Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by Sadiyamuhammadnasir · Mugun gani



A haka har suka iso kofar Makaranta, Kudi Fadila tafito dashi da niyyar bayar wa Mai Napep Mutumin nan yayi saurin  mika mishi "Mallam gashi ka dau kudin gaba daya" Hanu Mai Napep yasa ya karba tare da mika mishi sauran Changi.


Dago ido Fadila tayi da niyyar yin Magana Amma saita kasa cewa Uffan, sabida kwarjinin da Mutumin ya mata, Kana kallon fuskarshi kasan ba Yaro bane, ga cikar kamala data baiyana Agareshi, Jiki A sanyaye ta cire Airphone din dake Makale A kunnenta ta Ajiye A cikin jaka tare da wayarta.


Kanta A kasa tace "Nagode sosai da Karramawa" Fita tayi A cikin Napep din, da hanzari Mutumin ya fito tare da biyota "Um... Dun Allah Mallama kiyi hakuri idan bazan takuraki ba ina son Magana dake, wallahi sabida ke nazo harnan, Dun Allah ki taimaka Maganar ba zata wuce Mintuna Biyu zuwa Uku ba"


Tsayawa tayi cak "Ina sauraronka! saka_makon Girma da kima da kake dashi cikin idanuna, Uwa Uba hadani da Allah da kayi, Amma ina rokonka daka Gaggauta yin Maganar, domin Akwai Abinda zanyi mai mahimmanci Dun Allah"


Murmushi yayi "Nagode miki, Amma bazan so na katse miki Abinda zaki yiba, domin Abinda yake bakina Akwai yawa, sai dai ina bukatar Alfarma daya A wajenki, dun Allah ki taimakamin da Number ki, itace kadai hanyar da zan samu damar yin Maganar da nake son yi dake"


Dafa kai Fadila tayi tare da karanto mishi Number din wayarta, godiya sosai yayi mata, fuskarshi dauke da Annuri, sallama sukayi tashige cikin Makaranta, Wayarta ce ta soma ringin! tsayawa tayi Adan kasar wata bishiya domin ta sami damar Amsawa.


"Hello Rukky, kina ina gani na shigo school, dama yanzu nake da niyyar kiranki"


"Fadila ina hostel ina kwance ya Akayi?"


"Dun Allah kizo ki sameni A department mana?"


"Oh my God wallahi zaki takurani ina dan hutawa ta, ga zafi da Ake kodawa, Amma ina zuwa"


"Yauwa Rukky na shiyasa nake kaunarki" kashe wayar tayi tare da kara sauri karta 'bata wa Rukky lokaci wajen jiranta.


Sai wajen karfe Uku kafin ta kammala Abinda za tayi, saida ta tsaya A wajen Rukky taci Abinci tayi Sallar la'asar kafin ta kamo hanyar Gida.


Tana shiga harabar Gidansu ta hango Motar Sadiq A car park, tabe baki tayi tare da shigewa cikin gidan ta kofar baya, don batama so su hadu bare gaisuwa ta hadasu.


A Kichen ta sami Ummi tana hada Sinasir wa Abba, Ajiye jakarta tayi A kan stole "Ummi na gaji wallahi" Ummi da hankalinta kekan Abinda take tace "Sannu Maryam Fadila ta, Dama Makaranta Ai dole sai An wahala kafin A samu Abinda Ake bukata! Ke da kike burin kibar Qasar ma gaba daya, Ai kinga dole ki zage damtse ko?"


Murmushi Fadila tayi daya baiyana Ainihin kyanta, Karasawa wajen Ummi tayi tare da fuskantarta "Ummi na kinsa duk na daina jin Gajiyar dana kwaso, sabida farantamin Rai da kikayi da wannan zancen taki, Kinsan meye Ummi na?"


"Sai kin fada Fadila"


"Ummi ni Addu'ar da nake Ubangiji ya daurani Akan Abba ya Amince da wannan bukatar tawa, idan har hakan ta kasance zanji dadi sosai Ummi"


"Ameen Fadila insha Allah zaki tafi, kedai kicigaba da Addu'ah" haka suka cigaba da Aiki ita da Ummi har tsawon wani lokaci kafin suka kammala komai suka jera Akan Dinning.


Sai da suka tabbatar komai yayi kafin Fadila takoma kichen ta dau jakarta domin ta isa dakinta, Sadiya ce ta shigo hanunta rike da leda Manya guda biyu, Ajiyesu tayi A tsakiyar Palon ta dubi Ummi dake tsaye jiki Dinning "Ummi Sadiq ne yamin wannan shopping din gasu ki gansu" karasowa inda suke Fadila tayi tana karewa Ledar Kallo.


Durkusawa tayi ta bude ledar tare da ciro komai, baki washe ta dubi Sadiya "Kai Aunty Sadee nayi miki murna sosai, kingafa harda sabuwar waya wallahi" dariya Sadiya tayi "Allah Sarki Sadeeq" Ummi ce ta dubesu "Gaskiya yayi kokari kuma Angode sosai, yanzu ki Ajiye idan Abban naku ya shigo sai ki gwada mishi ko?"


"Toshikenan Ummi" kwashe kayan Fadila tayi ta shige dasu dakin Sadiya tare da nema musu wajen zama, dakinta ta koma ta watsa Ruwa.


Sai karfe Bakwai kafin Abba yashigo Gida, Haka suka fita Palo sukayi mishi sannu dawowa ko wacce ta koma dakinta, yana cin Abinci suna hira da Ummi ya dauko maganar Fadila "Hajiya Zali jiya 'Yarki tazo ta sameni Akan Maganar Fadila, ni bawai ina bakin ciki da Abinda Fadila zata zamo Anan gaba bane, Aa Ace karatu baza'ayi shi Ananba sai Anketare Hazo?


Bana so 'Yan_Uwa na suga gazawata Akan haka" Dubanshi Ummi tayi dakyau "Alhaji kenan Karatun nanfa kowa idan yasami damar nan tura 'Danshi zaiyi, kuma lokaci ya canza yanzu muna zamanine na karatu, Cikin Yan_Uwan naka da kake fadin za suga gazawarka Na yaushe kuma?


Akwai wanda cikinsu ya taba taimaka maka da kobo don hidimar Rayuwarka? Inace su tako suzo inda kake su ganka ma suna kyashin hakan sabida sun Raina Arzikinka? kuma na tabbata idan sune babu wanda zaiyi tunanin yabar wani hidima tasa sabida gudun bacin Ranka.


Dun Allah na rokeka kabar Yarinya taje Makaranta, inhar Akan Ahalinka ne kaki Amincewa" karashe Maganar tayi tare da tamke fuska sosai.


Dubanta Alhaji yayi yana mai nazari sosai Akanta, Tabbas Abinda Zali ta fada gaskiyane, Wasu hawaye masu zafine suka sauka kan idanunshi, A hankali yasa yatsun hanunshi ya share.


"Shikenan Hajiya Zali inhar hakan zai faranta miki Rai taje Allah ya bata sa'ah, kina da kima da daraja A rayuwata wanda bazan iya butulce miki sabida wani bukata don ni keda ikoba.


Kin soni A yayin da Jinina suka gujeni, ina rokon Allah yakara hada kanmu yasa mu rayu cikin Aljanna kamar yanda muke Anan Duniya , ya Allah kana ganin tsaka mai wuya dana tsinci kaina ciki, ka kawomin Agaji cikin wannan lamari, Ubangiji Kaji kan Iyayena"


Durkusar da kanshi yayi yana mai cigaba da zubda hawayen kunci da takaici, Mikewa Ummi tayi ta nufo inda yake jiki A sanyaye "Kayi Hakuri Alhaji da nasan wannan kalami da nayi! ya fama maka mikin dake cikin zuciyarka, Wallahi da banyiba, koda wasa bana so na ganka cikin ya nayi na damuwa, ka gafarceni insha Allah bazan sake ba"


Dago jajaye idanunshi yayi ya zuba Akan Nata "bakomai Hajiya Zali dole ne na zubda hawaye duk sanda na tuna Rayuwata da irin taskun dana fuskanta, wanda har yau Allah bai fitar dani ba"


"Hakane Alhaji Allah yasa mu dace, su kuma Allah ya ganar dasu" wanke hanunta tayi tacigaba da bashi Sinasir din da kanta har sai da ya koshi, Amma gaba daya kana ganin yana yinshi kasan Akwai damuwa A tare dashi, kwashe komai tayi ta nufi kichen dasu, tana fitowa ta samu ya shiga daki, Murmushi kawai tayi ta nufi dakinta domin tayi Sallah.


 

 *WAIWAYE ADON TAFIYA*


Alhaji Bashir Abdul_salam gawurtaccen Mai kudi ne, kuma dan siyasa ne wanda ya Amsa sunanshi kuma Akeji dashi A garin Bauchi Gaba daya, ya rike mukamai Masu Karfu , kuma yayi Aiki tukuru shiyasa har yau An kasa mancewa dashi A wannan Jihar.


Alhaji Bashir yana da Mata guda daya, wanda tun bai gawurta hakaba suke tare, wato Hajiya Salma, Hajiya salma Mata ce mai dattako da sanin yakamata, bata da kyashin takala ko kadan, Hakan yasa Jama'ar Gari ke ganin Kimarta.


Sai da suka shekara biyar da Aure kafin Allah ya basu haihuwar 'Dana Miji, wanda yaci sunan Mahaifin Alhaji Bashir wato Abdul_salam, Alokacin daya rike da Mukamin Senotor.


Ba karamin hidima Akayiba domin nuna farin ciki na wannan kyautar da Allah yayi musu.


Amma banda Kanin Alhaji Bashir wato Alhaji Ali, wanda shi sam baiso hakanba, domin yana kan lissafine idan Alhaji Bashir ya Mutu irin bakin dukiyar dazai samu, Shiyasa ya dauki tsanar duniya ya daura Akan Abdul_salam, duk wata hanyar dazai kuntata wa Salma yana kokarin bi, Amma sam takan yi biris dashi domin A zauna lafiya, bata burin Ace daga bangarenta An wargaza zumunci.


Kuma Alhaji Bashir da Ali Cikin Umma ne, Uwarsu daya Ubansu Daya, kuma su Biyu Iyayensu suka haifa suka bar duniya.


Tunda Ali ya lura da kaunar da Alhaji Bashir yake nunawa Akan Salma da Abdul, nan yayita saka munanan Abubuwa shida Matarshi Hajiya Mairo.


Hajiya Mairo Macace mai kissa da iya makirci, duk hanyar da zakibi don ki fahimci wani Mungun Abu daga gareta sam bazaki iyaba, shiyasa Hajiya Salma ta sake da ita sosai, domin A ganinta kaunarta takeyi, mu samman yanda take nuna kulawa Akan Abdul, hakan yasa har shawari Hajiya Salma takanyi da ita, Ashe ita bata saniba Duk duniya babu wacce ta tsana irinta.


A lokacin da Aka kad'a gangar siyasa, nan Mutanen Alhaji Bashir suka bashi shawari daya fito takaran Govnor, duba da Irin Aikin dakeyi A jahar, A take ya Amince musu, domin dama dansu yake komai, nan danan Aka shiga hidimar siyasa.


Cikin Nasarar Ubangiji suka lashe wannan zaben, tundaga wannan lokacin Tsananin tsanar da Ali yakeyi wa Salma yafito fili, haka yayi kutunguila har sai da yayi nasarar Hada Alhaji Bashir Aure da wata Yar Uwarsu Hajiya Mairo.


Sabida Makirci irinta Hajiya Mairo haka taje har Gidan Hajiya Salma tarinka kuka Akan ita bataso wannan hadinba, domin cin Amana ce Amma sam yarinyar taki Amincewa A janye.


Haka Hajiya Salma tarinka bata hakuri Akan bakomai Shi Ai Aure ibadane inhar za'a zauna lafiya shikenan, A haka har Akayi hidmar biki Aka gama.


Tundaga lokacin da Alhaji Bashir ya Aure Sakina Hajiya Salma ta fara fuskantar Ukubar Rayuwa, Wani lokaci sai taji kamar ta fice A guje, sam Gidan Mijin ya fita mata A Rai, ga tsoron Sakina da takeji kuma ta rasa dalilin hakan.


Sai suyi wata guda sam basu hadu da Alhaji ba, kuma babu mai damuwa da hakan A tsakaninsu, domin shi kanshi Alhaji Bashir din basu barshi haka banza ba, Asiri babu irin wacce basuyi mishi.


Kuma duk wannan Abinda yake faruwa! Akwai Hanun Alhaji Ali dumu_dumu, bayi da burin daya wuce Alhaji Bashir ya kori Hajiya Salma, ya kuma mance da Abdul cikin Rayuwarshi.


Ana cikin wannan hali Sakina ta samu ciki, sosai Hajiya Salma ta nuna farin ciki, Babu irin Habaicin da batayi mata idan sun hadu, Amma hakan bai sa Hajiya Salma kullatarta A Rai ba.


Alhaji Ali kuwa labarin Cikin Sakina na riskarshi da Azama ya isa inda Sakina take, nan sukayi Rikici sosai har saida Hajiya Mairo ta shiga cikin Maganar, Akan cewa ya zama dole Sakina ta zubda cikin Jikinta.


 Domin A cewarshi idan har ta Haifi Yaro Na miji ta ruguza mishi Aiki, Nan Hajiya Mairo ta yanke Shawari Akan idan har Sakina ta haifi Yaro to ya zama dole A Hallakashi, Amma idan Mace ta Haifa to Abarta, ba don Sakina ta soba ta Amince da wannan shawari ta 'Yar_uwarta


  

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.