Free chapter · Read without an account
Chapter 2
Shigo da Motor Zuby tayi, Sadeeq ya rufe musu Gate din Gidan, Da hanzari tayi parking din Motar ta fito, Kare wa Gidan Kallo tayi, sanna ta nufi inda Sadeeq yake, Signer tayi mishi tare da kama hanunshi ta rike cikin nata.
Kissing din yatsun hanunshi tayi tare da sauke Ajiyar zuciya "Dear nayi Missing dinka sosai" Murmushi kawai yayi mata suka karisa cikin Gidan.
'Daya daga cikin Kujeran Palon Zuby ta nufa tare da zaunar da Sadeeq, Juyawa tayi cikin takunta na Yaudara da jan hankali ta nufi Table din dake tsakiyar Palon tare da zama, After Dress din dake Jikinta ta cire, nan Kananun kayan dake sanye A jikinta suka baiyana, dago ido tayi ta dubi Sadeeq da hankalin shi yake jikin Wayarshi.
Ganin haka ya sata yin Magana cikin sigar shagwaba "Dear yau lafiya na ganka so silent?" dago ido yayi ya dubeta, nan idanunshi suka sauka kan Kayan da zuby ta saka! wanda bashi da Maraba da Babu, wani Miyau ya hadiye Mai d'aci daya yatsa mishi A Makogaro.
Ita kuwa Zuby ganin sakon nata yafara isa inda take bukata yasa ta sake turo Kirji tare da kada jiki kamar mazari, wani Murmushi ta saki ganin Sadeeq ya karbi sakonta, Mikewa tayi A hankali cikin takunta irinta yaudara ta isa inda yake, iska ta hura mishi A fuska tare da kai hanunta wuyarshi ta shafo A hankali, Ajiyar Zuciya sadeeq ya sauke tare da zaunar da Zuby gefenshi.
Nan take ta cigaba da Aika mishi da sakon ni masu zafi, kafin kace meye Sadeeq ya rikice, ganin haka yasa Zuby kama hanunshi suka nufi Bedroom, nan suka cigaba da saba wa Allah (Wa'iyazu billah) sai da suka kusa raba daren biyu kafin suka hakura da Juna.
Mikewa Sadeeq yayi ya shige toilet yayi wanka gamida Alola, kayan barci ya saka ya dawo ya zauna gefen gadon, kallon Zuby yayi da barci ya fara Awon gaba da ita.
"Zuby? Sadeeq ya Ambata A hankali, dan bude idanu tayi ta dubeshi, ba zaki tashi kiyi wanka bane? ko haka kike nufin zaki kwana da najasa?" wani irin hamma ta sakeyi tare da gyara kwanciya "gaskiya bazan iyaba sai Gobe ka kyaleni barci na keji" Blanket ta jawo ta sake lullube jikinta dashi.
Tabe baki Sadeeq yayi ya dauki Wayarshi ya fita palo, kwanciya yayi Akan kujera, ya zuba wa slim idanu yana mai cigaba da tunani, A haka har barci ya daukeshi.
Kiran Assalatu shiya dagashi, A daddafe ya mike ya nufi Bedroom dinshi ya dauro Alola ya fito zuwa Masallaci, sai da ya jima A waje yana duba harabar gidan kafin ya shigo, 'Dakin ya nufa, yanda yabar Zuby haka ya dawo ya sameta, har yanzu barcin ta takesha Bilhakki da gaskiya.
Fitowa yayi ya nufi Kichen ya daura Ruwan zafi domin ya samu ya gama shirin Office da wuri, A takaice dai har Sadeeq ya kimtsa Zuby barcinta takeyi sosai.
Karasawa yayi gefen Gadon tare da kwala kiran Sunanta da Karfi "Ke Zuby! wai ko kinsha wasu kwayoyi ne kam? Barci kamar wacce ta kwana tana Aiki?" bude Kananan idanun tayi ta zuba Akan na Sadeeq "Mai yasa zaka matsamin ina hutawa?" Harara ya doka mata gamida nuna mata A gogon dake Makale A hanunshi.
"Da fatan kin gane mai nake nufi, jakar Office dinshi ya dauka ya rataya A kafadarshi, 2Mint na baki ki hanzarta kizo na kaiki gida"
Ficewa yayi A dakin ya koma Palo, wayarshi ya dauko yayi Dialling Number Sadiya, sai da ta kusa tsinkewa kafin ta dauka "Hello Baby ka tashi? ya kake?" Murmushi yayi take fuskarshi ta nuna farinciki "Honney na farka da fatan kema kin tashi lafiya?"
"Alhmdullah Baby, gani na shirya zan fita Office yanzu"
"Masha Allah Baby, Allah ya karemun Kai, please idan ba zaka damuba ka bani 2mnt ina shiri kasan ina da zuwa Hospital" Dariya yayi wanda ya baiyana kyawawan Hakoran shi "Angama Gimbiyar Mata, nima barin hanzarta karna Makara, Allah ya kaiki lafiya Matata"
Dariyar tayi "Ameen Baby" kashe wayar tayi, ta cigaba da kimtsawa, shi dinma Mikewa yayi cikin takaici ya nufi dakin, Zuby tana Shirin fitowa sukaci karo, Harara ya doka mata, ganin haka yasa tayi sauri ta dauki jakarta ta fito.
Sai da ya rufe ko ina kafin ya fito daga Gidan, tana harde A jikin Motor ta zuba mishi idanu, Karasowa yayi gab da ita "Ke lafiyanki kalau kuwa? kin zuba min idanu kamar zaki cinyeni ko kina bukatar Qarine?" karashe maganar yayi gamida yi mata signer, Dariya tayi "Ai idan Kai ne banki mu kwana Ana Abu daya ba.
Tabe baki yayi gamida gyara Keys din Hanunshi, Dear Kullum ina fada maka Maganar nan kana ganin kamar Karyane, Har cikin Zuciyata so Nake naga Mun rayu Har Abada, Amma sam kaki bani hadin Kai Akan Maganar Auren mu" bude Motor yayi baice da Ita komaiba ya shiga.
"Zaki iya shigowa ne ko kuma? kinsan na Makara Ai" A hankali ta bude Motor ta zauna tana Mai kare wa Sadiq Kallo cike da So da Kauna.
Sai da sukayi nisa da tafiya kafin ya juyo ya dubi Zuby dake Kallonshi Kamar zata cinyeshi "Hajiya Ina zan kaiki yanzu?" dan shagwabe fuska tayi "kawai idan ka sami waje ka saukeni zan hau Adai_dai ta" Kallon Mamaki ya bita dashi sai kuma ya dauke Kai, Kamar mai koyar Magana yace da ita "Okey ba Matsala" gefen hanya yayi parking ya sauketa, Kudi ya miko mata masu yawa ta karba sukayi Sallama ta fita.
Zuby tana ganin kulewar Sadiq A layin, tayi Maza ta kira Number wani Saurayinta Akan yazo ya sameta A wajen.
Sadiq kuwa sai da ya biya yayi Breakfast kafin ya karisa Office, da hanzari ya fara Abinda ya kawoshi domin yadan Makara kadan.
Yana tsaka da Aikine yaji ringin din wayarshi, fuska dauke da Murmushi ya dauka tare da karawa A kunne "Ranki shidade Allah yakara miki lafiya da nisan kwana, Kaina A kasa A gafarceni, da fatan kintashi lafiya ya kuke A gidan?"
"Lafiya kalau Sadeeq ya Aikin dai? Ai tunani na fara ko lafiya jiya bamuyi wayaba gaba daya?"
"Ammie kiyi hakuri nikaina nasan nayi laifi Amma kigafarceni, jiya Azumi nayi kuma nadan wahala shiyasa nayi barci da wuri, yau din kuma na tashi A makare shiyasa Ayimin Afwa"
"Shikenan Sadeeq bakomai, dama Abinda yasa nakira, dun Allah Ina So idan kasami lokaci A weekend ka daure kashigo ina da bukatar ganinka"
"To shikenan Ammie Amma inace dai lafiya?"
"Lafiya kalau Akan zancen Auren Haneepa ce, Yaron nan har wajena yazo Akan Ayi mishi Alfarma Iyayenshi sun takura daya fito da Matar Aure"
Ajiyar zuciya Sadeeq ya sauke "Shikenan Ammie insha Allah zanyi kokari nazo"
"Yauwa sadeeq Allah yayi maka Albarka"
"Ameen ya rabbie Ammie na! ina sonki nagode" Kashe wayar yayi sannan yayi iso wa Custumer din dake layi.
Sadiya kuwa taso sudanyi hira da Sadeeq, kiran da Abban nasu yake mata Akan ta hanzarta shiya dakatar da ita, jakarta ta dauka tayi sallama wa Ummi suka nufi Teaching Hospital da Abba.
Tun A motor Abba ya kira Doctor din yake shaida mishi gasu zuwa.
Suna isa Asibiti ba tare da bata lokaci ba suka karisa Cardiollogies, nan danan Doctor ya shiga duba lafiyar Sadiya, sun dan jima A ciki kafin suka fito.
Office dinshi suka nufa dukansu Uku, waje ya nuna musu Akan su zauna, duban Sadiya yayi.
"Qanwata jiki Alhmdullah, domin ina ganin changies da yawa, da fatan zaki cigaba da bamu hadin kai domin ganin An dace?" kada mishi kai tayi Alamar Eh, murmushi yayi mata ya dan rubuta musu wasu Magunguna ya mika musu.
Karba Sadiya tayi "Nagode sosai Doctor" Hanu Abba ya mika mishi sukayi sallama, Mikewa Sadiya tayi suka nufi waje ita da Abba, Har suka nufi Motor Abba fuskarshi dauke da Murmushi, domin yaji dadin labarin Samun saukin da Sadiya take samu, A haka suka isa Gida sai hira sukeyi.
Fadila suna zaune ita da Ummi A palo suna hira Sadiya tayi sallama ta shigo "Kindawo Sadiya? barka ina Abban naku?" zama tayi tare dacewa "wash...Akwai zafi yau gaskiya, Ummi Abba Ajiyeni yayi ya wuce Office"
"Okey to yayi kyau". "Aunty Sadee ya jikin dai?" cewar Fadila, dago ido tayi ta dubeta "Alhmdullah Sister, Doctor ya tabbatar mana dacewa babu wani matsala insha Allah, matukar xan kiyaye bin ka'idojin daya gindaya min! to insha Allah komai zai zamo kamar tarihi"
"Congratulation My Auntie! Allah ya kara miki lafiya"
"Ameen ya Rabbi, ina zakije naga kinsha gaye haka?" mikewa Fadila tayi tare da daukar Mayafinta da Jakarta "Aunty Sadee zan shiga School ne Akwai Abinda nakeso nayi, Juyawa tayi gefen da Ummi take, Ummi barin samu inshiga School din"
Allah ya tsare hanya sukayi mata ta kama hanyar waje, A hankali take takawa harta isa karshen layin Gidan su, ga tsananin zafin Rana da Akeyi, garin babu hasken Rana sosai, Amma sai zafi mai shiga jiki da Ake.
Gefen hanya ta nema ta zauna domin tsayuwar bazai yuyuba, tadan jima kafin wani mai Napep yazo, Murya A sanyaye tace "Mallam Wuntin Dada zani" kada kai yayi Alamar ba zaije wajenba.
Kama kai tayi Alamar damuwa, domin harga Allah ta gaji da zama cikin wannan zafi, gashi babu wajen fakewa, takai Akallah 10minute babu Alamar wani Abin hawa, hakan yasa ta yanke shawarin karasawa Babban hanya.
Tafiya take cikin takunta ta nutsuwa, A haka harta iso Babban hanyar, Alhmdullah ta Ambata ganin Abin hawa sai wucewa sukeyi gwanin sha'awa, hanu tasa ta tare guda daya, tsayawa yayi cak, tana shirin fada mishi inda zata wani Bawan Allah ya nufo Jikin Napep, duban Mai Abin hawan Fadila tayi "Mallam Atap xani" .
"Okey yace da ita, kaifa Mallam tafiyane?" Murmushi Mutumin yayi "kwarai kuwa nima can na nufa" Zuba wa Fadila idanu yayi yana mai zurfafa tunani Akanta, "Mallam kaifa muke jira?"
Ajiyar zuciya ya Sauke tare da shiga cikin Napep din, sai da suka fara tafiya kafin Fadila ta bude Jakarta ta dauko Airphone dinta ta makalashi A kunnuwarta, A hankali wakar da takeji yafara karada cikin kwa_kwalwarta, jingina tayi A jikin Kujeran da take zaune gamida lumshe idanu, tana mai jin dadin sauraron Abinda takeji.
Shikuwa Mutumin nan ganin haka yasa ya maida hankalinshi gareta yana mai cigaba da kallonta, ji yake Yarinyar tana kara shiga cikin zuciyarshi.