Free chapter · Read without an account

Page 4

by BIL-SAN · WASU MAZAN

FREE

_Page 4_ 


*WASU MAZAN!*💔

_written by_

*BILLY S FARI*💎


*©️HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*


Gaba d'aya sun manta a inda suke sai masha'arsu kawai sukeyi, yayin da ita kuma Zeenat kecan tana qoqarin yin abunda zai faran tawa zuciyar mijin nata kafin yadawo,


Kimanin mintuna 40 suka d'auka a haka suna abu d'aya, Aasim ko sai sabbatu take yiwa Azeema tamkar wani wanda bai tab'a sanin mace ba aduniya, sai da yaji ya samu natsuwa sosai sannan ya fad'a ta gefenta kwance yana fitar da lumfashi a hankali, ita kuwa juyowa tayi had'e da d'ora kanta saman hannunsa tana wasa da lafiyayyen gashin dake kwance akan qirjinsa, 


"Aasim kai jarumi ne, bansan taya zan iya rayuwar aure ba in babu kai, pls na roqeka daka zo muyi aure" Azeema ta fad'a had'e da mirginowa tahaye ruwan cikinsa tana kallon idanuwansa,


"Aure Azeema? Kuma tsakanin ni dake?, ehmmm...Zanyi tunani akan hakan" ya bata amsa yana jajjaye qarin gashin daya fad'o mata a fuska izuwa bayan kunnuwanta,


Wata irin zabura tayi daga jikinsa had'e da miqewa tana tattara kayanta da sauri jin ana knocking a bakin qofar office d'in nasa sannan ta shige toilet d'in dake ciki, shi kuwa miqewa yayi hade da jan wani irin dogon tsaki saboda ba qaramar takurasa kowaye yayi ba, 


"Waye?" Ya fad'a a kasalance yana kimtsa kansa sannan ya koma mazauninsa tare da bada izinin shigowa,


Wani dogon tsakin ya sake ja ganin abokin nasa Anwar na shigowa,

"Mtsss...Kai banza ne wlh, na zata ma wani costomer ne ko kuma wasu baqi na musamman ashe kaine kazo ka katsemun jin dad'i! Mtsss.. man bakayi ba" mere baki Anwar dake qarewa office d'in nasa kallo yayi tare da neman d'aya daga cikin kujerun dake gaban teburin nasa yace,


"Aww to ko nakoma har ka qarasa jin dad'inka tunda ka zama d'an tsako...?"


"Sama kaqi dangi ba" ya qarasa masa karin maganar yana dariya suka tafe,


Daidai lokacin Azeema data gama shiryo kanta had'e da gyara jikinta ta fito tana taunar cingwam tare da nufar inda jikkarta take ta d'auka ta sagala a hannu had'e kallon Aasim da shima kansa ita yake kallon, ta ce


"Babyy am going, sai kuma yaushe?"


"Duk lokacin da yayi maki, but kafin kizo ki kirani, akwai wani abu na musamman da nake son tanadar maki, but before meet my friend Anwar" ya qare zancen yana murmushi tare da nuna mata Anwar da hannu da tun fitowarta ya tsareta da idanuwa, 'yan yatsun hannunta ta d'aga masa had'e da cewa,


"Hi Anwar barka da safiya"


"Hi..." Sai kuma ya kasa qarasawa tunda baisan sunan tab'a,


"Azeema" ta bashi amsa ataqaice tare da maida kallon nata ga mintin zuciyar tata wato Aasim,


Wata 'yar loka ya jawo dake jikin teburin dake gabansa hade da ciro rafar 'yan d'ari biyar biyar guda biyu ya taso yazo inda take ya saka mata acikin jikkarta sannan ya kamo hannunta yyi mata kiss,


"Thanks for the unexpected visit"


"Thanks Baby" ta fad'a tare da hugging d'insa tayi kissing gefen fuskarsa sannan ta fice,


Saida ya gama ganin fitarta tukuna ya dawo inda take ya zauna yana kallon Anwar dake shafar gemunso,


"Lafiya?"


"Kai sh*** ne Asim, a ina ka samo wannan zuqeqiyar yarinya kyakkyawa, kaga shape d'inta kuwa?"


"Then?"


"Haba ai malan yarinyar nan tayi"


"Kana so ne?"


"Ban fahimta ba, ba yarinyar ka bace?"


"Eh, Amma sam bazan iya aurenta ba, idan da gaske kakeyi nayi mata magana ko ALLAH zaisa ta taimaka bana mufiddaka a sahun gwauraye"


"Haba, wuce nan man, 'yar iskar zan aura?"


"Au kai ba d'an iskan bane?" Asim ya fad'a yana kwashewa da dariya har dasu dukan tebur, d'aure fuska Anwar yayi had'e da cewa,


"To ko d'an iskan nake sai naqare a auren 'yar iska? Kuma 'yar iskar ma taka? Tab! ALLAH ya kiyaye, kawai dai jin dad'in nan ne da kukeyi nake so nima na d'an d'ana, amma sam nikam bazan iya aurenta ba"


"Ai kuwa nikam bazan bari hakan tafaru a tsakanin kuba, Azeema tawace sai kuma mijin dazai aureta"


Zaro idanuwa Anwar yayi tare da cewa,


"Tab! To da hakan kai ka aureta mana"


"Zeenat fa?"


"Ka had'a su biyu"


Dakatar da cike-ciken files da yakeyi agabansa yayi tare da zubawa Anwar d'in idanuwa ya ce,


"Ai bazan iya auren kowace macce ba na had'a da zeenat, son da nakeyi mata nada matuqar girma da tasirin da bazan iya had'ata da kowace irin macce ba da sunan matata, Zeenat wata duniya ce daban a rayuwata da bana fatan wata halitta ta ziyarci wannan duniyar"


"Wannan ai zancen banza ne kakeyi Asim, tun yaushe kagama had'a Zeenat da wata macce?"


"Amma ba'a matata ba ko? Nifa duk matannan da kake ganin ina bi babu wacce nake so acikinsu, balle kayi tunanin zata kai matsayin da zan iya had'ata da matata zeenat, kawai aji dad'i ne a kuma more"


"Ai kuwa ina tausayawa ranar da jin dad'in nan naka zai qare, don kuwa idan zeenat taji wannan zance.."


"Dakata Anwar, don me zaka yimun irin wannan mugunyar fatar, taya Zeenat zataji wannan zancen sai in kai zakaje ka fad'a mata" Asim ya dakatar dashi cikin b'acin rai,


"Maida wuqar bawan ALLAH, ta Ina zanga Zeenat kai da baka barin muje gidanka, beside kasan ni kowaye, a matsayina na babban amininka ko wani yace ma zan aikata haka ai bazaka yarda ba balle har kayi wannan tunanin da kanka, let close the chapter muyi abunda ya kawoni"


Ajiyar zuciya Asim da tuni zuciyarsa tagama b'aci yayi tare da cewa,


"Ai kai d'inne baka da alqibla wani lokacin, Yi kake tamkar baka san kowaye ni ba, wlh da Zeenat taji wannan zancen qwanda narasa dukkanin abunda na mallaka aduniya, don na tabbata guduwa zatayi tabar ni, ni kuwa bazan iya jurar hakan ba"


"To kuwa idan hakanne sai kariqa taka tsantsan, kasan su mata ko cctv camera bata kaisu hange da iya tsinkayo abuba"


"Naji, uban 'yan iya magana, yanzu meke tafe dakai?"

seda ya gyara zamansa tukuna sannan yace,


"Maganar nan dai ce Alhaji Bukar ya sake turoni akan had'a hannun jarin da yake so kuyi ku saye kamfanin shinkafar nana (NaNa rice)"


Biron dake hannunsa yasa ya d'an murza gefen gashin kansa had'e da cewa,


"Amm..Anwar, nifa hannun jarin nan ba zan siya ba? Kawai yayi haquri ya nemi wani"


"Asim, kamfanin NaNa rice nada matuqar inganci d'ari bisa d'ari wajen sarrafa shinkafarsa, sune keda kaso sittin bisa ukku aduk fad'in qasar nan wajen cinakin shinkafa, a tawa shawarar, kaje ka sami hajia ka sanar da ita komai, kaga duk abunda tace sai kayi amfani dashi"


"Eh hakane, kaima ka kawo shawara, wato ba son siya ne ba nayi ba, matsalolin Alhaji Bukar d'inne nada yawa, shine rikici da wancan kamfanin, shine rigima da banki da dsi sauransu, shiyasa bana so natura kaina aciki tunda nasan halinsa, amma dai zan tuntub'i hajiyar, zuwa jibi zan sanar maka da duk abunda kenan"


"To shikenan babu damuwa, ai inaganin in sha ALLAH babu wata matsala, tunda a gabanka gaban kamfani, shedu da kuma shi za'a hannunta takardun kamfanin gareku, tabbacin cewa mallakinku ne da komai ma duka na arubuce, kaga kuwa duk rigimarsa dole ya shafa maka lafiya"


"Shi kenan, sai dai kaji yanda mukayi da ita"


Ya jima a office d'in suna fira shi kuma yana rarrage ayukkan dake gabansa kafin akira sallar azahar su miqe tare subar office d'in, masallaci Anwar ya nufa bayan sunyi sallama shi kuma ya nufi wajen motarsa ya tayar yayi gida,


***. ***. ***


A daidai bakin qofar wani d'an matsakaicin gida mashin ya ajiye umman shurieym ta tsaida sa ta shiga cikin ta karb'o masa kud'insa ta kawo masa sannan ta koma ciki,


"Maraba lake, maraba lale"


Kyakkyawar dattijuwar dake tsakar gidan tana sanwa ta fad'a tare da shimfid'awa Umman shurieym tabarma a gefen d'aki dake cikin wata doguwar baranda, fuskar Umman shurieym a sake ta ce,


"Adda barka da marece, mun same ku lafiya"


"Lafiya lau Batulu, ya mazajen nawa? Duk lafiya suke na ganeki ke kad'ai?"


"Lafiya klw Adda, girki kike? Bari na kama maki"


Shiru Adda tayi tana nazarin idanuwan Umman Shurieym da suka cika taf da qwalla, ba tare data hanata ba ta miqe itama ta d'auki jikkar data zo da ita takai cikin d'aki ta ajiye, fridge ta bud'e ta d'auko ruwa tare da dawowa ta d'ora akan shimfid'ar ta zauna,


"Zo Batulu ko ruwane kisha mana kafin kifara halin naki, ke kenan idan kinzo gidan nan bakya bari ko d'an motsa jiki nayi, yi wannan yi wancan ko gajiya bakyayi, ALLAH dai yayi maki albarka yajiqan mahaifinki da mahaifiyarki"


"Amin Addah, ina Yaya Ali ne?" Ta fad'a tare da zaunawa kan shimfid'ar ta d'auki ruwa d'aya dayake na pure water ne tasha, sai da ta shanyesu tas sannan ta d'ora ledar akan plate d'in da Addah ta d'oro ruwan akai ta d'ago tana kallonta, 


Duk qoqarin ta na ganin ta danne hawayen dake neman zo mata hakan gagara yayi, wani irin kuka mai cike da ban tausayi ta fashe dashi tare da fad'awa jikin Adda tana jin wani qatoton abu mai d'aci ya tsaya mata awuya, shi bai wuce ba kuma shi bai fito ba sai kokuwa yakeyi da igiyar lumfashinta,


*ALLAH KAJIQAN IYAYENMU 👏*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.