Free chapter 路 Read without an account

Babi na takwas

by BIL-SAN 路 FIL HUB

Free page 8


    *FIL-HUB*鈾ワ笍

           (Acikin so馃挊)

Paid Book: N500

  Written by

     Billy s fari馃拵

______________________________

  Ko da suka isa makarantar har anfara Assembly hakan ya sa bai tsaya bi takanta ba ya wuce gaban Assembly 蓷in inda malamai ke tsaitsaya, yana hawa wajen gaba 蓷aya idanuwan student suka koma kansa sai maganganu ke tashi sama sama na yanda suke yaba ha蓷uwarsa da tsarinsa, bayan an kammala duk wasu activities da aka sabayi wajen assembly 蓷in principal ta juyo ha蓷e da kallonsa cikin harshen turanci ta ce yazo ya gabatar da kansa ga student da kuma subjects 蓷in da zai 蓷aukesu, ganin yanda gaba 蓷aya suka zuba mashi idanuwa ya sashi 蓷aure fuska ha蓷e da takowa zuwa gaban assembly yanda zasu ganesa daidai, cike da 茩warewa cikin harshen turanci daya bala'in zauna masa ra蓷am a baki kai kace tun asali dama can Bature ne ya fara magana.

   "_Good morning student, sunana Hisham s dala, ni ne wanda zanci gaba da 蓷aukarku darasin Physics, ina fata kowane 蓷alibi zai bani ha蓷in kai wajen mayar da hankali, ina da matu茩ar sau茩in kai ga wa蓷anda suka maida hankalinsu ga abunda ya kawo su haka kuma ina da zafi sosai ga wu蓷an da basu san me ya kawo su ba, thanks to meet you all_"


Ya 茩are maganar ha蓷e da sakin murmushi yana 蓷aya masu hannu, gaba蓷aya tafi 蓷alibban suka saka tare da ha蓷a baki wajen cewa, "Thank you uncle Hisham, you're highly welcome to sardauna acadamic science school". Kamar dai yanda aka saba yiwa kowa ne sabon malami idan ya zo makarantar, Nauwara ce ta yi murmushi ha蓷e da juyowa ta kalli Madiyam da ta yi tsaki 茩asa-茩asa saboda jin haushin yanda aka wani karrama Hisham 蓷in, duk da kuwa ta san cewa al'adar makarantar ta su ce, ta ce "Madiyam ya akayi yau naga kinyi sakkon zuwa makaranta, ko dai aikin ya Hisham ne?" Ta tambaya don ta san halin Madiyam, ba ta shigowa school sai kusan takwas da rabi duk da tsananin da akeyi wajen taron latti, banza Madiyam ta yi da ita don har yanzu haushinta take ji tare da wuce wa class 蓷insu don assembly 蓷in ya watse.


SS 2 green nan ne class 蓷in su Madiyam a kujera ta biyu layi na farko ita da wani yaro ana kiransa Abdallah, tsarin makarantar kenan macce da namiji ake zama don private school ce ba ruwansu da wata a茩ida ko al'ada, ya yin da ita kuma Nauwara ke kujera ta farko duka anan layi na farko, sai da ta zauna sit 蓷inta sannan ta ce,


"Nauwara ha蓷in mun littafaina duka ki bani".


"Wai lafiya Madiyam? Hakama meya faru?" Ta fa蓷a ha蓷e da juyowa tana kallonta, kauda kanta gefe ta yi kafin tace, "Ba komai, kawai bana son harka da wula茩anci ne? Don na fahimci shi ya dodo yake son tata mun cikin mutane 茩ara in kama kaina kafin hakan ta faru". To 茩are zancen tare da mi茩a hannu ta jawo Jakar ganin ba tada biyar bata sai ma zubo mata idanuwa da ta yi cike da mamaki, ba tare data damu da hakan ba ta kwashe duka littafanta da sauran abubuwan karatunta dake ciki sannan ta mi茩a mata jakar tana fa蓷in,


"Menene wai? Na fa蓷a maki dalilina to meye na zuba mani idanuwa kina kallo kuma?"


"Babu" Nauwara ta fa蓷a tare da kar蓳ar jakarta tana tunanin ko me ya sa Madiyam ta yi hakan, don sam bata yarda da hujjar data bata ba.


Math suke da ita period ta farko da ta biyu, sannan Physics period ta uku kafin a fita breakfast, hakan ya sa Madiyam shiga tsoro da kuma tashin hankalin abunda zai faru idan ya Hisham ya shigo, don har ga ALLAH ba tada littafin Physics ma gaba蓷aya saboda yanda ta tsani subject 蓷in, sama-sama ta saurari fahimci bayanin da mai math 蓷in keyi masu har ya fita ba tare data iya komai ba, ko mintuna biyar bai yi da fita ba Hisham ya shigo fuskarsa a sake ba yabo ba fallasa, bayan sun gaishesa ya sake gabatar masu da kansa sannan ya shiga tambayar sunansu 蓷aya bayan 蓷aya suna fa蓷a masa har aka zo kan Madiyam, "You oyonbo, what is your name?" Ya fa蓷a don kusan tafi kowa haske cikin ajin, wani irin haushi ne ya kamata jin sunan daya kirata dashi ha蓷e da 蓳ata rai sannan ta ce, "Hauwa'u A dala". Ta fa蓷a tana turo baki, dariya ce ta kubcewa Abdallah deke kallonta ya yi saurin rufe bakinsa, "stand up" Hisham ya fa蓷a yana 蓷auke fuska don dama tunda ya shigo ajin ya ji tsarin zaman nasu bai yi masa ba kwata kwata, don sai da ya ji wani abu ya dakar masa zuciya ganin Madiyam tare da wani zaune waje 蓷aya, wata茩ilma har jikinsu na gugar juna, nan take ya ji wani irin kishi ya rufesa amma sai ya yi saurin tausar kansa, yanzu kuma ganin irin kallon da Abdallah keyi mata yana dariya ya sa abun ya motsa masa, nan take ya shiga sauya masu wajen zama, inda ya tada namijin dake tare da Nauwara a sit 蓷in gaba ya maido Madiyam a wajen, shi kuma Abdallah ya maida shi acan sit din baya tare da wani namijin, shi kuma ya 蓷auke maccen dake tare dashi ya maida wani wajen tare da macce 拼ar uwarta, nan take ya hautsine ajin gaba 蓷aya ya canza tsarin zamansu zuwa macce biyu a sit 蓷aya sannan namiji biyu a sit 蓷aya a bayansu sai kuma wasu mata biyu a sit 蓷in bayansu, ya kuma tabbatar masu da cewa daga yau haka zasu ri茩a zama musamman idan lokacin period 蓷insa ce, 


Ji Madiyam ta yi kamar ta aza hannu ta fashe da kuka ganin ta a sit 蓷in gaba, abunda ta fi tsana a rayuwarta kenan amma ya zo ya mai dota a wajen tsabar mugunta, yana ganin yanda take faman turar baki tana wani jajjaye jikinta ga Nauwara ya yi banza da ita ha蓷e da fara karantar dasu, cikin gwanewa ya fara gabatar masu da topic 蓷in da za su fara dashi ha蓷e da yi masu bayani a ta茩aice sannan ya ce su fiddo littafansu su fara rubutu don dictation zai yi masu ba note a board ba, salon d'aya shiga dashi cikin ajin na sassauya masu wajen zama shiya haifarwa da 蓷aliban mutuwar jiki ha蓷e da shiga taitayinsu, inda nan take suka fiddo littafansu ya fara yimasu dictation 蓷in suna rubutawa in banda Madiyam da tayi zaunenta tana wasa da bironta a saman benci, "Stand up". Ya fa蓷a tare da cigaba da abunda yake yi ba tare daya kalleta ba har suka cika paper 蓷aya suka juyo, sanin da ita yake ya sa ta mi茩e tsaye tana jiran me zai ce mata, bai kula ta ba har sai daya gama sannan ya 蓷ari kai yana kallonta, cikin harshen turanci ya ce,


"Me yasa bakya rubutu kamar sauran 蓷alibai?" Shiru ta yi masa bata ce ko uffan ba har sai da ya sake jeho mata tambaya ta biyu, " ina littafin ki?" Sannan ta ce,


"Ba ni da shi".


"Very good, wato irin ku ne 蓷aliban dake cutar da iyayensu bakwa tsayawa kuyi karatu, kuna sa suna hasarar biya maku ku蓷in makaranta da kuma na tara, a maimakon haka kamata ya yi ace kun zauna gida kun fa蓷a masu cewa ku bakwa son karatu wata 茩ila aure kuke so, sai su hutar da kansu da kashe ku蓷insu a banza, no matter what kike ganin kina da kyau matu茩ar baki tsaya kikayi karatu ba to kyanki na banza ne, beauty is nothing when the brain is empty, yan da kike ganinki a haka ilimi ne kawai zai taimakonki a rayuwa, all this 蓷aukar kai da shan toka da fizge fizgen kai da kike yi ba zai ta蓳a helping 蓷inki a rayuwa ba, so you better change before I decided to change you by force, and next time idan bakya da littafi kada ki shigo mun aji, idan kuma kika yarda na shigo bakya ciki to tabbas ki kuka da kanki don bazan 蓷auki wannan shashancin a acikin class 蓷ina ba".


Ya 茩are zancen tare da 蓷ago kai yana kallon sauran 拼an class 蓷in ya ce, "we can hold it next time" sanan ya fice daga ajin jin an tashi break.... 





*ALLAH KA JI茦AN IYAYENMU 馃憦馃槶*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.