Free chapter · Read without an account

1

by Noorul Huda · DAHLIAS: HAUSA NOVEL

Ko wace alaƙa tana da mafari. Tana da asali. Tana da dalili. A karƙashin ko wacce alaƙa dole zaka samu wani al'amari da asali shi ya fara shimfiɗata, kuma shi ne silar wanzuwarta. Tasu alaƙar ta fara ne a ranar da aka kafe musu sakamon jarabawarsu da suka zana ta first semester, lokacin data ɗaga ɗan siririn yatsanta manuniya ta zana wani layi daga kan registration number dake ƙasan tata har zuwa can gefe da aka buga GPA ɗin da kowa yaci. Daga kan GPA ɗin ta sake jan yatsan nata baya, tana sake tisa wannan layin zuwa registration number dai. Bata san daƙiƙa nawa ta ɓata ba, ta san dai students da dama sun zo sun tafi yayin da yatsanta keta kaiwa da dawowa yana tisa wannan layin dai. Daga bayanta kaɗan taji furucin wani.


“1.1 kika ci. Sai kuma CO guda biyu”


Wata ƙila shima ya lura adadin yawon da yatsanta ke yi ya fara wuce ƙima shi yasa ya kasa haƙuri har sai da ya ƙara jaddada mata points din. Wata ƙila kuma ya zaci bata iya karatu bane shi yasa kawai yaga gara ya faɗa matan, kuma cikin harshen Hausa, tunda wanda bai iya karatu ba, zaiyi wuya ace yana jin turanci.


Yatsan nata ta lanƙwashe ta mayar cikin ragowar ƴan uwanshi dake dunƙule sannan taja gefe ta tsaya, idonta kafe a kan wata bishiyar darbejiya dake can tsallaken titi kai kace cikin ganyayyakin bishiyar zata samu ɗaya tak da zai mata bayanin dalilin da yasa yaci wannan mummunan points ɗin.


“1.1 kika ci. Sai kuma CO guda biyu”


Kalaman mutumin nan suka sake dawo mata lokacin daya raɓa ta gefenta ya wuce. Fuskarshi cike da walwala. Daga gani result ɗinshi yayi kyau sosai. Ko da yake itama kamata yayi ta koma gida da irin tashi fuskar. Kamata yayi ta shiga gida da tsantar farin ciki da kuma alfahari. Ta rungume Mum ta faɗa mata results ɗinta. Idan daddy ya dawo da daddare kuma ta same shi a parlourn shi tace masa taci 5.0 points kamar yadda tayi masa alƙawari. Shi kuma sai ya dakatar da shan black tea ɗinshi, ya ajiye saucer cup ɗin dake ɗauke da black tea ɗin a kan center table, ya ajiye jaridar hannunshi,ya zare glasses ɗinshi sannan ya dubeta ya kuma ce mata zai cika alƙawarinshi tunda ita ma ta cika nata.


To amma result ɗinshi data gani yanzu ba zai bari tayi ko ɗaya daga cikin abinda ya kamata ta yin ba. Karo na farko a tarihin rayuwarta da gashi dai tayi nasara a jarabawa amma kuma bata jin nasarar har cikin ranta. Cikin sanyin jiki da rashin walwala ta fara taka ƙafafunta. Gurin notice board ɗin dake ɗauke da result ɗin nasu ta bari sannan ta nufi wannan twin theatre ta IBRAHIM HALILU UMAR.


Kamar kullum ɗan ƙaramin shagon dake cikin theatre cike yake maƙil da customers. Kowa da abinda yake son siya. Ƙamshin abinci kala kala na tashi musamman awara da ƙwai da ake soyawa. Ta gabanta wasu samari guda biyu suka wuce, hannun ko wannen su ɗauke da kofin shayi dake fitar da tiriri. Shayin dai baƙi ne kuma yayi mata kama da wanda daddy ke sha kullum da daddare. Mum ce take dafa masa. Bata saka masa madara ko milo sai dai tayi ɓarnar kayan ƙamshi wajen sarrafa shi. Bayan ta gama dafawa kuma sai ta juye cikin tea pot. Idan zata kai masa, sai ta ɗora a kan tray sannan ta jera saucer cups guda biyu a kai cikin jeren da ita kaɗai ta san yadda take abunta. 


Haka ta cigaba da ratsawa ta cikin mutanen da keta kai kawo har ta ƙarasa cikin ɗaya daga theatres ɗin dake ɓangaren hagu. A nan suke yawancin lectures ɗinsu. Samun kanta tayi da takawa zuwa jerin kujerun dake ɓangaren dama. A jerin farko ta ja ta tsaya, sannan ta zauna a kan kujerar farko kuma ta gefe. Ido ta zubawa kujera ta biyu, kujerar dake gefenta yayin da tuninta ya harba wasu watanni baya, ranar data fara ganinsa.


Ranar litinin ce, tushen aiki, ranar da yawancin ma'aikata ke komawa bakin aiki. Lecture Organic Chemistry ce da ita 8 na safe. Lokacin da agogon parlourn ya buga ƙarfe bakwai na safe, lokacin motar Yaya Mahmoud ta buga mata wani irin wawan horn. Dole ta ture ragowar shayin da take sha gefe sannan ta miƙe ta haɗa litattafanta tayi wa Mum sallama ta fita. Yaya Mahmoud, yayanta na biyu a gidan ne zai ajiyeta sannan ya wuce gurin aikinshi. Mahmoud Turaki irin mutanen nan ne da ko bature ba zai nuna musu punctuality ba. Yana da girmama lokaci da kuma san yin abu bisa ƙa'ida. Electrical Engineer ne. Co-founder na company nan na TURAKI HOLDINGS.


Yana mita, huci da harare harare dai haka ya tuƙata har cikin Jami'ar Bayero. A bakin IBRAHIM HALILU UMAR TWIN THEATRE ya ajiyeta sannan ya juya ya tafi. Ba tayi tunanin ana buɗe theatre da wuri ba. Ta dubi agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta. Ƙarfe bakwai da mintuna ashirin da biyar. Bin bayan students ɗin da taga sun shiga ciki tayi. A ɓangaren hagu ta zauna. Theatre wayam babu students da yawa dan kwata kwata basu fi su biyar ba. Sai kawai ta zauna shiru tana tunanin rashin lafiyar Malam Idi, drivern ta. Jiya da daddare ya aiko babban ɗanshi Habibu ya faɗa musu ba zai iya zuwa yau ɗin ba saboda zazzaɓi daya rufe shi. Kullum shi yake kawota ya kuma jira har sai ta gama lectures sannan ya maida ita gida. Takwas saura suke barin gida kuma kafin takwas ɗin sun isa. To daga Lugard Avenue ne fa zuwa BUK Old Site, kwata kwata tafiyar ba tafi ta minti ashirin ba. 


A karo na ba adadi ta kuma kallon matashin dake zaune a kujera ta biyu, jeri na farko a ɓangaren dama. Bata iya ganin fuskar shi tunda ya bata baya. Bata daɗe da zuwa ba yazo kuma tunda yazo yake duba littafin da taga ya zaro daga aljihu. Da yazo bai kula kowa ba sannan babu wanda ya kula shi cikin waɗanda suka zo bayanshi. Shi kaɗai ne zaune a wannan jerin farkon har lecturer, Dr Dutse ya shigo, lokacin har takwas ta gota.


Jefi jefi take ɗaga ido ta kalleshi. Ba sa mishi ido tayi ba. Allah Ya kiyaye ta saka wa wani ido, ta sakawa course mate ɗinta ido. Kawai dai yadda har yanzu kusan awa ɗaya da fara lecture tasu amma babu wanda ya zauna a kujerar dake gefen damanshi na dama da hagu ne ya tilasta mata yawan kallonshi. Wata ƙila Zuhra Turaki bata sani bane amma akwai wani dalilin, akwai wani dalilin da yake jan idanunta gareshi ya kuma tilasta mata yawan kallonshi. Lokaci! Lokaci ne zai faɗa mata!


Bayan Dr Dutse ya fita, taso taje ta same shi, taga fuskar shi ta kuma ji sunanshi walalla ta iya gane dalilin da ya hana kowa zama a kujerun kusa da shi. Jidda Khalil, wata ƙawarta guda ɗaya kaf faɗin ajin ce ta tsayar da ita.


“Kinga Zuhra bani note ɗinki nayi snapping anjima sai na kwafa”


Note ɗin ta zaro cikin ƴan books ɗin dake rungume a hannunta. Kullum tana riga Jiddan zuwa kuma idan tazo tana ajiye mata seat a kusa da ita. Idan lecturer ya shigo kuma bata ƙaraso ba, duk wanda ya tambaya tana bar masa seat ɗin, duk sanda Jiddan ta zo sai ta zauna a wani seat ɗin daban. Jiddan ta sha yi mata ƙorafi a kan ta rinƙa ajiye mata, ta daina bayar dashi, duk wanda ya tambaya tace akwai mai shi kuma kar ta bari kowa ya zauna har sai tazo ko da kuma bayan an shafe awa ɗaya ne zata zauna abinta. To amma Zuhra Turaki ba zata iya ba, tana da sanyi ainun da rashin son jayayya balle kuma masifa ko faɗa da hayaniya. Shi yasa duk wanda ya tambayeta kawai sai tace babu kowa, sai kawai ta janye littafin da take tare seat ɗin da shi wani ya zauna. 


Bayan ta miƙa mata note ɗin sai da ta maimaita mata ƙorafin data saba. Ƙorafin da zuwa yanzu Zuhra Turaki ta riga ta haddace shi.


“Zuhra kiyiwa Allah ki daina bayar min da seat. Na san yau ma kin ajiye min amma kuma kika bayar. Yanzu gashi saboda zaman da nayi a baya ko note ban samu nayi ba.”


“Na daina Jidda.”


Tana jin Jiddan na cigaba da mita amma bata tanka mata ba. Seat ɗin daya zauna ta kuma kalla amma sai taga wayam. Baya nan. Har ya tafi gida kenan? Bata tambayi sunanshi ba. Bata ga fuskarshi ba. Bata gane dalilin ba. 


Tun daga wannan ranar ta rasa nutsuwarta. Kullum ta shiga BUK sai ta neme shi ko zata sake ganinshi. Sai da aka shafe sati uku sannan ta sake ganinshi a lecture Organic Chemistry dai. Ranar ma a wannan seat ɗin ya zauna. Seat na biyu, jeri na farko a ɓangaren dama. Ranar ma babu wanda ya zauna a gefenshi, bata ga ya kula kowa ba kuma babu wanda ya kula shi. A ranar ta samu taga fuskarshi kuma wannan ganin na fuskarshi data yi na ɗaya daga cikin ababen da suka ingizata har ta rasa sukuni sai da ta gano registration number shi da sunanshi. 


“Umar Faruk!” Haka Class Rep ɗinsu ya faɗa mata lokacin data tambayeshi.


Ringing ɗin wayarta ne ya katse mata tunaninta. Cikin sanyinta ta ɗaga wayar ta kara a kunneta na hagu


“Hello Mum”


“Zuhra har yanzu result ɗin ne baki dubo ba? Kin san fa jiranki nake”


“I'm sorry Mum yanzu zamu taho.”


Bayan ta katse wayar sai ta sake duba seat ɗin gefenta na hagu. Wannan seat ɗin dai da akai kullum yake zama. Seat na biyu, jeri na farko a ɓangaren dama!


Bayan ta fita daga theatre kai tsaye inda Malam Idi yayi parking ta nufa. Yana kuwa cikin motar yana jiranta, ya buɗe kofar gefenshi yana shan iska yayin da radio keta faman aikinta. Tana shiga ya bawa motar wuta suka fara tafiya. Tana so tace masa ya kashe radion ko kuma ya rage volume to amma tana jin nauyin shi. Sai kawai tayi shiru tana sauraren waƙar da aka saka a gidan radion. Waƙar Ni da Ke Mun Dace ce wadda Umar M Shariff ya rera. Waƙar sai ta tuna mata da wani biki data taɓa raka Mum. Bikin ƴar wata ƙawarsu Mum ce, Hajiya Mariya. A wannan bikin ta fara jin wannan waƙar. Tunanin Zuhra Turaki bai tsaya a wannan bikin ba, sai ya cigaba da tafiya baya har zuwa farkon dawowarsu Kano daga Jalingo, lokacin Malam Ɗahiru ne drivern ta ba Malam Idi ba, lokacin flowers ɗin da aka shuka a farfajiyar gidansu basu ciko sosai ba, lokacin a primary school take bata shigo jami'ar Bayero ba sannan babu mangwaron data gani yanzu an kasa a bakin titi ana siyarwa.


©Noorul Huda










Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.