Free chapter · Read without an account
Chapter 08
ASHRAF: Beauty meets Ugly
08
Yau za a fita a camp. Kowanni ɗan bautan ƙasa ya sha ado cikin 6/7 na kayansu.
Qayyisah dai bata cikin 'yan fareti dan tun ranan farko da ta ji wahala ta gudu ta koma team ɗin 'yan Red cross.
Tana tsaye tana ɗagawa 'yan Platoon ɗinsu hannu dan ba ƙarya sun burge sosai. Ko cikin competitions da aka yi Platoon ɗinsu ta samu kyaututtuka da yawa.
Yau zasu bar camp. Kowa zai karɓi posting letter ɗinsa ya kai ma'aikatar da aka tura shi.
Tuni sun haɗa tafiyarsu da Paul da Lisa da kuma Ramlah, suma 'yan Jos ne da suka haɗu a cikin camp ɗin.
Ba a ƙare parade ba sai kusan ƙarfe shabiyu na rana.
Ana gamawa kuma aka fara rabon posting letter.
Khalifa ne ya fara karɓan nasa. Dama ya sani kamfanin Abba za a tura shi. Koda ba nan aka tura shi bama dole nan ɗin zai koma.
"Kai! Har yanzu ba a kira sunana ba"
"Ke kam ai ƙauye za a tura ki"
"Mugu saboda kai ka samu naka ko"
"Primary school za a kai ki kiyi ta fama da ABCD"
"Ba ABCD ba carmandudu zan musu"
Khalifa ya fashe da dariya.
Suna tsaye aka kira sunan Paul Ishaleku. Shi kam hankalinsa na kan Qayyisah ko sunansa bai ji ba. Qayyisah ce ta yi ɗagyalgyal ta karɓi letter ɗin tana dubawa.
Khalifa ya wafce letter ɗin ya miƙawa Paul yana faɗin "ke zaki faɗa masa inda aka tura shi ne. Ki bar shi ya karanta kayansa"
Paul ya karɓa idonsa na wiki-wiki lokacin da yake karanta takardar.
"Paul Ina aka tura ka?"
"Qayyis ki fita harkansa Dan Allah"
Shifa Khalifa tun farkon haɗuwarsu yake ƙoƙarin raba ta da Paul. Ya sha gaya mata cewa baya son alaƙarta da shi wai ta dena yawo da shi.
A gabanta yai wa Paul warning akan ya dena kula ƙanwarsa.
Paul ya ce bai isa ba.
Ita Zainab abin ma dariya yake bata. Idan suna gayawa junansu baƙar magana.
Kafin ta karɓi letter a hannun Paul aka kira sunanta. Aminu Zainab Qayyisah.
"Yes" ta faɗa da ƙarfi.
Khalifa ya karɓi letter ɗin saboda ya fita tsayi.
Bari muga ina aka tura ki.
"Khalifa ka bani abuna bana son gulma"
Yai dariya yace "Kuhuhu Village Primary School aka tura ki fa"
Ta fizgi letter har sai da ƙasan ya yage.
"Kaga abinda ka jawo ko"
"Kar ki damu zan printing miki sabo"
Paul ya karɓi letter ɗin yana dubawa.
"Kai bata abunta" Khalifa ya daka wa Paul tsawa.
Paul ya share shi ya ce "Zee you are lucky ooo. This is a big company"
"Kinga Qayyis zo mu tafi su Abba sun shigo"
"Kar ki damu kamfanin Uncle ɗinmu ne. Ba ki da wata matsala, suna biyan corpers ɗinsu sosai"
Su Abba sun shigo?.
Gaskiya ba zata iya haɗuwa da Abba ba. Caɓ! Idan Baba ya ji ta haɗu da Abba ai babu maganar service a Abuja.
"Khalifah barin je na ɗau jakata a masallaci"
"Ki bari ku fara gaisawa da su Abba Dan Allah. Wallahi saboda ke yace zai zo ya ɗaukeni. Har da Maryama suka zo"
Paul yana mata magana Khalifa ya ja hannunta suka bar wajen ta ɗaga masa wayarta tana faɗin zata kira shi.
Sai da suka yi nisa ta tambayi Khalifa ko shi ya working mata posting ɗinta.
Dariya yai ya ƙi ya bata amsa.
"Khalifa ka turawa Abba call-up number na ko?"
"Ke kin cika surutu"
"Yawwa! Ga motan Abba chan"
Salim ne ya tuƙo su. Kafin su iso ma har Maryama ta fito da gudu ta rungumi yayanta tana masa Congratulations.
"Maryama ga Qayyis. Kin tunata? Cousin ɗinmu dake Jos"
"Ba su ne Mamansu ta ƙone a faɗan Jos ba"
Wani kallo Qayyisah ta bita da shi.
Maryama ta yi saurin cewa "Allah ya ƙara mata rahama" tana kallon Qayyisah cikin khakinta daya mata ɗas a jiki. Itama dai saura shekara ɗaya ta fara saka kayan NYSC.
"Assalamu Alaikum" ta miƙa wa Qayyisah hannu ganin har yanzu bata ce mata komai ba.
Qayyisah ta amsa sallamar ƙasa-ƙasa ba tareda ta mata musabaha ba.
Salim ma ya fito yana teasing Khalifa yana ce masa kayan basu masa kyau ba.
Ya kalli ƙayyisa yace "Kopa Smallie ya ne. Longest time fa. The last time dana ganki kina 'yar haka" ya nuna tsayin gwiwarsa.
"Na san ba zaki gane ni ba"
"Taya zan manta ka kuwa, kai ne ana zaune a falo ka sake wani tusa mai shegen ɗoyi har Abba ya koreka a falon"
Khalifa ya saka dariya yana cewa ya tuna lokacin.
"Shegiya abinda kika tuna kawai kenan" yai maganar da jin haushinta.
"Na tuna abubuwa da yawa kada dai a fara tone-tone"
"Shegen bakin kin nan yana nan kenan. Anyways Congratulations"
Khalifa ya ja hannunta suka koma ɗaya gefen wajen inuwa inda Abba ke tsaye yana magana da wani babban mutum da shima ya zo duba 'ya'yansa.
"Abba ga 'yarka na kawo maka ita lafiya"
Qayyisah tayi kasaƙe tana kallonsa. Bai wani chanja ba a yadda ta san shi a baya sai dai ɗan tumbi daya ƙara sai kuma furfura a gemunsa.
"Zainab" ya kira sunanta yana ware mata hannunsa.
A hankali ta matsa jikinsa ya rungumeta yana faɗin "Congratulations my daughter"
Qayyisah ta sauke ajiyar zuciya hawaye na gangaro mata.
Abubuwan da suka faru a baya ne suke mata yawo a ka.
'Yanuwan mahaifiyarta suna da kuɗi amma a lokacin da abubuwa suka rincaɓe musu babu wanda ya tallafa musu sai ma zargin Baba da ake da kashe Umma.
Ba gida da dukiya kawai Baba ya rasa ba. Ya rasa matarsa kuma ya rasa 'yarsa amma basu duba wannan ba.
Su damuwarsu shine Baba ya bari an ƙona ƙanwarsu. As if Baba yana da ikon hana abinda ya faru.
Baba baya gari ma a lokacin ya je Bauchi wani taron wa'azi.
Itama ɗin yau da take raye Allah ne ya rubuta ba za a ƙona shagon da ita ba.
Amma kuma saboda ita an rasa Humairah har abada. Gara Umma an samu gawarta amma Humairah fa?.
"Ya kuke? ya 'yan'uwanki? Zaidu da waye ma"
"Aliyu" ta faɗa tana ƙoƙarin share fiskarta da handkerchief
"Alhaji Kabiru wannan fa 'yata ce itama ta fara service. Ka tuna ƙanwarmu da tayi aure a Jos"
"Wacce ta rasu lokacin faɗan Jos ɗin nan"
Abba ya amsa da eh. Suka shiga bada labarin irin rayukan da aka kashe lokacin faɗan Jos.
Shi Alhaji Kabirun yana tambayar Abba a 2008 ƙanwarsa ta rasu ko 2010. Abba yace 2008 ne.
Dama a kullum in za a kawo maganar Umma to maganar mutuwarta za a yi.
Ita ce ta yi bacci a shagon mijinta aka zo aka ƙona shagon bata farka ba ta mutu a ciki.
Koda yake a da chan ɗin Al-Iqra Bookstore babban shagon saida litattafai ne da yai ƙaurin suna.
Dan haka bayan komai ya lafa labarin ƙona bookstore da kuma mutuwar matar Malam Aminu Mailittafi a ciki ya bazu ko ina.
Allah yayi dai arziƙin Baba da kuma ƙaddararsa shine saida litattafai, amma ba dan haka ba da tun rasuwar Umma da ɓatan Humairah ya haƙura da wannan harka.
Gashi a hankali da wuya da daɗi sun sake buɗe Hawwah Humairah Bookstore kuma Alhamdulillah akwai albarka a ciki.
Kusan minti biyar kafin Abba ya rabu da abokinsa ya maida hankalinsa ga Qayyisah.
Itama ɗin waya take da Paul daya ke ta nemanta saboda sun riga sun samu motar da zata kai su Jos ita suke jira.
"Zainab zaki fara zuwa inda aka posting ɗin ki ko?"
Yanayin yadda yai maganar ya nuna ya san inda aka posting ɗinta.
Dama ta zargi hakan tun daga sanda Khalifa ya gaya mata kamfanin Uncle ɗinsu ne.
"Abba zan koma gida ne, sai next week in shigo in yi documentation"
"Zaki koma gida kuma. Rana yayi Zainab, tafiyar dare babu kyau, hanyar forest ɗin nan ana fashi da dare"
To an zo wajen. Itafa ba zata je ta kwana a gidansa ba.
Ta riga ta gayawa Baba yau zata shiga Jos.
Ina Jos ina Abuja da zai ce wai dare yayi.
"Ki je ki ɗauko jakanki, gobe sai na sa a kai ki gida da sassafe"
Qayyisah ta fara girgiza kai.
"Abba kayi haƙuri Allah mun haɗa tafiya ne kuma akwai saƙon da zan kai wa Baba yau ɗin"
Abba ya kalleta. Ya sani sarai bata son binsu ne.
Da gaskiyarta. Abinda ya riga ya ɓata shekarun baya da suka wuce ba zai gyaru lokaci guda ba. Dole sai dai a bi komai a hankali.
"To shikenan. Ki gaida Babanki da ƙannenki kin ji.
"Ga wannan ki yi kuɗin mota"
"Abba da ka barshi kawai"
Ya kamo hannunta ya saka mata kuɗin a hannu yana faɗin shi Babanta ne.
Ta ɗan risina ta masa godiya.
Khalifah ya ce kafin ta tafi ta tsaya su yi hoto.
Ta gyara tsayuwarta kusa da Abba ya ɗauke su hoto.
Maryama ta shiga suka yi tare. Salim kam ya tafi neman 'yanmata.
Suna gama hotunan ta wuce su bayan ta sake yiwa Abba godiya...
***
©AzizatHamza2023