Free chapter · Read without an account

ZAZZAFAR KAUNA 61-70

by Jameelarh Sadiq · DA'IMAN ABADAN ZAZZAFAR KAUNA

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺

_ZAZZAFAR KAUNA_

*~HOT LOVE AND FATE STORY~*


*BOOK THREE*


_STORY AND WRITING BY_

_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_


_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_


_Ban yarda yan audio su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! ***_


***


*61-70*


"Zulaihat." Murmushi ya saki yana girgiza kai sai kuma ya mike tsaye yana kashe komai ya shige room,wanka yayi ya kwanta yana tunanin duniya yana tunanin yanda komai ya chanza ya juye...komai ya juye ya chanza ya zaman mamaki da kuma al'ajabi har yau har gobe yana mamakin yanda ta sauya ta chanza hali yana mamakin yanda har yarinyar ta iya kallon kwayar idonshi tana gaya mashi maganar da ta ga dama ta zo bakinta.


Juyi yayi yana cewa a hankali.."yaushe kika sauya kika zama haka Zulaihat?yaushe kika koyi rashin kunya? wata irin tsana ce kike man?tabbas zaki soni kuma zaki kaunace ke da kanki zaki kawo man jikinki da kanki zaki bukace ni wannan alkwarine.


Shafa lips din shi yayi sai kuma ya tashi yaje gaban mirror yana kallon yanda lips din yayi ja,saboda taunar da yasha murmushi yayi kawai yana koma wa ya kwanta ya lublube da blanket yana tunanin duniya bacci yayi gaba shi.


*WASHE GARI*


Koda ya tashi bai wani kalli ko inda room dinta yake ba,daman yana da lecture yau 8 ganin yanda lip din shi bai karasa hucewa ba yasa ya kira captain yace yayi holding din lecture din sai 12 ya gaya ma su.


Yana zaune yana shan tea Moha ya kira shi waya dauka yayi yana cewa.."Ya dai.?" Tsaki Moha yayi yana cewa.."Yanda akayi dan rainin hankali,Kai fa matsalarka kenan." Lumshe Ido yayi yana furzar da iska ya ajiye cup din yace.."Kai ne ke da matsala wallahi daga tambayarka lafiya sai ka hau ni da masifa sai ka saka man ciwon kai ina zamana."


Yanda yake maganar a hankali kamar bai wani lafiya Moha yace.."Najeeb are you okay.?" D'aga mashi kai yayi kamar yana gabanshi yace..Yeah." girgiza kai Moha yayi yana cewa.."Sure.?"again d'aga mashi kai yayi yana cewa ."sure."


Dan shuru Moha yayi yana nazarin shi sai kuma can yace.."daman na kiraka akan komawar su Darling school banji kace komai ba har yanzun." Tsaki yayi yana cewa.."wacece kuma Darling.?" Shima Moha tsakin yayi yana cewa.."Dallah can Malan ban sani ba,ban san wulakanci fa Kai daman haka kake wallahi ba'a maganar arziki da kai,wa zan ce ma Darling duk duniyar nan ban da Matata."


Tsaki Najeeb yayi yana cewa.."Sannu tamtabara uwar aure,da anyi magana sai kace mata mata sai kace Kai d'aya ne kake da aure a duniyar nan kafa ishe ni ahtoh."


Dariya Moha ya fashe da ita yana cewa.."Taya ba zan yi maganar Matata ba,bayan ita ke sama man natsuwa sann..."Moha." Ya katse Moha yana furzar da iska dan daman kan shi yana mashi ciwo a hankali ya bude baki yayi kamar ana mashi dole yace .


"Duka yaushe akayi resume din school din da har zasu fara zuwa,and kuma naga ai bama a fara yi masu lectures din ba ko?su bari sai Monday a samu drive yana kai su."


Zaro Ido waje Moha yayi yana cewa.."wani Drive zamu ba matanmu yana dauka sai kace babu zuciya a jikinmu?kalle mana mata fah zai kama yi and har magana nasan sai sun yi ko da sau d'aya ne,ni kuma hakan ba zan laminta ba gaskiya."


Shuru Moha yayi yana cigaba da cewa.."Amman idan zaka iya kai sai ka sama ma Zulaihat drive nidai kam da kaina zan dunga daukar kayana Ina kaiwa, kuma Ina dawowa da kayana hankalina kwance haba Ina ma zan iya."

Furzar da iska yayi yana jan tsaki yace.."naji sai kayi yanda kaga ya dace,wa zaka nuna ma kishi Malan zaka wani kama cika ma mutane baki."


"Nidai iyakar gaskiya ta na fad'a ynzun dai sai monday ai zasuyi resume ko.?"


"Eh."


Yace a dakule dan har maganar ta fice mashi rai yaga Moha yana son ya nuna mashi bai san maiye so ba ko kuma yana son nuna mashi bai kishin matar shi?wani tsaki ya kuma ja yace ma Moha.


"Kowa ya ringa Kai matar shi idan sun je school sun hadu okay."daga kai Moha yayi yana cewa.."yanzun naji batu." Kashe wayar sukayi yana jan tsaki dan yaji haushin abunda Moha yayi mashi wani tsaki ya dauka yana tashi ya had'a wayoyinshi ya bar gidan.


Duk yinin yau bata fito waje ba tana cikin daki ta Kunshe kanta dan har yanzun boobs dinta basu bar yi mata zafi ba ,dan ba karamar matsa Najeeb yayi masu ba..tsaki tayi tana cewa.."Allah ya saka man nidai ba yafe ba." Agogo ta duba taga har karfe biyu na rana ya wuce,wanka ta Kara yi ta shirya cikin wasu riga da saket na atamfa ta gyara gashinta ta fito parlon


Kofar dakin shi ta wulla ma harara tana jan tsaki sannan ta wuce kitchen taliya ta girka jallof da ta zuba mata yan kan ku hanta sai tayi zobo mai yawan gaske ruwa ta dauka har create ukku ta Kai room dinta ta ajiye da su lemu sai zobo duk ta saka a freeze.


Zama tayi ta ci taliyar ta koshi ta bar plate din da tayi using da shi a parlo ko daukewa bata yi ba...ranta bata yi ba yanzun zai dawo ba dan haka ta zauna ta fara hadin donuts da cake sai cin-cin ,tana aikin tana duba lokaci dan bata bukatar ganin shi bata son ganin shi bata bukatar hakan.


Da ace akwai yanda zatayi da tayi ta bar ganin shi har abada,da akwai yanda zatayi da tayi ta raba wannan qaddarairen auren bata son auren bata son shi da ace Umma zata yi mata adalci da tayi mata magana tasa Najeeb ya tsinke igiyar wannan auren dan ita dai ba abun da auren nan zai tsinana masu daga ita har Najeeb ba.


Bata jin son shi ko kadan a zuciyarta bata jin komai a kan shi,sai ma tsantsar tsanar shi da take k'ara maimaye mata zuciya ba dare ba rana...takan rasa dalilin da yasa bata jin shi a zuciyarta tabbas tasan Najeeb mutune mai kyau ga kuma kudi ga kuma ilimin ga k'ira dan Najeeb ingarman namiji ne yana da tsawo da fadanden kirji ga kuma kwarjini da haiba.


Tsaki tayi tana cewa


"Matsalarka baka da kirki baka da tausayi kuma baka jin komai ka d'aga hannu ka bugi mace ,Kai hawayen mace basu karya maka zuciya sai ma Kara hawa da ita da suke."


Tsaki tayi tana mai cigaba da soya cin-cin din ta tace.."wanann halayen naka na rashin tausayi yasa naji bani sonka ban son ka kasance uban y'ay'ana,bamu dace da juna ba Najeeb bamu dace ba ko kadan,maiyasa idonka ya rufe baka hango rashin dacewar mu ba? maiyasa baka je ka nemo dai dai ka ba wanda ta dace kai,nima ka barni na auri dai dai ni wanda ya dace ni."


Haka ta kama masifa tana aikinta bata samu ta gama snacks din ba sai gab da mangariba,samun manyan bokitai tayi ta zuba donut din da cin cin har da cakes din ma da yake cupcakes ne tayi shiyasa.


Gyara kitchen din tayi tana fitowa da boket din ta kai daki tana kullewa tubewa tayi tana shigewa toilet ta tara ruwan zafi ta Kara gasa jikinta sannan ta fito tayi sallah zama tayi tana azkar har aka kira isha'i ta tashi tayi sallar sanann tashi ta nade sallayar sannan ta zauna saman stool ta shafe jikinta da creams masu kyau da kamshi wanda suke Kara ma jikinta kyau da glowing ,humra kawai ta murza tana hayewa saman gado ta dauko wayarta tana chating da Umma tana cin Donut din ta hankali kwance.


Bayan ya dawo daga wajen aiki ya shigo gida tsaye yayi yana kallon plate din da taci abinci ta bar shi yashe a parlo, tsaki yaja yana ida shigewa room dan ya kwaso gajiya sosai da sosai ga kuma wani Karin girma yau da ya shiga school din ya tadda anyi mashi dan dean of faculty aka bashi ba tare da yasan ma za'a bashi ba.


Da fari ya fara gardamar ansa amman ana ki bashi goyan baya dan duka staff din na faculty din kowa yana Na'am da bashi dean din dan ba ya iya ya ansa shiyasa bai dawo da wuri ba ga kuma ciwon kai...yana fitowa wanka ya fito ya dauke plate din ya maida kitchen yana daura indomie ya girka da kanshi har da markade Apple yayi Apple juice yasa wani freeze ya zuba wanda zai sha.


Da yake daman Najeeb ba daga baya ba wajen iya girki duba da zaman da yayi kano da kuma zaman da yayi a London duk shi yake masu girki shi da Moha a haka har shima Moha din ya kowa..da fari Moha bai biye mashi dan zuwa yake eatry yana samo abunda zai ce shi kuma Najeeb yana da kankami ba ko Ina yake iya cin abinci ba duk kyaun eatry kuwa ya gwanmace ya girka da kanshi.


Bayan ya gama cika cikin shi ya kwashe kayan da yayi using dasu ya shigar da su kitchen ya wanke sannan ya fito ya kalli labari wajen karfe goma na dare ya kashe kallon ya shigewarshi room din shi ,ba bacci ya kwanta ba dan baya jin bacci dauko laptop din shi yayi ya fara research yana research yana shan lemu...Dan yanzun duk wani kunci da takaicin da Zulaihat ta kunsa mashi ya nemai shi ya rasa yanzun zuciyarshi sawai take babu dacin komai a cikinta.


★★


*JIGAWA 🥀*


Weaving din hannunta tayi a saman fuskarshi tana dan hura mashi iskan bakinta tace.."Hi Beb." Firgigi haka ya kalleta yana lumshe Ido,fuskarshi dauke da murmushi yana kama hannunta yana murzawa a hankali ya kuma lumshe idonshi bai ce mata komai ba.


Durkusawa tayi a kasa tana cewa a hankali.


"Beb."


Again dagowa yayi yana kallonta can kuma ya bude baki a hankali yace.


"Na'am Partner hope kin tashi lafiya.?"


Turo baki tayi tana cewa.


"Uhmm nidai Ina ta missing din ka duk fa jiya ban saka a iso ba sai da kazo man a dreams dina kuma ko."


Ta ida maganar tana turo baki a cikin shagwaba kama bakin yayin yana cewa.

"Partner kin san mai.?"

Girgiza kai tayi tana cewa..."A'a." Murmushi yayi yana sakin bakin a hankali.."Ina tausayin randa bakin nan zai shigo hannuna dan sai na fanshe duk kwalelen da yake man." Sake turo bakin tayi tana cewa.."wayyo Allah Beb nidai gsky Beb a'a." Murmushi kawai yayi yana shafa gefen sajen shi can kuma ya ce.."Nima kina a raina Partner kin san yana yin aiki,abunka da tallaka ammam kina a raina kema kin sani lokacin da dawo har kin kwanta."


Jan hancin shi tayi tana cewa.."Amman aikin jiya yafi na kulle yawa ko.?" D'aga mata kai yayi yana cewa."kinsan Lagos naje motocina aka sauke a shekaran jiya sai costume suka zo su bani matsala haka kawai da mun fara maganar ta waya sai kawai naje na nuna masu takardu sannan suka sakar motocin kusan mota sama da 3k suka so su rike fa."


Zaro ido tayi tana cewa.


"Sama 3k." Murmushi yayi yana jan hancinta yace..."aikuwa duka kudina na kwashe nayi order din su kin san ai motoci nike saidawa."


"Hakane Allah ya Kara tsarewa Beb."


"Amin ya Allah."


Mika mashi wayarta tayi tana murmushi ansa yayi yana kallonta sai kuma yace.."Masha Allah Partner su waye wa'annan din." Ansar wayar tayi tana Kara kallon picture din tana cewa .


"My twins."


Kara anshe wayar yayi yana kare ma yaran kallon,yarane kyawkyawa Masha Allah farare tas kamar ba yan kasar nigeria ba ga gashi har saman baya, kallonta yayi yana kallon picture din sai kuma ya saki murmushi yana jin son yaran har cikin zuciyarshi da kuma tausayinsu da ya tuna waye ubansu kuma ba ta hanyar aure aka haife su ba ga dai kyau iya kyau amman basuyi dacen uba na gari ba.


"Partner Ina son su sosai,Allah yasa idan munje Gusau Mama ta bani su na dawo dasu Jigawa and Ina kika samu picture din su?ko daman can kina da su?kuma ai naga nan da girmamsu dan zasu Kai 7yrs kuma suna da 2yrs kika bar su."


Murmushi tayi tana cewa.."Nima yau na samu picture din ." "When?" yace mata, murmushi tayi tana cewa.."IG" kallon karin bayani yake mata cigaba da ce mashi tayi.


"Haka nan nayi creating din page a IG Ina yin sai nayi searching din Meenat dan nasan da User din da take Using a IG Ina yin searching aikuwa na ganta sai na shiga page din nata anan naga pictures din nasu da yawa ma har da wasu yara ma naga duk tana daurawa amman ban san su ba sune kawai na gane suma ba haka kawai na gane su ba akwai wani abu a fuskarsu wanda ta banbanta su tanan kawai nike gane Nana da Dejarh anan na gane su Nana ne."


Murmushi yayi yana cewa.."Allah sarki; Allah yayi masu albarka ya kuma rayasu ya karesu da kariyarshi " murmushi kawai tayi tana cewa Amin a hankali tana mai ajiye wayar ta kalle shi tace.


"Beb I love you."


Kamo hannunshi tayi ta cigaba da cewa.."Beb Ina sonka Ina kaunarka Beb,Kaine mafarkina Beb Kaine wanda nike fatan ya kasance mijina uban y'ay'ana har *DA'IMAN ABADAN* ,Beb Kaine komai nawa Kaine komai komai Ina nufi zuciya gangar jiki duk na mallaka maka."


Kissing din hannun yayi yana cewa.."Partner tabbas ni mai sa'a ne kuma dan baiwa ne har kullun ina mai k'ara gode ma Allah da ya bani ke a matsayin masoyiya nasan ba wayau na baine addu'a ta ce Allah ya ansa kuma Ina mai k'ara gode mashi."


Shuru yayi sai kuma ya cigaba da cewa..."Nima na mallaka maki kaina da komai nawa Partner dan farincikinki shine nawa ina fatan Allah ya tabbatar mana alkhari ya kuma saka kama albarka a rayuwar auren da zamu ya bamu zuri'a dayyaba ya kuma bamu damar ba su tarbiya dai dai gwargwadon mu."


"Amin Amin." tace tana murmushi tana mai kafe shi kallon shi sakar mashi murmushin kauna take,wani irin so da kauna take mashi ba, bata san yaushe ta kamu da son AK ba har haka ta wayi gari ta bude idonta ta tsince kanta a tarkon son AK har mamakin irin son da take mashi take...tana jin sonshi har cikin can kasan zuciyarta tana jin bata iya rayuwa babu shi a rayuwarta tana mamari da kuma fatan kasancewa da shi har *DA'IMAN ABADAN* tana fatan hakan, tana ji a ranta zata rayu da har *ABADAN* tana jin zata iya zama da shi a cikin ko wani hali,means da dadi ba dadi,ko a cikin halin kudi ko kuma talauci ta yarda taji ta gani zata zauna da shi *A HAKA* zata so shi a *A HAKA*.


hura mata iskan bakinshi yayi yana cewa. yana cewa...."HI." hura mashi iskan bakinta tayi tana cewa.."kawai Ina kallon handsome ,Ina godema Allah da ya bani saurayin kyaukyawa natsatse mai ilimi da tarbiyar Alhamdullahi Saurayina yafi na kowa."


haka suka kama soyayyar su sallah ce ta tadasu yana tashi ya kalleta yace.."hope Zaki shirya kafin na dawo,da na dawo zamu fita na nuna maki dutse kafin ki dawo da zamanta baki d'aya."


murmushi kawai tayi tana shigewa room dinta,wanka ta fara yi sai kuma tayi sallah ta zauna ta shirya cikin riga da siket na atamfa bata wani shafe shafe ba kawai cream ta shafa sai kwali da ta saka ma idonta ta kuma murza daurin kyallabinta mai kyau da daukar hankali.


sanda zata kammala shiryawa har shi AK ya gama har ya fito ya zauna zaman jiranta a parlo suna fira da su Ammie suna labarin su Nana suna yaba kyaun da Allah yayi ka yaran...bayan ta fito ta zauna ta gaida Ammie sai Koda yanda tayi kyau sosai take ita kuwa sai dai tayi murmushi tana maida kanta k'asa tana wasa da yatsen hannunta da suka sha kumshi sai wal kumshin yake yana daukar ido.


Bayan Ammie ta gama kodata suka tashi suka tafi rike da hannun juna haka suka fito har bakin mota da kanshi ya bude motar ya saka sanann ya shiga ya tadda motar direct a Galaxxy park ya fara nufa da ita.


D'aga wajen bayan sun gama zagaye wajen ya Kuma tafi da ita wani baban wajen shakatawa suka nufa ba inda bai zagaya da Beauter ba..duk wajen da yasan zata yi farinciki da nishadi sai da ya kaita sun dade sosai basu dawo gida ba sai wajen karfe goma na dare.


Nan suka dawo gida yawon da yayi da ita a dutse ya debe mata kewar Ukraine da take dan taga wajen da babu irin shi ma a Ukraine dan wani waje da ya kaita mai suna Stone castle yayi bala'in yayi mata kyau dan wajen kamar ba'a dutse ba sai ace Abuja ce ko lagos,dan ba kamaramin kyau Dutse tayi mata ba har eatry duk ya shiga da ita ta gani sun sha ice cream da su pizza shiyasa da suka dawo gida bama su kalli abinci ba dan a koshe suke.


kwanciya kawai tayi bayan tayi shirin bacci kafin baccin yayi gaba da ita sai da suka sha wayarsu ta soyayya sanann dan sun kusa kaita gida daman bari sukayi ta huta sai aje Gusau a ba su Baba hakuri akan abunda tayi dan bata kyauta ba da tabar gida akan saurayinta yaki aurenta.


★★


*ABUJA🥀*


Yau Monday yau su Zulaihat zasu yi resume a school, bayan ta gama sallar asuba tana sane da 8 gareta kuma ba wanda zai masu lecture din sai Najeeb,amman tayi kwanciyarta duk da ba bacci ta koma ba.


Kwance kawai take tana latsa waya game take hankalinta kwance sai kace bata da wata lecture dan hankalin a kwance yake ba mancewa tayi tana da lecture ba A'a kawai bata da niyar tashi ta shirya ne kan lokaci bata da shi.


Sai da ta mula ta sha iska sannan ta tashi tana duba lokaci 7:30 wani murmushi ta saki sanann ta shiga wanka hankalinta kwance ,Dan tana sane taki tashi da wuri duk da tun jiya yayi mata warning yana gaya mata ta tabbatar da ta shirya da wuri karda ta sake ta b'ata mata shi lokaci.


Ita kuma warning da yayi mata cikin Isa da gadara yasa taji bata tashi ta shirya da wurin sai ta tab'a mashi lokacin da yake gudu taga yanda zai yi da ita kulikuli zai maida ta ko kuwa gunduwa gunduwa zai da ita?.


Koda ta shiga wanka a natse take wankanta kamar yanda ta saba dan har sai da ta Kara 5mn akan yanda ta saba fitowa kullun,tana fitowa ta zauna saman stool ta fara kokarin shafa cream sai da ta gama shafa cream sannan ta kuma dauko lotion ta fara murzawa a hankali tana yin waka kasa k'asa.


Ita da ba shafa poder take tayi ba ,amman sai ta dauko poder ta hau shafawa sai da ta linde fuskarta tas da poder kuma ba karamin kyau poder din tayi mata ba,sannan ta dauko lipstick ta murzama lips din.


Wani dakeken laces ta dauko black sai daukar Ido yake dan a karance laces din zai Kai 150k a ma karance...dinki doguwar rigar akayi ma laces din ba karamin style mai kyau da daukar hankali aka zuba ma lace ba.


Abunka da farar fata tana zura lace din sai ya Kara fiddo da kyaunta sai wani walwal take tsabar kyaun da laces din yayi mata ba,ga rigar ta zauna dam a jikinta duk da ba matseta rigar tayi ba.


Amman ta fiddo mata da hips dinta sosai sai kuma boobs da suka zauna a cikin breastcup din so Masha Allah...V-shape tayi na daurin dan kwali tana yi mashi stepstep ta kuma ja dan kwali baya V din ya fita sosai gwanin bargewa.


Farin gyale ta dauko da hand bag sai ta saka sarkar gold da dan hannun da zobe sai wal suke a jikinta takalmi ta dauka ta zura marar tsini sosai,dan daman ita ba gwana bace wajen saka takalma masu tsini sosai.


Feshe jikinta da turaruka tayi masu saukin kamshi dan Zulaihat bata cika son turare masu hawan kai ba shiyasa bata ma using da su tafi saka masu saukin kamshi da zama kan zuciya.


Kallon kanta tayi a cikin mirror bata san tace..."Wooow." Ba dan ba karamin kyau tayi ba ita kanta tasan tayi kyau kyaun ma ba dan kadan ba,kallon time tayi taga 7:50 wani dadi taji ya ratsa ta tabbas tasan ta kunziga mashi ta b'ata mashi lokacin da bai son ta b'ata mashi kuma yanzun ta fara b'ata mashi lokaci da ita yake zance dan ta dunga kunziga mashi bakin ciki Kenan har sai ya gaji ya sake ta da kan shi.


Tafiya take kamar wanda take jin k'ank'amin taka k'asa haka take tafiyar ga wani karkarda jiki take kamar da gaiya haka take tafiyar...tunda ta bude kofar kamshinta ya doki hancinshi ,bai dago kanshi ba balle ya nuna yasan da fitowar ta ta,duk tarin b'ata mashi lokaci da tayi hakan yasa yayi d'aga lecture din ya maidata nine.


Surber tea yake a hankali yana kallon tv sai murmushi yake duk da ranshi a b'ace yake dan yaji haushin b'ata mashi lokaci da tayi bayan sai da ya ce mata ta shriya da wuri karda ta b'ata mashi lokaci,amman duk a banza sai tayi abunda ta saba yi tun tana gida .


Daman yasan ita ke jama Zubaida makara hakanan take cewa wai Zubaida ce to ai ga yarnune ta nuna ace tana da lecture early eight amman bata fito ba sai 10mn to 8 yaushe ta Isa cikin school din balle ta gano venue?tabbas kuwa idan har haka zatayi maganar gaskiya ba shiryawa zasuyi ba.


Dan ba tsayawa zai yi ba ta maida shi karamin mutun a idon students din shi idan ita bata san mahinmamcin karatunta ba to shi yasan mahinmamcin aikin shi dan ba a banza yakai mataki da yake ciki ba,ba kuma zai biye mata ba ta maida shi lusari ba ta maida shi unserious din lecturer a idon students din shi.

D'ago kanshi yayi yana kare mata kallo daga sama har k'asa ranshi yaji ya Kara b'aci fiye da wanda yake ciki,wannan wani irin hauka ne?show zata ko kuma gasar kyau ko wajen biki ko suna?wannan shigar da tayi ta daukar hankali sai kace ba matar aure ba,tana nufin a haka zata fita dan ta mai da shi sauna marar hankali da tunani ko kuma Shima ta maida shi mahaukaci irinta wanda bai san martaba da darajar aure irin ta ba?tsaki yayi yana buga mata tsawa yace....



*AMATULLAH DATA SERVICES*


*MTN*

500MB-140

1GB-270

2GB-540

3GB-810

4GB-1080

5GB-1350


9MOBILE

500MB-150

1GB-300

2GB-600

3GB-900

4GB-1200

5GB-1500



VIA✓8160508316

Jamila Bello Abubakar

Opay bank

VIA✓0777512438

Jamila Abubakar Bello

Access bank


*** for call or whatsapp


Share ✓

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.