Free chapter · Read without an account
Twenty three
Page 45-46.
Wannan ya sa take taka tsantsan da kaffa-kaffa da shi, ji take ko da yaushe zai iya kuma zuwa ya mata fiye da haka.
Ramlat ta warke sosai kuma Mamamn ya tsaya kai da fata wajen an sanya ta a makaranta har sai da haƙansa ta cimma ruwa, a islamiyya a ka jefata dan ya ce, "Ƙaranci addini ne ya saka ta take wannan shashancin."
A lokacin kuma Kakale ta zo ita da abokin wasan Ramlat. Duk da cewa zuwan na su ba ta yi murna da shi ba tun da ba su zo akan lokaci ba har sai da tawarke,a cewarta.
Su dai lallashi kawai suke ta sububuɗa mata har sai da ta daina kumfar baki.
Rayuwa na shuɗewa Ramlat sai zuba karatu a ke yi a makaranta.
Wanda da farko ta so kawo wasa amma ganin Mamman na mata ba wasa ya sakata nutsuwa dan duk san da ya dawo sai ya tursa ta gaba ya ji ko ta iya karatun ,in ba ta iya ba kuwa sai ta iya shi a tsaye kuma ta haɗa da wankin banɗaki.
Suna zaune Saudat, Aunty Rahma da Ramlat wadda ta ke bitar karatunta.
Saudat ta kalli Ramlat gami da faɗin,
"Yawwa na tuna ina batun aikin da na saka ki kwana ki daf da za ki kwanta ciwo.?" Ta jefawa Ramlat tambayar.
Ramlat da sarai ta gane in da ta nufa, amma sai ta waske da faɗin,
"Me fa? Wani aiki kuma.?" Ta mayar da mata martani da tambaya.
"Za ma ki waske ne yarinya ,wallahi ba ki yi ba sai na fallasa a siri, har yanzu fa naɗar sautin yana nan ban goge ba."
Da sauri har tana zabura ta ce," Dan Allah da gaske ko da wasa.?"
"Kin ga ina yi miki wasa ne.?" Saudat ta ce.
"Dan Allah ki yi haƙuri zan miki anjima kin ga yanzu bitar darasi na ke kuma in yaya ya dawo ya ji ban iya ba wallahi kashe ni ne kawai ba zai yi ba."
Saidat ta haɗe girar sama da ta ƙasa kana ta ce, "Oh! ba za ki yi ba kenan well, bari ya dawo sai ya yi mai gaba ɗayan."
Ko ta kan Saudat ba ta biba ta miƙe da azama ta haura sama.
Aunty Rahma ta dubi Saudat ta ce, "Wanne aiki ne wannan? Zai fi kyau ki barta bayan yaya ya ji karatun nata ta yi miki, amma kin san halinta in ya bi ba asi ita mai iya juya reshe da ganye ce."
Shiru Saudat ta ɗan yi kafin daga bisa ni ta ce,
"Kuma fa haka ne fa."
"Ah! to da dai ya fi miki."
Ta miƙe da sauri ta bi bayan Ramlat dan tsayar da ita.
Yanzu Ramlat ta juye zuwa hadda in da ganin hakan ya saka Mamman sakata makarantar Boko aka kaita aji biyar wato ss two.
Karatu ta ke yi babu kama hannun yaro, girma ya ƙaru sosai gaɓɓan jikin sun kuma bayyana abin ka da ma sha Allah.
Tun shigarta ta yi ƙawa mai suna Haulat, komai na su suke yi bisa tsari , Ramlat fa an girma wai har wani malami ne ke santa.
Tun daga js two gar zuwanta js three wanda sai a lokacin ke shaida mata, ba tare da ta yi tunanin komai ba ta amshi tayin soyayyarsa.
Ta manta da kashedin Mamman a kan cewa babu kula samari ko da da gajeriyar hirace balle dogowa.
Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya tak ta mai kaya.
Soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakaninsu in da Ramlat ta karɓi lambarsa tun da ba shi da waya. Har ta kai ta kan saci wayar Saudat ta laɓe in da ba za a ganta ba su sha soyayyarsu ita da shi.
Suna gab da fita ya ce mata zai turo magaba ta a yi magana shi so ya ke da zarar sun yi candy ya aureta. Ba ta musa ma shi ba ta ba shi address ɗin gidansu akan ya zo ya gaba tar da kansa.
Watansu biyu da kammalawa ya cika alƙawari ya zo har gidan sai kuma a ka sami a ka si ya gaba tar da kansa gaban MAMAAN a madadin gaban Abi.
Mai ƙosai.