Free chapter · Read without an account
Chapter 25
*💮DUK KYAN NAMIJI💮*
............. ....👳.... ..............
0️⃣2️⃣5️⃣
Cikin ƙwalƙwalwarta ta ke tariyo abinda ya faru a gidan Lubna. Ba komai ya fi ɗaga ma ta hankali ba irin yadda taga Lubnan ta chanja ma ta lokaci guda, ta yi wani fresh da ita har 'yar kiba ta ƙara. Lubna da ada ta ke lange-lange kamar ka hureta ta faɗi. Shine yanzu jin daɗi yasa ta cicciko ta yi fes da ita. Ta sani da gayya Hudu ya dinga yin abinda yayi a gabanta. Amma kuma salon na shi ya burgeta, irin soyayyan da ta yi muradin samu kenan a rayuwar auren ta da Suhail sai dai kuma ko kwatan abinda ta ke buri ba ta samu ba...
*Waiwaye*
Tsifa ta samu Umma na yiwa Lubna lokacin da su ka shigo tsakar gidan.
"Lallai ma Lubna!, yanzu sirikar taki ki ka zauna ta ke mi ki tsifa dan rashin kunya"
Lubna ta juya ma ta ido.
Umma kam murmushi ta yi tana musu sannu da zuwa. Sai da su ka gaisa da Umman sannan su ka wuce sashen su Lubna. Ruwa da fruits da kayan ƙwalama ta kawo mu su sannan ta zauna tana tambayar su Zahra ya gida. Su kam hankalin su ya tafi kan laptop ɗin ta da su ka samu a falon, sun buɗe suna duba animation films da ke ciki. Nafy kam ƙarewa falon kallo ta yi, ta sani tun a gida Lubna na da tsabta dan haka ba ta yi mamakin ganin ko'ina tsab-tsab ba, ga kuma ƙanshi mai daɗi da falon ke badawa.
" Rahma ke ce min kin yi ɓari satin da ta wuce da ta zo yi min sallama. Allah ya kawo wani mai amfani" Lubna ta amsa da Amin.
Shiru ya ratsa falon na minti biyu, kafin Nafy ta katse shirun da cewa "Ja'afar ya mi ki maganan Rahma ne?"
Cikin rashin fahimta Lubna ta girgiza kai.
"Sai na ke ga kaman soyayya su ke da Rahma"
Ba makawa Lubna ta jima da zargin hakan kuma koda ta tambayi Aabid bai ɓoye ma ta ba, ya sanar ma ta yana son Rahma sai dai bai gaya wa Rahman ba. Rahman ma dai ko makaho zai gane tana son Aabid, saboda shi ma ta nace sai ta je BUK, wancan shekaran da ba ta samu ba, haka ta yi zaman shekara ɗaya ba tareda neman wani wajen ba, sai wannan shekaran Allah ya amsa addu'ar ta.
Lubna ta ce " i dddddont think so"
Nafy ta ce "idan ta yi tsami zamuji ai"
Sallamar Hudu ya katse su.
Shigar shi ta manyan kaya yai, shaddar kalar ƙwai ɗinkin Jumper kuma ta ma sa kyau, 'yar haske da yai da ƙiba saboda kwanciyar hankalin aure ya sa Nafy ta tsura ma sa ido tana mamakin yadda ta ga chanji sosai tattare da Hudu Carpenter, jikin sa har wani yalƙi ya ke.
"Ashe Matar Suhail ne a gidan na mu yau" ya faɗi yana ƙarasowa wajen Lubna. Bakin ta yai niyyar kissing ta yi saurin kauda kai gefe sai ya kissing kumatun ta yana faɗin "yau ba welcoming hug ne baby nah?" Ba ta amsa ma sa ba sai ma harararsa da ta yi. Su Zahra su ka gaishe shi ya amsa.
"Malam Hudu, ya aiki" Nafy ta faɗa bayan ta farfaɗo daga dogon tunanin da ta tafi tun shigowar Hudun.
"Aiki Alhamdulillah, kin san labura sai a hankali"
abinda ya faɗa ya sa ta tuna hirar su da Sumy. Kenan Lubna na morewa a wajen Hudu ta ɓangaren da
ta gaza samu a wajen Suhail. Ta kawar da tunanin da cewa "Allah ya taimaka"
Hudu ya amsa da amin tareda janyo Lubna jikin sa yana faɗin "Hayaty na yi laifi ne ake ta shareni yau ɗin" ƙoƙarin janye jikinta ta ke amma ta kasa musamman yadda saukar lips ɗin sa a wuyanta ya saukar ma ta da kasala. Cikin diriricewa ta ce "mmmmmuna da baƙi fa"
Chak ya ɗauketa ya wuce ɗaki da ita ya bar Nafy a wajen baki buɗe. Zahra da Batool kam tunda su ka gaida Hudu su ka maida hankalin su kan Laptop dan haka duk abinda aka yi ba su gani ba.
Zuciyar Nafy ya fara tafasa, jijiyoyin jikinta su ka tattashi. Wato ma Hudu rashin kunya zai gwada ma ta saboda cin mutunci. Tuni ta fara danasanin zuwa gidan na su. Ta harzuƙa matuƙa ta ce " Zahra ku tashi mu tafi"
"Anty Nafy yaushe mu ka zo, ba mu ma gama tura films ba fa"
"To wallahi sai dai ku sameni a gida" ta ɗau jakarta ta nufi hanyar waje. Su kuwa su ka cigaba da abinda su ke.
Hudu bai dire Lubna a ko'ina ba sai kan gado.
Lubna ta haɗe rai ta ce " mi ka ke nufi?"
Hudu yai dariya ya ce "naga saboda Nafy ki ke ta wani shareni, shiyasa na nuna miki Idon Nafy bai isa ya hanani nuna mi ki soyayya ba"
Ta turo baki tareda tashi za ta fita ya jawota ya rungumeta sosai ya ce " ki min proper welcoming da ki ka saba sai na barki ki fita"
Ganin ba sarki sai Allah ya sa ta sake ta kissing ɗin shi sosai sannan ta ce " sannu da dawowa"...
Minti takwas kacal ta yi a ciki amma fitowarta ta tarar Nafy ta tafi, abin bai ma ta daɗi ba. Su Zahra kam sai da su ka ci abinci su ka yi sallar Isha kafin Hudu ya sa Ado mai Napep ya kai su gida...
.....................
Kwanaki sun shige kuma abubuwa sun cigaba da tafiya. Dawowar Suhail daga Camp ba abinda ya ƙaru na alkhairi sai ma saɓanin haka, bayan ya yi reporting a Jigawa da aka fara relocation sai ya dawo Bauchi bisa umurnin Abba.
Yanzu kam zuciyar Nafy ta aminta da cewa tun farko Suhail ba ya sonta kamar yadda yai ta iƙirari kafin auren su.
'Yan matan da ke kiran sa su wuni suna hira a waya ba adadi. Wasu kam takanas su ke zuwa ma sa gida, idan Nafy ta yi magana ya ce friends ɗin sa ne. Ita bawai zargin neman mata take ma sa ba dan ta lura shi sex bai wani dameshi ba, Falli ne kawai da taƙama da kyaun da Allah ya bashi ya sa ya ke biyewa 'yan matan da ke zuwa wajen sa ko su ke kiran sa a waya. Hiran da bai yi da matar ba, sai ya shafe awanni yana yi da 'yan matan waje, wanda hakan ke ƙonawa Nafy rai.
Tattali, kulawa, gata da soyayya da ta yi muradin samu babu shi a gidan ta, Ga uwa uba shaye-shaye wanda yanzu baya kunyar yi a gabanta.
Maganin ƙarfi da ta ƙarɓa a wajen Sumy ya sa ta ke jin Suhail dama-dama kuma ya ke nemanta aduk lokacin da ta bashi ya sha, tunda kuwa ya ƙare aka koma gidan jiya. Domin sai yai kwana uku, biyar ko sati bai nemeta ba, gashi Sumy ta tafi Niger.
A irin waɗannan yanayi sheɗan ke samun damar shi a kan 'yan Adam, musamman mutum mai sakaci. Balle dama tin kafin aure idon Nafy ya buɗe, tuni ta koma kalle-kalle da karance-karancen batsa saboda ta samu nitsuwa. Aure yasa ta gane ita ɗin mai yawan buƙata ce kuma ta haɗu da miji wanda baida ƙarfin sha'awa kuma bai damu da halin da ta ke ciki ba.
Ta kanji baƙin ciki idan ta je makaranta ta kalli Walidah, wanda kyakykyawar kulawa da kuma kwanciyar hankali da ta samu a nata gidan mijin ya sa kullum ta ke cikin farin ciki da walwala, Ƙaramin cikinta ya sa ta ƙara haske da ƙiba. Ko makaho ya san tsakanin Nafy da Walidah akwai banbanci a zaman auren su. Nafy tun tana yiwa su Harira da Zubaidah ƙarya akan gidanta har ta haƙura, dan yanzu kam ƙaryanta ya ƙare, zuwan su gidanta na ƙarshe a gaban su Suhail ya shigo da wasu 'yan mata gidan, su ka zauna su na hira har da cewa Nafy ta kawo wa baƙin sa ruwa...
...........................
Ranar Lahdi da yamma Nafy ta je gidan wata amarya da aka kawo ƙasan layin su don gaisuwa. A nan ta haɗu da Amal har su ka exchanging contacts, Amal ma matar aurece tana karatu a ATBU ajinta huɗu.
Amal na auren Alhaji Sani Darazo, wanda wani attajirin ɗan kasuwa ne. Kasancewa kasuwancin sa a Lagos ya ke ya sa yafi zama a chan, Amal itace matar sa ta uku kuma amarya, shekaransu biyu da aure. A wajen shashanci su ka haɗu inda bayan wata huɗu suna morar junan su Amal ta ma sa ƙaryar tanada ciki kuma cikin nashi ne. Da farko ya ƙi ƙarɓa daga baya ya amince da buƙatar ta na su yi aure, cikin wata ɗaya kuwa aka yi auren su. Inda ta zauna a gidan sa da ke Bauchi saboda karatu da takeyi. Sati biyu da tarewarta ta ce wa Alhaji ta yi ɓari lokacin yana Lagos.
Amal ta auri Alhaji Sani ne saboda matsin da ake mata a gida na ta fito da miji, saboda shekara talatin da ta ke shirin cikewa. Goggo da ta ke kakarta ta wajen Uba ita ta rantse matuƙar ba ta kawo miji ba sai dai a mata auren dole dan ba zai yiwu mace budurwa ta zauna mu su a gida shekara ashirin da tara ba miji ba. Sanin halin Goggo ya sa ta yi saurin fito da Alhaji Sani saboda shine kaɗai a lokacin zai iya aurenta a ɗan ƙanƙanin lokaci,kuma shine ba zai takurata ba tunda yafi zama a Lagos hakanan matan sa biyu duka suna chan.
Amal mace ce da tun a secondary school ta lalace kasancewar a Calabar su ka fara zama da iyayenta. Ya sa ta ke sha'aninta ba tareda sanin iyayen ba, sai da su ka dawo Kano inda nan ne asalin mahaifinta ta fara takura da sa'ido na 'yan uwa da 'yan anguwa. Diploma ta yi har tana aiki a wani kamfani daga baya ta cika DE ATBU saboda ta samu tayi nisa da gida, zuwanta Bauchi ya sa ta cigaba da sheƙa ayarta ba tareda wani tsoro ba. Inda a Bauchin ta haɗu da Alhaji Sani...
Abotar Nafy da Amal ya ƙara haɓaka, domin yanzu dukkan su biyu suna ziyartar gidan juna. Wani zuwan Amal gidan Nafy ta haɗu da Suhail, cikin hiran su ta ke cewa " Feenah kina auren kyakykyawan saurayi kamar wannan kice min ba ki jin daɗin auren ki, miye matsalar sa?"
Nafy ta yi dariya kawai....
..........................
Lubna ta yi kuka har ta godewa Allah, tun Hudu na lallaɓata yana rarrashi har ya haƙura ya barta. Shi kansa wannan tafiyar ta zo ma sa bazata, abune da bai taɓa tsammanin samu ba sai kuma Allah ya bashi.
A karo na ba adadi ya sake jarraba rarrashin ta "ni wannan kukan na rasa na menene, kukan za ki rabu da mijinki ne har na wata shida ko kuma kukan za ki missing kisses ɗina da hugs da suc....." Lubna ta wurge shi da pillow. Ya fara ma ta dariya yayinda ita kuma ta cigaba da kuka.
A hankali ya ƙarasa wajen ta ya jawota jikin sa ya ce "dan Allah kibar kuka Hayaty, sai ka ce mutuwa zan yi. Abin alkhairi ne fa ya same mu, ya kamata ki godewa Allah ba wai ki tsaya kina kuka ba"
"But hhhhhar wata shida fa"
"Kaman yau ne baby, kar ki damu kullum za mu yi waya sannan ga video call nan. Za ki dinga ganina koda yaushe" Lubna ta yi ajiyar zuciya ta sake shigewa jikin mijinta sosai...
Sai da ya je Abuja yai visa sannan su ka shirya zuwa gidan su Lubna saboda tafiyar ta shi cikin sati biyu masu zuwa ne. A machine ɗin sa su ka je bayan sallar Isha, falon Alhaji su ka fara zuwa kamar kullum. Bayan anyi gaishe-gaishe sannan Hudu ya bayyana abinda ke tafe da shi, kan tafiya ce ta sameshi zuwa ƙasar America na wata shida, saboda wani software da ya ƙirƙira ya submitting a wani gasa Allah ya sa aka zaɓi nashi a matsayin na ɗaya. Kuma kamfanin Google da ta shirya gasar ta nemi ya zo domin a karramashi sannan a developing software ɗin.
Duk rabin bayanin Hudu Alhaji ba ganewa yai ba saboda ƙarancin ilimi da ya ke da shi ta wannan fannin.
Alhaji ya ce " to yanzu za ka bar Auta a ina ne?"
"Dama za ta zauna da su Umma ne har zuwa na dawo ɗin" Hudu ya amsa yana kallon Lubna da ke ta murmushi.
Alhaji ya kalli Lubna ya ce " wai haka Auta, ba za ki dawo ki tayamu hira anan ba"
Lubna ta rufe fiskarta tana murmushi...
Ba su bar gidan ba sai ƙarfe goma.
..........................
Tunda ya tafi kullum sai ta kwana kuka, duk da kuwa su kan yi waya wani lokaci harda video call. Duk ƙarancin sashen na su sai ta ke ga ya ma ta faɗi. Umma ta nemi su Amina su dinga tayata kwana tace ta barsu ai gida ɗaya su ke, idan tana buƙatar wani abu zata mu su magana. Ta faɗi hakan ne dan kar su gayawa Umma tana kuka. Kafin ta saba da rashin Hudu sai da akayi wata, duk weekend ta kan je ta yi a gidan su ne saboda ta taya Mama hira. Duk da Maman ta hanata zuwa amma ta ƙi musamman da Alhaji ya nuna jin daɗin zuwan da ta ke yi.
Wata ranan Asabat tana gyara ɗakin Mama ta ji hajijiya ya kamata da ƙyar ta samu ta tsugunna ta dafe kan ta da ke sara ma ta. A haka Mama ta shigo ɗakin ta sameta.
"Lubna lafiya?" Ta tambaya tana ƙarasowa wajenta
"I just suddenly felt dizzy"
"Sannu ko, kin ga idan ya lafa miki yanzu zamu wuce asibiti kar a kuma irin ta jiya. 'Yan kwanakin nan ina zargin ki gara muje a tabbatar.
Kallon rashin fahimta ta yiwa Maman wadda ta tsareta da idanu...
Gwajin farko aka tabbatar da ciki gareta. Sannan aka bata magani saboda rashin cin abinci da kuma yawan tunani da ta ke yi ya sa mata rashin kuzari da kuma ciwon kai da ta ke ji. Daga asibiti gida su ka wuce inda Mama ta zauna ta fara ma ta bayanin yadda za ta ƙara kula da lafiyar jikin ta...
Mutum na farko da ta so ta faɗawa labarin cikin nan Hood ne, sai dai kuma da ta yi wani tunani sai ta fasa, tanaso ya zo ya ga surprise da idon sa. Ba a jimaba Umma ma ta gano ciki gareta da ta tambayeta rufe ido ta yi tana murmushi.
"Kin je asibiti ne" Umma ta tambaya
"Munje nnnnni da Mama sssssatin da ya wuce"
"To Allah ya raba lafiya"
Can cikin ranta ta amsa da Amin....