Free chapter · Read without an account

Page 4

by Halimatou Khabir · MUGUN NUFI!

*MUGUN NUFI*


     ©️ *Nana Haleema.*


*Page 4*


Ana idar da sallar i'sha dukkanin su suka hallara gabad'aya su ana cin abinci, Tasleem da Ahmad ne kawai babu a wajan sai daga baya suka shigo tare ya canja kaya zuwa marasa nauyi da alama har wanka yayi. Can gefe ya nema ya zauna Tasleem ta zauna a kusa dashi duk sukayi shiru babu mai magana a cikin su sai sautin cokali da yake tashi.


  Zuciyar sa yaji tana tashi dan yasan daman dole yayi amai abinda yaci d'azu hakan ya saka yake ta yatsine fuska, Mamy ta kalle shi tace, "Ya dai Ahmad?." Kallon ta yayi ya girgiza kai alamun babu komai. 


Dada ta ja tsaki tace, "Yo ke daman ina ke ina shiga shirgin wannan mutumin? Shi ba gwanin ta ake masa ba komai kika yi ba dai-dai ba." Kallon ta yayi ya mayar da idon sa ya lumshe yana jin yadda aman yake taso masa sosai. Anty Lubna da take kallon sa tace, "Kamar dai baka da lafiya ko?". Bai bud'e ido ba ya girgiza mata kai itama alamun a'a.


Abie yace, "Ahmad d'azu kunyi meeting da mutanen Germany baka fad'a yadda kuka yi dasu ba." Sai a sannan ya bud'e ido ya mik'e zaune sosai ya kalle su yace, "Abinda na shigo na sanar daku kenan d'azu aka d'auke min hankali, sun bani project d'in daga nan zuwa wata d'aya zan kai musu in yayi yadda ake so zasu cika alqawarin da suka d'auka na zuba hannun jari a b'angaren sarrafa magani" ya k'arasa fad'a yana cize baki sosai yake jin cikin sa yana juyawa.


  "Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya bada nasara" Abie ya fad'a da farin ciki a fuskar sa ya amsa da Amin kafin Abbah yace, "Mima kuwa ta samu shiga meeting d'in?, Mima lokacin da kika je kin samu shiga?" Ya fad'a yana kallon ta. D'ago kai tayi tace, "lokacin da naje basu jima da farawa ba na shiga ya koro ni a gaban kowa ana ta min dariya" ta k'arasa hawaye na sakko mata daman akan gab'a kukan nata yake.


"Mtsww, Ahmad me yasa kake yiwa k'anwar ka haka ne? Na sani tun farko ba son aiki kake da ita a waje d'aya ba tunda muka saka baki ai ya kamata ka dinga d'aga mata k'afa." Yaya Sulaiman da ya mik'e yana niyar tafiya yace, "itama fa Abbah da laifin ta kasan halin Mima da rashin kunya ta raina Ahmad kamar ba Yayan ta ba."


"Daman ai ko ruwa ta fad'a sai kun ce ta Tayar da k'ura, shi bakwa ganin laifin sa a koda yaushe sai ita? Ba shine babba ba shi ya kamata ya dinga jan girman sa" Hajiya Dada ta fad'a tana hararar Yaya Sulaiman. Y'ar dariya yayi yace, "Allah ya baki Hak'uri, ni kinga tafiya ta ma."


Ihu mai had'e da murna da Anty Lubna tayi ya sanya kowa kallon ta banda Ahmad da kansa ya sara ya dafe kai yana jin aman na k'ara tawowa bakin sa, Mummy ta kalle ta tace, "Ke kuma Lafiya?."

Hannun ta har rawa yake tace, "Ina seeds d'in da Ahmad ya samo yace zaiyi maganin ciwon kansar kwakwalwa? Kin ganshi yanzu w.h.o sun yi approving d'in sa an tabbatar da Ingancin sa an kuma tabbata zaiyi maganin ciwon, Abie kalli America, Germany, India, Egypt neman Ahmad suke akan ya siyar musu da seed d'in su sarrafa shi" ta fad'a da murna sosai tana nunawa Abie labaran.


"Alhamdulilah!, Alhamdulilah!!, ma sha Allah" shine abinda mutanen falon suke fad'a ko wanne da farin ciki a fuskar sa. Yaya Bello ya kalle shi ya k'arasa inda yake ya bugi kafad'ar sa yace, "Congratulations bro, ka kasance abin alhari ga dangin mu baki d'aya bama iya gidan nan ba, ina taya ka murna." 


Har lokacin idanun Ahmad a kulle yake yana jin su amma baya tunanin zai iya furta komai, Yaya Mubarak yace, "Kai kaji illar ka Ana maka magana kayi kunne uwar shegu kamar baka ji ba." Dada tace, "Ku wallahi kuna bani mamaki kamar kuna mantawa da waye a zaune, shi ai ba'a masa gwaninta ko kad'an ku gama murnar a sanar dani abinda yake faruwa."


Yaya Sulaiman zai sake yin magana suka ga ya mik'e tsaye ya k'arasa ina sink yake yana amai mara sauti, dukkan su kallon sa suke Mamy tace, "Nidai tunda na gan sa nasan bashi da lafiya, abinda yaci dan ya farantawa Tasleem ne gashi nan ya jawo masa amai." Hankalin Tasleem ya tashi ta k'arasa kusa dashi ta fara kuka tana fad'in, "Kayi Hak'uri Yaya Dr bazan sake bari kaci ba." Ruwan ya kunna ya wanke fuskar sa ya jima a tsaye yana sauke numfashi kafin ya mik'e ya fara takowa, yazo gab da Mima yaji tace, "Allah ya k'ara, inda zaka dinga cutar kullum ai da naji dad'i." 


Kamar bai jita ba ya wuce ya zauna Tasleem na biye dashi tana goge hawaye, kallon idanun ta yayi ya girgiza mata kai alamun ta daina kuka, cikin kukan tace, "To ba nice na saka kaci abinda ya saka ka amai ba." Murmushi ya mata kawai dan lokaci daya yaji bama ya son furta ko wacce irin kalma.


Abie ya kalle shi yace, "kaje ka samu ka huta nasan gobe kana da bak'i sosai kar abubuwa suyi maka yawa." Kallon Abie yayi yace, "No Abie I'm okay, Anty Lubna wacce gidan jarida ne sukayi posting?."


"Gidan jaridar BBC ne, ga daily trust ma naga sun saka, kaga CNN ma yaro ya zaka celeb" ta k'arasa fad'a da murmushi. Shima murmushin yayi yace, "Za dai mu gani."


Abbah yace, "To maza ku wuce ku tafi gida dare yayi, ke Lubna kin fisu nisa amma kin zauna kina hira." Dariya kawai tayi kafin dukkan su su mik'e suyi sallama ko wanne ya tafi gidan sa.


Shima mik'ewa yayi yace, "Abbah, Abie, Mummy na and Mamy na sai da safe" ya fad'a yana kallon su kafin ya dawo da kallon sa ga Tasleem ya sakar mata murmushin da ita kad'ai yake yiwa ya sunkuya ya mata peck a goshi ya juya da niyar tafiya. 

"Da baka yi min sai da safe ba zan tashi lafiya da izinin Allah in kaga dama ba cewar ka nake nema ba, kuma billahillazi in baka daina mana dabi'ar turawa a gidan nan ba sai ranka ya b'aci, gansamemen baligi da kai ka dinga kama goshi yarinya kana sunbata?, ku kuma da yake bakwa ganin laifin sa babu Wanda ya tsawatar masa kun zuba masa ido kuna kallon sa" ta k'arasa fad'a a hasale tana hararar su duka.


Murmushi Ahmad yayi me sauti daman yasan sai anyi haka ya juyo ya kalle ta yace, "haushi kika ji dai ban miki sai da safe ba ko?." Hararar sa tayi tace, "Uwar haushi da uban sa naji ba haushin kansa ba, kuma....." dakatar da ita yayi da fad'in, "Da kin fad'i gaskiya dana yi miki Wanda yafi nasu ma."


Sai kuwa tayi dariya tace, "Yo kaji d'an nema ba dole naji haushi ba ka kula kowa ka share ni." Dariya ta bashi yayi dariya mai sauti kad'an kafin ya daure fuska yace, "To bazan miki ba ai bake kika haifan ba." Abbah da yake jin su da kallon su ya yiwa Ahmad dakuwa yace, "Ahmad karb'i nan, shige ka fice ka bamu waje."


"Barni dashi yau dai-dai nake dashi kome yace ina da amsa, da bani na haife ka ba ai ni na haifi uban ka ko?" Ta fad'a a fusace. D'aure fuska ya kuma yi yace, "Kifa daina cewa ubana, kice mahaifi na in kika ce ubana zagi na fa kika yi?."

"Na zage ka ko zaka rama ne?."


Mummy tace, "Ahmad wai baza ka bar wajan nan ba?." Baice komai ba ya dawo da baya zuwa inda take zaune batayi tsamani ba taji ya mata kiss a kumatu. Sak tayi tana kallon sa ta kasa furta komai ya d'aga mata gira yace, "Kin tuna da tsohon mijin ki ko?" Ya fad'a yana sake daga mata girar sa a tare. Ganin ya kashe bakin ta ya saka shi ya sake cewa, "Wai tsohuwa ma tasan soyayya" ya fad'a yana juyawa ya barta dan yasan ya kunnowa su Abbah ita ya fice yana dariya.


Yana fita ta fashe da kuka su Abbah dasu Mamy sukayi wajan ta ana aikin rarrashin ta amma tak'i shiru sai sharar kwallah take tana jan majina, dak'yar aka lallab'a ta aka shiga da ita b'angaren ta kowa ya samu ya fice aka barta.


Ahmad kuwa koda ya koma receiving calls yayi tayi daga garuruwa da kasashe ana ta taya shi murna, duk inda ya zaga a social media zancen sa ake ana farin ciki da kasancewar sa musulmi na farko da ya fara samu wannan damar a duniya. Gajiya yayi da wayar ya ajjiye ya kulle idon sa nan take fuskar Husna ta gilma masa ya bud'e ido ya mik'e zaune sosai ya d'auki wayar sa ya shiga bincike ko zai ga number ta amma babu.


Tsaki yaja ya ajjiye wayar duk sai yaji babu dad'i zuciyar sa tana bashi bata koma Kaduna ba tana cikin garin Abuja wajan wani Alhajin, ya jima yan sak'awa da warwara kafin ya jawo laptop ya fara aiki bashi ya kwanta ba sai d'aya na dare. 


Da safe lokacin da ya fita safiya ce sosai bai samu ya shiga cikin gida ba ya hau mota ya fita daga gidan, asibiti ya nufa yana shiga direct lab yayi ya saka face mask da handgloves da hula ya shiga ciki. Ya jima yana ta aiki ya had'a wannan chemical d'in da wancan ya sake had'a wannan da wancan, ya kwashe sama da awa guda a ciki sannan ya fito ya cire kayan da ya sanya ya nufi office ya tarar da patients dankam ana jiran sa. 


Yana shiga office ya wanke hannu ya zauna yana sauke numfashi, Omar ne ya shigo office d'in da sallama ya amsa ba tare da ya kalle shi ba ya zauna yace, "Congratulations the young pharmaceutical scientists Dr, Allah ya taimaka ya cigaba da baka ikon nasara a duk abinda ka sanya a gaba." Murmushi Ahmad yayi yace, "Amin Omar, kaga abu kamar wasa ya zamo gaske?."


"Da naga news d'in jiya haka nace ikon Allah kenan kai kanka baka d'auka za'a yi approving d'in seed d'in ba."

"Nifa na manta wallahi tunda naga suna min yawo da hankali da farko sai na watsar ka sanni ba juriya."

"Gashi ka zama na farko a duniya musulmi me karancin shekaru kuma d'an Nigeria da ya nasarar samo sinadarin magance ciwon cancer kwakwalwa, me zamu cewa Allah in ba godiya ba?."


Numfashi ya sauke ya jingina da kujera kana yace, "Haka ne."

"Kuma kasan mene? Yawan taimakon fa da kake yi shiyasa Allah yake Bud'a maka a koda yaushe. Jiya ka samu project da company America yau kuma anyi approving sinadarin da ka samo, ka godewa Allah. "


Murmushi yayi kawai baice komai ba Omar ya sake cewa, "To yanzu wacce country zaka saidawa da seeds d'in?." Yatsine fuska yayi yace, "Ba wanda zan saidawa yadda nasha wahalar nemo shi ni ne zan sarrafa shi, meye amfanin pharmaceutical industry d'in mu? Ai scientists zamu nema daga outside countrys suzo mu had'a kai ayi manufacturing d'in maganin a nan in yaso ko wacce k'asa ta siya daga hannun mu. Last time haka kaga suka min akan covid 19 vaccine d'in nan dani aka sha wahalar neman chemicals d'in amma daga baya aka tafi dashi wata k'asar ka duba sai dai mu k'asar mu ta siya a hannun su, dis time baza'a yi haka ba gaskiya gwara mu muyi da kan mu."


Omar yace, "Gaskiya ne kayi tunani me kyau sosai, to what about shi na diabetes din da ka nemo?." Ahmad yace, "Nasan leaf d'in a ido amma ban san inda zan same shi ba, ance akwai shi a k'asar nan amma ban san inda zan ganshi ba."

"Ka sake bincikawa dai sai kaga ka gano shi."

"Zanyi" daga haka yaja bakin sa yayi shiru.


    "Zuwa yaushe zasu zo ayi lunching d'in tablet d'in?." Sai da ya tab'e baki wanda hakan ya kasance al'adar sa kana yace, "maybe nan da two weeks."

"Sai ka nemo mata da d'a." Da mamaki Ahmad ya kalle shi yace, "Kamar yaya kenan?." Omar yayi dariya yace, "ka manta last had'uwar ku dasu David yace in kuka sake had'uwa zaka nuna musu matar ka da y'ar ka kamar yadda kace musu kana dasu?."


Wara idanu yayi kafin yace, "Tabd'ijam ni kam ai na manta, illar k'arya kenan da nace musu bani da aure tun farko ai da ba haka ba." Omar ya sake yin dariya yace, "Sai kasan yadda zakayi ai yanzu." Mik'ewa tsaye yayi ya k'arasa inda files d'in sa suke ya shiga dubawa kana yace, "Ya zanyi kuwa? Sai nace musu bata nan tayi tafiya."


"Again? Ka manta last time ma haka kace musu?."

"So what?."

"It's shameful to u."


   Omar ya kuma cewa, "Kai kasan yadda turawa suke da matan su in ka sake cewa haka zasu d'auke ka kamar baka san mahimmacin matar ka ba zasu ga babban taro kamar wannan ace babu matar ka a ciki ai abin kunya ne." 


Baice komai ba ya dawo ya zauna a lokacin wyar sa tayi k'ara alamun shigowar sak'o, d'auka yayi ya duba ya d'ago ya kalli Omar yace, "Mail ne fa daga w.h.o suna son ganawa gani by 10am o'clock." Da mamaki Omar ya wara idanu yace, "Woww, yanzu ya za'ayi kenan?." Ahmad yace, "Yanzu eight tayi lokacin fara ganin patients yayi zuwa ten d'in sai mu tafi tare, but wa zamu barwa ragowar patients d'in nan? Kasan dai ko rabi bazan gani ba before ten."


Omar yace, "Abdul fa?." D'an k'aramin tsaki Ahmad yayi yace, "Banda shi ya cika san mata da yawa." Omar yayi dariya yace, "To kaga shine mai k'ok'ari kuma yana cikin asibitin, sai dai in Jamil zaka kira ka had'a su da Mima." Shiru yayi na wani lokaci kafin yace, "yarinyar can ta cika rawar kai ne, but a musu maganar da a bar patients d'in su kad'ai gwara a lallab'a."


Omar ya mik'e yana dariya ya fita shi kuma ya fara ganin patients. K'arfe tara da rabi ya fito daga office d'in patients suna ta kallon sa ya wuce zuwa office d'in Omar suka had'u shima yana niyar fitowa, "Ka sanar dasu?" Ya tambaya yana kallon sa. "Yeah na sanar da Jamil Mima ce ban ganta ba." Baice komai ba yayi gaba Omar yayi dariya ya shiga office d'in Mima.


A cikin mota ya same shi yana zuwa ya shiga ya ja motar zuwa address d'in da aka bashi, kafin yaje lokaci yayi kasancewar sa ba mutum bane mai African time goma dai-dai a gidan d'in tayi masa suka shiga ciki suka samu dukkan su an hallara yaruka da daban-daban ana jiran isowar sa.


Basu tashi daga meeting d'in ba sai azahar bayan sunyi sallah suka fito suka shiga mota suka koma asibiti, lokacin su Mima sun k'arar da patients d'in safe ya shiga ya zauna a office yana sauke numfashi.


A wannan lokacin wayar sa ta sake yin k'ara ya duba yaga wani sak'on aka sake tura masa, dafe goshin sa yayi ya kalli Omar yace, "Another mail, minister of health, minister of education and rest suna son gani na by 8pm." Omar ya fara clapping hannun sa yace, "you're lucky man Ahmad, rayuwar ka abin a kwaikwaya ce."

"Ka shirya muje anjima, ina da theater yanzu" yana fad'a ya mik'e ya fice ya bar Omar yana ta murmushi. 


Ta office d'in Mima yazo wucewa ya hango ta ita d Jamil suna ta hira da dariya abin su ya tab'e baki har ya wuce sai kuma ya dawo da baya ya bud'e k'ofar office d'in ya kalle su suma suka kalle shi fuskar nan a tamke yace, "Jamil we have alot of patients in emergency why zaku zauna kuna hira kamar wajan hira ne?."


Jamil ya mik'e ya d'an murmushi yace, "I'm sorry sir, kasan we're engaged today." Tsaki yaja yace, "And so?." Murmushi Jamil ya kuma yi yana kallon Mima da ta hade rai tan hararar Ahmad.


"Kuje kuyi abinda ya kamata" ya sake fad'a yana niyar wucewa. "Sarkin takura ba daman ya ganni ina hutawa sai ya d'aga min hankali" ta fad'a k'asa-k'asa tana hararar sa. Kallon inda take yayi dan sarai ya jita kamar zaice wani abun sai ya fasa ya wuce. Jamil y kalle ta yace, "Beauty let go kar y sake dawowa ya tarar damu." Mik'ewa tsaye tayi tace, "Tsinanniyar takura gare shi, wallahi wani lokacin kamar na shak'e wuyan sa haka nake ji."


Dariya yayi yace, "Mu je dai." Gaba tayi yan biye da ita har emergency.


*Kaduna.*


Yadda ta shigo gidan fuskar ta a had'e hakan zai nuna maka ranta a mugun b'ace yake ta samu waje ta zauna tana kallon gefe guda, wacce take zaune a falon ta kalle ta tace, "Lafiya na ganki kin shigo fuska a had'e haka?." Sai da ta sauke numfashi tace, "Yaya Rabi yanzu haka zamu zubawa Husna ido uban ta yana saka ta yawo kamar ba shine ya haife ta ba?."


Yaya Rabi tace, "Me ya faru kuma?." 

"Meye ma bai faru ba, jiya naje gidan su baki ga rashin kunyar da ita Husna tayi min ba shi kuma wai shine yake cemin na sake shiga sabgar d'iyar sa sai hukuma ta raba mu."

"To gashi kema kince yarinyar tayi miki rashin kunya. Gabad'aya ya cusawa ita Husnan tsanar mu a ranta bata ganin kowa da gashi zan iya rantsewa ma mantawa take damu a shafin rayuwar ta gabad'aya, akan wanne dalili mu zamu damu da lamarin ta?."


Anty Azumi tace, "Amma kuma Yaya Rabi ko mun ki ko mun so Husna y'ar muce, ki tuna amanar da mahaifiyar ta ta bar mana lokacin da zata bar duniya, sau uku tana maimaita min ki kular min da Husna da wannan kalma numfashin ta ya bar jikin ta, in muka fita daga lamarin ta bamu rik'e amanar da ta bar mana ba Yaya." Yaya ta sauke numfashi tace, "To ya zamuyi Azumi? Wacce kotu ce bamu kai k'arar Auwalu ba a fad'in garin nan?, da shari'a tazo k'arshe shi ake bawa rik'on y'ar sa ba mu ba. Allah yana ji kuma yana gani shine ya k'addara faruwar hakan, muyi iya bakin k'ok'arin mu akan rik'on ta ya dawo hannun mu tun ba yanzu ba amma abin yaci tura, har ita yarinya ta nuna tafi son zama da uban ta a kan mu ya kike so muyi to?."


Shiru tayi bata amsa ba Yaya ta kuma cewa, "Addu'a kawai zamu dinga mata dan wani lokacin lamarin Husna kamar me aljanu ta fifita uban ta a kan kowa abinda ya sanya ta shi take yi, muyi mata addu'a Allah ya kawo silar shiryuwar ta ya kuma shirya ta."


"Amin, ana ta zagin mu a gari na sani ana cewa dan ba mune muka haife ta ba." Yaya ta kuma cewa, "Duk wanda ya zage mu sai Allah ya saka mana domin kuwa munyi iya yin mu wajan ganin ta dawo hannun mu." Anty Azumi tace, "Shikenan Allah ya kyauta." Ta amsa da Amin suka cigaba da tattaunawa akan lamarin.


*Abuja.*

*8:00pm.*


Katafaran falo ne na isa da alfarma suke a zaune ana tattaunawa, Ahmad ya canja shiga zuwa manya kaya da suka amshi jikin sa haka ma Omar suna zaune ana tattaunawa akan yadda abubuwan zasu gabata. Yadda yake sarrafa harshe ma abin kallo ne da burgewa in yayi hausa ya koma English su kan su sake burge su yake yi.


Basu tashi ba sai k'arfe tara da rabi na dare suna fitowa daga d'akin da suka tattauna Ahmad ya yatsine fuska yace, "Nifa yunwa nake ji gaskiya." Omar yace, "Ai dole kaji yunwa nasan rabon ka da abinci wata kila tun jiya, muje gida na mana muci gabad'aya."


"A'a bazan je ba mu k'arasa restaurant d'in cikin hotel d'in nan muci." Omar yace, "Okay better, nasan daman baza ka ba ina jin matata ce bata iya girki ba" ya fad'a suna jerawa suna tafiya.


Baice komai ba har suka k'arasa suka zauna a out basu shiga ciki ba aka kawo musu menu, scanning din menun yyi a wayar sa ya fara duba abinda zasu ci yana fad'awa waiter tana rubutawa har ya gama ya ta tafi ta kawo musu.


Omar yace, "To yanzu Ahmady a kan wacce matsaya kake?." Jingina yayi da kujerar yace, "abinda nace maka tun farko shi zanyi, babu wani industry da zan saidawa da seeds d'in nan, haka babu wani company da zanyi had'in guiwa dashi wajan manufacturing d'in maganin sai wanda naga dama. Su turanwa in suka nemo nasu suna bamu ne? Mu sai mu dinga mayar da kan mu baya akan kud'i."


"Gaskiyar kane wallahi, kuma kana siyarwa duk wahalar da ka sha ya tashi a banza da wofi dan za'a manta da sunan Kaine ka samo shi." A lokacin aka fara ajjiye musu abinci Ahmad baice komai ba ya d'auki spoon ya dibi shinkafar ya kai bakin sa kenan idon sa ya fad'a gefen sa inda mata da maza suke a zaune.


Cak ya dakata da kai abincin bakin sa ya mayar da spoon d'in y ajjiye d'in ya had'e hannayen sa ya tokare hab'ar sa dasu yana kallon inda matan suke, Omar ganin ya dakata a saka shi shima tsayawa ya kalli inda yake kallo.


Omar y kalle shi yace, "Wannan fa ba sabon abu bane indai a hotel d'in nan ne dandalin sharholiyar y'an mata da samari kenan." Baice komai ba kallon Husna kawai yake da take zaune a tsakiyar maza cikin k'ananun kaya mara tsaho kanta babu d'ankwali hannun ta rik'e da shisha tana zuk'a su kuma mazan suna sha mata jikin ta.


Wani irin abu yake ji yana taso masa daga zuciyar sa har zuwa kan harshen sa me mugun d'aci hakan ya saka shi kasa furta komai sai kallon ta da yatsa yi cike da zallar takaici da kuma bak'in ciki. Kamar ance ta kalli inda yake ta juyo karaf idon su ya had'u ta goge idon ta ta sake kallon wajan taga dai shine kuma kallon ta yake sai ta firgita ta mik'e daga cikin su tana kalle-kalle kamar 6arauniya.


Cak ya mik'e ya d'auki makullin mota ya bar wajan ganin haka Omar shima ya mik'e ya biya su kud'in yabi bayan sa da sauri yana kallon Husna da idanun ta suka ciko da k'wallah.





Share it sabida Allah👏🥰

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.