Free chapter · Read without an account

91&100

by Jameelarh Sadiq · DA'IMAN ABADAN SANADIN SHI

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺

_SANADIN SHI_

*~HOT LOVE AND FATE STORY~*


*BOOK TWO*


_STORY AND WRITING BY_

_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_


_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_


_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! ***_


***


*NO EDITING*


*91-100*


Koda na shiga gida room dinmu na shige nayi wanka na fito nayi sallah,sannan na zauna muka hau fira da su Yaya Teemarh,da yake ban nan suka shigo kallonta nayi Ina cewa.

"Masha Allah,Yaya Teemarh kinyi kyau kin chanza kamar ba ke ba,nikam bai Momy ke baki da kika je birnin kebbi kika sauya haka."?

Murmushi kawai tayi tana cewa.."ni ai naga kamar ma kin fini yin fresh din Kulu maiye sirrin."? Dariya duka akayi ana cewa ai ba Wanda ya Kai amarya kyau da shek'i kuwa,haka muka kusan kwana Muna fira nidai d'aya nayi na dare na kwanta dan ba zan iya wanann doguwar firar ba.

Washe gari aka tashi da hada hadar daurin aure karfe biyu na rana aka daura auren Fatima Abdullahi Jibir da angonta Abubakar Sadiq Aliyu akan sadaki naira dubu dari biyu.

Bayan an daura aure aka fara shirin daukar amarya sosai gidan ya dauki harami na biki ga kuma kukan da amarya take na rabuwa da gida,har damu wajen kuka dan had'a kai mukayi waje d'aya dani da ita da Meenat muna kuka dakyal aka banbareta daga jikinmu aka shiga mota da ita.


Sai da na tabbatar da duk wanda zashi kai amarya ya shiga mota,sanann na koma bayan gida na dauko dinku nan mu na dinner da yake ba'ayi komai ba a biki sai da dinner da za'ayi itama da ace anbi ta son rain Yaya Teemarh to ba'ayi ba.

Fitowa nayi naji wayata tana ringing fiddowa nayi Ina duba mai Kirana bakuwar number ce,burus nayi ban dauka ba na cigaba da tafiyata wani Kiran ne ya Kara fitowa a karo na biyu sai da ta kusa zama misscall sannan na dauka Ina Kara wayar a kunne nayi shuru.


"Kina Ina."?


Tambayar da akayi man kenan,lumshe idonu nayi Ina bude su dan nayi missing din shi sosai bama kamar voice din shi,rabona dashi tun jiya da muka dawo daga wajen cin abinci .


"Gida."


"Okay ba zaki je gidan amarya ba."?


"Zani na tsaya daukar kayana ne wanda zan saka da anjima idan zamu dinner."


"Okay Ina bakin gate idan kin gama ki fito sai na kaiki."


Murmushi kawai nayi Ina kashe wayar na koma cikin gida a room na dauko takalmi da jikka sai kuma sarkar gold da yanhannu da zobe da Mama ta saya mana muyi kwaliyar biki.

Jingine na tadda shi bakin motarshi yana danna waya,karasowa wajenshi nayi Ina sallama,kallona yayi yana aika man da wani irin kallo mai wuyar fassara sai kuma can yace.


"Madam yau dai na hukuntu." Turo baki nayi Ina cewa.."da akayi maka mai." Hararar wasa yayi man yana bude back seat ya ajiye kayana sanann ya kama hannu ya shigar dani mota ya zagayo ya shiga muka tafi.


"SP yau har kusan kuka sai da nayi fa."


"Ayya PP waye wannan mai tsotsayin da ya kusa saka man kai kuka."?


Langwabar da Kai yayi yana cewa.."Uhmm!Allah sarki ni dan bawan Allah,Sp ai kinsan wanda ta tab'a ni dai."

Murmushi nayi Ina cewa.."nidai kam ban sani ba sai an gaya man nayi mashi hukunci." Samun waje yayi bakin titi yana parking maido hankalinshi yayi wajena yana nuna man zuciyarshi yace.


"Zuciya bata da jumurin rashinki ko da minti d'aya ne Sp amman kuma kikayi punishment dina da rashin ganinki ko?yanzun da ban kiraki waya ba da shikenan ba zaki nemaini ba."


Kamo hannunshi nayi Ina cewa.."Sorry PP amman kana sani kana raina duk wuni yau da kewarka nayi shi,kuma ai kaine jiya ka rikeni har sukayo kunshi da gyaran gashi banda ni shine fa nima naje akayi man nawa yau kuma baka ce yayi kyau ba."


Shafa hannuna yayi yana kallon kumshin kiss yayi mashi yana cewa.."Yayi masifar kyau Sp tunda kika fito ya tafi hankalina Ina kokarin nayi magana ai."


Janye dankwalin kaina yayi yana sunsuna kamshin man da akayi man gyaran gashin dashi,shafa kwantaicen gashin yayi yana cewa.


"Masha Allah,SP gaskya gyaran gashin nan yayi kyau haka ma kumshin,sai kamshi kike mai dadi."


Kamo kunnena yayi yana radaman.


"Amman ba kamshin nan naki ya kusa ya na aika wani abu Babe." Ja da baya nayi Ina turo pitch lips dina,kallon lips din kawai yayi yana girgiza kai sai kuma yayi murmushi yana shafa aim din shi,yayi ma mota key muka tafi .


Ba gidan Yaya Teemarh ya tafi dani ba wajen makeup yayi dani sai da ya gama biyan komai sanann ya tafi ya barni akan zai dawo anjima ya daukeni lokacin yasan an gama da yake na tadda wajen mutun biyu a gabana duk da banda bajet din makeup din amman yana kawoni sai na sama raina son yin shi .


Bayan ya tafi aka kira sallar mangariba tashi nayi na shiga toilet ta dauro alwallah nayi sallah sai da za'a kusa gamawa ta biyu lokacin sallar isha'i tayi sai na tashi nayi sallah Ina gama sallar aka kama fuskata aka fara yi man makeup din.


Karfe tara da wani abu na dare ya dawo lokacin an gama man komai na dan jira shi ma amman ba sosai ba,har bakin mota mai makeup din ta rakani tana ta yaba kyaun da nayi dan tayi man pictures yafi sau goma, munyi exchange din content akan zata turo man idan na natsu itama ta samu ta natsu.


Fitowa yayi yana bude man motar na shiga ya kulle ya zagaya Shima ya shiga godiya yayi ma makeover din yana dauka kudi ya Kara bata sanann muka dauki hanya.


Motsi kadan sai yace.


"Babe kinyi kyau kamar na maidaki a ciki haka nike ji."


Ni kuwa sai fari da idanu nike mashi Ina ta zuba mashi shagwabe yana ta biye man,bakin hall din da za'a yi dinner din yayi parking yana waigowa ya kalleni sai kuma ya dan b'ata fuska yana cewa.


"Am jealous fa Babe."


Dariya na fashe da ita Ina cewa.


"Jealous din mai kake yi PP."


Kamo hannuna yayi yana cewa.."duk mazan da ke wajen nan sai suna kalleman ke ni kuma ina kishi sosai gsky ga yanda kikayi kyaun nan gaskya asan abun yi nidai."


Daura kaina nayi a chess dinshi Ina cewa.


"Kamar yanda yanmatan da ke wajen zasu kalle man kai ba,ni ma ina kishinka sosai ya za'ayi PP."?


Dan shuru yayi sai kuma yace.."shikenan dai muje,amman ki sani ba dan raina na so ba,dan Ina bala'in kishinki da kuma kaunarki kice rayuwata."


Murmushi kawai ina kissing dinshi muka fito muka shiga wajen,Muna shiga kallo ya dawo wajenmu sai yaba kyaun da mukayi family and friends suke mana.


Nidai nawa murmushi kawai Ina gaisawa da mutane ,bamu dade da zama ba amarya da ango suka shigo,Masha Allah ba karamin kyau Yaya Teemarh tayi ba so Masha Allah.


Bayan kowa ya zauna nan aka fiddo babbar kawar Amarya ta fadi biography din amarya,Meenat ce a fiddo ita ba bada biography din Yaya Teemarh bayan ta gama Yaya Auwal ya fito yaba da na ango dan angon abokinshi ne sosai.


Bayan sun gama mawaki Auta waziri ya fito ya fara show dinshi sosai abun ya bada kala dan komai a cikin tsari akayi shi bayan Auta waziri ya gama Show din shi aka fara serving din abinci aka ci aka Sha aka koshi aka gode Allah.


Koda cikin yayi nauyi sai yanmata suka fad'a fili aka fara tashewa da wakar Auta waziri mai take Ina kike ne tunda muka fara rawarmu Yaya Haidar yake man barin kudi ko gajiya ba yayi,nima idan na dan samu chain Ina yi mashi sai wajen karfi sha biyun dare sanann dinner ta tashi amarya ta tafi gidan ta da angonta sauran mutane kuma kowa ya gama gabanshi inda yake kwana.


Bamu bar wajen ba sai da muka tabbatar da kowa ya tafi sannan muka tafi a hanya nasha jagula a wajen Yaya tun ina hanashi har dai na saka mashi Ido Ina kallon iKon Allah dan gaskiya Yaya Haidar ba daga baya na jarababan mutun za'ayi dakyal na samu na kusto na shigo gida Shima sai da mukayi fad'a sannan ya kyaleni.


Washe gari


Tun da safe muka fara gyaran gida,dan rabin da kwantan baki sun tafi gida..kadan ne suka rage tare dasu suka taimaka aka gyara gidan aka maida komai need gidan sai kamshi yake kamar ba'ayi wani biki ba a gidan.


Bayan mun gama gyaran gida nida Meenat muka shiga kitchen muka samu muka soya Irish sai muka dafa tea muka jera a kitchen nasan su Yaya Haidar ba zasu shigo yin breakfast ba saboda akwai sauran mutane kula na samu na zuba masu yanda zai ishesu sai kuma na zuba masu tea a flasks na saka a backet na tashi da kaina naje har wajensu nayi nocking sau biyu Ina bugawa sannan Yaya Bash yazo ya bude.


Kallonshi nayi Ina cewa.."bai dai har yanzun baku tashi ba."?


Tsaki yayi yana cewa.."ai ga alamu nan kin gani." Ansar basket din yayi ya juya yana kulle kofar,time na duba naga goma na safe har ta wuce amman wai basu tashi bacci ba ko ciwon jiki basu gudu.


Wanka na fara yi na shirya cikin doguwar riga sannan na fito na zauna nayi breakfast,sai da muka gama break sannan muka dauki gara muka Kai gidan amarya bamu dawo gida ba sai wajen la'asar Muna dawowa bamu tadda kowa a parlon ba.


Nidai ciki na shiga nayi wanka sanann nayi sallah na fito, kitchen na shiga naga mai aka girka ba abunda suka girka kodan sunga ba kowa a gidan oho!Yaya Haidar ya fado man a rai shi mai suka ci tun kallacin safe? Duk da nagaji da bacci nayi niyar yi.


Amman sai na fasa na zage na samu abincin mai saukin dafuwa na girka mana ban gama girkin ba sai wajen biyar da rabi dan harda watermelon lemonade nayi mana da mango juice.


A dinning na jerasu sannan na shiga na sake yin wanka na shafa cream kawai na dan fesa turaruka na shafa kwali na fito,komawa kitchen nayi na dauko backet na zuba ma su Yaya sannan na wuce dan kai masu abinci dan nasan basu ci komai ba tun kallacin safe.


Tafiya nike a hankali kamar wata mai tausayin kasa,jikin juyawa yake ko Ina idan Ina tafiya Wanda bai sanni ba sai yace da gaiya nike irin tafiyar sai dai ni bansan Ina yi ba sai angayaman ,ba kuma yanda banyi ba wajen ganin ma gyara tafiyar tawa amman na kasa dole mama sai dai hakuri tayi ta saka man Ido.


Ji nayi an rikoni anyi wani size dani kamshin turarenshi na shak'a shiyasa na dan ji hankalina ya kwanta..kurama juna Ido mukayi muna kallon kallon a tare muka sauke ajiyar zuciya,kwantar da kaina nayi bisa kirjinshi Ina shafawa dan dagowa nayi Ina mai hura mashi iska a fuska.


Lumshe Ido yayi yana sakar man murmushi,shafa sajenshi nayi ina cewa.


" I miss you PP." Rungumoni yayi yana cewa.


"Missing uh too SP."


Nuna man kumatunshi yayi yana murmushi, dan rufe fuska nayi ina murmushi kwabe fuska yayi yana cewa.."Please Babe sau daya tak kawai."


Dan kwabe fuska nayi nima sai kuma manna mashi unexpected kiss mutuwar tsaye yayi yana shafa inda na sakar mashi kiss din,kamoni yayi ya tura bakinshi a cikin nawa ya fara tsotssr harshena sai da ya gaji dan kanshi sannan ya ciro bakinshi yana kallona yace.


"Inason na dunga kissing dinki Babe bakinki yana da wani testing mai dadi,Ina sonki ina kika shige yau ban ganki ba."? Kwantar da kaina nayi a saman kirjinshi Ina cewa.


"Kana raina Babe." Shafa cikinshi nayi Ina cewa."Allah yasa yunwa bata ilata man kai ba." Shima shafa cikin yake yana cewa.."ai Babe nasha lemu fa."


Turo baki nayi Ina cewa.."ai lemu ba zai rike maka ciki ba,idan kuma ulcer ta kamaka ai na aka jamawa."


Jan hancina yayi yana cewa.."ai yanzun zanci tunda idanu sunyi kallaci da abincinsu sai kuma ba'a ciki nashi ko."?


Murmushi nayi Ina kama hannunshi mukayi bangaresu har parlo na shiga Yaya Muhd ne kwance yana danna waya,gaidashi nayi Ina ajiye backet din naje na dauki na safe Ina cewa ..."aci lafiya." Da dan karfi yace.."Allah yasa Babe I love you." Da sauri na ida fita a parlon har ina had'a hanya kamar zan kife kasa,tare sukayi dariya shida Yaya sannan suka zuba abinci suka fara ci.


"Mama zan tafi."Kallona Mama tayi daga sama har k'asa dan shuru tayi sai kuma tace."Jiddah ki kula sosai bansan wanann rawar kan da kike akan Haidar,wannan wata irin soyayya ce?nidai ki kula da kanki ki kama kanki ke diya mace ce dan haka ki iya takunki ki kuma rage nuna so a fili."

Murmushi kawai nayi ina tafiya,jingine jikin mota na tadda shi murmushi muka sakar ma juna sannan ya bude man mota na shiga ya kulle muka tafi.Wani entry muka shiga bayan yayi mana order din chicken da salad,ana kawo kazar muka fara ciyar da juna sai da muka koshi sanann muka tashi muka taho wani wajen shakatawa yaje ni bayan mun shiga wajen ya kamo hannuna yana lumshe ido furzar da iskan bakinshi yayi yana cewa.


"Babe zanyi missing dinki sosai ji nike kamar na tafi dake Jiddarh."


Murmushin karfin hali nayi kawai dan ma wani zafi nike ji idan na tuna gobe zai koma Birnin kebbi dan acan zaiyi intership din shi.bansan sake yarda na kamu da sonshi ba sai yan kwanakin nan da yake shirin koma gida,dan sati ukku ya kara bayan angama bikin Yaya Teemarh,duka sati ukkun da ya k'ara muna tare da juna bacci ne kawai yake rabamu soyayyarshi ba wanda bai tusa man ba a jinin jiki da jinjiya Ina jin ba zan iya yin Koda minti goma ba ban saka shi a Ido ba.


Bansan taya zan kwatanta maku son da nike ma Yaya Haidar ba,baki ba zai iya furtashi ba tsabar girmanshi idanuwa ba zasu iya fallasashi ba haka gangar jiki,domin Yaya Haidar ya mallake komai nawa inajin zan iya sadaurkar da raina akan shi,bansan b'acin rainshi kamar yanda shima baison nawa.


Bansan sanda naji hawaye na tsiyaya a idona ba, hunging dinshi nayi Ina mai sakin dan karamin kuka marar sauti sosai!rintse idonshi yayi yana hunging dina tight yana shafa bayana cigaba da kukana kawai nike dan ni kadan nasan yanda zuciyata take man na rabuwa da zanyi da Masoyina har na dan watan ni,watan ni sunyi man tsauri da yawa ji nike kamar za'ayi shekaru ban sakashi a idona ba i'cant ba zan iya ba sam.


D'agoni yayi daga cikin jikinshi yana share man hawayen,amman sunki daina zubowa rungumoni yayi ya fara lashe hawayen da harshenshi munfi minti biyar a haka yana lashe hawayena da suke fitowa daga Ido,bayan na samu na tsadasu sun bar zuba sai ya koma lasar fuskata yana lashe duk inda ya samu a fuskata har yazo bakina,tura bakinshi yayi cikin nawa yana cabko harshena ya fara yi mashi wani irin tsotsa mai dauke da sakonni daban daban, lumshe idona nayi Ina tura hannuna cikin laulausar sumarshi yana Sosa mashi kanshi wani irin numfashi yake sake yana Kara damkar harshena yana sakar mashi lafiyaiyen french kiss bansan sanda na Kara tura mashi bakin ba Ina sauke wani numfashi mai tsawon tsiya.


Dagone yayi yana kallona sai kuma ya sakarman murmushi ya kamo hannuna yana cewa.."Babe." D'agowa nayi Ina kallonshi ina sauke ajiyar zuciya furzar da iskan bakinshi yayi yana cigaba da cewa."ki kula man da kanki,ki kula man da komai naki."


Shuru yayi yana kallona sannan ya cigaba da cewa.."inada masifar kishi Babe Ina masifar kishinki dan haka ina mai k'ara tuna maki ki kama kanki a duk inda zaki ban yarda kiyi ma ko wani namiji magana ba balle wanann murmushin naki mai tsada."


"Monday ai zakuyi resume school ko."?


D'aga mashi kai nayi kureni da Ido yayi yana shafa kumatuna da babban tsayarshi, murmushi kuma yayi yana cewa.."ki rike alkwari Babe ki tuna kice rayuwata na bar maki komai nawa,wallahi zuciyata zata iya fashewa idan har na kamaki da yin double dating,duk yanda kike tunanin Ina sonki ya wuce haka Hauwa'u,kishinki yayi katutu a zuciyata kece komai nawa wallahi inajinki har cikin jinin jiki na ban lamince maki da kula ko wace kawata ba bayan Wasi Jiddarh hope kin gane."


Kwantar da kaina kawai nayi a chest dinshi Ina,bance komai ba shima bai damu da nace komai ba na dad'e a jikinshi sai da na gaji da kaina sanann na d'ago Ina cewa.


"Yaya Haidar."


Kallona kawai ya dunga yi bai ansa ba cigaba da cewa nayi.


"Inason ka sani Ina sonka Ina kaunarka PP, ban ganin kyaun ko wane d'a namiji ban ganin kowa sai kai Kaine komai nawa bani fatan abunda zai rabamu,ko mutuwa bani fatan ta fara daukarka ta barni ba zan iya jurar rashinka ba PP,I love you I love you I love you very very much."


Cigaba da shafa kasumbarshi Ina cewa.


"Dan haka zan kula maka da kaina zan taitala maka kaina Kaine kadai mallakin Jiddarh babu wani bayan Kai fatana Allah ya tsare man kai a duk inda kake,Allah ya kauda idon makiya a kanka PP."


Turo baki kuma nayi Ina cewa.."Allah ya rabaka da mayun matan nan masu nacin tsiya,Ina kishinki banjin zan iya share dinka da kowa dan Allah ka zama nawa no d'aya banda wata PP."


Kamo hannuna yayi yana murzawa a hankali a hankali sai kuma yayi murmushi kawai ya girgiza kai turo baki kawai nike kama bakin yayi yana dan ja kadan sanann ya sakarman kiss a saman lips din yace.


"Ki sa a ranki ni naki ne ni d'aya ba wata bayan ke SP."


Murmushi nayi na hunging dinshi Ina dan tintido na sakar mashi kiss a gefen fuska shafa wajen yayi yana murmushi da lumshe Ido yace.


"Yaje Babe."


Dariya kawai nayi nan muka cigaba da soyayyarmu bamu baro wajen ba sai gab da mangariba muzo daidai fita wajen Ina waigawa mukayi Ido hudu da Ahmad gabana faduwa yayi na fara innalillahi a cikin zuciyata.


Ni tsoro lamarin ya fara bani mudun zamu zo park ko entary da Yaya Haidar to conform sai naga Ahmad Shima kuma ba abunda yake sai dai ya kura mana Ido yana kallon yanda nuke shan soyayyarmu.


Taya hakan ke faruwa?taya?nasan halin Ahmad nasan waye shi nasan abunda zai iya Wanda ba zai iya ba,karda yayi ma Yaya Haidar wani abu in shiga ukku ya zaman asara,take jikina yayi sanyi dan nasan ba banza ba yake bibiyarmu.


Hankali na kwanciya yayi da kalli Yaya Haidar na kalli Ahmad ta gefen Ido nasan ko giyar wake Ahmad yake sha ba zai iya da Yaya Haidar ba dan yafi shi komai nesa ba kusa.


Yaya Haidar yana da quality sosai gashi ingarman namiji ga tsawo ga kiba ga kuma kyau Masha Allah, shi Kuma Ahmad baida wanann tsawon sosai kuma kamar a karya tsabar rashin kiba dan kuhun nan kamar marikar lema, murmushi kawai nayi na kara lefewa jikin Yaya muka cigaba da tafiyarmu muna Yar firarmu irin ta masoya.


Koda muka koma gida sai da nayi wanka sanann nayi sallah ban fito parlo ba ana isha'i nayi sallah muka cigaba da wayar mu ta gado da Yaya dan yazun nida shi munbar zaman parlo ayi hira muna manne da waya muna gaya ma irij son da muke ma juna.


Sai karfe sha daya na dare muka kashe wayar muka kwanta cike da shukin son juna..washe gari ban fito parlo ba sai wajen 2pm shima Yaya ne ya fiddo ne yunwa yake ji,bayan mun gaisa da Mama ma fada kitchen na girka mashi indomie da Irish a cikinta na juyo na kawo mashi.


Duka ya tada indomien nan dan da gaske yunwa yake ji baiyi breakfast ba,yana can yana IG dan ba daga baya ba wajen IG baida aiki sai posting din pictures dinshi kuma yana follows da yawa sai dai most of them dinsu matane.


Duk da ba son yawan posting dinshi nike ba ,amman na saka mashi Ido tunda ya saba idan yayi posting a da sai munyi fad'a idan naga comment session naga yanda yanmatan ke crushing dinshi suna yaba kyaunshi suna kodashi sai nai ta fushi.


Ganin banso ya dan rage amman da kullun sai yayi kamar wata ibada,ko yanzun nasan abunda ya tsaya yi kenan har ya kai irin wanann lokacin baici komai ba ga 4pm flight din zai tashi zuwa birnin kebbi.


Bayan ya gama ci na kawo mashi ruwa mai dan sanyi ya sha dan shi Yaya baya hudda da ruwan sanyi sosai,zaunawa yayi akayi fira dashi harda Baba da yake yau sunday bai fita campany ba yana gida.

Daman duk Sundayn duniya Baba baya zuwa company yana gida yana kallon movement din kowa idan da rabon ayi maka fad'a zaka shashi dan Baba bai raina abun fad'a ko kadan kuwa...nidai kawai jinsu nike suna magana amman bansan mai suke cewa ba dan zuciya ba dadi take man ba,duk jina nike sukuku da ace hutun school dinmu bai kareba da ba abunda zai hanani bin Yaya Haidar muje birinn kebbin tare Ina imagine din yanda zan yi ne kawai wanann tafiyar da zaiyi.


Duk da yace man duk bayan sati biyu zai dunga zuwa zance wajena zaizo Friday ya koma sunday,amman duk da haka Ina hango nisan satin biyun.

D'ago kaina nayi muka hada ido dashi duk da daman inajin jikina kallona yake dan gangar jiki ta sanar dani,dan murmushi kawai nayi shima murmushin yayi yana man sign da na daina damuwa karda shima na sashi a damuwa.


Murmushi kawai na kuma sakar mashi Ina duba time 3 har tayi harda wani abu mean sauran yan minti fa ya rage ya tafi ya barni nidai kam bansan ya zanyi ba..cigaba da firarsu kawai sukayi sai 3:30 sanann ya tashi ya tafi dan ya shirya nima tashin nayi na shiga room dinmu.


Sai da na dan matse kwalla na sannan na shiga wanka cikin yolk din laces na shriya dinkin coke shape ne sosai rigar tabi jikina ta fiddo man da shape dina ,ganin 3 harda minti 55 na tashi nayi sallah first sannan na shirya wayata naga tayi haske na duba murmushi kawai nayi na dan fasa turare sannan na dako gyalena na fito.


Har airport muka rakashi da ni da Yaya Muhd kawai muka tafi..Muna zuwa airport din Yaya Muhd ta fita motar yana answering din waya,Shima Yaya Haidar fitowa yayi ya dawo baya yana kallona sai kuma ya kamo hannuna yana kissing din kumshin hannun, shafa fuskata yayi a hankali yace.


"Zanyi kewarki Babe,zanyi kewar wannan kyaun naki Babe da komai naki take care take care take care please and please Babe I love you muah." Ya sakarman kiss a lips lumshe idona kawai nayi Ina murmushi mun dade a cikin mota muna jimamin tafiyar da zaiyi sai da aka fara announcement din za'a fara tafiya ya fiddo wasu kudi masu yawa ya damka man a hannu yana cewa.


"Ki fara manage da wannan 200k ce kafin na dawo."


Kallon kudin nayi Ina kallonshi sai kuma na girgiza kai Ina cewa.


"Yaya sunyi yawa sosai."


Dan daure fuska yayi yana cewa.


"Nine nan nike da hakin yi maki komai Jidda saboda an bani ke iyaye sun gama magana karatunki kawai ake jira ki karasa na dan watan ni ke ida zama tawa,dan haka karda ki sake ki sake yi man haka karda ki sake ki tambayi Baba kudi ko Mama ko kuma su Muhammad komai kike so ni zaki tambaya a shirye nike nayi maki komai kike so a duniya Ina sonki inasonki Ina kaunarki Jiddarh."


Fadawa nayi jikinshi Ina kuka Ina cewa Ina kaunarshi sosai Nima dakyal ya rairasheni ya fito Ina kallo ya shiga jirgi nan na Kara sakin wani sabon kuka Muna tsaye suka tashi suka tafi,nan na Kara volume din kukana har muka iso gida Ina kuka tun Yaya na lailashina nayi shuru har ya fara yi man fad'a akan na isheshi da yankoke koke.


Koda muka dawo gida ban tsaya sauraren kowa ba na shige room Ina kukana ban bar kuka ba sai da ya kirani ya gayaman har ya sauka sanann yace na bar kukan hakanan ya isa haka ..lokacin Sallah yayi muka kashe wayar bayan isha'i ya kirani muka sha wayarmu sai wajen sha biyu muka ajiye wayar cike da kewar juna.



*AMATULLAH DATA SERVICES*


*MTN*

500MB-140

1GB-270

2GB-540

3GB-810

4GB-1080

5GB-1350

6GB-1620

7GB-1890

8GB-2160

9GB-2430

10GB-2700


9MOBILE

500MB-150

1GB-300

2GB-600

3GB-900

4GB-1200

5GB-1500

6GB-1800

7GB-2100

8GB-2400

9GB-2700

10GB-3000


VIA✓8160508316

Jamila Bello Abubakar

Opay bank

VIA✓0777512438

Jamila Abubakar Bello

Access bank


*** for call or whatsapp

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.