Free chapter · Read without an account
Chapter 13
Murmushi Sadiya tayi ta sunkuyar da kanta cike da Kunyar Maganar Abba, Shi kuwa Sosai ya tsaya yake kallonta cike da nazari, tabbas yanayin Sadiya ya nuna taji dadin Maganar da yayi "Yar Gidan Abba ina so ki fada mishi idan har da gaske yakeyi, nace ya turo magabata A tsayar da Magana.
'Dago idanu tayi da zuba cikin na Abba, cike da Mamakin Maganar daya fito daga bakin shi "Ince ya turo? Mai_maita Maganar ta sakeyi cikin Zuciyarta, Abban da baya Kaunar inyi nesa dashi koda A cikin Gida, shine yau zaiyi Mun Maganar Aure
Muryarshi ce ta dawo da ita daga tunanin data fada lokaci Guda "Kwarai Sadiya, Nasan kina Mamakin Maganar daya fito daga bakina, Sadiya ina so ki sani, duk son Kasancewa ta dake A Muhalli Daya dole wata Rana dakin Mijinki zaki, Kuma kin kai minzalin da yaka mata Ace kina da Aure, Ya kamata Maganar Fadila tazo A karshe tunda Allah yasa kina da wanda yake Sonki Sadiya.
Tabbas idan nabi ta zuciya to bazan taba baki wannan damar kasan cewa A 'dakin Miji ba, tausayinki shike Rikitamin Tunani A kullum, Ba naso kije ki wahala Sadiya, duk Abinda zai taba zuciyarki bani So, Nida Mahaifiyarki Mu mukasan irin Wahalar da kika sha A Duniya kafin kisamu lafiya haka.
Amma ya zanyi? Ni Musulmi ne! kuma mai Yarda da Qaddara Maikyau ko Akasin haka, kuma tabbas wanda ya yarda da Ubangiji shine maiyi toya gama komai.
A koda yaushe idan nayi Sallah nakanyi Addu'a Allah shi yaye miki wannan Mummunar cutar da kike fama da ita, kuma na tabbata Allah yana jina, domin shiya ce mu rokeshi.
Sadiya duk Abinda zai zamo Farin cikin A gareki To muna So, kuma duk hanyar da zai sadaki da hakan muna bi, Kuma duk Mai hankali da hangen nesa yasan tabbas kina son ki kasance cikin 'Dakin Mijinki! Amma tsananin kunya dayi mana Biyayya yasa kika kasa nunawa koda A fuska.
Ina so kisani Auren da zakiyi bashi yake nufin zaki rasa farin ciki daga gare muba, duk Abinda kike so Sadiya zamuyi miki shi iya Iko, kuma da Gaggawa matukar bai saba wa Al'ada da Addini ba, don haka ki kwantar da hankalinki kiyarda Ubangiji shine maiyi, shima kuma zan fada mishi matsalar inkuma jaaa mishi Kunne, ya rike mana ke Amana! Allah ya muku Albarka"
Ameen Suka Amsa Gaba daya, Murya A sanyaye Sadiya ta dago idanu ta dubi Abba "Nagode sosai da irin kulawarku gareni Abba da Ummi, bani da bakin da zanyi muku godiya, Allah ya saka muku da Alkairi ya bani ikon kyautata muku kafin nabar Duniya" kuka ta fashe dashi sosai, saukowa Abba yayi ya kwantar da Sadiya A cinyarshi tare da shafa Kanta "kiyi hakuri kinji Yar_Gidan Abba, Maganar da nayi miki ne bata miki dadi ba yasaki zubda kwallah?"
Kada mishi Kai tayi da sauri "Aa Abba na, kawai irin Kaunar da kuke nunamin shiya sani zubda hawayen Farin ciki, Hakika ni kaina nasan nayi dacen Iyayen, shiyasa koda wasa bana tunanin na kuntata muku! don ganin baku son bacin Raina, Ina Kaunarku Abba, Batun Sadiq kuwa ya jima yana rokona Akan na bashi dama ya turo Baffan shi Gidan mu Amma naki, dalili kuwa bana son Rabuwa daku, kuna bukatar kuna ganina A kusa daku! sabida lalurar da take damuna"
"Bakomai Sadiya, Soyayyar da zamu gwada miki A yanzu shine mu Aurar dake kuma ga wanda kike So, fatan da zamu biki dashi Ubangiji ya baku zaman lafiya yasa ya rikeki kamar yanda muke rikeki" Ameen suka Amsa gaba daya, Murmushi Abba yayi ya zaunar da Sadiya sannan ya koma Kujera ya zauna.
Shikenan ku tashi kuje dama Abinda yasa nace kuzo kenan" Jiki A sanyaye suka miki suka bar Palon, babu kamar Fadila daji take kamar Ana watsa mata garwashin Wuta A zuciya, Sam bata ji dadin Maganar da Abba da yayi Akan Aunty Sady ba, sam hankalinta yaki kwanciya da wannan Sadiq din, domin Rawar Kanshi tayi yawa.
Ko wacce dakinta ta nufa ta kulle kofa ta nemi waje ta zauna cike da nazari Iri da kala, Sadiya kuwa wayarta ta dauka A kasan Pillow tayi Dialling Number Sadiq. yana kishingide yana dannan systerm kiran wayar ta shigo, Murmushi yayi ya dauka tare da Sallama "Sadiyati Farin cikina barka da dare, Fatan kina lafiya? ina kika Ajiye wayarki nakira baki dagaba kusan sau Uku"
"Huhm wallahi ban ma lura da kiran naka ba, Abba ne ya kirani, tun dazu ina Palo yanzu shigowata"
"Masha Allah! inace Lafiya Diyati?"
"Kalau Baby, magana mai dadi Abba yamin, kuma tsakanina da Kai ne, Amma saika bani tukuici kafin na fada maka wannan zance" rufe systerm yayi tare da gyara zama kamar tana Kallon shi, Fuskarsa dauke da murmushi "Honney nayi miki Alkawari fadi duk Abinda kike so nikuma zan cika miki shi da Gaggawa, domin nasan Watakil nesa ce tazo kusa"
Dariya tayi "Kai Baby? ba wannan ba, Maganar Tukuicina, na baka zabi ka bani Abinda yafi dacewa dani, domin kafi kowa sanin Abinda zai sanyani Farin ciki, kiran da Abba yamin, yace na fada maka idan ka shirya Aure na! katuro magabata Ayi magana Mai karfi"
"Wooow... ya Ambata da karfi, kai Alhmdullah wannan labari yamin dadi, dole ki samu babban tukuici! Maganar waya bazata gamsheni ba, gashi dare tayi da kin ganni A Gidanku yanzu, Diyati kinsan Barci na soma ji? Amma yanzu kinsa duk na daina jin barcin ma, yanzu zankira Ammie in fada mata wannan labari mai dadin, kinsan zance na da ita kenan na karshe Akan maganar Aure na dake! kafin na baro Gombe?"
"Haba Honney Ai dare tayi saurin meye kakeyi haka? kabari dun Allah da safe saika fada mata Ai inaga kamar zaifi, yanzu haka Ammie tayi barci, haka kawai ka tasheta? kuma dun Allah kaima ina so kayi barci kasan Gobe Akwai zuwa office gashi kayi tafiya, idan baka yiba nima bazan yiba Baby"
"Karki damu Diyati! wallahi zanyi yanzu ma kuwa, Maganarki Ai tamkar Umurni ce A gareni, duk Abinda zai takuraki bani So, nasan A halinki ba zakiyi barcin ba" Murmushi tayi "to shikenan karna cikaka da surutu sai da Safe ko?"
"To Allah ya kaimu Sadiyati ina sonki da yawa" kashe wayar sukayi cike da kewar juna, ga tsananin Farin cikin da suke ciki na zancen Abba.
Fadila kuwa gaba daya ji take Duniyar ba tayi mata dadi, Zuciyarta sai mata zafi take wanda ba tasan dalilin Hakan ba, Mikewa tayi zuwa Jikin Kofa tayi Key wa dakin domin bata bukatar damuwa.
Zama tayi Akan stole na Mirro ta saki wani irin Marayan kuka, wanda idan za'a tambayeta dalilin yinshi bata san meye zata fadi ba, takai A kallah kusan 20mnt Tana zubda kwallah kafin taji zuciyarta tayi mata sanyi.
A daddafe ta mike domin Kanta wani irin sara mata yake, Toilet ta nufa ta wanke fuskarta da tayi jazur sabida kukan da tasha, Alola tayi tafito ta gabatar da Sallar isha'i tare da Addu'oi sosai Akan Allah ya tabbatar da Alkairi tsakaninta da Muktar.
Ya kuma kare Aunty Sady daga bakin Cikin 'Da Na Miji A gidan Aurenta, ta jima sosai kafin ta nade Abin Sallah ta kwanta, lamo tayi tana nazarin Rayuwa har barci yayi Awon gaba da ita.
Karar wayarta shiya farkar da ita, ji tayi Kanta ya sara mata, wash ta Ambata tare da jawo wayar, Number Muktar ta gani, Murmushi tayi ta dauka tare da Sallama, da Muryarta kamar wacce zatayi Kuka "Subhanallah Gimbiya, Baki da lafiya ne naji Muryarki haka? ko Barci kike na tadaki?"
Murmushi tayi "wallahi Yaya Muktar Kaina kemin ciwo, kusan dashi na Kwana"
"Innalillahi Sannu Gimbiya Allah ya baki lafiya barin barki ki kwanta ko? dama na fito Sallah ne nace bari Inji ya Amaryata ta tashi"
"Aa Yaya Muktar bazan koma Barcin ba zan mike na gabatar da Sallah"
"To shikenan Gimbiya duk kinsa Jikina tayi sanyi"
"Ka kwantar da hankalinka insha Allah da zaran nayi barci zai lafamin karka damu"
"To shikenan Allah ya kara miki lafiya, Insha Allah kafin na wuce Office zan shigo na dubaki, Ina sonki Sosai Fadila ta" Kashe wayar yayi Zuciyar shi cike da tambayoyi, A haka har ya isa Gidan shi, Fatima tana zaune Akan Sallaya ya shigo, zama yayi A gefen gado gaba daya zuciyarshi batayi mishi dadi.
Tunani ya fara! shin Maiya haifar wa Fadila ciwon Kai, ko dai Abbanta yazo mata da Maganrsu ce kuma ta wata siga, Innalillahi wa'inna Ilaihi Raju'um... ya Ambata A hankali tare da runtse idanu, zuciyar shi tana bugawa da Karfin gaske, yakai Akalla 2minute A haka, kafin ya bude idanu ya zuba A jikin Slim "Ya Allah ka bani Fadila A matsayin Matar Aure! idan hakan Alkairi ne A gareni, ina son Fadila Soyayyar da bantaba yi ma wata 'Ya mace ba"
Fatima kuwa Harta idar da Addu'a ta iso inda yake bai saniba "Yaya lafiyanka kalau kuwa? ka fita gida lafiya ka dawo da damuwa?" Ajiyar Zuciya ya sauke "Bakomai Fati zo mu kwanta"
Kallon Mamaki ta bishi dashi "Inzo Mukwanta fa kace? Dubi Idanuwarka yanda suka koma Jaaa! kace min babu Abinda ya dameka, gaskiya Yaya nikan banga Alamar lafiya Anan ba, sai dai idan bazaka fadamin ba shikenan" juyar da kai gefe tayi ta turo baki, Ajiyar Zuciya ya sauke ya jawota jikinsa, ya rungume da karfi kamar wani zai Kwace mishi Ita.
"Fati na kenan, to Matsalata tana wajenki" zare jikinta tayi daga nashi ta dubeshi "Ni kuma Yaya? ban fahimta ba"
"Kwarai kuwa kewarki nakeyi Amma bana so na takura miki sabida Zazzabin da yake damunki, Amma kamar yanda na fada miki babu wani Abinda yake damuna bayan wannan" Sosai take Kallonshi tana nazari, yanda ya zuba Mata idanu kamar zai cinyeta shiya gaskatar mata da zancen shi gaskiya ce.
Saukar da Kanta tayi Qasa tana Murmushi "Yaya ni takace baka da shamaki A kaina, hakkinka ne Matukar ba ciwo bane ya kwantar dani! zanyi kokarin faranta maka iya iko" kama hanunshi tayi ta rike cikin nata "Nagode miki Fati, ina matukar Girmama Soyayyarki gareni, baki da sa'ah Fati, ina rokon Ubangiji ya Amsa Addu'armu A wannan kwanciya da zamuyi, Allah yasa muga Jinin mu Fati na"
"Ameen ya rabbil Alamina". ta Amsa, Murmushi suka sake wa juna nan zance ya canza salo, 08:00 ya kammala shiri tsaf ya fito, Abinci ya samu Ajere Fati tana dakon Jiranshi, nan yazauna suka fara karyawa cike da Kaunar Juna, yanda yake dura Abincin da sauri yasa tayi gyaran Murya "Lafiyanka kalau kuwa Yaya? saurin meye kakeyi haka? so kake ka shake ne?"
Kallonta yayi yaci gaba dacin Abincin sa "Fati kenan ba sauri nakeyi ba, kawai dadin Abincin yasa nake ci da sauri inaji kamar wani zaizo ya cinyemin" dariya tayi sosai harda tafa hanu "Kai kam Yaya wanda baisan halinka Akan zolaya ba Anbarshi A baya, duk hanyar da zaka kare kanka ka sani"
Signer yayi Mata "na yarda! Kinsan Ance Yabon Gwani ya zama dole, Kuma Ai Matar tawa takai Ayabeta ne tako ina, shiyasa nake Ce miki baki da Sa'ar Karawa Fati na, don haka barni kinji" Murmushi kawai tayi tana Kallonshi, Kaunarshi tana kara rikita mata kwanyar Kai.
Haka ya samu ya kammala ya fito da sauri ya kama hanyar Gidan su Fadila, tun kafin ya isa ya kira Numberta domin ya shaida Mata gashi A Hanya, Ajiyar Zuciya ya sauke! take yaji wani ya ratsa ilahirin Jikinshi, jin Muryarta ba kamar ta dazu da sukayi waya ba.
Ta bangaren Sadiq kuwa! tunda ya gabatar da Sallar Asuba bai koma barci ba, Ruwa ya jona ya fara shirin Office, domin Baya so Ya makara! gashi yana So yaje yaga Sadiya, 07:15 ya fito daga Gida, kanshi tsaye Gidansu Sadiya ya nufa, A kofar Gidan yayi parking Motarshi ya fito, Baba Mai gadi yana zaune Akan 'Yar bencin shi ya hango Sadiq, da fara'a ya karaso ya mika mishi hanu.
"Barka Baba da fatan Antashi lafiya?"
"Alhmdullah Oger yau kaine da safe haka? kwana biyu bana ganinka"
"Eh Wallahi bani Gari ne Baba naje gida ganin Mahaifiyata"
"To Alhmdullah haka Akeso Allah yakara lafiya mai Anfani"
"Ameen ya Ambata ya wuce ciki, kiran wayarta yayi ringin daya ta dauka kamar mai Jiran Kiran "Baby Barka da safiya ya katashi?"
"Barka Sadiyati, lafiyata kalau gani A harabar Gidanku" dafa kirji tayi "Kai Baby da wuri haka?"
"Kece kike ganin tayi wuri, karfa ki manta Aikina Akwai doka, ba'a latti, ke dai fito kawai"