Free chapter · Read without an account
Na huɗu
Page 4
Karaf gwaggwo ta amshe zancen da faɗin,
"La'ilaha ilallah! Yau nake ganin zamani. Lallai ba shakka yarinyar nan ƙwaƙwalwarki ta soma taɓuwa tunda soyayya tasa za ki soma raba gardama damu ko? Nuriyya me ya ke damunki ne?."
Baffa ne ya ce,
"Me kuwa ya ke damunta in banda rashin hankali da shashanci, kuma kin ji na rantse aure ne kam babu fashi sai dai idan ba na raye. Ta shi ki bani waje mara kunyar yarinya"
Ya ƙarasa faɗa cikin fushi haɗi da fusata.
Miƙewa ta yi ta shige ɗakinta yayin da zuciyarta ke rayamata ,
"Kada ta yarda ta aure kowa in ba Nasir ɗinta ba."
Baffa ya kalli gwggwo ya ce,
"Ni kam al'amarin yarinyar nan ya soma ba ni mamaki wannan wace irin soyayyar zamani ce haka? Ɗazu maganar da mu ka yi da Inna ke nan dan na biya ta wajenta, amma a gaskiya na gaya mata ba zan iya karya alƙawarin da na jima da ɗaukarsa ba, shiyasa ita kanta ta ce min "Shawara ta ke son ba ni ba umarni ba."
Gwaggo ta numfasa kana ta ce,
"Ai lamarin nan sai dai mu ce Allah ya kyauta kawai, kuma ba shakka ni ma ina goyan bayanka."
Baffa ya girgiza kai kana ya ce,
"Ameen dai ya rabbi."
__________
YASIR_________
Kwance ya ke, ya zubawa silin da ke saman rufin ɗakinsa manyan idanuwansa masu jan hankalin ƴan mata. Ji ya ke yanzu sam ba abin da ya ke yi masa daɗi, ko kaɗan baya san ganin Nuriyyarsa cikin wani hali .
Ya lumshe idanuwansa a hankali take ƙwaƙwalwarsa ta soma tariyo masa haɗuwarsu ta ɗazu da yadda suka rabu. Idanuwansa suka shiga hango masa yadda ya barta cikin rashin walwala. Ji ya ke inama suna tare da ba yadda zai yi ya barta ta zubar da ko da da ɗigon hawaye.
"In sha Allahu sai na aureki kin zama uwar ƴaƴana my"
Ya furta a hankali tamkar ba ya san yin maganar.
Ummin shi ce ta turo ƙofar ɗakin nasa bakinta ɗauke da sallama.
Ganin siraran hawayen da suka ziraro ta gefen kunnuwansa ya sanyata saurin ƙarasawa inda ya ke kwance.
"Son lafiyarka ƙalau ka ke kuka tamkar ba jarumin ɗana da na sani ba.?"
Sai a lokacin ya ji wata nutsuwa ta ratsa tsokar zuciyarsa jin yadda Ummin nasa ta tambaye shi. Miƙewa ya yi zaune ya jingina da fuskar gadon da yake kwance cikin rauni ya ce,
"Ummi za su raba ni da Nuriyyata. Ummi dan Allah ki sa baki ki taimaka mini zuciyata za ta yi bindiga kada ki rasa tilon ɗan ki ."
Ummi ta sanya hannunta ta shafa sumar dake kwance luf a kansa kafin ta ce,
"My son inaso ka sa ni dukkan tsanani yana tare da sauƙi, sai dai shi sauƙin ya kan daɗe bai zo ba, amma ya kanzo a lokacin ma da ba ayi tsumayinsa ba. Ka sani cewar matar mutum kabarinsa muddin Nuriyya matarka ce to lallai ba shakka ko da sama da ƙasa za su haɗe sai ka aureta. Ka yi haƙuri ka miƙawa Allah lamuranka ka ji ."
Gyaɗa mata kai kwai ya shiga yi tamkar ƙadangare.
"Good ya yi kyau ma za ta shi ka zo ka ci abincinka ka da ya yi sanyi."
Ummi ta ce.
"To Ummi ga ni nan fitowa bari na ɗan watsa ruwa."
Nasir ya ce yana mai ta shi zuwa bayi.
"Ok" kawai Ummi ta ce da shi tana mai ficewa daga ɗakin.
Nasir Adam Fillo. Shi ne ainihin cikakken sunansa. Matashin saurayi mai shekaru talatin da uku a duniya mai ji da kyau mai matuƙar zarra da kwarjini.
A salinsa ɗan gari Adamawa ne amma yanzu suna zaune a garin Kano shi da mahaifiyarsa, amma yana aiki a garin Abuja yana zuwa ne duk sanda aiki ya samu in ta kama kuma ya kanje ya yi kwana huɗu ko ƙasa da haka ya dawo.
Nasir maraya ne ta fannin mahaifi dan tun yana da ƙananun shekaru ya rasu, ba shi da wa ko ƙani shi kaɗai ne wajen iyayensa har lokacin da Allah ya amshi ran mahaifinsa.
Bayan mutuwar mahaifinsa Ummi ta sanya shi a makaranta kasancewar su ɗin suna da rufin asiri duk abin da za ayi in dai da kuɗi ne to tabbas za su yi shi, kuma su ɗin masu neman na kansu ne, ilimi na zamani da na addini ba wanda ba sa da shi hakan ya sanya Ummin na shi sanya shi makarnta dan ya yi karatu.
Yana aji biyar na secondary ta tattara kayanta da komatsanta suka baro garin Adamawa zuwa Kano, dalilin rashin kirkin da dangin mahaifin nasa suke mata na rashin kyautatawa da tsangwama.
Sanda suka dawo ta nemi wata makarantar ta sanya shi ita kuma ta ja jari da kuɗin ta taho da su a hannunta, ta kuma siya musu ɗan ƙaramin gida.
San da Nasir ya yi wayo da hankali ya gane abin da ahlin na sa suka musu sai ya ji kaf ɗinsu ya tsanesu ba ya san zuwa inda suke ko kaɗan itama Ummin ganin in ta yi masa magana baya so sai ta dai na yi masa maganar .
Nasir ya yi karatu iya karatu inda ya zama cikakken lawyer, baya aikin gwamnati yana aikinsa ne a ƙarƙashen kansa da kansa kuma suna da kafaffiyar ƙungiya wanda shi ne shugaba kuma shi ne ya kafata a garin Abuja.
Bayan ya soma gina kansa ya je har Adamawa ya sa aka raba gado aka ba shi nasa da na Umminsa ya sai da ya dawo Kano ya kafa kasuwancinsa inda Allah ya ɗaukaka shi matuƙa albarka ta riƙa yaɗuwa a gare shi.
Nasir tun yarintar shi bayan rasuwar mahaifinshi bai san wata kulawa da soyayya ba in banda wacca ya samu daga wajen mahaifiyarsa danginsa kam babu batun wannan maganar daga garesu.
Akwai shi da halin dattako duk da ƙarancin shekarunsa, mutum ne shi mai sauƙin kai amma ta wani fannin yana da wuyar sha'ani.
Asalin sunan mahifinshi shi ne ADAM ADNAN FILLO shi ne familyn suke amfani da FILLO amadadin ADNAN. Mahaifiyarsa kuwa sunanta Aisha Ahmad.
*******
Sanye yake da wani irin haɗaɗɗen yadi mai matuƙar kyau, uwa uba yadda yadin ya matuƙar karbar jikinsa.
Sauri ya ke sosai tamkar zai ta shi sama wanda hakan ya samo asali ne dan son ganin masoyiyarsa.
Kamar daga sama ya ji an ce,
"Yaya Nasir "
Juyowa ya yi dan san ganin muryar da ta ambato sunansa, ganin fuskarta ya sanya shi murtuke tasa fuskar tamkar bai taɓa sanin mece ce fara'a ba.
Ƙarasowa ta yi inda ya ke tsaye cikin yalwar fara'a da ɗoki ta ce,
"Yaya Nasir ina za ka haka kake ta faman sauri?."
Ya kuma haɗe fuska kana ya ce,
"Ba hurumin ki ba ne ba, ba sai kin san inda za ni ba saurin da na ke kuma bai shafeki ba."
Ta ɗanyi guntun murmushi mai cin rai kana ta ce,
"Haba yaya Nasir. Yanzu dan na tambayeka shi ne kake tada jijiyoyin wuya ni fa kawai tambaya na yi."
"Ya isa haka Nusaiba, ya kamata ki san irin kalar ɗakin da za ki shiga ba kowanne ɗaki a ke shiga a sami fadar wajen zama ba."
Yana ida faɗin haka ya yi gaba abinsa .
Ita kam ƙwafa ta yi tare da faɗin,
“Wallahil azeem yau ɗin nan ko saurin me kake yi sai ka saurareni, kai sai na san ma uban me ka kewa saurin." Tana gama faɗin haka ta mara masa baya.
Nusaiba ke nan ƴa ga kawunsa wanda suke ƴan wa da ƙani ga mahaifinsa shi kaɗai ne ya biyosu bayan Nasir ya je da buƙatar kuɗin gadonsu, shi ne ya biyo shi shi ma ya sami gida ya zauna lokacin shekarar Nusaiba 17 a duniya. Ita kam ala dole sonsa ta ke yi.
Yana isa bayan layin gidansu Nuriyya ya tadda ta zaune kan dakalin da suka saba zama kansa su sha soyayyarsu.
Sai waige-waige ta ke yi ta ga ta inda sahibinta zai ɓullo. Hango shin da ta yi ya sanya ta ɗan haɗe fuska.
Kama kunnensa ya yi duka biyun da hannayensa biyu alamar neman afuwa.
"Tuba na ke ranki shi daɗe na tsaya wajen Ummi ne ita ce ta riƙe ni plz amin afuwa."
Nuriyya ta kalle shi kana ta ce,
"Ba wani nan kawai dai za ka fake da Ummi dan na haƙura."
Nasir ya rausayar da kai kafin ya ce,
"Da gaske na ke sarauniyata amin afuwa."
Ta ɗan yi murmushi kana ta ce,
"To shi kenan na ji ya wuce"
Ya matso daf da ita tare da faɗin,
"To ki ɗanyi min dariya mana sai na ji sanyi a cikin birnin zuciyata."
Ya faɗa cike da tsokana.
Dariya ta yi kana ta ce,
"Kai dai yaya Nasir ka cika wayo Allah."
"Yo to in banda abin gimbiya ai dole na koyi wayo haka kurum na je na zama gaula wani ya sace min zuciyar masoyiyata."
Nasir ya ce.
Nuriyya ta yi murmushi kan ta ce,
" Wallahi har yanzu babu wanda zai iya sace zuciyar Nuriyya, zuciyata tana tsananin kasantuwa da kai, kai ne mahaɗinta bugunta bugun zuciyarka ne."
Nasir ya lumshe manyan idanuwansa kafin ya ce,
"An gaida sarauniyar birnin masarautar da ke mulkar cikin birnin zuciyata. Shiyasa kullum na ke ƙara jin mararin sanki a cikin ƙahon zuciyata, Ina sanki my ina ƙaunarki."
Mai ƙosai.