Free chapter · Read without an account

Chapter 9

by Fattuma · PART OF OUR DESTINY

@fatymasardauna


PART OF OUR DESTINY

*free page*


*CHAPTER 9*


Ahankali ya k'arasa haurawa saman, kasancewar yana jin duk jikinsa amace, wannan yasa yana k'arasawa saman bedroom dinsa ya nufa.

Wayarsa dake hannunsa ya wurga akan gadon, tare da zare long sleeve din dake jikinsa, akasalance yabi gadon ya kwanta, idanunsa ya lumshe ahankali, yakejin bugun zuciyarsa na daidaita. 

Hakanan yake jin kamar ya sauk'e wani nauyin da shi kansa bai san na menene ba, yayinda daga can k'asan zuciyar tasa kuwa wani bak'on lamari ne ke wanzuwa batare da sani ko Kuma yarda da amincewar shi ba. 


Still sake gyara kwanciyarsa yayi, akaro na barkatai ahaka har baccin da bai shiryawa ba ya d'auke sa. 


Yayinda acan k'asa kuwa sam Aamma ta kasa yin nesa da yarinyar, wacce take jiran farkawarta, gudun kada sai tayi nisa yarinyar ta tashi.

Kallon yarinyar take cike da ciwon sanin wani ya b'ata mata rayuwa da k'ananun shekarunta, hannunta tasa ta kawar da tarin hargitsatssen gashin yarinyar daya rufe mata gefen ido, wanda hakanne ya bata daman kallon fuskar yarinyar da kyau, tausayin ta me tsanani ne ya k'ara shiganta, domin atashin farko take jin yarinyar kamar y'arta ta cikin ta, duk da cewa Allah bai azurtata da haihuwar y'a mace ba, d'iya mace abune da take so, shiyasa ayanzu take jin Yacine din ak'asan zuciyarta. 


Sauk'ak'akk'iyar doguwar rigar atamfar dake jikin yarinyar ta kuma kalla, wanda kana gani kasan bawai suna da isasbshen arziki bane saidai rufin asiri, komai na jikin yarinyar me sauk'in kud'ine in banda natural soft skin d'inta, Wanda yake d'auke da tsananin hasken dake nuna babu alamar wahala atarrare da Ita, kasancewar farinta irin me d'aukar hankalin nan ne, ga kuma tarin suma me tsananin laushi dake kanta, wanda tsawonsa ya kai har bayanta, tamkar Tuareg din Algeria haka take amma yanayin shape din fuskarta da kuma hasken fatarta yasa kaitsaye zaka iya danganta ta da Mauritanian🇲🇷. 


Ajiyar zuciya Aamma ta sauk'e tare da janye idanunta daga kan yarinyar, wanda hakan yayi daidai da farkawar Yacine din, ahankali ta soma bud'e idanunta, da take jin duk sun rirrik'e, domin dama bawani iya gani take yi da kyau ba, saboda wahalan da tasha.

Idanunta ta ware bisa saman d'akin, kafun ahankali taja wani dogon numfashi tare da soma yunk'urin tashi dan tabbatar da inda take, domin duk da bata da cikakkiyar nutsuwarta ta tabbatar da cewa nan ba hospital bane. 

Saidai kamar yanda taso ba hakan ne ya kasance ba, domin ajikinta babu wannan k'arfin da zata iya tashi, hasalima allurar da akai mata baigama sakinta ba, ji take yi komai na duniyar baya yi mata dad'i, wanda hakan yasa ta sakin wani irin kuka, cikin muryar ta dake shaking ta soma kiran sunan.


"Khalty! Khalty!!"


Da sauri Aamma dake zaune acan gefe, jin tana kiran sunan khalty yasa ta juyo, tare da matsowa kusa da ita, cikin kulawa tace.

"Sannu, kwanta ki huta kar kice zaki tashi." 


Bak'uwar muryar da taji ta daki dodon kunnenta ya sata juyowa ahankali, ido hud'u sukayi da Aamman, wacce ganin idanun yarinyar yasa tajin wani irin matsanancin harbawan zuciya.

Domin aduniya awajen mutum d'aya take ganin irin way'annan k'wayan idon, duk da cewa Akwai wani d'an banbanci atsakanin nasa idanun da nata, amma shi kad'ai ke da irin way'annan idanun da cikinsu ke d'auke da rare grey.


Numfashi me k'arfi Aamman taja, tare da k'wak'ulo murmushi ta aza akan fuskarta, batare da ta samu da kallon da Yacine din keyi mata ba, atausa she tace.


"Sannu, har kin tashi ya jikin naki?"


Idanunta da sukayi narai narai ta zubawa matar, da fuskarta ya kasance bak'o agareta, wacece ita? inane nan kuma aka kawota?

Way'annan tambayoyin sune ke circulating acikin zuciyarta, wanda hakan yasa murya can k'asan mak'oshi tace.


"Waye ke? Inane Nan? Ina Khalty na? ciwo nake ji acikin jiki na, inajin zafi sosai dan Allah ki kiramin Khalty na...." 


Ta k'are maganar tana me jujjuya kanta, had'i da yunk'urin tashi zaune amma still ta kasa.


Tausayinta ne tsantsa ya kama Aamma da lokaci d'aya taji hawaye nason zuwar mata, wannan yasa asanyaye cikin tausayawa tace. 


"Kwantar da hankalin ki kinji Khalty zata zo, amma bazan kira miki ita ba har sai kin daina wannan kukan, sannan sai kin yarda na gasa miki jikin ki tukunna, saina kira miki Khaltyn, yanzu ki nutsu ki fad'amin ina da inane ke miki ciwo?"


Hannunta ta d'aura adaidai kan mararta wanda da alama, har yanzu pain na disvirgin dinne sam bai saketa ba, cause har yanzu tana jin zogi awajen, tunda abun yazo ta sanadiyar fyad'e ne, kasancewar ba a bi da ita ahankali ba, yasa dole ta samu raunuka da yawa. 

Ganin hakan yasa Aamma mik'ewa batare da tace komai ba ta wuce bathroom din dake cikin dakin, towel ta d'auko ta fito bayan ta tara ruwa me dan madaidaicin zafi acikin bathtub.


Koda ta fito daga toilet din, samun Yacine din tayi taci gaba da kukanta tare da kiran sunan Khalty, hannu tasa ta tayar da ita zaune, cikin tausasawa tace. 


"To daina kukan, kina so kiga Khaltyn ki?"

Kai ta jinjina alaman "Eh."


"To taso muje kiyi wanka sai akaiki wajen Khaltyn ki, Idan ba haka ba Kuma bazaki je ba."


Idanunta ta d'an tsurawa kyakkyawar matar, abad'inance so take tayi mata musu, amma kuma azahirance hakan ya gagara, ganin yanda ta tsaya tana narai narai da ido, yasa Aamma jawo hannunta.

Da wannan damar tayi amfani wajen jan ta zuwa bathroom d'in.

Koda suka shiga bathroom din Aamman da kanta ta cire mata doguwar rigar dake jikinta, kasancewar bata da kuzarin da zata iya yiwa kanta komai.

A wannan ruwan zafin dake cikin bathtub din Aamma ta zaunar da ita dab'as.

Wani irin k'ara had'i da ihun azaba ta sakarwa Aamman alokacin da zafin ruwan ya ratsa cikin p*ssy d'inta, yunk'uri ta soma yi dan fita daga ruwan.

Ganin haka yasa Aamma fara lallashinta had'i da ban baki, ahaka har ruwan ya gama ratsa ta, ita kam Aamma har ta manta da wacece Yacine din awajenta, batare da tayi la'akari da batasan ko asalin yarinyar ba, jinta kawai take yi tamkar y'ar da tahaifa acikin cikinta, musamman saboda k'ank'antar shekarun yarinyar da ta gani, innocent girl ce da har yanzu bata gama sanin kanta ba, dole tana buk'atar kulawar uwa agareta adaidai wannan lokacin. 

Hakan yasa Aamman tsayawa da kanta tayi mata wanka, bayan sun kammala ta bata bathrobe ta sanya ajikinta, saboda ta lura har zuwa lokacin bata gama dawowa hayyacin ta ba, akwai alamun yanayin mayen bacci atattare da ita.

Hakan yasa ahankali ta rik'o hannunta suka fito daga toilet din.

Akan lallausan bed din Aamma ta zaunar da ita tare da cewa.

"Inazuwa."

Ta fad'a tana me ficewa daga cikin d'akin.


Da idanunta wanda sukayi wani iri tabi Matar da kallo, had'i da sake k'ank'ame jikinta, saboda wani irin sanyi da take jin na ratsa ta, duk da cewa kaso 10 na cikin pain din da takeji ya ragu, amma har yanzu tana jin kanta cikin wani irin tsoro me tsanani, wanda yasa ta soma bin d’akin da kallo tana jan sheshshek'an kuka cikin rashin sanin takamaimai inda take. 


Ab’angaren Aamma kuwa tana fitowa daga d’akin direct dining table ta nufa, hot tea ta had'a acikin mug, had'i da plate d’in dake d’auke da pancake wanda aka yayyanka strawberry asamansa bayan an shafesa da Nutella, abubuwan da ta had'a mata kenan, hannunta rik’e dasu ta nufo falon. Ammabuwa kuwa dake zaune dirshan sai faman cika da batsewa take, Aamman bata tanka mata ba ta wuce, da kallo Ammabuwan ta bita tana me hararar mug din tea din had’i da plate din Pancake d’in dake hannun Aamma'n.

Oh ita kam tana ganin ikon Allah acikin gidan, ita ahanata cin abu me dadi, wasu kuwa da bakoman komai ba abasu, k'wafa tayi tare da mikewa tsaye cikin sand'a tana mejan feet dinta da suka kumbura ta k'arasa dining table din, acikin ranta take cewa.

"Duk abunda nake so shi zanci, tea me kauri ma zan had'awa kaina nasha, babu ubanda ya isa kasheni kwanana bai k’are ba." 


Ahankali Aamma ta tura kofar dakin ta shiga, har yanzu tana nan zaune a inda tabarta, saidai ayanzun ta takure jikinta ne waje d'aya, tana aikin rafka kuka.

Anan kusa da ita Amma ta zauna tare da dubanta, cikin yanayin rarrashi tace.


"Kiyi shiru kinji, babu wanda zai cutar dake anan gidan, Khaltyn ki kuma zata zo, amma sai kinci abinci, saboda Emraan ya cemin akwai yunwa sosai acikin ki, ko bakyaso ki samu sauk'i ne?" 


Kai ta girgiza, tare da zubawa Aamman idanu, na tsawon minti guda, kafun ahankali cikin rashin k'warin jiki tace.


"Inane nan? Waya kawoni? dan Allah ki maidani wajen Khalty na, ni banason abinci ni Khalty na nakeso..." 


"To shikenan, zan maidaki wajen Khaltyn ki, idan kikaci abincin nan, maza bud'e baki."


Amman ta fad'a tana me kawo mug din tea din daidai saitin bakinta, wanda jin za a maida ta wajen Khalty, yasa babu musu ta bud'e bakin.

Abayyane yake cewa cikinta na matukar bukatar abinci duk da cewa ita d’in bata fahimci hakan ba.


Kurb’i uku zuwa hud’u ta yiwa tea din ta janye kanta haka ma Pancake din, wanda Aamman ce da kanta take bata, ji take kamar tana tauna mad'aci abakinta madadin zak'in dake d'auke da tea da kuma nutellan dake jikin pancake din, Sam babu wani taste na d’and’anon dad’i abakinta, tanajin kamar zatayi amai shiyasa ta janye kanta gefe, tana me sake k’ank’ame jikinta dake ta faman b’arin sanyi. 


Kallonta Amma tayi akaro na barkatai ita batasan dalilin da yasa takejin yarinyar acikin zuciyarta sosai har haka ba, haddai idan yarinyar ta kalleta, takanji wani iri ajikinta, saboda k'wayoyin idanunta dake tuna mata da siffar halittan cikin idanunsa. 


"Har kin koshi?."

Aamman ta fad'a cikin tausasa muryar da yasa Yacine din, rumtse idanunta, madadin tayi magana kuma saita saki sabon kuka me sauti had'i da tsuma zuciyar mai sauraro, da yasa Aamman mik’ewa tsaye, cikin rashin k’warin guiwa ta fice daga d'akin, kaitsaye ya nufi d’akin Dr. Emraan dan sanar dashi halin da ake ciki.


Tashinsa daga bacci kenan, batare daya tashi akan gadon ba, yana rik'e da kansa dake sarawa kad'an kad'an, kamar daga sama yaji ana knocking din k'ofar nasa, yunk’urawa yayi da sauri ya tashi zaune dan yasan baiwuce Aamma ce ke bugawa, dirowa daga kan gadon yayi, tare da k’arasawa cikin nutsuwa ya bud'e k'ofar. 


"Aamma."

Ya fad’a yana me kallon Aamma’n dake tsaye.


Wacce ganinsa yasa ta zuba masa ido, tare da cewa.


"Wato kazo ka kwanta abunka kamar bakasan ka kawo yarinyar mutane cikin gidannan ba, kabar ni da ita sai faman kuka take min, sai kazo muje ka rarrashe ta ai." 


Cewar Aamman dake harararsa, batare da ta jira cewarsa ba kuma ta juya tayi tafiyarta, idanunsa ya dan lumshe ahankali, hadi da biyo bayan Amman.

Saidai kafun ya karaso ma ita ta riga data sauka kasa. 


Dakin da Yacine din ke kwance ya nufa direct, saboda tun kafun ya karaso yake jiyo sambatu hadi da gunjin kukanta, tura kofar dakin yayi, tare da shiga kaitsaye, kwance ya hangota akan gadon sai faman rawar sanyi take, yayinda Aamma dake gefe ke kokarin lullub'e mata jiki da blanket, duk tayi wata buju buju da ita, jik'akk'en gashin kanta dake watse akan pillow ya kalla, kana cikin sanyi da muryarsa wacce take da matsanancin taushi, yakira sunanta 


"Yacine" 


Kanta ta d'ago saboda jin sautin amon muryarsa acikin kunnuwanta, ido hudu sukayi da shi, duk da tana cikin yanayin fever amma bata kasa ganeshi ba, bakinta ta bud'e ahankali murya araunace tace.


"Khalty na, ina Khalty na." 


"Khalty tana zuwa, ita kikeson gani?"

Ya tambaya, cikin lumshe ido.


Kai ta jinjina masa alaman "Eh"


"Is okay Khalty zata zo, amma saikin daina kuka, yanzu gaya min me yake miki ciwo, fad’amin kinji.”


Hannayenta dake karkarwa ta daura adaidai saman mararta, cikin yanayi irin wanda ke bayyana tsananin ciwon da takeji, wanda zafinsa ke fitowa tun daga kasan zuciyarta, lips d’inta na b’ari tace.


"Nan d'ina ne, zafi nake ji awajen, kuma inajin wani abu na suka na, inajin fitsari sosai, amma fitsarin bazai zoba saboda zafi wajen yake yi, ni banason shi banason ganinsa, banason wannan sautin da nake ji acikin kunnuwa na, banassooooooooo....." 


Ta k'are maganan cikin matsanancin kukan da yasa, Dr. Emraan runtse idanunsa, saboda duk yasan me take ji, yayinda Aamma dake gefe kuwa hawaye ne suka cika idanunta, na tsananin tausayin yarinyar da wani ya gurb'atawa rayuwa. 


Dr. Emraan kuwa ahankali ya d'an sunkuyo daidai saitin kanta, hannunsa ya d'aura akan forehead dinta, wani irin zafi zau yaji jikin nata, sam yarasa wani irin zazzab'ine haka ajikinta da yaki sauk'a.


Da idanu yayiwa Aamma alama akan ta bashi tablets din daya bata d'azu, kasancewar dama suna gefenta yasa da sauri ta mik'a masa.

B'allan magungunan yayi, hannunsa rike da bottle water atausashe yace. 


"Tashi kisha magani sai mu tafi wajen Khalty ko."


Har lau dai taso yin gardama amma jin za akaita wajen Khalty yasa ta bud'e idanunta saidai kasancewar bata da karfin tashi, yasa Aamma ce ta d'ago ta, da kansa ya zuba mata magungunan acikin bakinta sannan ya bata ruwa.

Hannunta dake dauke da cannula ta daura bisa saman nasa hannun dake rike da bottle din, da k'arfi take tuttulawa cikinta ruwan kamar wacce bata tab'a sha ba.


Idanu ya zuba mata, saboda yanda take shan ruwan yasan dole zatayi amai, ai kuwa ko gama kammala tunanin nasa baiyi ba, ta kelayo aman ruwan rabi ajikinta rabi a hannunsa.


"Sorry"

Ya fad'a yana me lumshe idanunsa, domin shi mutum ne me tsananin kyankyamin amai, idan yaga amai ransa yakan b'aci, saidai wani abun mamaki for the first time yaji ransa bai baci ba, sam baiji k'yank'yamin aman nata ba, da hannunsa wanda bai b'aci da aman ba yayi amfani wajen jawo tissue, anutse ya goge aman daya tab'a masa jiki.

Ita kuwa dama tana gama aman ta koma ta kwanta, saboda jikinta daya sassake, ko mintuna 2 ba’a cika ba, bacci ya kwashe ta. 


Ahankali ya soma goge mata aman, yanajin wani irin gumi na ketowa daga cikin gashin kansa, yayinda daga cikin kirjinsa kuwa zuciyarsa ce ke wani irin bugawa. 


Tsam Aamma tayi tana kallonsa da idanunta, wanda suke kokarin bayyana mata kad'an daga cikin gaskiyar abunda ke b'oye, hannunsa dake rawa wanda ya d'aura agefen bakinta yana me goge mata aman, ta tsurawa ido, tana me nazartarsa acikin zuciyarta.

“Meye hakan kenan, Emraan tsoron mata yake?"

Tayiwa kanta tambayar wacce tasan bata da amsarta, saboda ganin yanda duk jikinsa ke rawa.


Idanunta ta ci gaba da zuba musu domin tanaji ajikinta cewa akwai wata sabuwar k'addara dake tartare dasu, saboda tana iya jiyo k'arfin wani kusanci dake tunkarosu, ita macece me baiwar jiyo ko hasaso kaddara, kamar dai yanda yanzu takeji ajikinta, saidai batasan wace kalar k'addarace ke tunkarosu ba, me dadi ne ko kuwa akasin haka. 


Ajiyar zuciya ta dan sauke tare da kawar da idanunta daga kansu, daidai lokacin Dr. Emraan din ya mike tsaye.


"Tayi bacci."

Ya fad'a batare daya bari sunyi ido hud'u da Aamma'n ba, wacce ta jinjina kai alaman 

“To."

Juyawa yayi zai fita asanyaye, har yakai bakin k'ofa, Aamman tace. 

"Idan ka fita gobe ka saya mata kayayyakin sawa, ko ka kira y'an gidan nasu sukawo mata kaya."


"To."

Ya amsa yana me k'arasa ficewa, yayinda Aamma kuwa ta shiga gyara mata kwanciya, bayan ta kammala ta kashe AC'n dake cikin dakin tayi ficewarta, zuwa side dinta. 


Har cikin dare Aamma tazo ta duba ta, amma saita samu tana bacci, tana matukar tausayin yarinyar k'warai, musamman ma dai ayanzu da takejin yarinyar ta k'ara shiga ranta. 


Washegari, da sassafe Aamma ta tashi ta had'a kayan breakfast, saidai koda ta lek'a d'akin Yacine din, bacci tasamu tanayi, kamar dai yanda ta barta d'aren jiya haka ta same ta, da alama magungunan da Emraan ya bata masu k'arfi ne, sake gyara mata rufa tayi, sannan ta fito.

Tana fitowa Emraan din na saukowa shida Abbou atare, dukansu sanye suke cikin shirin suit, saidai shigar Emraan din yau ta zama ta musamman sosai.


"Wannan kwalliyar batayi kama dana mutumin da zaije duba marassa lafiya ba, sai ina?."


Cewar Aamma tana kallonsa. 


Murmushin dake k'ara bayyana tsantsar kyaunsa yayi.

Murya atausashe yace.


"Hospital mana Aamma, muna da important meeting ne, nama so na makara." 


"Okay come and eat your breakfast to before ka wuce." 

Amman ta fad'a tana me k’arasawa dinning table d’in nasu.


"No Aamma yau coffee kawai zan sha, banson cika cikina da abu me nauyi." 

Ya amsa yana me bin bayanta.


Coffee din ta had'a mishi, yayinda Abbou kuwa ta had'a masa Beef teriyaki with mashed potatoes kasancewar shine favourite dinsa, da kuma shredded chicken meal, Aamma mace ce da ta matukar san kanta wajen iya girki, shiyasa koda wasa basa garaje wajen missing food dinta, musamman Abbou da yake ganinta mace d'aya da tafi masa kowace mace aduniya, duk da tarin arzikinsa, amma gani yake alfarma tayi mishi da ta aureshi, saboda tsananin kyaun da take dashi. 


Abincin Abboun ya faraci cikin santi kamar yanda ya saba, yayinda Aamma kuwa ke zaune agefensa tana gyara masa zaman neck tie dinsa wanda agarin sauri ya d'aura ba daidai ba. 


Mug din coffee din dake hannunsa ya ajiye, fuskarsa akan iyayen nasa da ako yaushe suke bashi sha'awa, tare da tayar masa da ciwon dake yawo acikin zuciyarsa cikin kowani second na rayuwarsa, had’i kuma da tunatar masa da mummunar k'addararsa dake sanya bugun zuciyarsa tsayawa.

Wani yawu me d’aci daya tsaya masa amak’oshi ya had'iya ahankali cikin sanyin murya yace.


"Saina dawo Aamma, zanje naci wannan a mota."


Ya fad'a yana me d'aukan marinated slice bread, wanda yaji caramel sauce asaman sa. 


"Bakaje ka duba patient din naka ba, kuma zaka fita, duk da ma naga bacci take yi.”

Cewar Aamma dake binsa da kallo.


"Zan makara ne, please Aamma ki duba ta idan kin tashi." 


Ya k'are maganar batare daya waigo ba, kana cikin sauri ya fice.


Kai kawai Aamman ta girgiza tare da maida dubanta ga Abbou, wanda yake tambayarta akan patient din, kasancewar daren jiya tayi masa bayanin komai, kuma dama agabansa Emraan din yayi maganan kawo ta.


"Ya jikin nata?"

Abboun ya tambaya.


"Da sauki, saidai har yanzu zuciyata akaraye take dangane da ita, matukar tausayinta nake ji, har yanzu na kasa gane rashin tausayi irin na wasu mutanen, k'aramar yarinya kamar wannan anyi mata fyad'e, an lalata mata goben ta, daga ni kuma iyayenta masu k'ananan k'arfi ne, inajin yarinyar har cikin zuciya ta."


Murmushin daya bayyana kamanninsa dana Dr. Emraan yayi, tare dasa hannunsa ya shafi gefen kyakkyawar fuskarta, cikin kulawar daya saba bata yace.


"Ke ai dama me tsananin tausayi ce, har yanzu zuciyarki tana da rauni sosai, komai naki baya iya canjawa." 


Murmushi kawai tayi masa, saboda batajin zai fahimci yanda takeji adangane da yarinyar, yayinda shi kuwa ya ci gaba da cin abincinsa, daya dauke sa tsawon mintuna kafun ya kammala, Aamman da kanta ta rakasa wajen mota ya tafi. 


Wajajen 10 ta muskuta daga kwanciyar da tayi tsawon awanni batare da ta motsa ba, duk da cewa bawai bacci take yi ba, saidai idanunta arufe suke gam, yayinda jikinta ke karkarwar dake bayyana tsananin tsoron dake tasowa daga karkashin zuciyarta.

Wani irin fargaba take ji, na rashin sanin me zata tarar idan ta bud'e idanunta, tasan cewar wannan duniyar da take ciki daban take da wancan nata duniyar, wannan rayuwar ba ta ta bace, rayuwar da wasu suka bata ne, ba it-ace wannan Yacine din ba, ba itace Yacine din da zuciyarta ke cike da hope ba, ba itace wannan yarinyar dake rayuwa batare da sanin wani k'alubale ba.

Ayanzu zuciyarta ce ke bugawa sosai, yayinda wasu siraran hawaye ke gangarowa ta k'asan idanunta, tanajin komai daya faru agareta yana dawo mata sabo.

Wannan mummunan pain din keta mata haddin shike ci gaba dayin circulating acikin brain dinta, abune na daban da bata tab'a sani ba aduk rayuwarta, taya zata iya mance yanda yayi mata mummunan tabon da bazai tab'a gogewa daga cikin k'undin tarihinta ba. 


Abubuwan tamkar azahiri haka take ganin komai, birkitaccen kukan daya taho mata kaitsaye ta saki, wanda sautinsa ke bayyana yanayin ciwon dake zuciyarta afili, wanda fitar kukan nata kuwa yayi daidai da shigowar Aamma cikin d'akin, zama tayi akusa da ita, tare dasa hannu ahankali ta tab'a ta.


“Yacine."


Azabure ta bud'e idanunta da sukai ja, cikin yanayi na tsoro take kallon balarabiyar matar.


Murmushi Aamma tayi mata, had’i da sake matsowa kusa da ita. 


Da sauri ta sake matsawa baya tana me kare jikinta, cikin muryar kuka da magiya tace.

"Dan Allah karku cutar dani, karku sakemin wani abu, kar ku maidani wajen shi, ku kiramin Khalty na, ku maidani gida." 

Ta ida maganar tana me had'e hannayenta biyu waje guda alaman rok'o.


Hawayen tausayine suka cika idanun Aamma, domin k'warai ta fahimci tsoron dake tartare da yarinyar, hakan yasa atausashe tace.


"Bazamu miki komai ba kinji, bazamu cutar dake ba Yacine, taho kinji kiyi kuka nasan hakan shizai sama miki sauki, ki d'auke ni tamkar uwa mahaifiya, taho kinji zo kiyi kuka ajikina." 


A'amman ta k'are maganar tana me jawota jikinta, nanfa ta shiga rera kuka me tsuma zuciyar me sauraro, dan jinta ajikin Aamman yasa tajin kamar tasamu mafakar b'uya, kuka tayi son ranta Aamman na rarrashin ta, saidai ganin taki yin shiru yasa Aamman fara shafa bayanta, ahankali take fad’in.


"Ya isa daina kukan haka kada kanki yayi ciwo, muje toilet ki wanke fuskan ki, anjima kad'an Khaltyn ki na zuwa sai ku tafi gida ko."


Da wannan kalaman Aamma ta rarrasheta, ita da kanta ta kaita toilet ta wanke mata fuska, bayan sun fito daga toilet din, Aamma ta wuce daki ta dauko mata wani Moroccan Jallabiya, wacce da gani kasan na maza ne, sannan anjima ana ajiyeta, duk da kuwa cewa riga ce da takai tsawon shekaru 3 tana ajiye, amma komai nata tsabtsab, Aamman da kanta ta taimaka mata wajen sanya rigar, saidai yayi mata yawa kasancewar rigar nada tsawo, saidai duk da haka ya amshi kyakkyawar white skin dinta, dake surke da launin ja. 

Kallonta Aamma keyi, saboda ganinta acikin jallabiyar ya tuna mata da abubuwa da yawa, ciki kuwa harda babban mikin dake kwance acikin zuciyarta. 


Nannauyan abunda ya tsaya amakoshinta ta had'iya, tare da kamo hannun Yacine din.

“Muje falo ko.”

Ta fad’a cikin sakin rai, saboda bata son jin sheshshek'an kukan da yarinyar keyi, tare da jawo hannunta suka fito.

Aamman na rik’e da ita haka suka fito.

K’afarta na dama da ta fara jefawa acikin parlorn, yasa ta sake kankame jikinta, saboda wani irin sanyi me tsanani da taji ya dake ta, wanda shiya tilasta mata bud'e kumburarrun idanunta dake lumshe.

Ahankali ganinta na farko ta sauke su akan wani tafkeken, frame d’in hoto dake facing dinta, wanda cikinsa ke d'auke da hoton wani wanda bazata iya tantance kalar fuska ko yanayinsa ba.



#fatymasardauna

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.