Free chapter · Read without an account

Chapter 6

by Azizat Hamza · Duk kyan Namiji

*💮DUK KYAN NAMIJI💮*

............. ....👳.... ..............


Please follow me on

Wattpad: Azizat_Hamza

Arewabooks: Azizat Hamza



Free book

0️⃣0️⃣6️⃣



Washegari da wuri ta tafi school, ba ta da lecture sai 10am amma tun 8am ta ke school ɗin. Kamar wata sokuwa haka ta je ta tari Walida lokacin da ta fito daga motar ta. Dama tuni ta ke zaune dakon jiran ta a tunanin ta Suhail ne zai kawo Walidan sai dai kuma ta yi rashin sa'a domin Walidan da motar ta ta zo.

A dararance dukkan su su ka gaisa saboda ba sabawa su ka yi ba.

"Walida na gode fah, jiya sai gashi har gida ku ka kaimu" ta faɗi ta na washe baki.

Galala Walida ta tsaya kallon ta Fiskar ta ɗaure.

"Plz ki gaishe min da Suhail ki ce ina godiya"

"No need" Walida ta faɗi tare da barin wajen. Duk da Nafy ta ji haushin abin amma ba yadda ta iya domin za ta shanye komai in dai akan Suhail mai kyau ne.

Da ta shiga class wajen da su ka saba zama da su Zuby ta je ta zauna. Zuby na ganin ta ta ce "an dai ji kunya wallahi"

Nafy ta yi murmushi ta ce "ba za ki gane bane Zubaida"

Sai da aka fito daga lectures ɗin 10-12pm sannan Harira ta shiga zancen. Zuby ce ke shirin wucewa ba tareda ta jira su ba.

"Wai dan Allah miya faru ne tsakanin jiya da banzo school ba, dukkan ku sai wani haɗa rai ku ke da juna" Harira ta faɗi ta na kallon su ɗaya bayan ɗaya.

"Ni ban san mi na ma ta ba, na ga saurayi ina so, shi ne ta ke ta haɗa rai tun jiya" Nafy ta faɗi hankali kwance.

Harira ta kamo hannun Zuby ta ce " sweetheart zo ki ba ni labari, na san ki ba kya fishi hakanan sai da babban dalili"

Rai a ɓace Zuby ta ce " ban yi zaton Nafisa will stoop so low akan namiji ba. Kin ga yadda ta ke rawar jiki jiya kamar wanda ta ga Annabi Yusuf. Abin haushin ma wai ba ta damu ko shi saurayin Walida bane, mtsww"

Harira ta ƙarasa daf da ita a hankali ta ce " give me details ƙawata na ga alama ba ƙaramin show aka yi jiya ba"

Zuby ta bata labarin komai. Nafy kam ko a jikin ta.

Harira ta taɓe baki saboda duk kyan namiji ita kam ba za ta iya abinda Nafy ta yi ba.

"Well Zuby, ai gaba ta kaimu gobarar Titi a Jos"

Ta kalli Nafy da ke faman latsa wayar ta tace " idan za ki ba da dubu goma zan nemo mi ki numbar sa, infact ni ina da info akan shi wanda za ki so ki ji"

Nafy ta ɗago da sauri " dan Allah?"

Harira ta kamo hannun Zuby su ka zauna kusa da Nafy.

"Ina ganin kuɗi a ƙasa za ki ji komai"

Nafy ta ɗan turɓune fiska "haba Harira, dubu goma sai ka ce wanda na ci bashin ki"

Harira ta ce " ashe son Suhail bai kai ki kashe mi shi dubu goma ba kenan?"

Ganin fa da gaske Harira ta ke dole ta fara neman ta rage ma ta kuɗin wanda ita Harira ta yi ƙirmisisi akan ba za ta rage ko ƙwandala ba.

Da ƙyar Zuby ta sa baki ta rage ma ta dubu huɗu. Sai da Nafy ta tura ma ta dubu shida ta ji alert tukunna ta fara ma ta bayani.

" Suhail dai cousin ɗin Walida ne"

Nafy ta yi tsaki.

Harira ta cigaba " Baban sa da Baban Walida wa da ƙani ne. Sai dai kasancewa tun ya na yaro Baban sa ya rasu shi ya sa a gidan Alhaji Inuwa ya taso. Wannan kyau na shi da ki ke gani saboda Mahaifiyar sa Buzuwa ce 'yar Niger. A halin yanzu ya na karatu a Malaysia"

" akwai soyayya tsakanin sa da Walidah?" Nafy ta tambaya tana tsare Harira da ido.

" wannan ban sani ba, sai dai duba da gida ɗaya su ke komai zai iya faruwa"

"Amma Allah ya shirye ki Harira yanzu akan wannan sai da ki ka sa na baki dubu shida"

" ke ki ke matse da sanin waye Suhail. Yanzu kinga idan aka tashi Kaza zamu je mu ci ni da sweety" ta yi maganan ta na fari da ido.

Nafy ta ɗan bugi kafaɗar ta ta na faɗin saura nambar sa kuma.

"Kar ki damu zuwa gobe"....

Sai da su ka rabu da Nafy Zuby ta tambayi Harira a inda ta san Suhail.

Harira ta yi dariya ta ce "wallahi abokin saurayin Amiran mu ne, ranar da ya zo hira su ka zo tare. Kin sanni da bin ƙwaƙwaf. Da su ka tafi na ke tambayanta ina Hassan ya samu aboki balarabe? Sai ta ke ce min wai Maman sa Buzuwa ne" 

Zuby ta yi dariya ta ce "shegiya tawan" ...

.....................................

A ɓangaren Nafy ji ta ke kamar gari bazai waye ba. Da ƙyar ta iya bacci, takanas ta nitsu ta ke tsara irin kalaman da za ta gayawa Suhail idan ta kirashi. Da sassafe ta kira Harira tana tambayarta batun number. Harira ta ce sai sun haɗu a school. Ba yadda Nafy ta iya dan ta san halin ƙawartata da kafiya musamman yanzu da ta san Suhail weakness ɗin ta ne.

A school ma dai sai da Harira ta ja ma ta aji kafin ta bata numbar. Jiki na rawa ta karɓi takardar a wajen Harira, gudun kar takardar ya ɓata a take ta yi saving numbar. Tsiyar da su Zuby ke ma ta ya sa ta fasa kiran shi a wajen, ta bari sai ta je gida. Amma gaba ɗaya hankalinta ya na kan agogo. Idan ba lecturer ɗin da su ke da shi ya na da tsauri wajen ɗaukan attendance ba da tuni ta tafi gida.

Su na fitowa ta wuce gida saboda ta ga Idan ta biyewa su Harira ba fita za su yi a makarantan da wuri ba.

Ta dai daure ta yi sallah kafin ta kira shi, har da rufe ƙofa dan kar Rahma ko sauran yaran su shigo su dameta. Sai dai sau biyu ta kira amma ba a ɗauka ba. Ta sake duba numbar da Harira ta bata da wanda ta kwafa ko akwai mistake amma dai-dai ne. Ta ajiye wayar a gaban ta ta na kallo. Gaba ɗaya yinin ranan da waya a hannu ta wuni saboda jiran kiran sa. Farko ma sai da ta kira Harira akan ko dai number ƙarya ta ba ta. Harira ta ce kar ta dameta ta katse kiran...

Ƙarfe tara na dare ya kira lokacin ta na karanta post na wani littafi da aka turo. Da ƙyar ta iya tattare nitsuwar ta ta ɗau kiran.

A nitse ta ke magana, maganar ma kaman wanda sai ta aunata kafin ta fito. Ta na ma sa kwatancen ko ita wacece ya gane ta. Duk da dai shi ba wai ya sa ta a rai bane amma ya ganeta sarai dan a kanta Walida ke fishi da shi tun ranan ɗin.

Sosai ta ke jan sa da hira ta hanyar kissa da ƙisisina. A hankali ya sake jiki da ita...

Mace kenan, cikin kwana uku Nafy ta gama da Suhail. Tun da ya ce ma ta babu soyayya tsakaninsa da Walidah hakan ya ƙara ba ta ƙarfin gwiwa. Har ranta ta ke jin ta mallaki Suhail an gama. A ranan na ukun ta nemi ya zo su gaisa tunda ya ce saura sati biyu ya koma Malaysia.

.....................................

Tun da su ka haɗu a class ta ke zancen zuwan Suhail mai kyau. A yadda ta ke ta nanata zancen sai da ran Harira ya ɓaci cikin fushi tace

"ni kam Nafy ke ba budurwar Hudu carpenter ba ce"

"Kutmelesi, Allah ya isa Harira. Waye Hudu da zaki haɗani da shi"

Harira ta kwashe da dariya "lallai Nafy, abinda za ki yiwa Hudu kenan Duk halaccin da Hudu ke mi ki"

" mi Hudu ya min?, yanzu dan ɗan chicken change da ya ke kashe min shi ne abin tada jijiyar wuya"

Zuby ta sa baki a zancen.

"Wallahi mu nan shaida ne Hudu ya miki gata. A mutum mai ƙarfin sa kam ya nuna bajinta da ƙoƙari a kan ki"

"Allah kun raina ni, duk kyau na da gata na ashe fatan na ƙare da Hudu carpenter ku ke"

"To miye a ciki?" Harira ta faɗa a harzuƙe.

" ba laifin ku bane. Laifi na ne da na bawa Hudu dama har ya kai wannan lokaci tare da ni"

A take ta lalubo numbar Hudu wanda rabonta da shi tun ranar da ya zo ta masa walaƙanci. Ta tura ma sa text akan lallai ya zo yau akwai maganan da za su yi.

Zuby ta ce " Nafy ga shawara, ko za ki rabu da Hudu kar ki walaƙantashi, ku yi rabuwar mutunci dan Allah"

Nafy ta ce " riƙe shawarar ki"

...........................

Tun da ya ga text ɗin Nafy ya ke cikin farin ciki a tunanin sa za ta ba shi haƙuri ne bisa abin da ta mi shi ranan. Yau kuwa Umman sa ke ce ma sa ya haƙura da Nafy saboda yadda ta ga ya damu cikin 'yan kwanakin nan.

Ya so ya zo tun yamma sai dai ya dawo daga shago ya na shirin shiryawa Umma ke ce ma sa ya zo ya kai Ɗahe asibiti tun jiya ya kwana da zazzaɓi gashi har yanzu abin bai sake shi ba sai amai ya ke ta yi. Ba musu ya ɗau Ɗahe su ka tafi asibiti. Da ya ke an ƙara ma sa ruwa ya sa ba su dawo da wuri ba sai bayan sallar maghrib.

Bayan ya yi wanka yai sallah ya shirya cikin farar shadda wanda aka ma ta aiki da baƙin zare. Ya sa baƙar hula zanna da baƙin shoe, ya feshe jikin sa da turare sannan ya fita.

Tana tsaka da kwalliya saboda tarban Suhail kiran Hudu ya shigo. Sai da ta yi tsaki kafin ta ɗauka. Ce ma ta ya yi ya iso. Da kamar za ta ce ya bari sai gobe sai kuma ta yi tunanin gara ayita ta ƙare yau ɗin.

Abin mamaki minti bakwai da kiran ta sai ga ta ta fito. Irin ado da kwalliyan fiskarta kuwa tamkar biki za ta je. Shi kan shi Hudu shagala yai da kallon ta har ta iso, dan ta tafi da shi gaba ɗaya.

Ta zauna inda ta saba zama.

"Gimbiya duk wannan kwalliyan tawa ce?" Hudu ya faɗi ya na murmushi.

Itama murmushin ta yi ta ce "kwalliya irin wannan ai tafi ƙarfin ka Hudu"

Jin maganar yai tamkar sukar mashi a zuciyar sa.

Ya daure ya ce " Nafisa mi hakan ke nufi?"

Ta ɗan yi ajiyar zuciya ta ce "Hudu dama ina son baka haƙuri ne....." sai kuma wayar ta ya shiga ringing. Jin special ringing tone da ta sawa Suhail ne ya sa ta yi saurin ɗauka ta na murmushi.

"Ka shigo da motar ciki, ina ma zaune a compound" ta faɗi tareda katse kiran. Ta kalli Hudu da ya ƙura ma ta ido ba ko kiftawa ta ce "gashi ba mu gama magana ba kuma my heartbeat ya iso, ko za ka dawo gobe ko kuma dai ma za mu yi maganar ta waya"

Hudu ya dunƙule hannunsa da ƙarfi ya cizi leɓen sa na ƙasa a lokaci guda kuma idon sa ya chanja kala. Yai wuf ya tashi tsaye ya kalli Nafy ya kuma kalli motan da ke shigowa cikin compound ɗin.

"Ba sai mun sake wani maganan ba, na riga na ɗau saƙon da ki ke son isar mi ni. Allah ya bamu alkhairi" ya na gama faɗin haka ya bar wajen. Clashing su ka yi da Suhail da ya fito daga motar sa. Hudu ya ma sa sallama ya miƙa ma sa hannu su ka yi musabaha sannan ya wuce wajen machine ɗin sa.

Sosai courage ɗin Hudu ya birge shi ya wuce wajen da ya hango Nafyn ta na zaune...

Guntu a kace da faɗin rai. Sosai Hudu ya ke jin ɓacin rai da ƙyar ya iya kai kan sa gida. Da ya je ma kwantawa yai kan gado ya na sauke ajiyar zuciya akai-akai. Ya jima ya na ayyana abubuwa dayawa a ran sa kafin daga baya ya tashi ya fara haɗa kayan sa. Da ya gama ya je yai wa iyayen sa sallama akan gobe zai koma Portharcort. Baba bai kawo komai a ran sa ba sai dai Umma ta san Lallai dalilin tafiyar sa gobe bai wuce saboda Nafy ba dan a yadda ya faɗa mu su da saura kwana huɗu ya tafi. Sai dai tunda ya nuna ba wani matsala ya sa ba ta wani damu sosai ba. Ta san halin ɗan ta nan da lokaci kaɗan zai koma dai-dai.....

AzizatHamza©2020

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.