Free chapter · Read without an account
Chapter 32
*💮DUK KYAN NAMIJI💮*
............. ....👳.... ..............
0️⃣3️⃣2️⃣
Mama ce ke zaune da ita lokacin da ta farfaɗo, ganinta da ta yi a asibiti ta san asirinta ya tonu.
"Ya jiki?" Abinda ta ce da ita kenan
"Da sauƙi" ta faɗi a hankali.
Ƙarfe goma da rabi na safe aka sallameta har lokacin ba ta ga Hajia ko Alhaji ba. Jikinta duk ya bi yai sanyi. Kai tsaye motar Mama su ka wuce. A cikin motar ma ba wanda yai magana. Sai da su ka yi nisa da asibitin sannan Mama ta ce " kin bani mamaki Nafisah, ashe abin na ki bai tsaya a neman kashe auren 'yar uwar ki ba, harda bin maza. Da ki ka san ba za ki iya riƙe kan ki ba miyasa ki ka kashe auren ki"
"Mama ya isa haka, ba sai kin nemi gaya min magana ba, wanda ki ka yi ranan ya ishe ki. Lubna kuma ke kan ki kin san saurayina ta aura"
"Allah ya shiryeki Nafisa, sai dai ki sani duk abinda ki ka yi ba iya kan ki zai tsaya ba. Darajar gidan gaba ɗaya za ki zubar" daga haka ba ta kuma cewa komai ba har su ka isa gida.
Sai da za ta fita a motar Mama ta ce " Alhaji na jiran ki a falo"
Da ɗarɗar ta bi bayan Mama har su ka shiga falon Alhajin.
Alhaji na zaune jugum lokacin da su ka shigo.
"Fatima kira min Zainab" abinda ya faɗi kenan ya bi Nafy da kallo, tana durƙushe ƙasan kujera chan nesa da shi. Har Mama da Hajia su ka shigo bai ce da Nafy komai ba.
Hajia ma idon ta ya firfito saboda kuka tunda aka ce mu su zubar da ciki Nafy ta yi hankalin Hajia ya tashi, ciki! bayan wata na shida kenan da mutuwar auren Nafyn .
Mama ta miƙe za ta bar falon Alhaji ya ce " ki yi zaman ki"
Ya dubi Nafy ya ce " ke! Ɗaga idon ki ki kalleni"
Ta dai ɗago fiskarta amma ba ta kalle shi ba.
"Ki ka kawo mijin da ki ke so na miki aure, ki ka kashe auren ki, ban mi ki magana ba na barki kina zawarcin ki hankali kwance. Yanzu kuma cin fuskar da za ki min kenan? Dan Uban ki da ki ka san ba za ki iya riƙe kan ki ba miyasa ki ka kashe auren. Iye!"
Ya daka ma ta tsawa
"Alhaji ka yi haƙuri, ka ga ba ka da lafiya" Mama ta faɗi da tausashshiyar murya.
"Ba wannan ba, da uban wa kike shashancin har ki ka samu ciki?"
Shuru ba ta yi magana ba.
"Ba magana na ke mi ki ba!"
Still ba ta yi magana ba. Ya tashi a harzuƙe ya nufi kan ta, ya fara bugunta ta ko'ina. Da ƙyar Mama ta riƙe shi tana bashi haƙuri, Hajia kam tana zaune duk baƙin ciki ya isheta.
"Alhaji dan Allah ka yi haƙuri abi abunnan a hankali, duka ba shine abinyi ba "
Sai da ya zauna sannan Mama ta kalli Nafy ta ce " ke ma ki bashi amsa mana, ba fa isashshiyar lafiya gareshi ba"
Nafy ta ɗago ido ta kalli Alhaji da ya zuba ma ta ido yana huci ta ce " Hudu ne"
"Ya Subhanallah!" Mama ta faɗi cikin kiɗima
"Hudu? wani Hudu?" Alhaji ya tambaya yana neman ƙarin bayani dan shi bai kawo Hudun Lubna ta ke nufi ba.
"Hudu Carpenter, mijin Lubna" ta faɗa kanta tsaye.
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'oun. Kinada hankali kuwa Nafisah"
"Shi ne ma ya ce na cire saboda abin kunya ne ace yana auren Lubna kuma aji ya min ciki. Ita kan ta Lubna ta taɓa ganinmu tare, kawai dai Mama ce ba ta son maganar ta fito shiyasa ta hana Lubna ta faɗa ma ka"
Mamakin kalaman Nafy su ka sa Mama ta kasa magana...
.....................
Yana shago kiran Alhaji ya shigo wayar sa. Ya ɗauka da sauri dama ya kwana biyu bai kira sirikin na sa ba.
Da ƙyar Alhaji ya amsa gaisuwar sa, cikin murya me haɗe da damuwa ya ce " ina son ganin ka yanzu"
Cikin nuna damuwa Hudu ya ce " Alhaji kana kasuwa ko gida?"
"Ina gida" iya abinda ya faɗi kenan ya kashe kiran.
Muryan Alhaji ya nuna akwai damuwa dan haka ya bar shagon a hannun yaran sa. Gida ya wuce a gurguje ya watsa ruwa ya chanja kaya sannan ya wuce gidan su Lubna yana fargaban mi zai tarar acan...
Har lokacin ba wanda ya motsa daga inda ya ke zaune. Kunya da baƙin ciki ya sa Hajia za ta tashi a wajen amma Alhaji ya hanata.
Ganin iyalen haka ya san akwai babbar matsala. Gaishe su yai sai dai Mama ne kawai ta iya amsa ma sa.
Alhaji ya fara bayani "Hudu ka san ina son ka kuma ina ganin girman ka, dan haka ka faɗa min gaskiya tsakanin ka da Allah"
"Tunda ka auri Lubna ka taɓa neman Nafisah?"
Hudu ya zaro ido ya ce " Allah shi ne shaida ta, Alhaji tun da na rabu da Nafy ban kuma neman ta ba"
Alhaji ya kalli Nafy ya ce " ke kuma algunguma maimaita abinda ki ka faɗa mana ɗazu"
Nafy ta fara kame-kame sai da Alhaji ya daka ma ta tsawa sannan ta ce " ni da Hudu muna neman junan mu, shi ya min ciki kuma shi ya ce na zubar da cikin"
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" shine abinda Hudu ya faɗi, ya dafe kan sa yana cigaba da karanto addu'o'in da za su kawo ma sa nitsuwa.
"To kaji abinda ta ce, kuma ta ce Lubna ta taɓa kama ku tare, mi za ka ce gameda wannan?"
Dalla-dalla yai wa Alhaji bayanin abinda ya faru ya ƙara da cewa " Alhaji ka bani lokaci zan kawo ma ka shaidar saƙonni da kuma kira da ta ke min. Na san na goge su amma whatever it takes whatever it will cost za ka ga saƙonnin nan"
Ya kalli Nafy ya ce " ke kuma tunda raba ni da farin cikina kike son yi, mu je zuwa akwai Allah" daga haka ya tashi ya fita...
Bayan tafiyar Hudu Alhaji ya ce kowa ya tashi ya tafi.
Ranan har dare Alhaji bai samu nitsuwa ba, ya fi ganin Nafy ƙarya ta ke ma sa amma kuma idan ya tuna cewa Hudu ya taɓa neman Nafy a baya sai zuciyarsa ta zargi Hudu...
Hudu kam gida ya koma dan ba zai iya komawa shago ba. Ya jima yana jimamin sharrin da Nafy ta ma sa kafin daga bisani ya sawa ran sa dole ya kare kan sa da martabar sa koda kuwa za su shiga kotu da Nafy. A haka Lubna ta dawo daga wajen aiki ta sameshi.
"Mr Carpenter ya akayi kana gida a wannan lokaci? Kar ka zama lazybone fa" Lubna ta faɗi lokacin da ta shigo ta sameshi kwance kan kujera.
Ganin bai amsa ba ya sa ta ƙaraso wajen da sauri " are you Ok, are you sick?"
Jawota yai jikinsa ya rungumeta sosai ya ce " i dont want to loose you, please trust me Hayaty"
" mi ya faru wai, rrrrremember ka ce daga yanzu ba secret tsakanin mu"
"Ki yi hakuri ka da ki ɗaga hankali da duk abinda za ki ji"
Ya warware ma ta duk abinda ke faruwa.
Kallonta ya ke cikin fargaba saboda bai san mi za ta ce ba, fatan sa Allah ya sa ta yarda da shi.
'Yar dariya ta yi sannan ta ce " saboda wannan ka ɗaga hankalin ka"
Mamaki ƙarara ya bayyana a fiskar sa.
"Da gaske ran ki bai ɓaci ba?"
"Ranan Mama ta ce min idan na biyewa Nafy za ta maidani divorcee kamarta, and ni kuma ban shirya ba. I love my husband"
Murmushi yai ya ce " Thank you Hayaty. And I Love you too"...
...........................
Alhaji ya kira Alhaji Inuwa akan yana neman Suhail dan numbar sa da ya ke da shi ba ta shiga. Abba ya ce ma sa Suhail yana Abuja kuma ya sake number.
"Idan ba matsala Alhaji ka turomin numbar da ya ke amfani da shi yanzu"
"Alhaji duk da yanzu babu aure tsakanin Suhail da 'yarka, hakan bai rage girmanka da na ke gani ba. Maganar gaskiya shine Suhail yana ƙarɓan taimako ne a can Abuja. Alhamdulillah saura ma sa wata ɗaya ma a sallameshi kuma gaskiya ya chanja sosai"
Cikin rashin fahimta Alhaji ya ce " mi ya sameshi"
Abba ya ce " ka san yaron nan bai bar shaye-shaye ba har bayan auren sa, abin takaici har cocaine fa ya ke sha"
"Ikon Allah"
"Masha Allahu dan yanzu ya samu nitsuwa ya watsar da komai"
"Alhamdulillah, Allah ya ƙara shiryar ma na da yaran na mu"
Abba ya amsa da amin.
"Dan Allah Alhaji Inuwa ka min alfarma ɗaya mana"...
...............
Kwana biyar kenan da zubewar cikin Nafy, tashin hankalin da ta ke ciki ba kaɗan ba, wannan karan har Anty Amarya da ba ta cika sa baki cikin maganarta ba sai da ta sa baki, sai dai duk inda za'aje ba za ta chanja maganar ta ba dole ne yadda ta ji kunya Hudu ya ji kunya kuma dole auren Lubna ya mutu.
Ladidi ta sameta a ɗaki akan Alhaji ya ce ta shirya ƙarfe huɗu yana son ganinta a falon sa. Dama yanzu Ladidi kaɗai ke ma ta magana daga Hajia har Mama kowa ya fita harkanta, balle Alhaji da ko ƙeyar sa ba ta gani ba tun ranan...
Ana sallar la'asar su ka ɗunguma gidan saboda tun da safe Alhaji ya kira akan yana son ganin su duka biyu da ƙarfe huɗu.
" ka ga mun makara, ƙarfe huɗu harda minti takwas"
"Sai dai kin bani kafin ki fita"
"Oh! Mr Hood kkkka barni na fita fa"
" i just ask for a simple kiss"
Ta ɗan turo baki ta ce " to ka rufe idon ka"
Murmushi yai sannan ya rufe idon sa. Bai ji komai ba sai rufewar ƙofa.
Dariya ta fara ma sa lokacin da ya fito daga motar.
"Kin gudu ko, zan biki bashi ai"...
Alhaji,Hajia,Mama,Nafy su ke nan a falo lokacin da Hudu da Lubna su ka shigo.
A dararance su ka gaisa sannan a kaci gaba da zama wanda kowa a ransa ke canki-cankin musabbabin kiran wannan taro da Alhaji ya yi.
Bayan minti sha biyu da zuwan su Lubna aka kira wayan Alhaji.
"Ka shigo kawai" abinda Alhajin ya faɗa kenan.
Sallamar da su ka ji ya sa dukkan su su ka bi ƙofar da kallo. Sun yi mamakin ganin wanda ya shigo ɗin sai dai Nafy ba a mamaki ta tsaya ba tsoro da fargaba ne ya bi bayan ganin Suhail da ta yi.
Sai da ya zauna ya gaishe da Alhaji da su Mama wanda Alhaji ne kawai ya iya amsa ma sa. Sannan Alhaji ya fara magana
"Na kira wannan taro ne domin a samu mafita kan abinda ya ke faruwa, Suhail zai gaya mana dalilin da ya sa ya saki Nafisah har saki uku bayan auren su shekara ɗaya ne da watanni"
Ya dubi Suhail ya ce "Bismillah"
Suhail yai gyaran murya sannan ya fara ba da labarin abinda ya faru tun daga lokacin da abokinsa ya gaya ma sa ya ga Nafy a hotel har zuwa kamata da yai da namiji a gidan sa.
Hankalin Alhaji ya tashi, jijiyoyin jikin sa su ka tattaso. "Ashe ke karuwa ce Nafisah, dan uban ki anyi haka ko ba'ayi haka ba?"
"Ƙarya ya ke wallahi. Maganan ɗan shaye-shaye ba abin yarda bane" Nafy ta faɗa tana neman tudun dafawa.
Suhail yai dariya ya ce "daɗin abinma inada shaida"
Ganin yana shirin ciro wayar sa a Aljihu ya sa ta ƙwalla ƙara tana kururuwa.
"Ki mana shiru!" Alhaji ya daka ma ta tsawa.
Suhail ya miƙawa Alhaji wayar sa ya ce ka buɗe videon za ka ga gaskiyar komai.
Hannu na rawa Alhaji ya buɗe videon abinda ya gani ya sa hankalin sa ya tashi, wayar ta faɗo daga hannunsa yayinda yai saurin dafe ƙirjin sa yana numfashi da ƙyar.
Mama da Lubna su ka yi kansa da sauri...
©AzizatHamza2020