da hakan ne" kura mishi idanun suka yi, babu wanda ya iya magana domin iskancin Malam kara girmama yake, har ya gama shirmen shi ya futa bata ce mishi kala ba, "Inna kiyi hakuri wata rana sai labari in sha Allah Bimbi zata zama wani abu." "Hmmm Amin Ya Allah, tsoro na daya ne kar na mutu Bimbi ta shiga wani hali." "Ayya Inna babu wanda yasan gawar fari" "hmm" ta ce, suka cigaba da hiran su. Dake akwai dakin su na samari nan ya wuce ya kwanta.

Washi gari da asuba, bayan sun yi sallah asuba. Daukar allonta tayi ta nufi hanyar waje da hijabinta. A tsakar da ta hadu da Innar su, dake aiki ya sha manta jan rigar ta tai, tana kallon ta. "Zaki makaranta ne?" Lumshe idanunta tai, sannan ta mata murmushi. Shafa kanta Inna Laminde tayi tana faɗin. "A dawo lafiya " murmushi tayi da ya fito da jerarrun haƙoranta. Ta nufi hanyar waje. A bakin kofar fita taga baffansu. Hàdiye yawu ko ta ya zata yi karatu ita da ba magana take ba. Asara yawun barci. Dauke kai yayi ya cigaba da jin labaran karfe shida da rabi na BBC Hausa. Yana wurin har Bakwai saura, suka dawo ita da yan uwanta. Kallon Rabi da Harirah yayi cikin farin ciki, "Allah ya muku albarka rabi da harirah." "Amin Baffa" wuce su tayi abinta, tana shiga wanka suka wuce, sai fushi take ita ba kome ya sata fushi ba iya iyaka yau Monday, kuma zata makarantar boko, sai ta fara jin ba dad'i.

A can birnin Shehu kuwa, tun ranar Friday Prince Aliyu ya ga inda aka yi Poster din shi, amma yaki tafiya domin so yake lallai ya wuce Illorin, sai da Ummin shi ta mishi fada ya hakura, tun safe aka shirya dogaran da zasu raka shi, wurin karfe goma suka nufi bangaren Mai Martaba Shehu Abubakar Shehu, ya mishi nasiha da fada, sannan ya mika mishi wani takarda wanda shi kan sa Prince yake da yakinin kudi ne, godiya yayi sannan ya nufin inda ake jiran shi, koda ya isa bude mishi motar aka yi ya shiga, daga nan suka nufi Binji local government, gidan Hakimin Binji suka fara sauka anan aka kai su local government SC suka yi abin da zasu, sannan suka wuce Maikulki, a gidan Mai gari aka sauke shi a ɓangaren wani dan mI gari da yake aiki a lagos, dake ɓangaren ya fi ko ina a gidan kyau da tsari, ko dar Mai gari bai ji ba, yasa aka gyara mishi daya daga cikin dakunan, flat ne mai mugun kyau da haduwa. Duk da an saka mishi kome a gidan sai dai babu wutar lantarki, tunanin shi ya tsaya ne lokacin da ya zaro laptop din shi, da wayar shi. Fitowa yayi yana murmushi domin yara sun cika bangaren wai sun ga baturen cikin tv. A hankali ya fito. "Yallabai me kake bukata?" "A'a Baba Abu turab zaka kira ni, nima d'anka ne." "Wane mutum Yallabai dai, kana bukatar wani abu ne?" "Eh tow Baba" ya fada yana sosa kai, "me kenan?" "Hmm dama tambaya zan yi ana samun wuta ne?" "Eh amma ba sosai ba, kuma sai da nayi tunanin zaka bukaci wuta ko dan irin kayan aikin ku na zamani." "Eh Baba" "gashi babu." "Ba damuwa, bari na fita zamu koma Binji mu nemi injin" "tow madalla, dake kaga Habibu zuwa yake da na shi ya kuma koma da ita, da ya barta ai da na saka mai sai ka kunna don Allah kayi hakuri da yanayin garin mu" "ba kome fa" ya fada yana murmushi. Yara suna bin shi. "Kai ku b'ace anan" Mai gari ya faɗa. "Kyale su Baba." Ya fada yana murmushi. Durkusawa yayi yana kallon Yaran. Sai su kalle shi sai su koma da baya, "eh Bature na" sai su tab'a hannun shi su koma da baya, dariya suka ba shi ya mike yana faɗin. "Abokaina bari na je na dawo " "laaa kunji Yaren yake " ita kanta Hausar shi cewa suke yare na, yana fita fadawan da suka rako shi har biyu suna nan. "Kun san me? Zaku bar min motar ne kamar yadda mai martaba ya ce, zamu Binji sai ku wuce sokoto" ya fada yana wucewa gaban motar ya zauna a daya wuri me zaman banza, yana nazarin abubuwan da yake bukata. Lokacin da suka isa har tasha ya kai su, sannan suka fita ya musu alkhairi domin ya koyi haka daga iyayen shi, sai sa yaga tashin su, sannan ya koma kasuwa yayi sayayya, kafin ya juyo garin yaran nan kuwa kwalin biscuit da chocolate ya saya musu. Sai yar karamar gas wacce zai yi amfani da shi incase. Lokacin da ya iso ya shake motar da kayayyakin amfani da generator. A gajiye ya dawo lokacin ana sallah azhar, shi da wani dan me gari Nazifi suka sauke kayan shi bai samu jam'i ba. Haka suka nufi cikin gidan da kayan. Yana ajiye kayan yayi alola sannan ya nufi masallaci, sai da yayi Sallah suka kuma gaisawa da mutane, sannan ya shigo cikin gidan. Aka kawo mishi abinci bai saba ci shi daya ba, ko a Sokoto da mutane yake ci, domin ko a gida a tare da Ummin su da Ummul aiyman suke ci. Fitowa yayi yaga Yaran nan, daukar butar da aka kai mishi yayi ya kira su, suka wanke hannun su, sannan ya shiga dakin ya kawo musu praying mat. suka zagaye shi a tare suka ci abincin, kusan sune suka ci har da wawar su, murmushi yayi yana kallon su. Mikewa yayi suka biyo shi dakin shi, bude kwalin biscuit da chocolate yayi ya dauki wani laida ya zuba musu. "Kuje a raba muku kun ji" a guje suka fita suna ihu. Suna fita Mai gari yana shigowa, shima fita yayi zai tattara kayan abinciin. "Ba dai basu abinci kayi ba Yallabai?" "A'a Baba " ya fada yana murmushi. "Ga zahiri nan kamar an zubawa kaji abincin, nace ko zan kira maka wani Yaro ya taya ka haɗa wutar ne?" "Eh Baba " haka ya fita ya sa aka kira mishi lawi, suka hada wutar. Sai da ya kunna inji din domin da mai ya sayo abin shi, sai yaga iya bangaren shi ne da wuta. "Dan uwa,ko zaka iya hadawa da wutan gidan baki ɗaya " " ba matsala Yallabai " domin yana zuwa mai gari ua gaya mishi tow yarima ne daga Masarautar Sakkwato. A take ya shiga girmama shi. Komawa yayi daki ya kwanta, ya bar lawi da aiki. Sai da ya gama daidai ana kiran la'asar, suka fito tare. Mika mishi kudin aikin yayi ya ce."a'a yallabai mai gari ya bani" "karba nace" ya fada yana sassauta faraa shi. "Allah yasaka da Alkhairi" share shi yayi. Alola suka yi aika suka shiga Masallacin. Bayan sIlun isar da sallah, ya jima a masallacin kafin ya fito yana kallon garin yadda ya burge shi. Nufo shi mai gari yayi yana faɗin."ko zaka zaga garin nan na kira maka Nazifi" "Eh ba zan ki ba" kiran Nazifi yayi suka shiga zaga garin, har sai garin ya fara duhu suka dawo, a can hanyar rugar su Sa'ade suka samu wata saniya ta kasa, an yanka ana niman masu saya, abin ka da jini yana yawo a jikin shi, a take yasa domin yana da kauna tare da amana da tsakanin su da nama, shi yasa yana gani ya saya, abin ya faru akan idanun Malam,domin da aka yanke kudin saniyar bai zata A.A zai saya ba, sai yaji ya ce tow a biyo shi da saniyar zai biya. Sai da aka yi sallah magriba ya biya kudin, sannan mai gari ya saka aka nimo Yaran shi suka shiga gyaran saniyar. "Yallabai ya zamu yi da saniyar?" Mai gari ya tambaye shi, " a kai cikin gidan sai su fada abin da za a basu, ina son a soya min shi yadda zai kwana biyu sauran kuma a rabawa kowa da kowa." "Sannu bako me cida dan gida" tuwon shinkafa miyar kuka da yaji kayan kamshi, ga shi zabuwa aka burge a miyar. Sai tashin kamshi. Lokacin da yaga tuwon sai da ya kira Ummin shi, bata dauka ba. Kiran Rumaisah yayi. "Addah wai me yasa Ummina bata daukar kirana?" "Abu Turab Sultanah tana wani uzuri ne a wannan gabbar ka mata uzuri don Allah " "tow princess fa?" "Ka tambayi Ummina" ta gaya mishi tana kashe wayar ta. Domin karfin hali tayi ta mishi magana domin Ummin su, ta gargade su da kar wani ya gaya mishi. Halin da ake ciki, fita ya yi bayan aka ayi sallah isha ya dawo gida. Kunna inji yayi ya kwanta abin shi. iskar fanka yayi awon gaba da shi domin ya gaji sosai. Bai san lokacin da injin din ta mutu ba, domin tunda na Nazifi ya shigo ya samu yana barci wurin karfe biyu na dare sai ya kashe injin ɗin. Suma a lokacin suka gama gyaran saniyar, sai a sallah asuba suka hadu. "Kuyi hakuri na bar ku da aiki, sannun ku da kokari." "Ba kome wallahi, Ni na kashe maka injin jiya da karfe biyu na dare." "Hmm ka kyauta domin ma gaji ne jiya nima " sosai suka sake da juna kamar sun shekara da sanin juna. "Nazif gashi ka basu su sayi abin bukata da shi. " "Ai baba ya bada kudin su mangyada da sauran su " "wato ba zai huta ba ko? Tow don Allah ka basu, su kara in case" dake Abu turab yana da mugun cika idanu da kwarjini bai musanta mishi ba ya amsa. Shi kuma ya wuce bangaren shi da yaga an kawo mishi babban flask da karami. Shiga ban daki yayi ya dauki bokiti ya wanke tass, sannan ya juya ruwan, ya shiga dakin ya sauya kaya ya fito ya wuce ban dakin. Yayi wanka sannan ya fito ya shirya, anan ya kira Ummin shi, babu wani kulawar da ya saba samu sai baki daya yayi laushi. "Ummina nayi laifi ne kuke hukunta ni da abin da ban sani ba?" Ya fada idanun shi yana cika da kwalla. "Baba karami, kayi hakuri kayi abin da ya kawo ka. Wata tara kake da shi please ka tabbatar kayi abin da ya dace karka manta da alkhairi da sadaka" "in sha Allah" ya fada yana gyada kai domin yayi kewar ta sosai. "Ummina Ummul Mansurah" "kayi hakuri gaskiya bata nan na tura England wurin su yayan ka." "Shi ne ba ku gaya min da wuri ba." "Tow uban masu gida na gaya maka yanzu ko?" "Shi kenan zan tafi makarantar da aka turo ni." "Allah ya maka albarka, ya tsare ka da sharrin maraici da dare, ya hada ka abokan alkhairi na gari, kar ka manta da yin alkhairi tare da sadaka domin maganin masifa ce, yawan ta Alkhairi yana cika mizani, sadaka maganin masifa ce, yawan nafilla yana kara kusancinsa da Allah, don Allah kar ka cutar da wani domin ba iya kai zai tsaya ba. " Nasiha masu ratsa zuciya da jiki haka ta gama mishi fada, sannan suka yi sallama, shima ya fito. Cikin gidan ta shiga ya nufi bangaren da aka nuna mishi na uwar mai gari, ya gaida ita tare sa bata hakurin yazo ba shi shigo gaida su ba, sai aiki ya kawo. Cikin fara'a ta amsa mishi, "ba kome ai mun ga aiki kake yi shi yasa baka shigo ba, da fatan wurin bai takura maka ba." "A'a ba kome " "sannu da kokari mun ga tsaraban yara" "babu kome Umma" sauran dakunan yabi suka gaisa sannan ya mikawa Uwargidan mai gari key dinki shi. Kana ya musu sallama. Ya nufi waje ya samu an goge mishi motar shi, kafin ya kalli Mai gari. Ya ce mishi."Baba ai da kafa zan tafi naga makarantar babu nisa." "Tow shi kenan Allah ya dawo da kai lafiya." "Amin Ya Allah" ya nufi makaranta.

"Yau naji labarin malamai daga Binji sun iso Allah ya baku damar ɗaukar nauyin yaran, akwai yarinyar da nake so don Allah ka saka idanu akan ta Yallabai" "ina jinka" ya tattara nutsuwar shi ya daura akan shi. "Yarinyar kurma ce bata magana kuma, akanta aka kawo ku," "babu wata gamayyar kungiyar Handicapped ne a nan?" Girgiza kai yayi yana faɗin"ko wancan satin na samu labarin uban zai fita da ita niman taimakon kan sa, kwana ɗaya nayi da kai na fahimci kome akan ka, ka taimaka mata shekaran ta goma baki ɗaya" shiru yayi yana kallon Mai gari kafin ya ce. "Allah ya bamu ikon taimaka mata domin kai ne sanadin haka" kallon Aliyu yake domin bai tab'a ji ko ganin matashi irin shi me saukin kai ba. Dan manyan mutane wanda kana ganin shi kasan kudi da mulki ya zauna a jikinsh. Sallama yayi Nishi.

------------

"Malam Aminu kana nufin Bature ne aka kawo garin nan?" "Ina gaya maka jiya a kan idanu na ya sayi saniyar da ta kasa a mutunce , da alamu me arziki ne." Inji Malam Aminu, gyara zama malam Musa yayi ya ce. " Kai haba? Kasan dai gobe zaka kai Yarka wurin niman taimakon nan ko?"

ASHRAF, SANIN GAIBU,TSINTUWA is not free, Pay N400 ONE, TWO N800, THREE 1K to 0008219237, Jaiz bank Azizat Hamza


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.