Free chapter · Read without an account

ZAZZAFAR KAUNA 11&20

by Jameelarh Sadiq · DA'IMAN ABADAN ZAZZAFAR KAUNA

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺

_ZAZZAFAR KAUNA_

*~HOT LOVE AND FATE STORY~*


*BOOK THREE*


_STORY AND WRITING BY_

_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_


_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_


_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! ***_


***


*11-20*



Shirin dawowa kasarsu ta haihuwa Beauter suke dan har ta saki gidan da take haya a Ukraine ta taitara duk kayanta a cikin trollys ta maido a gidan su AK ba abunda ta manta bata kwashe ba bama kamar kananun kayanta da kuma kayan gyaran jiki sai da ta kwashe komai...motarta kuma a kasuwa ta sakata ta saida kayanta ta sa kudinta a account duk da tana jin zatayi kewar kasar Ukraine dan ta saba da rayuwar Kyiv sosai rayuwace ta yanci ba ruwan wani da wani kowa hidimar gabanshi kawai yake.


Amman kuma yanzun hankalinta kwacokam ya dawo gida nigeria bama kamar gusau ji take kamar ta rintse idonta ta bude ta ganta tsindun a cikin gusau ...gusau din ma a cikin gidansu parlon Mama da sai yanzun take jin wani kewar parlon tana adfdaba mata,sai yanzun take jin kewar dramar gidansu da comedy din su Yaya Bash,daman shi Yaya Bash yana da saukin rai kuma akwai shi da zuciya mai zafin tsiya bai daukar shashanci amman yana wasa da yara.


Saukowa daga saman bene tayi tana cewa.."Sorry Beb tashi mu tafi." Kureta yayi da ido yana Kara jin tsoron Allah a zuciyarshi ya kuma Kara yarda babu abun bautawa da gaskiya sai Allah,kuma ba wanda ya isa yayi hallita sai Allah tabbas Allah yayi hallita a wajen Beauter...Allah ya azurtata da kyau wanda ko ita yana jin bata san ta da shi ba komai nata mai kyau ne gata wata irin colar ce Allah yayi mata wanda da wuya a samu mai kalar fatar da suka Kai goma a duniya dan fatar ba baka bace amman brown skin ce mai shike da kuma daukar ido.


Hura mashi iskan bakinta tayi tana girgiza shi tace.


"Beb."


Turo baki tayi tana yarfa hannu cikin shagwabar ta da ta zamai mata jiki tace.."mu tafi kaga muna cinye time fa." Murmushin shi mai tsada ya sakar mata yana shafa gefen fuskarta da yatsunshi guda biyu yace.


"I love you Partner."


Lumshe Ido kawai tayi tana jan hancinshi a hankali tace.. "Are the best Beb!Oya let go."


Jan hannunshi tayi suka fita daga parlon da kanta ta bude mashi motar ta saka shi sannan ta fiddo key din motar a aljihunshi ta shiga driver seat tayi worming din motar tana dannna horn gateman ya bude mata kofar ta fisgi mota suka dauki hanyar.


Waka ta kunna ta can kasar tana maida volume din k'asa dan a hankali sound din wakar yake fitowa tana kadai Kai tana dan bin wakar a hankali dan tana son wakar sosai and tana son wakar mawakin daman dan yana sakin sabuwa take download dinta...duk da ita ba ma'abociyar jin waka bace ace ma game ce to ba daga baya ba a wajen tasan ita boss ce indai kan game ce.


Kallonta yayi yana cewa.


"Partner gobe kamar yanzun mun dauki hanya."


Murmushi tayi tana kanne mashi ido d'aya tace.."Yeah." Sai kuma ta dan waigo tana kallonshi tace.." Kai din na mussaman ne Abdulkadir kayi man abunda har na mutu ba zan tab'a yi mantawa dakai ba and Kai ne silar fitowa ta d'aga kazamar rayuwa..rayuwa irin ta dabbobi dan mutun mai hankali da tunani ba zai tab'a yin rayuwa irin tawa ba,dan duk wanda zai ta had'a jikinshi da mutane barkatai sai marar hankali wanda bai san ciwon kanshi ba,ban taba ji da son jin nima inason nayi aure tun bayan barina gida sai da Allah ya hadani da kai, kaine farinciki rayuwata kuma kaine hasken rayuwata ka rike wannan."


Murmushi yayi yana kamo hannunta yayi kissing din hannun a hankali yana Kiran sunanta yace.."Jiddah." D'agowa tayi tana kallon shi tace."Na'am." Furzar da iskan bakinshi yayi yana cewa.."Tabbas inasonki kuma Ina kaunarki Jiddarh ki nike son ki zama abokiyar rayuwata har *DA'IMAN ABADAN* kuma Ina murnar komawarki a wajen mahaifinki amman kuma ina jin tsoro a wani bangaren."


Dai dai bakin salon din da za'ayi mata gyaran gashi ta parka motarshi tana waigowa ta kalle shi tace.."tsoron mai kake ji.?" Langwabar da Kai yayi yana cewa.."Ina tsoron karda iyayenki su hanani ke Jiddah ko kuma karda ke kice ba zaki aureni ba cousin Broth dinki zaki aura." Dan shuru yayi sai kuma ya cigaba da cewa.."ni kuma Jiddarh zan iya mutuwa idan na rasaki, qaddarata shine sonki da Allah ya jarabeni da shi wallahi Jiddarh ban tab'a fadawa a tarkon son ko wace y'a mace a rayuwata sai a kanki and Jiddah wallahi ban san maiye so ba kuma ban san maiye zafin so ba sai a kanki Jiddah ki taimakeni karda ki gujeni ki so ni ki aureni ki rayu dani har *ABADAN*"


Shuru tayi tana kallonshi take idanuwanta suka sauya kala daga shinning din milk suka fara komawa ja,tabbas ya tuno mata da Yaya Auwal ya tuno mata da irin soyayyar da Yaya Auwal ya nuna mata kamar zaiyi hauka amman idonta ya kulle taki ta soshi duk da yanda kowa nata yaso ta soshi amman ita ta kasa, ta kama Kara da kiyashi daukar marar sani,bayan iyayenta to bata ga mai sonta kamar AK ba dan son da yake mata na gaskiya ne ba na karya ba ,ba kuma dan wani abu nata yake sonta ba,dan bata da abun da zai sota kyau ya fita haka kudi haka komai na rayuwa balle ma da ya ganta a gantale a titi amman ya ji ya gani ya dauka taya zata juya mashi baya kenan zata kasance butulu marar cika alkwari.


Furzar da iskan bakinta kawai tayi tana shafa gefen fuskarshi tace..."Beb zanfa dad'e zaka iya jira.?"D'aga mata kai yayi yana cewa.."zan iya jiranki partner Koda kuwa shekara zakiyi a ciki." Kumatunshi kawai taja tana bude marfin mota zata fita, dan rikota yayi yana bata ATM card din shi, kallonshi tayi tana cewa.."akwai kudi a hannuna kuma itama Ammie ta bani ATM card dinta yana a cikin bag."


D'aga mata kai yayi yana cewa.."I know,nasan kina da kudi amman da nawa kudin nike bukata ayi using." Har ta bude baki zatayi magana ya daura hannunshi a saman bakinshi yana gaya mata pin din murmushi kawai tayi tana ficewa daga motar tana shiga ciki.


Tana shiga ta samu waje ta zauna gaisawa tayi da mutanen wajen da yake an saba da ita a wajen dan duk gyaran da ake yi ma gashin Beauter a wajen take yin shi ,bayan layi yazo kanta aka fara yi mata sosai aka wanke kan aka gyara aka yi ma gashin style mai kyau da daukar hankali bayan angama aka gyara mata farcenta sukayi gwanin birgewa da daukar hankali.


Yanda ta barshi a cikin mota haka ta tadda shi dan ya dan jingina kanshi a jikin kujara yana bin suratul lukuman baiji isowarta ba sai dai kamshinta da ya bugar mashi hanci,bude idon yayi a hankali yana saukewa a samanta ya sakar mata murmushi maida mashi da martani tayi tana shiga.


Key tayi ma motar suka dauki hanya sai ya dan kalleta yana cewa.."sannu Partner fatan ba'a gajiyar man dake ba sosai." Hurar da iskan bakinta tayi tana cewa.."Yauwa tam ba laifi Beb,amman yau na dan ji zafin gyaran gashi ba laifi."


"Ayya Partner sannu dan biya damu St mu dan huta ko.?" Kallonshi tayi sai kuma tace.."kace zaka tuno baya?wai mai ya kaika St-sophia's cathedral Beb.?" Murmushi yayi yana sosa gefen gemunshi sai kuma ya kalleta yace.."ke mai kika anso a cikin bakar leda a St-S.?" Furzar da iskan bakinta tayi tana cewa.."Oh God Beb,ya haka da yin tambaya bayan baka bani ansar tawa tambayar ba.?"


Ido d'aya ya kashe mata yana cewa.."Uhm!kuma ina jiran ansar ba." Dariya tayi tana Kara ba motar wuta ba inda tayi ma tsinke sai a St-sophia parka motar tayi tana kure babban wajen shakatawar da kallo abubuwa da suka faru da ita mai dadi a wajen yana dawowa mata a lokacin da take jin tafi kowa ba ta biyunta,idan ta shigo a St-S ko wace yar'iska maiji da kyaunta da gashinta da kuma karuwarcinta sai ta sara mata ta bar mata fili.


Sauke ajiyar zuciya tayi tana kamo hannunshi tace.."a wajen nan ake baje dealer coken( hodar ibilis) and a wajen nan duk wata karuwa a kasar nan take baje kolin duk tsiyar da ta gama ga clubs mai dadi da cire kewa wajen nan yayi Beb kuma duk wanda kaga yazo wajen to harka ce ta kawo shi dan 99% din mutanen wajen nan yan harka ne but Kai mai ya Kawa wajen.?"


Cewa yayi.."na yarda dan zuwana wajen nan sai da nayi nadama yafi sau goma ina cikin nadamar zuwa wajen ke kuma kika bankadeni kina goge man hadda kika kasa na rasa duk wani kuzarina kin kuma tsorata ni a lokacin Partner duba da shigar da ke jikinki da kuma yanda kike sauri kinyi barna baki tsaya bada hakuri ba,ba hakurin bane a gabanki kawai dai so kike ki ganki a inda kike son zuwa nayi mamaki sosai sai kuma gakin fito da bakar leda so nike naji maiye a cikin ledar.?"


Dariyar tayi tana cewa.."coken ce kawai." Murmushi yayi yana cewa.."okay ni kuma a lokacin wani course mate dina ne da suke zaune a wannan kasar ya matsaman nazo mu gaisa dan na ce mashi mun shigo kasar ya kuma gaya nazo a St-S na samaishi ban san ya wajen yake ba sai da nazo gaisawar da bamuyi ba kenan a ranar sai dai next day."

Dariya kawai tayi sun dade a wajen suna hira suna tuna farkon haduwarsu sanann suka dauki hanya dan komawa gida.


★★★


*NIGERIA🥀*


Tun da ta kulle daki bata sake fitowa ba ga wata yunwa da ta kankarar mata ciki kamar tayi kuka haka take ji,ga tana son fitowa amman tsoro take ji karda ta fita ya riketa ya masga dan tasan halinshi ba mutunci ya cika ba yana iya cewa zai bugeta kuma bayan ta fishi gaskiya tunda shi ya fara janta ta rama.


In banda rashin son gaskiya Ina ruwanshi da ita da zai wani rungumota yana wani shafawa sai kace wata yar'iska ,dan kuma ya raina mata wayau ya kama shafeta sai yazo yace mata kwaila...haka fa yayi mata jiya ya balle mata towel ya kalleta har da kama mata nipples dinta yana wani lailayasu yana cewa baiga abunda zai rude shi ba bayan tabawa yake yana jin dadi dole tayi mashi katangar karfe da jikinta...tashi tayi tana yin tsaki ta nufa kofar fita tana cewa.


"Wallahi ba zan zauna yunwa ta kashe ni ba sai na fita..ni Ina ma ruwana da mutun kuma wallahi ya sake yace zai tab'a ni sai na cize shi idan yasan wata ai baisan wata ba Thank God Ina da hakora daman ba dan cin nama ba kadai akayo su."


Murmushin mugunta ta saki tana hasaso irin cizon da zatayi mashi mudun yace zai yi mata wani,bude kofar tayi tana cin magani ta fito a cikin parlon sai wani kicikicin take da fuska tana daurewa ta nufi dinning,duk da ta ganshi zauna yana kallo kuma yana daina waya.


Tsaki taja a hankali tana cewa.."aikin Kenan mutun bai da aiki sai daina waya yana kallon matan mutune a media." A hankali tayi maganar tana bin ta gefenshi zata wuce ji tayi an fisgota sai dai ta ganta a tsugune gabanshi ya daure fuska,duk da ta tsorota da irin fisgar da yayi mata amman sai ta hadiye tsoron tana daure fuska itama tana kallonshi,buge mata baki yayi da bayan hannunshi yana cewa.


"Yaushe na zama abokin ki.?". Banza tayi dashi sai turo baki take gaba tana kauda kanta gefe,tsawa ya buga mata yana cewa.."Hy am taking to you,am your mate.?" Again bata ce mashi komai ba kuma bata fasa cinno baki ba tana harararshi ta kasan ido tana gunguni,duk abunda take yana ankare da ita wani irin abu yaji ya tokare mashi zuciya ya tsani raini da hauka da rashin kunya a rayuwarshi ya kuma lura yanzun ba abunda ke dawainiya da yarinyar sama da rashin kunya da kuma wani taken balaga da yake Kai mata karo.


Rasa mai zai mata yayi dan shi daman can bugu baya cikin sabgarshi balle kuma ace ya doki mace,kuma ya rasa wa zai daka sai Zulaihat baya iyawa bar shi dai yayi mata hargagi amman yasan hannunshi ba zasu iya bugata a wannan matsayin da take takawa a rayuwarshi sai dai mai ba zasu tab'a zama inuwa daya ba mudun tace haka ta zabar masu su gudanar da rayuwar auren su zata sha wahalar shi ne .


Wata uwar tsawa ya buga yana cewa.."keeee." Hirgicewa tayi tana fadawa samanshi tana boye fuskarta a jikinshi,jikinta sai mazari yake tsabar tsorata har sai da ta bashi mamaki yanda yake karmar tsoro sai kace wanda taga abunda zai hallakar da ita,tsaki yaja mai tsawo yana tureta daga jikinshi tana faduwa k'asa dirsam wulla mata wata uwar harara yana cewa.


"Ki kama kanki and ki shiga hankalinki idan ba haka ba zanyi maganin wani iskancin da kika tsiro dashi zaki sha wahala ne a banza a wofi sai nayi maki abunda har ki mutu ba zaki tab'a mantawa dani ba useless."


Kara janyota yayi gabanshi yana kama kunnenta ya murde babu tausai ba tausayawa yana cigaba da cewa..wallahi tun wuri ki farka daga baccin da kike idan kuma ba haka ba kece masha wuya dan ni ba raga maki zanyi ba."


Turo baki tayi tana cire hannunshi daga kunnenta tana cewa.."to sai mai?mu zuba mu gani nida kai wa zai gaji dan wallahi nima dai-dai nike da kai dan haka wanda ya gaji shi zai daina." Murmushin gefen baki yayi yana kure dan karamin bakinta da Ido kokonto yake anya kuwa Zulaihat din da ya sani ce a da?kodai chanza ta akayi da wata marar kunya bai sani ba?Ina tsoronta yake da saurin kuka duk sun tafi anya kuwa?wai shi take kallon idonshi take ce mashi su zuba su gani?Tabb ai dole ya nuna mata true color din shi,ai tace wanda ya gaji shi zai daina ai kuwa zata sha bakar wahala a wajenshi.


Kureta yayi da Ido yana cewa.


"Haka kika ce ko?."

Murguda baki tayi tana cewa.


"Eh haka nace mu zuba mu gani wanda ya gaji shi zai daina."


Kallonta yayi yana girgiza kai yace.


"Keeee."


Dagowa tayi tana mashi kurri da Ido tace.


"Gani fa,sai dai Malan ba suna na Kee ba dan haka idan zaka iya kirana da Zulaihat to idan kuma baka iyawa is better ka bar Kiran sunan baki d'aya tunda daman babu kudinka a wajen sayan ragon da aka radaman sunan."


Bugu ya kawo mata tana kaucewa tana cewa.


"Da da yanzun ba d'aya bane Malan, wallahi wannan ne na karshe da zaka sake gigin cewa zaka kai wannan hannun naka a jikina dan ba baiwa aka kawo maka ba da zaka buga."


Bai san lokacin da ya taso yayo kanta ba,tashi tayi tana yin dinning da gudu ta wauci cooler din abinci tayi room dinta da gudu tana cewa.


"Na dai gaya maka sai a kiyaye okay."


Kaima iska bugu yayi yana yin kwafa ya kuma ya tsaki yana cewa.


"Sai nayi maganinki a gidan nan idiot."


Tana shigewa room dinta ta kulle tana jinjina a jikin kofa tana mamakin kanta yanda ta iya daurewa har ta kalli idon Dr Najeeb ta gaya mashi wannan maganar,tasan da ace za'a auna jininta to ila ya kai 300 tsabar hawan da yayi,baki d'ayanta a tsorace take tasan waye Najeeb amman ta shirya mashi ta dunga kunduga mashi bakin ciki Kenan tunda ya nace ya aure ta sai ta sashi kuka da idonshi balle ma da ta gano logonshi baya son karami ya gaya mashi magana.


Najeeb mutunen mai bala'in son girman tsiya yana son yaga ana respecting din shi yana son yaga ana tsoronshi kuma shi mutumin ne mai son yaga yana jiya mutun kamar waina(masa) a cikin tanda..ita rainin da ba zata iya dauka ba Kenan a wajenshi idan ta dauka a baya to yanzun ba zata iya dauka ba .


Ji yayi zaman parlon ya fice mashi rai kuma baya bukatar zaman cikin bedroom sai kace wata sabuwar amarya,tashi ya yi ya dauki wayarshi ya sauko k'asa tana ficewa daga part dinshi ya samu waje bakin pool ta zauna ya tunanin yanda zai gyara ma yarinyar zama...fuszar da numfashi yayi yana lumshe idonshi yayi banding a saman rest chair din da ke bakin pool din, kurema ruwan cikin pool Ido yana jin wani b'acin rai yana ratsa mashi zuciya can kuma bude baki kamar ana mashi dole yace.


"Tabbas ta rainani,rainin ma mai girma amman fine soon zan gyara maki zama soon zan sauke maki wannan haukan I promise to you I promise."


Dan d'aga kanshi yayi yana hangon Moha da Zubaida a bayan part dinsu cikin lambun da akayi masu a bayan sai guje-guje suke suna dariya,kuresu yayi da Ido sai can kuma ya dauke kanshi yana tsaki yana cewa.


"Ina za'ayi wannan abun arzikin da wancan sakarai." Mts ya ja tsaki ya tashi ya taitara kayanshi zai bar wajen yaji Moha yana cewa.


"Hi Ango."


Waigowa yayi yana kure shi da ido sai kuma ya dan dakata yana cewa.


"What."


Murmushi Moha yayi yana ida karasowa inda yake yana cewa..."Ango mijin Zulaihat ansha kamshi ya na ganka nan Kai d'aya Ina ita madam din take,ko dai jiya ba'a je mata a hankali ba.?" Ya ida maganar yana d'aga mashi girar daya,takaici ya kamashi yana wurga ma Moha harara yace.


"Wallahi kaji kunya katon banzan katon wofi baka da aiki sai unnecessary talk."


Dariya ya fashe da ita yana cewa.."yanzun daga tambayar Amarya har nayi laifi,da dazun zamu zo gidan ku ai, nace A'a ta bari sai anyi sati biyu sannan karda muzo mu takura maku kuna cikin gurzar amarci."


Harara kawai ya wulla mashi yayi gaba yana cewa..."kodai ku takura kanku ba, daga kai har ita Zubaida na lura daman a hannu kuke." Da kallo Moha ya bishi yana dariya yana cikin dariyar Zubaida ta iso tana cewa.


"Habibi har ya tafi.?"


D'aga mata kai yayi yana janyota jikinshi yana lasar gefen kunnanta ya rada mata.."Darling kin iya swimming mu shiga muyi.?" Girgiza mashi Kai tayi tana Kara lafewa jikinshi tace.


"Aa ni ban iya ba amman ita Zulaihat ta iya."


Jan hancinta yayi yana cewa."iKon Allah kamar ni da Najeeb Kenan,ni na iya amman shi bai iya ba shi tsoron ruwa yake yakan dai tsaya daga nesa ya kalla amamn bai tab'a gwada shiga ciki."


Murmushi kawai tayi tana jan gemunshi tace.."anyi masanje kenan.?" D'aga mata kai yayi yana cewa.."Yeah." Haka suka kama labari suna soyayyarsu cikin son juna da kauna.


★★


Su Beauter na isowa gida basu zauna parlo ba kowa ya wuce room din shi,tana shiga ta cire kaya ta fad'a toilet ta watsa ruwa duk da sanyin da ake a garin amman sai taji tana jin gumi na keto mata a jiki.


Saboda ba karamin yawo suka sha ba ita da AK tun 4pm suke waje amman basu dawo ba sai 10pm shima dan Ammie ta matsa masu da kira da basu da niyar dawowa a lokacin.


Tana fitowa ta zauna ta shafa cream tana zura doguwar night gown sannan ta saka hijab a saman rigar ta sauko k'asa, tana saukowa ta samu kusa Ammie ta zauna tana cewa.


"Ammie mai aka yi for dinner?"


Murmushi Ammie tayi tana cewa."ba dole kisha yunwa ba kin biye ma Son, mutumin da bai damu da yunwar cikinshi ba,haka zai kama yawo dake bai tunanin tsayawa ya sama maki abunda zaki ci sai yai tunanin duk d'aya kuke baki jin yunwa."


Murmushi kawai tayi tana chanza channel din kallo ta maida wild,Mai aiki Ammie ta kwala ma kira ta kawo mata cheap sai kuma kunnun gyada,ana kawo mata yana saukowa shima kasan ya zauna yana daura kanshi a saman cinyar Ammie yace.


"Myluv sannu da hutawa."


Shafa kanshi tayi tana cewa.


"Yauwa Luv shine kabar Babe da yunwa ko?idan Kai baka jin yunwa an gaya maka kowa irin ka ne.?"


Kallon Jidda yayi sai kuma yayi murmushi yana cewa.."ai laifinta ne da bata ce a biya wajen cin abinci ba." Yana gama fadin haka ya saka hannu ya fara cin cheaps din da aka kawo mata..sama tayi da plate din tana kallon Ammie ta turo baki tace.


"Ammie kin ganshi ko zan cinye man,bayan kuma ya gama daura laifin rashin cin abincin kan lokaci a kaina."


Dakuwa Ammie tayi mashi tana cewa.."maza matsa daga wajen nan kasan kana jin yunwar kaki tsaya a eatry kaci."


Langwabar da Kai yayi yana sunsunna Ido yace..."Wayyo Ammie please ki barni naci kadan zanci fa haba Partner ki barni nine fa Beb dinki."


Gwalo tayi mashi tana cewa.."Uhmuhmm naki da wayaun ka.bani bace mai laifin ba naji na ansa amman ba zaka ci man abinci ba kasa a kawo maka wani."


"Ayya sorry naji laifi nane ba zan kuma ba,kuma ni naki nike son ci idan kuma ba haka ba na koshi."ya ida maganar yana langwabar da kanshi gefe dariya tayi tana zura nashi daya a baki taunawa yayi yana cewa.


"Aaaaa Partner akwai dadi." Dariya tayi ta ajiye suka cigaba da ci tare ana labari a haka Dad ya dawo ya taddasu shima Ammie ta tashi da kanta ta hado mashi nashi dinner din yaci...bayan sun gama dinner da kuma fira har da kallon wildlife sanann kowa ya tashi ya tafi room din shi dan kwantawa dan karfe 11am zasu bar kasar Ukraine zuwa Nigeria..washe gari kafin 10 duk shirya suna zaune a dinning sukayi breakfast bayan sun gama Dad ya sallami yan aiki suka koma BQ suka kulle ko Ina suka tabbatar da sunyi off din wani fan da Ac da tap da komai dai sannan suka shiga mota drive ya kaisu airport ya jiyo gida,11:30 duk passenger sun gama shiga a cikin jirgi ya lula dasu sararin samaniya ya doshi hanyar kasa Nigeria kasan mai tarin addinai da kabuli iri iri kasar mai tarin albarka Noma da kuma kasuwanci Kasa daya al'umma d'aya nigeria kenan.


*Wattpad bakuyin voting why? sisters Dan Allah kuyi fallowing dina a Wattpad @Jameelarhsadiq masoyana a taimaka ayi follow ayi man books dina vote pls🥰*


*AMATULLAH DATA SERVICES*


*MTN*

500MB-140

1GB-270

2GB-540

3GB-810

4GB-1080

5GB-1350

6GB-1620

7GB-1890

8GB-2160

9GB-2430

10GB-2700


9MOBILE

500MB-150

1GB-300

2GB-600

3GB-900

4GB-1200

5GB-1500

6GB-1800

7GB-2100

8GB-2400

9GB-2700

10GB-3000


VIA✓8160508316

Jamila Bello Abubakar

Opay bank

VIA✓0777512438

Jamila Abubakar Bello

Access bank


*** for call or whatsapp

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.