Free chapter 路 Read without an account

Chapter 03

by Azizat Hamza 路 Duk kyan Namiji

*DUK KYAN NAMIJI*

............. ....馃懗.... ..............



0锔忊儯0锔忊儯3锔忊儯


Engr Hussain Ahmad Ningi suna zaune da matar sa lafiya.

Zaman Su gwanin sha'awa.

Haihuwar farko Maryam ta haifi

namiji aka sa ma sa Ahmad

amma su na kiran shi Aryan,

shekaransa uku ta haifi

Khadijatul Khair, tsakanin Khair

da Ja'afar ma shekara uku ne, da

shi ke sunan mahaifin Maryam

gareshi sai suke kiran shi da Aabid.

Watan Aabid Shabiyar aka haifi

Lubna wanda kamar cikin ya zo musu ba zata ne.


Bayan ta haifi Lubna ta fara

planning saboda ba ta son sake

haihuwa da wuri. Sai dai kuma

tun da ga Lubna ta dena

haihuwa.

Daga baya ta yi da na

sanin planning 蓷in da ta yi. Shi kuwa

Engr Hussain bai damu ba cewa

yai yara hudu sun ishe su.


Rayuwar gidan kamar na

turawa. Da safe Engineer da

matarsa za su fita aiki yara kuma su

tafi Makaranta sai dare ake

haduwa. Weekend kuwa wuni su

ke yi a waje wajen shakatawa ko

shopping. Idan ka gansu gwanin sha'awa. Ko Hausa yaran ba su iya sosai badan gidan turanci a ke yi.

Mommy ce kadai ke kokarin yi

mu su Hausa amma Engr kam

turanci zalla.


Duk cikin yaran Lubna ce ta dauko kamar Engr

idan ka dauke manyan ido irin

na mommy sauran duk kamannin

Engr ne shi ya sa ya ke son ta

sosai.

Matsala daya Lubna ke da

shi wato i'ina (stammering)

lokacin ta na Karama abin sosai

ya ke daminta, dan wani lokacin

har hawaye ta ke yi kafin magana

ya fito. Hakan ya sa Engr su ka

kai ta asibiti. An dai ba ta wasu

magunguna tareda cewa a

hankali ta na girma abin zai ragu.

Hakan kuwa a ka yi ta na girma

abin yana raguwa.


Duk karshen shekara su ke

zuwa Ningi hutu da ya ke Engineer ya

gina gida a chan, idan sun zo nan

su ke sauka.

Daga Ningi su ke wucewa

Yobe su gaida 'yan uwan

mommy.


A cikin yaran Lubna da

Aabid sun fi shakuwa, idan ka

gansu kamar wasu 'yan biyu.

Makaranta masu tsada yaran

ke zuwa wanda boko kawai aka

sa a gaba.

Tun safe sai karfe biyar ake tashi saboda bayan

school activities ana tsayawa

lesson. Ranakun weekend ma a

boko ya fi tafiya dan karfe

takwas zuwa sha biyu shi ma na

lesson ne da ake yi mu su a gida,

sai Karfe biyu zuwa hudu wani

malami ke zuwa koyar da su

kur'ani. A takaice dai ba sa zuwa

islamiyya. Shi ya sa tarbiyan yaran

ya karkata zuwa na turawa.


Mommy ce mai kokarin takura

mu su wajen tsaida sallah amma

still yaran sai a hankali, musamman Lubna wanda ta ke

sakaliya, har ta kai shekara sha

daya a duniya sai ta ga dama ta

ke sallah. Infact sallar asuba kam

dama jazaman ne ba ta yin ta

akan lokaci. Sau tari sai sun

shirya za su tafi makaranta

mommy ke tilastawa ta yi sallar

asuba, wanda za ta yi shi ne a

gurguje kamar Wucewar

walkiya.


Lokacin da ta fara al'ada ne

ma mommy ta dage akan sallarta

nan ma din da kyar ta ke yi. Idan

mommy na ma ta fadan sallah

kuwa indai Engr na wajen sai ya

karba mata ya dinga cewa ai har

yanzu yarinya ce karama. Wata

rana da abin ya tunzura mommy

tace haba Daddyn Aryan, yanzu Lubna ce yarinya, 'yar shekara sha biyu ce yarinya. Yarinyar da wata

takwas kenan da fara

menstruation dinta. Mi addini

ya ce gameda Sallah?".

Ranar sai da masoyan su ka samu sabani

saboda fadin gaskiya da mommy

ta yi.


Engr irin mutanen nan ne da

boko ya mu su illa, wanda hakan

ya raunatar da imanin su. Shi

komai a yi shi yadda mutum ba

zai takura ba ko da kuwa ibada

ne.

Wata rana mommy ta tirsasa

Lubna ta dau Azumi a lokacin

Ramadan saboda Lubnan ta

balaga, amma ba a kai karfe sha

biyu ba ta karya wai da wahala.

Washe gari ma haka, ta dinga

pretending kamar ta na Azumi

amma idan ta je school ko kuma

tana daki sai ta sha ruwa ta ci

snacks ko biscuit. Ranar azumi

na shida asirinta ya tonu hakan

ya batawa mommy rai har sai da

ta daketa. Da Engr ya dawo ya

fara fada, irin yadda su ke fada

tun daga daki ana jiyowa a falon

kasa. Yaran su ka yi cirko-cirko

a falo dan tunda su ke iyayen su

ba su taba fada ba. Abin dai har

sati guda iyayensu na zaune

hakanan ba shiri har makwanci

Sun raba.

A wannan lokaci

Lubna ta tsinci kan ta da shiga

damuwa musamman yadda

Aryan da Khair su ka sa ta a

gaba akan ita ta hada mommy da

daddyn su fada. Da kan ta ta je

ta bawa mommy hakuri tareda

alkawarin za ta jure ta dinga yin

azumin. Hakan ya kasance duk

da ta na wahala idan ta dauka

amma ba ta kuma karya azumin

ta ba.

Wannan abinda ya faru ya

fargar da mommy daga irin

tarbiyan da su ke yiwa yaran su.

Ta yi kokari ta shawo kan Engr

har ya yarda aka saka yaran a

Islamiyya su ka daina lesson din

weekend ya koma Islamiyya su

ke zuwa a wadannan ranakun.


*Da ma tun yara su na kanana

ake koya mu su son ibada, a da

iyayen mu na kokari sosai akan

haka. Amma iyayen mu na zamanin

yanzu wanda boko ko

shagaltuwa da lamarin duniya

ya sa mu kan mu ba mu yin

kokari wajen ibada balle kuma

mu daura yaran mu akai. Sai ka

ga mace ta wuni gindin TV ta na

kallon soap operas na India ko

series na turawa ko kuma ta yini

ta na danna waya. Batun itama ta

yi sallah akan lokaci bai taso ba

balle kuma ta lura ko yaran ta

sun yi sallah ko ba su yi ba. Kai

ko dan shekara biyu ki ke da shi

ki sabar mi shi ko ma ta da

sallah, duk lokacin da za ki yi

sallah jawo shi kusa da ke ku yi

tare, za ki ga yaron zai dinga

dungure dungure ya na

kwaikwayon ki a haka zai ji son

sallah, ya na dada girma da

wayo ya na dada kara son abin.

Amma wasu iyayen sai ka ji

komai su ce yaro ne ba yanzu ba,

by the time yaron ya girma ya

kai munzalin yi kuma sai ya

dinga ki ko da an takura shi

saboda bai saba da abin ba. Allah

ya sa mu dace ya kuma ba mu

ikon tarbiyantar da 'ya'yan mu

bisa tafarkin addini amin.*


Lokacin da Aryan ya Kare

secondary school 蓷in shi Oxford

Engr ya ne ma masa kuma ya

samu. Lokacin da zai tafi har

party aka shirya na tafiyar sa

wanda hatta Alhaji Hassan sai da

ya halarta bikin. Kwana uku da

bikin ranar Talata da safe Engr

da matar sa su ka raka Aryan

airport , da ya ke sauran yaran su

na exams shi ya sa su biyun ne

su ka yi rakiyar. Sai dai kuma a

hanyar su ta zuwa airport din

kaddara ta afka mu su.


Su ka yi hatsari, Aryan da

mommy a take su ka rasu shi

kuma Engr sai da ya kwana biyu

a asibiti kafin ya cika.

Tashin hankali wajen yaran da

'yan uwa da abokan arziki abin

ba a magana, mussaman Alhaji

Hassan.

Lubna kam kusan hauka ta yi,

a ranar rasuwan su mommy sai

da ta suma sau uku, Karshe

alluran barci aka mata. Da Engr

ma ya rasu tashin hankalin ya fi

na da dan ranar da zai rasu sun yi

magana da Lubnan.

Tunda abin ya faru Lubna ba

ta iya bacci, idan ta kwanta haka

za ta farka tana sunbatu a haka

aka fara ba ta maganin bacci dan

ya taimaka ma ta. Daga baya

Alhaji Hassan ya hana. Sai da su

ka koma gidan Alhaji a Bauchi

ne ma ta ke iya yin bacci amma

dole sai an bar wuta a kunne.


Lubna na shekara sha uku

iyayenta su ka rasu Aabid na sha

hudu yayinda Khair ke sha

bakwai lokacin ta na SS 3 ma.


Wajen Mama Alhaji Hassan

ya damka yaran saboda yasan

anan ne za su samu kulawa da

tarbiyya mai kyau bil hakki ba

tareda Mama ta nuna mu su

banbanci ba.

Wannan abin da Alhaji ya yi

ya kara dasa tsanar Mama a ran

Hajiya, haka nan ya sa ba ta

kaunar yaran, ko kusa ba ta jansu

a jikin ta, yadda ta ke kishi da

yaran Mama haka ta ke kishi da

yaran Engr.

Lubna sa'ar Nafisa ce da wata

uku ta girmi Nafisan. Zaman

yaran wajen Mama ya sa ta gyara

mu su tarbiyan su musamman

Lubna, a hankali ta dinga nutsar

da su wajen son ibada da kuma

kokarin bin dokokin musulunci.

Dan ada yaran kwata-kwata ko

dan kwali sai sun ga dama su sa

idan za su fita, a gida kan batun

sa dankwali babu shi, da wannan

Mama ta fara lokacin da aka fara

kawosu, a hankali-a hankali

dabi'ar su ta fara sauyawa sai dai

abinda ba a rasa ba.

Kasancewar Mama ba ta taba haihuwar mace

ba ya sa ta ke son Khair da

Lubna sosai tamkar 'ya'yan cikin ta...


Tun lokacin da Lubna ke yarinya ta ke

son computer, ta na da shekara

bakwai Engr ya siya ma ta laptop

duk da kuwa akwai computer da

ya dasa wa yaran a gidan takanas

saboda su kadai amma saboda

yadda su ke fada da yayunta

wajen amfani da computern

ya sa ya siya ma ta mini laptop.


Zaman da Adnan yai a gidan su

kafin ya tafi Stanford karatu ya

sa ta sake jin son computer sosai.

Lokacin ta na shekara tara, shi ya

fara koya ma ta programming.

Khair na gama secondary ta

cika Masscom a ABU Zaria, su

ka bata International studies, ta

na aji hudu Adnan ya fara

maganar auren su saboda tun

zaman da yai a gidan su na Lagos

ya ke son ta.

Adnan dan yayan

mommy ne. Lokacin da ya kare

secondary ya zo ya zauna dasu

a Lagos anan ya shiga wata ga sa

na computer programming wanda da ya ci

aka ba shi scholarship na karatu

a Stanford University da ke

America. Da ya kare karatu ya

samu aiki acan.

Khair na aji

hudu aka yi bikin su amma ba ta

tare ba sai da ta gama bautar

kasa. Yanzu haka su na chan

America shekarar su hudu da

aure har da diyar su 'yar shekara

biyu Maryam su na kiran ta

Abidah.


Aabid kasar waje Alhaji ya ke

son kai shi karatu amma saboda

abinda ya faru da Aryan ya sawa

Aabid phobia, shi ko ba karatu

bama tsoron fita barin kasar ya

ke ji. Ya nemi BUK kuma ya samu

inda ya ke karantar

Architecture yanzu haka ya na

aji uku.


Nafisa ATBU ta ke inda ta ke

karantar Microbiology ta na aji

biyu. Lubna ce ta ke Makaranta a

Federal polytechnic da ke Bauchi tun da

ta yi Jamb ta cika BUK ba su ba

ta admission ba ta watsar da

zancen University ta zabi karatu

a Poly inda ta ke da yakinin za ta

samu abinda ta ke so wato karatu

a bangaren computer.

Har ga Allah kuma ta ji dadin

haka lokacin da ta yi ND hakan

ya sa ta koma yin HND a chan.

Duk da Alhaji Hassan bai yi

karatun boko ba amma ya dage

akan karatun yaran sa.


Abdallah

dan sa na fari yana

service a Lafia sai Abubakar da

ke BUK ya na karantar Law sai

Ahmad da ke aji biyu a unimaid yana

karantar MBBS.


Muhammad Salim ya na aji daya

a ABU Zaria ya na karantar

Veterinary medicine.

Idan ka ji hayaniya a gidan to

dalilin Hajiya ce har yau ta kasa

rike su Lubna a matsayin yan

gida. Ta ko wanni fanni sai ta

nuna mu su warayya. Yaran kam

ba ruwan su gaba daya an zama

daya. Nafisa ce kadai ke kin

Lubna saboda wani dalili na ta

na shirme.

Alhaji na ji da Lubna

sosai dan yadda ya ke janta jikin

sa ko asalin 'ya'yansa albarka,

yana daya daga cikin abin da yasa da Hajiya da Nafisa su ka

tsani Lubna...




















Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.