Free chapter · Read without an account
17
BAK'AR SHUKA...!
NA
HAUWA A USMAN
JIDDARH
Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh
1️⃣7️⃣
Kwana biyu kenan baiga giccinta ba, yana so ya tambaya amma kunya ta hanashi, dole ya daure Ammu na zaune a falo tana kallan Sunna Tv ya zauna kusa da ita yana fad'in " ina yini?
"Lafiya lau, ya aikin?
"Alhamdulillah, ya bata amsa kafin duk sukayi shiru babu wanda ya sake magana, " Ammu inaga fa next week zamu wuce dama neman visan Deeyanah ne ya bani wahala amma komai ya dai-dai ta da izinin Allah, ya fad'a yana tsokano maganarta.
Hankalinta ta mayar kanshi tana murmushi me kama da dariya tace " masha Allah! wacce rana zaku tafi?
"Maybe nan da kwana bakwai ko takwas, in sha Allah.
"Kace mu hau shiri da dake-daken yaji da kuka da kub'ewa ko?
Kanshi ya shafa yana murmushi, " ka sanar da Deeyanah?
Da sauri yace " a'a, dan anzo inda yake san aje.
"Ai ya kamata ka sanar da ita da wuri idan da shirin da zatayi tayi shi da wuri ba sai lokaci ya k'ure ba.
D'an shiru sukayi, Ammu ta nisa tana fad'in " ka shiga tana bedroom d'inta, guntun murmushi yayi batare dayace komai ba, sanin muddin tana wajen bazai iya tashi ya shiga bedroom d'inta ba yasata mik'ewa tabar falon, ai tana mik'ewa ya mik'e yayi wuf ya shige bedroom d'in har yana bigewa da k'ofa.
Kwance ya sameta k'asan tiles daga ita sai siket d'in undi tayi amai duk ta dame jikinta da aman, saurin k'arasawa inda take kwancen yayi, bai damu da yadda ta b'ata jikinta da amai ba ya d'ago ta ya rungume ta cikin jikinshi, bai direta a ko'ina ba sai ciki kwamin wanka, ya kai hannu ya zame siket d'in jikinta tare da sakar mata shower, ajiyar zuciya ta sauke had'i da k'ank'ame shi, tana ji tana gani babu yadda zatayi yayi mata wanka yayi mata brush ya nad'o ta a towel kamar Baby.
K'ofar bedroom d'in ya bud'e ya d'an lek'o ganin ba kowa yasa shi fita yana d'auke da ita a jikinshi bedroom d'inshi ya kaita ya kwantar da ita saman bed yaja mata blanket ya rufe ta ya fita, d'akinta ya koma ya gyara shi tas tas ya wanke mata bathroom ya kunna humidifier ya feshe ko'ina da Air freshener ya saka mata turaren wuta a buna ya isa gaban wardrobe d'inta ya d'aukar mata pant da bra sai doguwar rigar atamfa da hijab da plate shoe, da kanshi ya saka mata kayan ya rik'eta gam a jikinshi suka fita, Ammu na kitchen na girki Deerah na taya ta da aikin surutu.
A hankali cikin nutsuwa yake tukin har ya isa asibitin Sahal a kame ya fito ya d'auke ta, cikin kunnenshi ta rad'a mishi " ka sauke ni zan iya tafiya da kaina, kamar baiji abinda tace ba ya cigaba da tafiya da ita.
Bayan likitan ya gama jin duk bayananta ya nisa tare da kallan Deen yace " ciwon maran dake damunta alaji ne na wani abu da take ci ko take sha wanda jikinta baya so akwai possibility d'in idan tayi sex ta daina, impact ma ciwon mararta bashi da maganin daya wuce sex sai dai a bata pain reliever kallan juna sukayi ita dashi tayi saurin duk'ar da kanta k'asa, magunguna ya rubuta musu ya mik'ewa Deen yana fad'in " idan kunje gida a sami ruwan d'umi da towel me tsafta a d'an gasa mata marar.
Ta kula da yadda yake kanne dariya amma tayi banza dashi, yana tallafe da ita ya shigar da ita bedroom tare da zaunar da ita gefen gado ya fita, bai dad'e ba ya dawo d'auke da tea mai kauri ya bata, dakyar yana lallab'ata tasha tea d'in, ya fita, ya dawo d'auke da roba a hannunshi ya shiga bathroom ya sirko ruwan zafin ya fito da d'an k'aramin towel, ita tama manta da batun wani wai a gasa mata mara, ita fa tunda take bata tab'a jin inda ake gasa mara ba, anya likitan nan yasan me yake yi?
Saukar hannunshi data ji a gadon bayanta ya katse mata tunani a tare suka sauke ajiyar zuciya tana san ta dakatar dashi amma bazata iyayin hakan ba.
Doguwar rigar jikinta ya cire tare da cire bra d'in jikinta yakai hannu zai zame pant d'inta tayi saurin rik'e hannunshi idonta cikin nashi dake ruwa-ruwa saboda tsabar jaraba, ta girgiza mishi kanta alamar a'a, d'ayan hannunshi yasa ya zame hannunta dake kan nashi had'i da zame pant d'in wani yawu ne ya wuce mishi ba shiri in banda ya dake ya rik'e kanshi da sayya gwari amma duk da haka saida yayi tari.
Lallausan hannunshi yakai ya shafa saman mararta zuwa saman HQ idanuwanta ta lumshe gami da fitar da nannauyan nishi, cikin shauk'i yake goga mata towel d'in had'i da d'an danna marar, cikin kunnenta ya rad'a mata " Doctor yace sex ne kad'ai maganin dazai warkar dake ya kika gani?
Harararshi tayi, yayi murmushi tare da cewa " shidai ya fad'a bani ba, idan kin yarda yanzu na baki maganinki?
Hannunshi dake kan mararta ta ture had'i da juya mishi baya, dariya yayi sosai yace " ni dai ba ruwa na bani na fad'a ba ai, cikin nufin Ubangiji ciwon ya lafa mata ta d'anji sauk'i, ya bata magungunanta tasha bata dad'e dasha ba bacci yayi awon gaba da ita.
Deen shiya rink'a yi mata komai, shine yake jinyar ta, shike kula da ita, duk wata kulawa da kuka san za'a bawa marar lafiya Deen ya bata, ya kula da ita sosai, dan tattara gaba d'aya lokacin shi yayi akanta, cikin kwana biyu ta warke ras yadda kasan tab'a yin rashin lafiya ba.
******** Jikinta sanye da zumbulelen hijab while k'asan daga ita sai towel ta mik'e daga bakin gadon da take zaune ta nufi bathroom, wanka take san tayi shigowarshi ya hana ta shiga wankan, Yana zaune kan sofa ya d'ago kanshi ya kalle ta yace " ko in zo inyi miki wankan?
Hararshi tayi fuskarta d'auke da murmushi ta shige bathroom, yayi dariya gami da mik'ewa ya fice.
Deen wani irin mutum ne da koyaya sauro ya cije shi sayyayi zazzab'i shiyasa yake mugun kiyayewa dan gudun karka yayi maleria, gashi Allah yayi shi baya san rashin lafiya dan idan da abinda yafi tsana yabi bayan rashin lafiya.
Tun daren jiya yake jin alamun zazzab'i amma bai kula ba, tana shigewa bathroom d'in ya mik'e ya fice bedroom d'inshi ya shiga ya jawo first aid box d'inshi dan baya rabuwa da maganin zazzab'i, maganin Maleriya ya sha me guda ukun nan, yana sha amai ya soma taso mishi dama haka maganin yake, kwanciya yayi yana mayar da numfashi kan kace kwabo zazzafan zazzab'i me k'arfi ya rufe shi, yaja bargo ya rufe jikinshi yana rawar sanyi.
Data fito daga wanka bata ganshi ba tayi tsammanin fita yayi kan shirye-shiryen tafiyar su dan haka ta cigaba da sabgar gabanta, har dare bata sake bi takanshi ba, falo ta fito kasancewar ta jiyo muryarsu Azrah fuskarta fayau ba make up sai uban haske data k'ara ta zauna kusa da Azwah tana fad'in " ina yininku?
Azwah ce ta amsa sallamar yayinda Azrah ke binta da kallo baki bud'e " lafiya dai!?
Deeyanah ta fad'a cikin basarwa, " kodai har an gamu ne tun anan?
"Kedai kin shiga uku wallahi, Azwah ta fad'a tana hararta.
"Kyale ta imma na gamu ai miji na ne aiko?
Suka kwashe da dariya, Azwah tace " ya jikin naki?
"Alhamdulillah da sauk'i, bakin Ammu d'auke da sallama ta shigo falon tare da zama kusa dasu, jin sunyi shiru yasa Ammu cewa " kodai in tashi ne hirar ba tawa bace?
Da sauri had'a bakin wajen cewa " a'a Ammu.
"A toh na sani ko hirar yaran mata ake yi kota 'yan uwa, kallanta ta mayar ga Deeyanah tace " wai ina Deen?
Tana kallan Ammu tace " ban sani ba, d'azu dai yana bedroom d'ina dana shiga wanka kafin na fito ya......!
Ido ta runtse had'i da d'an dukan goshinta ta kwafsa, ya akayi ma ta bari tayi irin wannan sub'ul da bakan, Azrah ta kwashe da dariya tana fad'in " ashe har bedroom d'inki yake zuwa?
Yadda kasan Ammu bata ji abinda Deeyanah ta fad'a ba ta basar had'i da cewa " ga abincin shi na rana can baici ba gana dare can ma, agogon bango ta kalla k'arfe 9:12pm na dare tasan baya kaiwa dare haka a waje sai dai idan da wani abun, ji tayi gabanta ya fad'i lokaci d'aya yanayin jikinta ya canja.
Bata san sanda ta mik'e tana fad'in " bari na dubo Bedroom d'inshi ba, bata jira amsa ba tayi gaba Azwah tabi bayanta da kallo tana dariya tare da fad'in " su Deeyanah manya.
Ammu tayi murmushi batare data ce komai ba.
A hankali ta tura k'ofar d'akin ta shiga bakinta d'auke da sallama, wani iri taji d'akin ba yadda ta saba jinshi ba, fitilar d'akin a kashe take duhu dund'im, da lalabe ta kunna fitilar d'akin, yana kwance lullub'e da blanked sai rawar sanyi yake yi, tsaye tayi bakin gadon saitin kanshi tana kallanshi tace " baka da lafiya ne?
Dakyar ya girgiza mata kanshi, cikin sanyi tace " kasha magani?
Kanshi ya d'aga mata, " in kawo maka abinci?
Kanshi ya sake girgiza mata, muryarta a sanyaye tace " sannu Allah ya sauwak'e, ta juya zata fice......
JIDDARH