Free chapter · Read without an account

49

by Hauwa A Usman · BAK’AR SHUKA…!

*BAK'AR SHUKA...!*



NA


*HAUWA A USMAN*

~ JIDDARH~


Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh

ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh


4️⃣9️⃣


Hankalinta kwance take tuk'in tana bin wak'ar Ranar Aure na ta mawak'i Umar me Sanyi da gidan radio suka saka, takai hannu ta k'ara volume, tana rausaya kanta alamar tana bala'in jin dad'in wak'ar, ana gama wak'ar gidan Radio suka sak'o wa'azin Malam Ibrahim Daurawa me taken ILLAR ZINA, wata irin muguwar fad'uwa gabanta yayi, Malamin yayi gyaran murya yayi sallama kana ya fara magana " in Allah ya yarda yau zamuyi magana akan illolin zina, zamu tab'o har b'angaren matan auren dake ZINA DA AURENSU, dammmm! dammmm! dammmm! gabanta ya shiga dokawa da tsananin k'arfi.


" Tsira da amincin ALLAH sutabbata ga ANNABIN dababu wani bayanshi


Salati da tsira da amincin Allah su tabbata bisa Jagoran Annabawa da Manzanni, Shugabanmu Annabi Muhammadu (ﷺ)tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Maɗukaka.


ILoLin zina da kuma Hukuncinta


Ya tabbata a cikin hadisi an tambayi Annabi

(ﷺ) a kan wane zunubi ne ya fi girma, sai

Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Shirka da Allah,

Alhali shine ya halicce ka, " Sai aka ce sai wanne? Sai ya ce "Sannan kashe ɗanka don

kada ya ci tare da kai." Sai aka ce "sannan sai wanne ? " Sai ya ce "Ka yi zina da matar

makwabcinka, (Bukhari) yadda ruwaito.


Allah Maɗaukakin sarki ya sanya hukuncin wanda duk ya yi zina kuma ya taɓa aure ko yana da aure a jefe shi, namiji ko mace, idan kuwa bai taɓa aure ba, sai a yi masa bulala ɗari, sannan a

baquntar da shi a wani gari daban tsawon shekara guda.


Duk wanda ya kalli hukuncin zina, zai ga Allah Ya keɓance shi da wasu abubuwa masu yawa, saboda munin zina, ga kad'an daga cikin abubuwan da hukuncin ya kunsa.


1. Kausasawa wajen ukubar mazinaci, ta hanyar jefewa, ko kuma bulala da bakuntarwa shekara guda.


2. Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya yayin da ake musu ukuba Allah yace :-


ٱلزَّانِيَةُ وَٱلزَّانِى فَٱجْلِدُوا۟ كُلَّ وَٰحِدٍ مِّنْهُمَا مِا۟ئَةَ جَلْدَةٍ ۖ وَلَا تَأْخُذْكُم بِهِمَا رَأْفَةٌ فِى دِينِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْءَاخِرِ ۖ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَآئِفَةٌ مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِين


"Mazinaciya da mazinaci to ku yi bulala d'ari ga kowanne ɗaya daga gare su, kuma kada tausayi ya kama ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kuna yin imani da Allah da ranar lahira, sannan wani yankin jama'a daga muminai su halarci azabarsu. (Annur : 2). .


Ayi musu ukuba a gaban mutane ba'a yarda a yi musu a boye ba.


Imamul Bukhari ya kawo a cikin ingantaccen littafinsa daga Maimun Al-audiy ya ce,


"A lokacin jahiliyya na taɓa ganin wani biri da ya yi zina da wata biranya, sai sauran biran suka taru suka jefe su.


Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da mahaifiyarsa, sai da muharramarsa, sai wadda zai yi da matar makwabcinsa, Allah ya kare mu.


ILLoLin Zina: Babu shakka duk mai hankali ya san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, waɗanda suke shafar mazinacin ko mazinaciya, ko su shafi al'umma gaba daya.


1. Zubar da mutunci da jawo wa kai k'ask'anci, Duk matar da ta yi zina to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta ƙasƙanci, ta kuma zubar musu da mutunci a idon duniya, Idan har ta sami ciki ta haihu, sannan ta kashe ɗan, to ta haɗa laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai, In kuma ta bar shi, to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta, wanda ba ya cikinsu, Idan kuwa mai zinar namiji ne to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da taɓewa, wanda hakan lalata duniya ne gaba daya.


2. Zina ta haɗa dukkan sharri gaba ɗaya, saboda a cikin zina akwai rashin tsoron Allah, rashin kunya, rashin tsantseni, rashin cika alk'awarin, ƙarya da butulci da sauransu, Duk kuwa waɗannan munanan halaye ne a Musulunci.


Manzon Allah (ﷺ) yace Allah ya la'anci mai sake al'aura da mai kallon al'auran wani. Baihaqi ya ruwaitoshi


An karɓo daga mu'azu ɗan jabal (r.a) ya karɓo daga manzon ALLAH (ﷺ) sai yace

" ranar alk'iyama ranar hasara ce da nadama Allah zai ta da al'umma daga ƙabarburansu siffa goma sha biyu (12).


Siffa na biyar daga ciki.


Za'a tashe su daga cikin ƙabarinsu suna wari kamar dunge mai kira yayi kira da fuskar Ubangiji waɗannan sune masu zina sun mutu batare da sun tuba ba, basuji kunyar Allah maɗaukaki ba wannan shine

sakamakonsu makomar su zuwa ga wuta.


(Faɗin ALLAH maɗaukakin sarki)


ﻳَﺴْﺘَﺨْﻔُﻮﻥَ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺴْﺘَﺨْﻔُﻮﻥَ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻫُﻮَ

ﻣَﻌَﻬُﻢْ


( ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ – ﺍﻵﻳﺔ108 )


Suna neman ɓoyewa daga mutane kuma ba su neman ɓoyewa daga Allah, alhali

kuwa shi yana tare da su.


Siffa na takwas


Za'a tashesu daga cikin kabarinsu wani ruwa mai yauk'i (na bala'i) yana fita daga farjinsu mai kira yayi kira da fuskar Ubangiji " waɗannan sune masu zina sun mutu batare da sun tuba ba wannan shine sakamakon su makomar su zuwa ga wuta.


(Faɗin ALLAH maɗaukakin sarki)


ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻘْﺮَﺑُﻮﺍ ﺍﻟﺰِّﻧَﺎ ۖ ﺇِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻓَﺎﺣِﺸَﺔً ﻭَﺳَﺎﺀَ ﺳَﺒِﻴﻠًﺎ


‏(ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ 32- )


Kuma kada ku kusanci zina, lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga

zama hanya.


Duk matar auren da

tayi zina ba zata sadu da mijin ta ba har sai tayi istibra'i..! Annabi

SAW yayi hani da cin wannan kudin da aka bata na wannan zinan, Zina dai wani aiki ne da Allah ya hana muslmi ko musulma aikatawa, kai ba ma aikata zinan ba, hatta

kusantar ta ma Allah

mad'aukakin sarki ya hana

Allah ya gargad'e mu a cikin Alkur'ni mai tsarki cewa 'kada ku kusanci zina ( wala ta k'arabuzzina).


Zina dai tana cikin manyan zunubbai, wato ALKABA'IRA, sannan kuma manzon

Allah SAW yace " mutum baya aikata Zina sai an cire mishi imaninshi gaba d'aya idan kuma ya gama aka za'a mayar mishi, ba'a mayar mishi da gaba d'aya imanin nashi, ashe ke

nan da mazinaci zai mutu a wannan halin ya mutu a mara imani.


" Babu abinda mutum yake samu a zina banda taɓewa da nadama da yake biyo baya, zina babu wani alheri dake tare da ita banda ƙasƙan ci da wulakanci da mutum yake tsintar kansa akai tun daga nan duniya kafin aje lahira.


Zina tana jawo masifu da bala'i wanda duk mai hankali idan yayi tunani bai kamata ya kai kansa cikin ta ba koda babu Shari'ar da zata hana yin taba. Illar da zina take jawowa yafi dukkan yadda mutum zayyi tunani. 


Shiyasa cikin hikima da Buwaya irin ta Ubangiji yace kada a kusance tama balle a aikata ta saboda irin illar da take jawowa dan Adam.


Zina tana jawo fushin Ubangiji ya sauka ga bawa komai yaki da dadi, tana jawo tawayar arziki da rashin sanin manufa a rayuwa, tana saka kuncin zuciya da munana zato ga mutane, tana tafiyar da kwarjini da ƙima a idan mutane, illar zina yana shafar har zuria ta kuma jawo musu ƙasƙan ci, tana tafiyar da imani da kunya ga mutum, tana sa mutum ya rayu cikin nadama da wulakanci.


Illar zina da munin ta yafi karfin a rubuta su, ku nisan ci zina domin babu wani alheri dake tare da ita. Allah ya tsare mu ya kare mu. Aameen!.


Sosai Malamin ya zage yayi wa'azi akan zina ya fad'i azabobin da Allah ya tanadarwa masu aikata ta, da irin bak'ar masifar da zasu tsinta tun daga zarar ransu zuwa kwanciyar kabarinsu.


Rawar da jikinta keyi ce ta haifarwa da motar yin tangal- tangal a saman titi tana yawo daga wannan hannun zuwa wannan hannun dakyar ta samu ta iya tsaida motar a tsakiyar titi masu mashina da motoci da Napep sai zaginta suke amma bama tasan suna yi ba,  jin babu iskar da zata shak'a kwata-kwata yasata bud'e motar da sauri jikinta na wani irin b'ari da kyarma, yadda kasan wacce ke shirin hawa iska, ko motar bata tsaya rufewa ba ta durk'ushe a k'asa tsakiyar titi tana mayar da numfashi kamar me Asthma, sosai take hakki while hannunta dafe da k'irjinta, wani abu take ji me zafi da k'arfi yana fita daga k'irjinta, yayinda da zuciyarta ke bud'ewa tana tarwatse, gaba d'aya tsikar jikinta a tashe take saboda tsabar tashin hankali, idanuwanta sukayi jajir kamar gauta, har wani yaji take ji kamar wacce aka shak'awa tiyagas.


Baki take san bud'ewa ta furta Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un amma abun ya gagara ko kalma d'aya ta gagara fitowa daga bakinta, a jikinta take jin yadda jijiyoyin jikinta ke tsinkewa jinin jikinta na tafasa, babu bata gab'a ta jikinta da bata karye ba, in banda rawa da kerrrrma babu abinda jikinta keyi, so take tayi kuka amma ta kasa, sosai take kokawa da numfashi, tayi iya bakin k'ok'arinta dan ta samu sassauci da sauk'i amma babu sauk'in.


Dakyar ta yunk'ura zata mik'e aiko sai amai ta shiga kelaya amai sosai, cikin aman ta durk'ushe ta saki wani irin mahaukacin kuka me rikitarwa yadda kasan ranta ake zarewa, kallo d'aya zakayi mata kasan da duka zuciyarta take kukan, cikin ihuuuu da hargowa take fad'in " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un 'yar wuta ce ni.


"Wuta zan shiga! 'yar wuta ce, in na mutu a haka wallahi wuta zan shiga, na shiga uku! idan ban tuba ba wuta zan shiga, zanyi mummunan k'arshe, na shiga uku na lalace na cuci kaina da rayuwa ta, nayiwa kaina da kaina babbar illa, illar da har abada bazata dawo dai-dai ba, na tarwatsa komai, tarwatsawar da bazata tab'a dawowa dai-dai ba, na shiga uku, na jawowa kaina abin kunya, na jawowa iyaye na da ahalina abun fad'a, Allah ka yafe min, ta k'arasa maganar had'i da d'iban k'asa tana zubawa kanta tare da dukan kanta da hannu bibbiyu.


Kuka takeyi sosai dake fitowa daga can k'ark'ashin zuciyarta, tana ihuuu tana d'iban k'asa tana zubawa jikinta, in banda Allah ya taimake ta unguwar babu mutane da an taru ana kallanta, har masu yi mata video ma da an samu, ta dad'e cikin wannan mummunan yanayi kafin ta mik'e fuska kace-kace da majina da hawaye, dakyar take iya tuk'in tana tafe hawaye na zuba danta kasa tsaida hawayenta, bama tayi k'ok'arin tsayar dasu ba, dan ita zubar ma da sukeyi sauk'i ne a gare ta.


A bakin get tayi parking motar ta fito ko rufe motar batayi ba ta tura k'ofar shiga gidan wacce ba get ba ta shige, yadda take tafiya tana had'a hanya ga k'afarta babu takalmi yasa ma'aikatan kallanta baki bud'e, tana tafe tana tangad'i while hawaye na d'iga ta mik'awa d'aya daga cikin drivers d'in gidan key d'in motar batare data ce komai ba, hannu na rawa ya amsa, ta shige gida, dama can cikin motar tabar takalmin da jakarta da wayoyinta, duk abinda ke faruwa Ajlaal na jinta, shu'umin murmushi ya saki had'i da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yace " kin makara Deeyanah, kin riga kin makara, wallahi baki isa ki raba kanki dani ba, dan zan iya yak'ar duniya na k'arar da kowa da komai daga doran k'asa, duk wanda yace zai shiga gaba na akanta ni kuma nayi alwashin kawar dashi daga hanya ta, zanyi komai danna mallakeki, ya k'arashe maganar yana fashewa da mahaukaciyar dariya......


JIDDARH....


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.