Free chapter · Read without an account

53

by Hauwa A Usman · BAK’AR SHUKA…!

*BAK'AR SHUKA...!*



       NA


*HAUWA A USMAN*

    ~ JIDDARH~


Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh

ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh


5️⃣3️⃣


Har cikin d'aki ya raka ta, ta zauna saman gado, ya jawo dorowar gefen gado, ya ciro ledar magungunan ta ya b'allar mata ya mik'a mata had'e da ruwa ba musu ta amsa had'i da runtse idonta da k'arfi saboda bata san shan magani, ta afa maganin ta kora da ruwa, " ki kwanta ki huta, ya fad'a tare da ja mata bargo, bai sake magana ba ya fice, tabi bayanshi da kallo tana tuno a baya idan bata da lafiya yadda yake lallab'a ta yana tarairayarta kamar kwai, musamman idan akazo fannin shan magani daya san bata so, sai ansha daga da gwagwarmaya ta zuba sangarta da shagwab'a san ranta kafin tasha maganin, amma yau ita dashi tamkar bak'in da basu tab'a ganin juna ba.


"Ubangiji kayi min sassauci, kayi min afuwa ka yafe min ka dai-daita tsakani na da mijina ya Rabbi, tayi addu'ar tana zubar da kwalla har lokacin idaonta na kan k'ofar.


A hankali bacci ya soma fisgarta, tana lumshe ido tana bud'ewa bacci na d'aukarta ta ganshi tsaye kanta, da fari ta d'auka gizo yake yi mata ko kuma idonta ne, sai da ta bud'e idon ta ganshi tarrr a gabanta, a firgice ta mik'e zaune tana k'ok'arin sake bud'e idanuwanta da sukayi mata nauyi saboda cikin magungunan akwai me sa bacci, ta zuba su akanshi gami da cewa " me.....me...ya...kawo...ka?


Ta fad'a bakinta na rawa, " me kazo yi gidan aure na Ajlaal?


"Ka dai rantse saika k'arasa wargaza min rayuwata ka lalata duniya ta meyasa Ajlaal?


"Meyasa baka jin rok'o da magiya?


"Yanzu bazaka barni na rayu cikin salama da guntun farin cikin da nake k'ok'arin samarwa kaina ba?


"Wai me yayi saura Ajlaal bayan komai ya k'are ka riga ka gama tarwatsa komai?


Hannunta ta had'e waje d'aya kukan bak'in ciki na kufce mata tace " dan Allah, dan girman Allah ka barni Ajlaal, ka barni haka, dan zatin Allah, ta fad'a cikin rikitaccen kuka.


Bisa mamakinta sai taga ya zube gabanta gami da rusa kuka wiwi shima ya kifa kanshi kan k'afafuwanta, yadda kasan wuta ya zuba mata kan cinyoyinta tayi saurin zame su kanshi ya bugi katakon gado, duk da haka bai damu ba, ya tallafe kanshi da duka hannayenshi yana rusa kuka wiwi kamar mahaukacin daya gudo daga gidan mahaukata, a tsorace take binshi da kallo kamar kace mata arrrrr ta ruga.


"Ina sanki Deeyanah, bazan rayuwa babu ke ba, dan Allah ki taimaka min ki dawo gare ni idan ba haka ba mutuwa zanyi, tunda kika barni rayuwata ta shiga tangard'a, mutuwa zanyi muddin kika barni Deeyanah, dan Allah ki taimaki rayuwata karki barni, karki barni ina sanki, kece duniya ta, kece hasken rayuwata please...!


"Ni kuma bana sanka Ajlaal idan dakai a cikin rayuwata komai nawa lalacewa zayyi dan Allah ka barni.


"A'a Deeyanah ba haka bane, kizo muyi aure mu haifi 'ya'yanmu mu rayu cikin salama da farin ciki, zan baki dukkan farin ciki da jin dad'in duniya da kowacce mace ke burin samu a wajen d'a namiji, zan mayar dake macen tafi kowacce mace a fad'in duniya, zan mantar dake kowa da komai babu abinda zaki rink'a tunawa sai ni da yaranmu da zamu haifa, nayi miki alk'awarin zan shinfid'a miki rayuwata a k'asan k'afarki, nayi miki alk'awarin zan yi miki biyayya bazan tab'a sab'a umarnin ki ba har izuwa fitar da numfashi na k'arshe, nidai fata na kada ki barni, ki zauna tare da ni please, yayi maganar yana durk'ushe gabanta while yana rusa kuka.


"Kai tamkar wani gajimare ne daya wanzu a rayuwata kuma ya washe, kai ba komai bane face mummunan mafarki dana tab'ayi dakai da babu duk d'aya ne a ryuwata, danni a waje na babun ma ta fiye min dan baka da amfanin komai a wajena sai tarin rashin amfani.


" Deeyanah an halicce mu ne dan junan mu, nine mijinki, nine wanda zaki rayu dashi.


"A'a ya isa dan Allah ya isa haka, bani da wani miji a duniya da lahira bayan Deen, shine mijina duniya da lahira, ina fata ya zama mijina har a aljanna, shine uban ya'yana dashi ne zan haihu, shi kad'ai zan haifawa 'ya'ya, danshi aka halicce ni, danni aka halicce shi, bana sanka Ajlal, Deen nake so, danshi zuciyata ke dokawa, shine zab'in rai na, kuma shine zab'in iyaye na, dashi kad'ai zan rayu nayi farin ciki.


" Yanwa anzo wajen dama nasan shi d'in ba zab'in ki bane, kina tare dashi ne saboda shine zab'in iyayenki amma a bad'iri nine zab'inki, dan Allah kada ki azabatar da zuciyoyin mu ta hanyar nesanta mu da juna hakan kan haifar da rugujewar rayuwar mu.


" Ya isa! Ta fad'a cikin tsawa, zayyi magana ta nuna mishi k'ofa tace " fice min daga gani daga yau kada ka sake nuna min wannan bak'ar fuskar taka, me mugun nufi, bak'in azzalumi, shaid'an mai san raba sunnar Ma'aiki, ka fice min bana fatan sake ganinka a rayuwata.


" Dan Allah Deeyanah kada kiyi min haka please, mik'ewa tayi had'i da fincikar gaban rigarshi ta hankad'a shi waje, ta karkad'a mishi yatsa a fuska tace " karka sake zuwar min gidan aure in ba haka ba.... ta cije leb'enta na k'asa da k'arfi.


Hawayenshi yasa d'an yatsa ya goge yana murmushi ya kalli cikin kwayar idonta yace " kisa a ranki ke tawa ce ni kad'ai kuma zan tabbatar miki da hakan, nayi miki alk'awarin babu wani d'a namiji daya isa ya rab'eki a fad'in duniya duk wanda ya kuskura yayi gangancin rab'arki ya cije leb'enshi na k'asa yana murmushi ya juya yabar wajen.


Bata damu ta furucin da yayi ba ta koma cikin d'akinta ta fad'a saman gado had'i da sakin rikitaccen kuka me cin rai tana fad'in " na cuce kaina na jefa rayuwata cikin masifar da bazan iya fitar da kaina ba, wayyo Allah kaico na kaicon rayuwata.


Yana kwance d'akinshi ya jiyo sautin kukanta kad'an-kad'an d'an sararawa yayi danya tabbatar, tabbas kunnenshi bayyi mishi k'arya ba da gaske kukan nata ne, " wai me yake damun yarinyar nan ne?


Ya fad'a yana mik'ewa silifas d'in dake gefen gadonshi ya sanya ya fita yana d'aure igiyar rigar baccin jikinshi, zaune ya iske ta gefen gado tana rusgar kuka, har ya shigo ya tsaya kanta bata sani ba, ya d'an dad'e tsaye kanta yana kallanta, sai da ya sauke ajiyar zuciya kana ya zauna kusa da ita ya dafa k'afarta had'i da kiran sunanta " Deeyanah!


Firgigit tayi a tsorace dan bata san shigowar shi ba, murmushi yayi mata da suka had'a ido cikin dakewa yace " komai yayi tsanani maganinshi Allah, Ubangiji ya dank'a mana maganin damuwar mu a tafin hannunmu tunda yayi mu a musulmai masu imani, ya bamu Alkur'ani da addu'o'i, koma wacce irin matsala kike ciki idan kika dage da addu'a kina kaiwa Allah kukanki da sannu zai yaye miki dukkan matsalarki, kiyi hak'uri ki dangana ki mik'awa Allah komai, kiyi imani akan zayyi miki maganin dukkan damuwa da matsalarki.


Hawayen ta goge ta d'aga idonta ta kalleshi cike da girmamawa tace " bazaka tambaye ni komai ba Yaya?


Kyakkyawan murmushi yayi yace " bazan matsa miki kamar wancan karon ba, idan kin so kinga na cancanci nasan damuwarki, keda kanki zaki sanar dani komai, bana san sake haifar miki da wata damuwar bayan wacce kike ciki.


Wani abu dake neman huda k'irjinta ta danne tace " kayi hak'uri Yaya, na jefa rayuwarmu cikin matsala, na mayar da gidan mu tamkar gidan zaman makoki, na gurb'ata kyakkyawar alak'ar dake tsakanin mu, na wargaza farin cikinmu, na lalata komai, kana da matarka ta aure ta sunna na mayar dakai tamkar gwauro duk da nasan kana da yawan buk'atar mace amma saboda san zuciya ta na rufe idona, nak'i tausaya maka, na danne maka duk wani hakk'inka dake kaina, na tauye maka damarka da Allah ya baka a kaina, amma duk da haka kayi hak'uri dani, ka jure duk wata musgunawa ta, na jefa rayuwar mu cikin bak'in bala'in da babu me fitar damu sai Allah, ka yafe min dan Allah, ta k'arasa maganar cikin matsanancin kukan dake huda zuciyarshi.


"Kiyi addu'a in sha Allah komai zaizo mana da sauk'i, da yardar Allah komai zai gyaru.


"Kayya kayya Yaya, adayyi shiru kawai amma har abada babu abinda zai gyaru.


"Subhanallahi haba sai kace ba musulma ba, sai kin yiwa kanki bak'in bakin da zai biki, babu abinda zai gagari Allah kedai kiyi addu'a.


Murmushi ya sake yi mata ya mik'e yaja mata bargo ya rufe ta yana fad'in " ki kwanta sai da safe.


Tana san tace ya tsaya ya taya ta kwana amma tana jin kunyar fad'ar hakan, tana ji tana gani ya fice bayan ya kashe mata fitilar d'akin, ta sauke nannauyan numfashi had'i da rufe idonta tunaninka kala-kala na zuwa kanta, har bacci yayi awon gaba da ita.


*************************************


" Ajlaal wai meke damunka ne?


"Duk kabi kayi wani zuru-zuru dakai kamar mahaukaci saban kamo, Abbanshi ya fad'a yana kallan shi.


A fili Mama ta sauke ajiyar zuciya had'i da cewa " jibi yadda ya lalace ya rame ya jeme, ka fad'a mana abinda ke damunka matuk'ar baifi k'arfin mu ba zamuyi maka maganinshi da izinin Allah.


"Ina santa! Itace rayuwata, ita kad'ai ce macen da nake so, dan ita numfashi na ke fita, dan ita zuciya ta ke bugawa idan na sake rasata a karo na biyu bazan iya jurewa ba, mutuwa zanyi, dan Allah ku taimaka min ina santa da duka zuciya ta.


Kallan juna Mama da Abbah sukayi cikin mamakin dake bayyane saman fuskarsu k'arara, mayar da kallanshi Abbah yayi kan Ajlaal yace " bamu fahimce ka ba?


"Kayi mana k'arin bayanin inda kalamanka suka dosa wacece kake son?


A wahalce muryarshi na rawa yace " Deeyanah! Abbah Deeyanah ce ina matuk'ar santa akanta zan iya aikata komai, please ku taimaka min karku rasa ni.


Sake kallan juna Mama da Abba sukayi a karo na biyu sai dai wannan karon ba mamaki bane bayyane saman fuskarsu ba, tsoro ne, tsoron kodai tilon d'ansu ya haukace ne, dan su a iya saninsu Deeyanah ta dad'e dayin aure, bama zasu iya tuna adadin shekarun ba, a k'iyasi dai sun san yanzu tayi yara hud'u, amma ita yake magana yanzu?


"Meyasa kake magana akan matar wani?


"Meyasa kake magana akan Deeyanah bayan kafi kowa sanin tana da aure harda yara?


"Meyasa bazaka hak'ura da ita ka nemi wata ka aura ba?


"Ita dai Abbah, Deeyanah daka sani ita.


"Kodai ka fara shaye-shaye ne Ajlaal bamu sani ba?


Abbah yayi maganar yana kallan Ajlaal d'in cikin tashin hankali.


"Ban fara ba amma ina gaf da farawa a kowanne lokaci.


"Wata k'ila ma ta dad'e da mantawa dakai a rayuwarta tana can tana rayuwarta cikin farin ciki ka tsaya kana azabtar da kanka a banza, please ka sawa ranka hak'uri da salama ka dangana ba komai muke so muke samu ba a rayuwa, sau da yawa zaka ga abinda muka so bashi ne yake zama rabon mu ba, haka ba shine alkhairin mu ba.


" Rasa wanda muke so nuni ne na cewa raban mu yana ta can wani wajen yana neman mu, dan mun fad'i a soyayyar wani ba yana nufin mun rasa soyayya ta har abada bane, ba asara bane danka rasa wanda kake so, asara shine ka rasa kanka wajen k'aunar wanda kai a wajenshi ba komai bane, sauk'i yana tare da tsanani, mai hak'uri yana cimma dad'i, mai kyauta baya tab'a rasawa, duk wanda yaji tsoron Allah Ubangiji zayyi mishi mafita, manta da damuwa ka fuskanci rayuwa, kowa ka gani a duniya da akwai abinda ya dame shi.


" Fadadawa rayuwa ce, tsukakewa mutuwa ce, rayuwa itace yiwa kowa fatan alkhairi, san wawashe komai wa kanka ba komai cikinsa face halaka, a kowacce mu'amula ka zama mai gaskiya da rik'on amana saboda baka san yaushe ne, a wanne lokaci a ina ne cutar dakai zata farauci rayuwarka, duniyarka da farin cikinka ba........


" Kai dalla can dakata shashasha sauna asararran banza kawai ba wa'azi yazo yace kayi mishi ba ka cika mutane da surutun banza duk kabi ka tofe mu da yawu, haka ka tsaya shirme a wancan lokacin na baya har ya rasata, Mama ta fad'a cikin masifa tana galla mishi harara kamar idanuwanta zasu fad'o k'asa, lakwas Abbah yayi duk da yana san ya sake yin magana amma tsoronta dake danne shi ya hana.


Kallanta ta mayar ga Ajlaal tana huci kamar wacce tayi tseren gudu tace " kaima kai ka tsaya kana b'atawa kanka lokaci wannan gantallen daka d'auka a matsayin uba wacce uwar zai iya yi maka?


"Ka fita kaje ka nemi soyayyarka ta kowanne hali, kada ka sake ka dawo min gida batare da suruka ta abar k'aunarka Deeyanah ba, kayi koma meye danka mallake ta.


Cikin sanyi cike da fargaba Abbah yace " koma meye kika ce f..... kallan data watsa mishi yasashi had'iye sauran maganar dole.


*********************************


Tana zaune saman sallaya ta d'aga hannayenta tana tsiyayar da hawaye me k'una da take jinsu tamkar soyayyan mai, addu'a take yi sosai ta neman yafiya.


"Ya Ubangijin al'arshe ya Ubangijin sammai da k'assai, kaji k'aina ka yafe min zunubaina, Kai mai rahama ne, mai tausayi ne, mai yafiya da afuwa ne, ya Allah na sani ni mai tarin zunubai da manyan laifuka ne wad'anda suke rinjaya ta, ya Allah ka.......


Banko k'ofar da akayi yasata saurin d'agowa ta kalli k'ofar, ya fad'o d'akin tamkar an jeho shi, yayi tsaye k'erere kanta, daga k'amshin turaren jikinshi ta gane shine batare data d'ago kanta ta kalle shi ba.


A galabaice ya kira sunanta " Deeyanah!.


Yadda kasan ba sunanta ya kira ba ta cigaba da addu'arta.


"Ina sanki Deeyanah dan Allah karki barni, karki juya min baya a sanda nafi buk'atarki, wallahi nafi Deen sanki, ki yarda dani, kizo mu gudu muyi ta can wani b'angaren duniya, muyi rayuwa daga ni saike sai yaranmu.


Addu'ar ta shafa kana ta mik'e ta ninke sallayar ta aje, ta nufi gado ta kwanta yadda kasan bata san da mutum ba, jikinshi na wata irin rawa kamar mazari ya isa gareta yasa hannu ya d'ago ta ya mannata da k'irjinshi, a fili ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in " a wajenki kad'ai nake samun irin wannan nutsuwar dan Allah karki guje ni.....


A zuciye ta fisge jikinta daga nashi tana jin turirin azabar da fatar jikinta ke fitarwa tamkar ya watsa mata wuta, cikin matsanancin b'acin rai ta yarfa mishi mari a saman kuncin shi, zayyi magana ta dakatar dashi da hannunta tace.


"Kamar ban tab'a fad'a maka bana bana san kana tab'a min jikina ba?


"Sau nawa kake san na sanar dakai illa da bak'ar masifar dake tattare da hakan?


"Sanki ne ke neman haukata ni.


"K'arya kake baka so na Ajlaal, wallahi da kana so na daka so min kyakkyawan k'arshe da gamawa da duniya lafiya, da kayi min sha'awar rayuwa mai kyau, daka yi min fatan kusanci da Allah da samun rabauta duniya da lahira, da kayi min addu'ar shiga Aljanna, da kayi min addu'ar neman tsari da wuta, da kayi min fatan rahamar Allah,

amma kai da kake ikirarin kafi kowa so na, kaine zaka kama hannuna ka shigar dani wuta.


"Kana tak'amar kana so na d'inne zaka nisanta ni da mahaliccina?


"Kana so na zaka nisanta ni da samun rahamar Ubangiji?


"Kana so na zaka rabani da dukkanin farin ciki na?


"Kana so..... " Dakata Deeyanah!


Ya fad'a yanayinshi yana canjawa!


" Wallahi idan duniya zata tashi, babu mahaluk'in daya isa ya rabani dake koda kuwa keda kanki ne, koda hakan yana nufin kawo yak'in duniya na k'arshe, ban damu da adadin mutanen da zasu rasa rayukansu ba, dan haka ki dawo cikin hayyacinki, a baya na baki zab'i biyu kink'i d'aukar ko d'aya, to yanzu ma zan sake baki wani zab'in imma ki dawo mu d'ora daga inda muka tsaya ko kuma ki kashe aurenki kizo muyi aure ko kuma in turawa mijinki video dan yana nan a wayata har yanzu, kinga ai dole ya sake ki ki dawo min.


Ta bud'e baki zatayi magana ya d'ora yatsanshi saman lips d'inta yana zagaya bakinta had'e da cije lips d'inshi ya lumshe idanuwanshi yana shafa k'irjinshi yace " ina san bakin nan naki, yana da dad'in tsotsa, ya k'arashe maganar had'e da rankwafowa zai sha bakinta, ta hannayenta ta hankad'ashi baya da iya k'arfinta gami da nunashi da yatsa tace " Allah yayi min tsari dakai la'ananne mai mugun nufi, yayi dariya yana cewa " karki manta lissafin kwanakin fa sati d'aya yana nufin kwanaki bakwai, bai jira tayi magana ba ya fice, rasa abinda zatayi ne yasata durk'ushewa a k'asa ta fasa rikitaccen kuka.


Anan k'asa tana kuka bacci yayi awon gaba da ita, sha biyu dai-dai na dare ringing d'in wayarta ya cika dak'in ta farka firgigit cikin rashin nutsuwa, da sauri ta kaiwa wayar raruma hannunta ya danna wajen amsa kira batare data sani ba, "irin wannan bacci haka kamar ina kusa dake, yayi maganar sautin dariyarshi na ratsa cikin kanta, " tik tok tik tok lokacinki yana tafiya fa yau saura kwanaki shida, batayi mishi magana ba ta datse kiran had'i da kashe wayar tayi jefa da ita gefe.


Tun daga wannan rana kullum Ajlaal sayya kira layinta ya tuna mata lissafin kwanaki, yauma tana tsaye a kitchen tana yankan albasa wayarta ta soma vibrating ko inda wayar take bata kalla ba ta cigaba da aikin gabanta, kira akayi tayi akai-akai, ta wawuri wayar a zuciye zata kashe ta, ganin ba number shi bace yasata sauke ajiyar zuciya a fili had'i da d'aga wayar, " ahhhhh! k'aunata yankan albasar ne ya hanaki d'aga wayata?


Wayar ta raba da kunnenta da niyyar kashe wayar yayi saurin fad'in " saura awanni 72 bi ma'ana kwanaki uku suka rage miki, na rantse miki da girmin Allah idan har baki yanke hukunci kafin wad'annan kwanakin ba saina sanar da mijinki duk abinda ke tsakaninmu na kuma bashi tabbaci ta hanyar tura mishi video.....


"Idan kuma ni na fad'a mishi da bakina fa?


D'auke wuta yayi d'if dan jin maganar yayi a bazata, d'auka yayi baiji abinda ta fad'a sosai ba, dan haka yace " eh!


"Eh!, nace idan kuma na riga ka na fad'a mishi komai da kaina fa shikenan barazana ta k'are?


Dariya yayi sosai me isar shi, dan dakyar ya iya tsayar da dariyar yace " wasa kake! wai irin ki bani mamakin nan, ko giya kike sha kya soma tunkarar Deen da wannan maganar?


"Zancen banza ma kenan, murmushi tayi me ciwo had'i da fitar da numfashi ta kashe wayar batare datace komai ba, gas d'in da take girkin ta kashe ta koma falo ta shiga safa da marwa tana tunani.


" Gwara kawai na fad'a mishi koba komai na huta da barazanar Ajlaal, kuma zan ji sauk'in nina fara fad'a mishi akan ace Ajlaal d'in ne ya fara sanar dashi, d'aki ta koma ta zauna saman gado, kamar an tsikare ta ta mik'e zambur ta shiga bathroom, babu abinda tayi a bathroom d'in ta fito ta sake komawa falo, ji tayi gaba d'aya gidan yayi mata zafi, tabbas da ba musulma bace ita da kirat d'in giya zata siyo ta shiga d'aki ta rufe kanta tayi tsirara ta sha giyar tayi mankas, wata k'ila idan ta bugu zata d'an manta damuwarta koda ta wucin dagi ce.......


JIDDARH.....


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.