Free chapter · Read without an account
2
DA UBA AKE ADO
(Bada riga ba)
HASKE WRITERS ASSO💡
*بسم الله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…*
ZAYNAB BAWA
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid ₦ 300
*ƘADDARAR RAYUWA*
*BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI?)* ₦500
*IYALAINA (A'ilaty) ₦500
Page 2
Haba Aysha wannan wane irin saurine haka? Yakamata kijiramu fa sai kace wacce zaki tashi sama.
ÆŠan dakatawa tayi da saurin da take."Banason jerawa da wannan Æ´ar raining hankalinne bakiji maganganun da takeyi ba? Sai kace tace na koya mata fillanci nace bazan koyarda ita ba,
"Da'allah shareta nima ai naji haushin maganarta tunda mahaifiyata bafulatana ce kuma itama kishi kawai ke damunta amma kina kallonta kinga bafulatana ai, tanajin haushin yaran fulatanci da bata iya bane a matsayinta na bafulatana shiyasa takeson huce haushi akanki" Badiyya ce take maganar cikin son kwantarwa da Aysha hankali, Nadeeya tasake cin murr taji an taɓo mata yanda yake mata ciwo.
"Da'Allah rabu da ita duk duniya babu wanda ta raina irina ni kaɗaice nake faɗan maganar da take ɓata mata rai amma bayan ni kowa zaiyi abu sai dai ta kalleshi ta wuce sai tsoro kamar farar kura"
"Koma menene ai kema haka kikemin koh?" sukaci gaba da magama har suka ƙarasa cikin asibitin gynea wards suka nufa Saboda nan ne fanninsu bayan sun gaisarda manyan Doctors da suke office sannan suka nufi office na Dr Hadiza bayan knocking tabasu umarnin shigowa, Babbar matace a ƙalla takai 55years tana zaune a kujerarta tana aiki a system, bayan sun giasheta ta amsa da fara'a sannan ta ɗauke kanta daga system zuwa garesu.
"Ma sha Allah kun shigo kenan?" tun safe ma Mommy mun tsaya É—aukan darasi ne" kai Dr ta jijjiga. "Toh ga aikin ku nan kowa da files dana ajiye mata kowacce akwai patients da zata duba a ciki" É—aya bayan É—aya ta nuna musu wanda zasu É—auka kowacce ta É—auki nata Zulaiha da ChubaÉ—o kuma nasu babu yawa.
"Mummy yau aikinmu babu yawa kenan?" chubaÉ—o ta faÉ—i.
"Eh zaku juyo nan kafin 12 dan Dr Hafiz yasaka sunanku a Surgeryn da zaiyi a lokacin saiku samu nutsuwa kafin time É—in idan kun dawo dawuri"
"Aysha akwai aikin da zasuyi da Dr Ahmad idan yashigo tace nayi assiting dr ni kaÉ—ai, da yamma zasuyi aiki itama" zulaiha tafaÉ—i. Harara Aysha ta wurga mata jin tace Dr Ahmad. Dasauri Zulaiha ta gyara harshenta
"Oh sorry Abbanta" ƴar dariya Dr Hadiza tayi ta gyara gilashin idonta, "Anywhere shi Dr Hafiz zai sanar daku yanda za'ayi and koma ba wannan ba ki dawo dawuri nan akwai file da nakeso ki dubamin zanyi tafiya akwai patients da nakeson damƙata ƙarƙashin kulawarki" kai na gyaɗa mata mukayi mata Sallama muka fita kowacce takama hanyar yanda zataje.
Nida zulaiha cikin ƙanƙanin lokaci muka gama duba patients data haɗamu dasu muka dawo mata da files duk wani abun daya kamata muka sanar mata bayan mun rubuceshi a cikin files ɗin Zulaiha ta sallami kanta domin taje tasamu hutu dan baifi saura 30minute 12 ɗin tayiba. bayan tafita Dr Hafiza ta dubeni.
"Aysha Dr Hafiz banjin zai ɗaga ƙafa akan surgery ɗinnan dan sunanku yashiga list a shawarce kawai kije kiyi, surgery da zakuyi bazaifi 1:30minute ba zaki samu interval na 2hours kafin mahaifinki yazo, nasan zakiga kaman muna baki aikin dayafi ƙarfinki No bahaka bane domin kuwa Mahaifinki yasamu horaswa fiye da haka kamar yanda kike da ƙoƙari haka mahaifinki yake muna school shine best student da banajin akwai kamarsa kamar yanda kika gani har yanzu babu kamarsa a cikin likitocin da muke dasu, wata rana ki samu lokaci ku zauna da mahaifinki zai baki labarin lokacin muna makaranta da yanda muka horu har muka zama abunda muka zama a yanzu, munaso ke idan kika tashi kifimu ƙwazo da jajircewa, nasa yaƙini akanki in sha Allah zakiyi har zakifi haka, mahaifinki yasaka hope akanki sosai shiyasa har ya ɗauraki a wannan layin, abubuwa dayawa sun faru kafin samuwarki a duniya tun kafin kizo duniya mahaifinki ya ɗaura muradansa dayawa akanki kiyi matuƙar ƙoƙari wajan ganin koda wannan mutaɗi guda ɗaya baki watsa masa ƙasa a ido akansa ba, idan kinsan ma'anar sunanki da mahaifinki ke kiranki dashi (Chubaɗo) nan zaki tabbatar da cewa mahaifinki ya zaɓeki akan wasu lamura na rayuwa. dan haka kitashi kije kushiga surgery da Dr Hafiz wannan ma wani ƙarin ɗaukaka ce da yar dar Allah" kai chubaɗo ta gyaɗa.
"In sha Allah Mommy zanyi hakan"
"Yawwa Allah yamiki albarka yasa kuyi surgery cikin sa'a"
"Amin Mommy nagode" chubaɗo tayi mata sallama tatashi tafita" kai tsaye ɗakin da likitoci suke shiryawa idan zasu shiga surgery ta nufa tasamu zulaiha harta fara shiryawa cikin sauri ta saka Surgery outfit blue tayi kyau sosai ta tattar kayanta ta sanya cikin drawer ta atare suka fito suka nufi wajan doctors da suma sun rigada sun shirya lokaci kawai suke jira, Dr Hafiza matashin likita wanda bazai wuce 35years ba shine ya tsaya yayi musu bayani sosai akan surgeryn da zasuyi tunda dama shine zaija ragamar Surgery ɗin bayan yagama musu bayani suka shiga daga palourn wajan theatre room suka wanke hannunsu sukayi ciki daga nan bata sake bari hannunsu yataɓa wani abunda har saida suka shiga theatre room ɗin suka sanya hand-globe kowanne daga cikinsu yasan abunda zai kama kowanne ya tsaya a matsayarsa bayan komai ya kankama an duba am tabbatar babu wata matsala za'a iya fara gudanarda aiki Dr Hafiza yafara gudanarda aikinsa cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki Chubaɗo na gefensa tana bashi duk wani taimakon dayake buƙata. Hysterectomy Surgery shine aikin da suka gudanar akan wannan matar bayan matsalmtsalu da take samu wajan haihuwa sannan da bincike yayi bincike suka gano akowani irin lokaci akwai barazanar mahaifarta zata iya kamuwa da cutar cancer basuda wata hanya face su Cire mahaifar.
Anyi aiki cikin sa'a da nasara kuma surgery ne wanda sukabi method da ba'a cika binsa ba amma cikin sa'a sunyi kuma yazama successful. Bayan sun fito Dr ya yabawa ƙoƙarin da sukayi sannan yajuya wajan chubaɗo yana mata magana cikin harshen fillanci, watsewa suka fara saboda haka yakeyi ko da mutane a wajan idan zaiyi mata magana sai ya canja harshe. Ko a cikin theatre ɗazu ya canja harshe wajan yimata magana wanda sunada tabbacin shi kansa baisan yayi haka ba sabo da yine kawai. Bayan yagama yabawa ƙwazonta ya sallamesu kowannensu yatafi dan hutawa.
Masallaci suka nufa kai daga nan sukayi sallah Ajiyar zuciya kawai suke sauƙewa kamar wanda sune suka jaa ragamar aikin.
Cafeteria suka wuce daga masallaci suka samu abunda zasu sakawa cikinsu Akwai abincin da basu suka bar cikin wajan ba sai 3o'clock, hakanma kiran mahaifin Chubaɗo yasa suka bar wajan saboda ya sanar da ita yana office. Miƙewa chubaɗo tayi zata tafi wajansa Zulaiha ta miƙe itama.
"Dan Allah Aysha muje wajan Abbanki nima ki roƙamin shi yashiga surgeryn dani wallh inason ƙaruwa da ɗaukan ilimi a wajansa, murmushi Chubaɗo tayi.
"Toh muje amma babu tabbacin cewa surgery ɗin zamu shiga dan bai sanar dani hakan ba sai dai idan ya sanar dani saina roƙeshi"
"Yawwa dan Allah muje Allah yasa yayarda" Amin ta amsa suka wuce. Office ɗinsa suka wuce kai tsaye da take a hawa na biyu a cikin asibitin kusa da office na director. A jikin ƙofar office ɗin an rubuta DR Ahmad Giɗaɗo knocking sukayi ya amsa yabasu damar shiga zulaiha taja ta tsaya, Chibaɗp ta kalleta ganin yaja ta tsaya.
"Kije bansan ko zakuyi wata magana ba duk yanda kukayi saiki kirani" Toh kawai tace ta shige ciki yana zaune yana duba Files É—in wacce zasuyi wa theatre. ta zauna kujerar gabansa da duba patients bayan tayi masa sannu saida yagama kallon file É—in sannan ya É—ago zuwa gareta kallon kayan jikinta yayi sai taga yayi murmushi, "Kunyi aikin tare da Dr Hafiz kenan?" ta gyaÉ—a kai. Cikin jin daÉ—i yace.
"Ma sha Allah sannu da ƙoƙari Allah ya ƙaro nasara sai adage koh?" "In sha Allah abba" files ya miƙo mata. "Yimin bayani akan abunda kika fahimta gameda me wannan files dana baki kwanakin baya, batareda ta buɗe ta ajiye file gefe tafara yimasa bayani dallah-dallah yana jijjiga kai cike da gamsuwa saida takai iya duk wani abunda ta fahimta sannan ta dakata.
"Toh aganinki wace hanya za'abi a magance wanann cuta?"
"Toh dafarkl dai za'a fara É—aurata akan magani Har indai magani baiyi aiki ba na tsawom wani lokaci dole babu wata hanya sai dai a gudanarda aiki"
"wane irin aiki kenan ba?" ya jefa mata tambaya, cikin ƙwarewa ta yimasa bayani dalla-dallah yanda za'a gudanar da aikin da yanda za'abi batareda wata matsala ba ya jijjiga kai dan ya gamsu da bayaninta koshi kansa da yayi shekara talatin da biyu a harkar likitanci idan zai ƙara wani abun akan bayanin da tayi toh ba wani abu mai yawa zai ƙara ba sai dai dake shi ya goge a lamarin kuma yayi irin aikin wanda shi kana sai ya zauna kafin yasan yawansu. "Kishirya 4: in sha Allah zamu shiga muyiwa wannan matar aiki idan akwai wani nazari da zaki Ƙara kafin lokacin saiki fara kafin ashiga" kai ta gyaɗa sannan kuma ta marairaice murya.
"Abba dan Allah ƙawata zulaiha tanaso kashiga surgeryn da ita tace na roƙeka" kallonta yayi batareda ɓata lokaci ba yace.
ZAYNAB ALABURA.