Free chapter · Read without an account
Page 16
*MUGUN NUFI*
©️ *Nana Haleema.*
*Page 16*
Dak'yar Allah ya taimake shi ya dafa bango ya tsaya da k'afafun sa da suke k'ok'arin gagarar d'aukar sa yana sauke numfashi. Duka akan idon Mima hatta sunan da ya furta ta ji me yace bata da kwarin yin magana ne duk da allurar ta sake ta.
"Auta lafiya?" Mummy ta tambaya tana kallon sa. Girgiza kai yayi alamun babu komai ya fita daga d'akin ya shiga office ya shiga band'aki office d'in yana zubawa fuskar sa ruwa yana kallon kansa a mudubi.
Hoton da aka turo masa ne yake masa yawo a fuska ya runtse idanu ya cize bakin sa ya fito daga band'akin ya zauna a kan kujera yana sauke numfashi, k'arar shigowar sak'o yaji kamar zai share sai kuma ya duba yaga number Husna ce ya bud'e.
_Kayi Hak'uri Dr nayi k'ok'arin komawa yadda kake so amma na kasa jure hakan na riga na saba da maza bazan iya kwana biyu babu namiji ba, nagode da taimakon ka a gare ni ka yafe min da babu lallai ka kuma gani na. Husnah._
Yana kaiwa k'arshe ya mayar da kallon sa sama zufa na tsatstsafo masa daga jikin sa ya b'alle b'allin gaban rigar sa yana ji kamar babu a.c a office d'in sabida zafin da yake ji.
Anty Lubna ce suka shigo ita da Omar suka kalle shi Omar yace, "is done komai ya k'are yanzu, dole ka fita daga lamarin ta tunda baza ta iya cika alqawarin data d'auka ba." Baice komai ba har lokacin wayar tana hannun sa Anty Lubna ta zare wayar daga hannun sa ta karanta message d'in tace, "kema babu lallai ki sake ganin sa karuwar banza da wofi. Yanzu ai ka ajjiye batun ta a gefe ka fuskanci abinda yake gaban ka tunda ba matar ka bace ko k'anwar ka ba."
Shi dai baice komai ba dan Allah kad'an yasan yanayin da yake jin zuciyar sa a ganin sa in ya bud'e baki zaiyi magana aman wuta zaiyi sabida zafin da k'irjin sa yake masa. Omar yace, "Wai kai ina kai ina kishin karuwa?."
"Shirme mana Omar, muje mu bar shi ya dawo dai-dai maganar wata Husnah dai dole ya ajjiye ta in ba haka ba kuma wallahi na had'a shi da Abbah dan shi kad'ai ne maganin sa" ta fad'a suna fita suka bar shi a zaune.
Allah kad'ai yasan lokacin da ya d'auka a haka kafin ya samu ya mik'e ya d'auki wayar sa ya fita. Allah ne ya kare yake tuk'i a nutse dan baya tare da nutsuwar gabad'aya haka yake jin sa kamar an canja shi. A haka ya isa gida ya shiga b'angaren sa ya kulle bai sake bud'ewa ba.
B'angaren Husna tana kwance a jikin Mahmud tana aikin kuka bayan komai ya lafa, shafa kanta kawai yake da bayan ta baice mata komai ba dan yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta k'ok'i. Ganin kukan nata yak'i ya tsaya ne ya saka shi yace, "Haba Baby ya kamata ki daina wannan kukan haka."
Kallon sa tayi tace, "Dr zai min kallon mak'aryaciya mai sab'a alqawari kuma ba haka bane in yanayi na ya tashi bana iya sarrafa kai na." Ya mata kiss a goshi yace, "Kar ki damu bazai ga laifin ki ba ki bashi lokaci kar ki saurari inda yake, kar kije kar kuma kiyi masa waya koda kun had'u a wani waje ki nuna baki gan shi in ya miki magana kar ki kula shi hakan shine zai nuna masa kin san kinyi laifi kuma kina neman afuwar sa da kansa zai nemi ki."
Ta kalle shi tace, "Da gaske kake?."
"Da gaske nake mana Baby kin san ai ina son abinda kike so, ki bashi nan da kamar sati d'aya mu gani." Ta koma jikin sa ta kwanta tana goge ido tace, "To, amma kaima dan Allah in ka ga ina cikin wannan yanayin ka daina zuwa kusa dani ko zan mutu."
Murmushi yayi yace, "Kar ki damu Baby na" ya fad'a yana rik'e ta sosai a jikin sa yana murmushi a zuciyar sa yana gamsar da kansa alaqa tsakanin su ta datse kenan har abadah.
******
Duk yadda Ahmad yaso yakice ajjiye damuwar Husna ya ajjiye kasawa yayi ko yaya ya kulle idanun sa abinda aka turo masa yake gani. Alqawarin da tayi masa yake tunawa lokaci d'aya sai yaji ran sa ya kuma b'aci wani abu mai kama da tsanar ta na neman samun gurbi a zuciyar sa.
Haka ya kwana a zaune bacci sai b'arawo bai samu bacci sosai ba sai an bayan sallar asuba hakan ya saka bai tashi da wuri ba sai sha biyu na safe. Har ya farka bai dawo dai-dai ba a gaggauce ya shirya ya fito shiga cikin gida ya same su har sun dawo gida har Miman suna zaune a falo ya shigo da sallama ya zauna suka gaisa bai ko kalli inda Mima take ba ya mik'e zai fita Mummy take cewa, "Ahmad baka ci komai ba."
"Bana jin yunwa in naje office zan ci" ya fad'a a sanyaye yana niyar mik'ewa. Mamy tace, "Lubna da Omar sun fad'a mana komai akan yarinyar dan haka tun kafin su Abbahn ka suji labari kayi gaggawar ajjiye lamarin ta tunda bata son hakan."
Runtse ido yayi ya sauke numfashi ya kasa ce musu komai yana d'ago ido suka had'a ido da Mima ya d'auke idon sa baice komai ba.
Mummy tace, "Kaji ai abinda akace maka ka bar maganar yarinyar nan kayi abinda zaka iya Allah kuma ya gani ka bar maganar nan bana son ka sake waiwaiyar ta."
Nan ma shiru yayi baice komai Mummy tace, "baka ji bane ba?."
Kallon ta yayi da idanun sa da suke a lumshe yace, "To Mummy to Mamy zanyi."
"Allah ya taimaka" Mummy ta fad'a tana shiga ciki aka barshi da Mamy da Mima. Kamar zaiyi kuka ya kalli Mamy yace, "Mamy...." Sai kuma yayi shiru y fasa fad'a ya mik'e kawai ya fita a zuciyar sa yana kudurin ya bar lamarin Husna har abadah.
*Kaduna.*
A zaune yake ya d'ora k'afa kan d'aya ya gama amsa waya ya sauke wayar daga kunnen sa yana sakin kyakykyawan murmushi kana yace, "Ahmad Abdulsamad, kana wasa dani kana min kallon biri ne ina maka kallon ayaba, kad'an ka fara gani akan lamarin Husna nan gaba sai kaji ina ma baka tab'a sanin Husnah ba a rayuwar ka kenan."
Ya fad'a yana murmushi mai kyau ya kunna video d'in da ya d'auka lokacin da suke kwace da Husnah da Mahmud ya saki murmushi ganin yadda aka cire fuskar Mahmud aka mayar da fuskar Ahmad tamkar shine suke a kwance shida Husnah d'in.
D'aure fuska yayi yace, "Wannan videon makami ne tsarwatsa duk wata alaqar dake tsakanin ku, wannan makami ne da zai saka ka tsani Husnah Ahmad, wannan makami ne da dangin ka da kowa naka zasu tsane ta su tsani rayuwar ta. Kayi hak'uri Ahmad ba b'ata maka suna zan yi ba ina k'ok'arin raba ka da wacce bata dace da kai bane, ina kuma k'ok'arin na had'a ka da wacce ta dace da kai."
Numfashi ya sauke ya koma b'angaren hotunan wayar sa yazo kan hoton Ahmad da Husnah da Mima yayi kyakykyawan murmushi yace, "gwara ki kasance a gare shi da dai y'a ta ta kasance kusa dashi, nafi amincewa da bare a kan wacce na haifa." Abinda ya furta kenan ya mik'e ya shiga ciki yana jin zuciyar sa wasai kamar an wanke ta.
Share it sabida Allah🤗🤗