Free chapter · Read without an account
Na sha huɗu
*ƘADDARATA CE A HAKA*
©Maryam Abdulaziz_Maiƙosai(Matar Abdul)
P_14
“Amma dai kai ni kam baka da tausayi da imani ko kaɗan. Mutumin dake kan siradin rayuwa da mutuwa kakewa wannan batun, idan har sannu ba ta sadaka da shi to baka yi wani furucin a gare shi ba. Yanuz kai ka yarda da abin da ake tuhumar da baban ita Nuriyyan?”
Idris ya masa kallon mahaukaci kafin ya ce, “Ai da yake kai gidahumi ne ba, yo ga zahirin abu kana gani kake neman kaucewa gaskiya. Bai aikata ba ai ba za a tuhumeshi da hakan ba.”
Saurayin ya girgiza kansa kafin ya sake furta, “ Kuma a haka kake cewa kana son diyarsa?"
A fusa ce Idris ya yo kansa tamkar zai rufe shi da duka, “Kaga malam ja tsumman rigarka ka bar wajen nan ko na yi maka kwalliya a fuska ka koma dan daudu yanzun nan.”
Ba tare da saurayin ya sake Magana ba yaja ‘yan matan kafafuwansa ya bar wajen, domin ya san halin Idris idan rashin kirkinsa ya motsa babu wanda yake ragwantawa.
Nasir.
Kwanansa uku yana baci bai motsa ba, hakan kuma ya samo asali ne ga doguwar suman da ya shiga, duk da cewa likitoci sun ba su tabbacin zai farka amma dukansu zukatansu sun tsinke.
Nuriyya kuwa ji take yi tamkar an zuba mata garwashi a kirjinta, so take yi kawai Nasir ya bude idanunsa ya yi arba da nata idanun cikin nasa. Idan ta kalleshi ta jikin tagar dakin da yake ciki ko kuma ta sami iznin ganin shi tausayinsa sake nunkaya yake cikin zuciyarta, ya rame ya zama tamkar wanda ya yi jinyar shekaru, tamkar ba Nasir dinta ba, ya yi duhu sosai idan har ba ka yi masa farin sani ba to ba za ka iya cewa Nasir ne kwance ba. An yi bandejin wuyanshi,yayin da hannunshi na dama ke naɗe da bandeji tun daga kan kafadarshi, kafafunsa kuwa duka rauni ne a jikinsu hatta da kansa sai da ya sha naɗin bandeji. Tilas idan ka yi tozali da Nasir ka tausaya mishi.
Baffa.
Yaune aka zauna zaman karshe a koto, inda kuma koto ta yankewa Baffa hukuncin zaman gidan kaso har na tsawon rayuwarsa, bisa tuhumarsa da ake yi kan kasha wasu da kuma raunata wasu ta hanyar sanya hannu a shigo da gurɓataccen magani. Rashin samun lauya ya sanya dole aminta da hukuncin da koton ta yi masa, domin sun gaza samun mai tsayawa Baffa wanda zai kare shi har gaskiya ta bayyana, ko da yake tabbas ta sani ciki da gaskiya wuka ba tataba huda shi’ kuma in sha Allahu sai gaskiyar ta bayyana ba zai kare rayuwarsa cikin gidan kurku ba. Ana fitowa da shi dan tafiya gidan kason da aka tanadar masa, mutane suka yo kansa, wasu na aika masa duka, wasu na kai masa jifa da takalma da abin da ya sawwaka. Da gudu Nuriyya ta yi cikin cincurodin mutanen ta shiga kutsawa a kokarinta na san tarewa mahaifin nata abin da mutane ke yi masa, da kyar ‘yansanda suka shawo kan al’amarin bayan sanya Baffa cikin mota, shi kuwa babu abin da yake yi sai zubar da hawaye, zuciyarsa na yi masa suka.
Zuciyarta ta yi mata ƙuna, wani daci na mamaye ilahirin bakinta, yayin da ta ji wani abu ya tokare makwallaton wuyanta, kirjinta ya yi mata nauyi sosai tamkar wacca aka dorawa buhun siminti biyu. So take yi ko yaya ta zubar da hawaye ko ta sami sa’adar radadi da zafin da take ji amma ta gaza yin hakan. Ashe ma hawaye rahma ne?
“Ya Allah duk wanda yake da hannun a kan halin da Baffana ya shiga ka hana shi kwanciyar hankali, ka sanya masa rashin nutsuwa da wadatar zuci har sai ya bayyana kansa.” Ta rushe da matsanan cin kuka tare da durkushewa kasa, kowa kuka yake yi a cikin gidan, yau gidan tamkar na makoki haka ya koma.
***
Bayan kwana hudu da faruwar wannan al’amari Munira ta yi sallama gidansu Nuriyya tare da tambayarta ko ta je wajen Nasir kuwa?”
“Allah na gani bazan iya jurar ganin halin da Nasir ke ciki ba, zuciyata ta yi rauni abubuwa da yawa sun rufta mata Munira a yanzu ta kai makura ba za ta iya daukar wani abu bayan waɗancan ba.”
Munira ta ɗan numfasa tabbas tasan ƙawarta ta tana cikin waani yanayi amma ya za ta yi haka za ta daure tana dan zuwa tana duba shi, ko dai addu’arta ya samu ai ta yi.
“Na sani amma duk da haka ki daure, ina so idan ya farka ya soma zira idanunsa cikin naki yadda zai ji kwari har ya iya magantuwa.”
Ta kara numfasawa kana ta sake cewa, “Kuma koba komai za ki dinga debewa Ummi kewa, na san yanzu haka tana can kuma ita kadai ce “
Ta mike ba tare da ta tankawa Muniran ba ta janyo hijabinta ta sanya kana ta ce, “ Mu je asibitin”
Sunyi zugun-zugun tamkar masu zaman makoki, a haka su Nuriyya suka shigo asibitin suka iske su.
Bayan sun gaisa Ummi ta sake yi musu jajen halin da Baffan nata ya tsinci kansa ciki.
“Hasbunallahu wani’imal wakil” shi ne furucin da ya doki dodan kunnuwansu. Da sauri suka nufi inda Nasir din ke kwance. “Nasir” Ummi ta kira sunan shi.
“Nasir” Ta sake kiran shi a karo na biyun daidai saitin kunnen shi. Yayin da shi kuma ya soma maganganu masu karya zuciyar mai sauraro, “Tausayin Ummina kawai nake yi zan mutu na barta, Allah kada ka sa na riga Ummina tafiya na barta cikin waannan duniyar da babu tarin komai sai kunci da bakin ciki, ina tausayin Nuriyya na ci burin aurenki Nuriyya sai dai kaddara ta riga ta shata mana layi, ga shi zan mutu ban sami tsatso daga jikinki ba, na so a ce na samar da zuri’a daga jikinki. Ina sonki kada ki rabu da ni ko bayan raina ki kasance a tare daa ni, ki yi mini alkawari za ki zama matata a lahir…” Gaba dayansu kuka ne ya kufcee musu irin kalmomin da Nasir ke furzarwa sosai suka kama zukatansu musamman Nuriyya da take jin idan babu shi itama ba za ta iya yin wannan rayuwar ba.
“Ji nake tamkar na cire ciwon dake rataye da kai na dawo da shi kaina yaya Nasir dina, ina sonka zan kuma aureka na kasance tare da kai ko da shi ne silar fiewar numfashina na karshe”
Ummi ce ta kai dubanta ga su Hamza kana ta ce, “ Ku dan ba mu waje mu ga ni” Babu musu suka saka kai suka fice aka bar Ummi da Nuriyya kadai a dakin. Nuriyya kuwa gefen kirjinsa ta samu ta kwantar da kanta tana mai shasshekar kuka.
“Ki daina yi mini kuka, addu’a za ki yi mini”
Ummi ta sake matsawa gare shi kana t ace, “Tana yi maka, haka kowa ma yana yi maka Nasir. Buɗe idanunka ka kalle ni.” Bai ce komai bai kuma aiwatar da abin da ta umarce shin ba, haka ya sake bata damar sake furta masa, “Bude idanunka ka dube ni Nasir daure ka ji.’
Ya soma kokarin bude idanuwan na shi tamkar dan koyo.
“Yawwa maza bude su ka gani duk mutanen da kake so ne, kake da muradi gabanka.” Ummi ta ce.
Ya rumtse idanun ya sake kokarin budesu a hankalin ya waresu tar.
“Ka gane ni? Wace ce ni?” Ummi ta jefa masa tambayoyin.
“Ummi” Ya furta a hankali. “Wace ce wannan?” Ta yi nuni da Nuriyya da da tun ɗazu take kallon fuskarsa. “Nuriyya ce” Ya bata amsa da hakan.
“Alhamdulillah! “ Ummi ta ce, yayin da Nasir ya sake rufe idanun shi tare da sake budewa. In kiya ta yiwa Nuriyya akan taje ta kira mata su Hamza, babu musu ta fice sai ga su sun dawo a tare.
“Alhamdulillah! Nasir ya farka ba tare da wata wahalar ba, kai Ahmad je ka sanar da likitan dake kula da shi ko”
Cikin tsananin farin ciki Ahmad ya saka kai ya fita bakinsa ya gaza rufuwa. Bai wani dade ba ya dawo, nan likita ya shiga duba shi, ganin komai daidai ya dube su kana ya ce,
“ Alhamdulillah! Ya farka kuma komai daidai, sai dai duk da haka ba a bukatar yawaita sanya shi Magana ko doguwar Magana ma, sannan har ya kai sati guda abincin ta robar da aka sanya masa za a dinga ba shi sannan mai dɗan ruwa-ruwa kuma maras nauyi kamar su shayi da makamantansu.”
Ya juya yana mai barin dakin.
Maiƙosai✍🏼