Free chapter · Read without an account
8
Yana tsaye a ƙofar ɗakin sai da ya fara yin knocking jin shiru yasa ya kama handle ɗin ƙofar sannan ya tura hango Abba yayi tsaye jikin window da farar jallabiyya ajikinsa yana kare da waya a kunnensa. Jin qarar buɗe ƙofa ne yasa Abba ya ɗan waigo, zama Junaid yayi a cikin sofa ɗin ɗakin yana jiran Abba ya gama wayar da yake. Abba ne ya qaraso gabansa yana miqa masa wayar hannunsa, hannu Junaid yasa ya karɓi wayar tare da karata kunnensa, jin muryar Mamma ne yasa ya gaisheta da respect ta amsa tana tamabayarsa ya yake "Mamma naji muryarki wani iri kamar kina mura."
“Murane tun tsakar dare na fara amma zan shiga clinic yanzu shiyasa ban sha magani ba."
“Mamma baki da lafiya ki kwanta ki huta mana? Doctor Hakeem yana gari nasan zai kula da komai."
Junaid ya kalli Abba yana wani dakune fuska yana miqa masa wayar yake faɗin “Ka faɗa mata tasha magani mura take Abba." Ya ƙarasa maganar yana miqawa Abba wayar ya ciro tasa wayar dan kiran Abdul-hakeem din, kusan Abdul-hakeem ya zama kamar ɗan uwa a wajensa, duk da abokinsane tare sukayi karatu a Oxford University dake England wanda scholarship ya samu qarqashin PTDF da wannan ne har ya taka matsayin da yake a yanzu. Kasancewar Abdul-hakeem ɗin ya fito ne daga gidan tallakawa,
hakan ne yasa Junaid dikko yake kaunar Abdul-hakeem ɗin ganin karatunshi ne a gabanshi duk da Hakeem ɗin shima ba wai saboda dukiyar Junaid ɗin suke tare ba, kawai dai sunyi karatu waje ɗaya ne haka idan yaga Junaid ɗin yayi ba daidai ba yana basa shawara.
Yanzu ma saboda Junaid ɗin ne yake aiki da (dikko special hospital) Yai ta ƙiran wayar Hakeem ɗin a kashe yasha mamaki sabida Abdul-hakeem ɗin baya kashe waya dole ya hakura.
Da suka fito falo suna breakfast yana yiwa Abba bayani idan suka koma garin Katsina zai haɗa meeting da duk wanda ke karkashin(Dikko hotels) kuɗi sama da miliyan biyar sun fita, wanda ba'a san ta hanyar da suka fita ba Abba ya bashi dama akan yai binciken, shi Junaid dikko yafi zargin Manager ɗin wurin ne wanda ya kasance abokine ga Ali dikko koma dai menene sai ya gano ta inda kuɗin nan suka fita.
A hankali ta turo kofar dakin Mum, lokacin tana tsaye gaban closet ɗinta tana shirya kayan gugar da aka shigo mata dasu da safen nan ta juyo tana kallon Amaah dikko wacce tayiwa kanta masauki gefen bed ɗin ɗakin Mum dai kallonta kawai take tana kallan Mum ɗin tace “Mum zan shiga school.” Baki buɗe Mum ɗin ke kallonta "Dan zaki shiga skull sai akace ki saka hijab dama da hijab kika saba zuwa makaranta?" “To ya zanyi? Mum kin manta yadda yaya Junaid yace idan na kara karya ɗaya daga cikin rules ɗin da ya kafamin cireni a makarantama za'ayi? Kuma Abba ya yadda kina gani agabansa amma baice komai ba?”
“Ke kuma dan kina shasha sai kibi yadda yakeso shi gasa ubanki kou?” Mum ta faɗa a fusace tamkar zata kaiwa Amaah ɗin mari "Kin san yadda nakeson karatuna Mum Right? Ni bana son wani abu ya taɓa min karatuna idan na shiga school zan riqa saka mayafi, ga shinanan ma a bag ɗina." Ta faɗa tana xuge zip ɗin jakar tana nunawa Mum ɗin ɗan qaramin mayafin da ta ɗauko mai shige da kalar kayan jikinta, dan takaici sai Mum ɗin tayi shiru bata qara magana ba ta cigaba da gyaran kayanta "Please mum." Amaah ta faɗa da wani yanayi a muryarta “Ki ɗauki car key ga shinan akan mirror dressing."
“Drivern Yah Junaid yana waje yana jirana." Wani irin kallo Mum ɗin ke bin Amaah dashi yadda taga yar ta ta canza lokaci ɗaya duka saboda dokokin Junaid dikko na banza"Mum sai na dawo.” Da haka Amaah ta nufi ƙofa ta fice daga room ɗin bata jira mai Mum ɗin zata sake faɗa ba ta fito suka wuce school.
Suna zaune da Rufy kusan qarfe biyu na rana, Rufy na kallonta tana faɗin “Ya zakiyi da zuwa birthday ɗin Fu'ad dan naga wannan yayan naki zafin kansa yayi yawa." Tamkar Amaah zatayi kuka take kallan Rufy tace "Ban san yadda zanyi ba Rufy ke kin san qarfe shidda na yammah kawai muke a waje, a duk inda muke ka'idar gidanmu ne haka, ina ga kawai zan fadawa Fu'ad ya hakura bazan samu zuwa ba dan da gaske bazan iya haɗa karatuna da kowa ba Rufy, ina kaunar karatuna bazan so wani abu ya taɓamin karatuna ba, dan daga ranar da Junaid dikko yasan muna dating da Fu'ad nasan tawa ta qare."
"Kina nufin ba zaki je ba kenan? Amman kin san Fu'ad bazaiji dadi ba kou?" Rufy ta qarasa maganar da rashin jin daɗi a muryarta "Kawai ki faɗawa Mum nasan bazata hanaki ba, nasan birthday party ɗin nan iyakarsa an dade idan an kai 10, dan Allah be a gud girl Amaah."
Itadai Amaah jin Rufy kawai take dan bata gamsu ba, ganin wayarta ta soma ringing ne yasa ta fiddota cikin bag ɗinta sunan Fu'ad ke yawo a jikin screen ɗin wayar, ɗauka tayi ya faɗa mata gashi ya shigo cikin school yana mota yana jiranta, ita kuma ta faɗa masa tana zuwa "Karkije ki fusata sa kin san bayada hankali ko kaɗan Amaah" Rufy tai maganar tana kallanta, ita kanta a tsorace take da Fu'ad ɗin duk da tana yiwa Fu'ad ɗin soyayyar da bata san lokacin da ta fara ba, sai dai wani irin mugun tsoronsa da takeji, sanadinsa ko mazan ajinsu bata kulawa saboda mugun kishin Fu'ad idan kuma wani ya kulata a cikin school ɗin ko yayi mata magana a ranar tashin hankali za'ayi acikin makarantar, ko maza yaga suna kulata a social media suna liking ɗin posting ɗinta anan zai riƙa mata bala'i ya ɗora laifin akanta yace ita take kulasu.
Tun da ta fito daga hostel gabanta ke mugun faduwa, yau bata san da wacce rigimar Fu'ad yazo ba, addu'a take Allah yasa har su rabu bazai ɗaga mata hankali ba, buɗe gaban motar tayi ta zauna, gabanta babu abunda yake sai faduwa idan tana gaban Fu'ad manta kanta take, dogayen fingers ɗinta ta shiga ja, zaman shiru ya ratsa a tsakaninsu kafin Fu'ad ɗin ya riqo hannunta, tana ƙoƙarin janyewa ya zuba mata idonsa masu ƙassara ta, idan akwai abunda ta tsana acikin halayyar Fu'ad to bai wuce yawan ta ɓata da yake ba, tayi masifa har ta gaji.
"Kin gaji ne?" Ta ɗaga kai tana kallonsa sai ya dage mata gira ɗaya still dai yana riqe da hannunta "Ko muje kici abinci idan yunwa kikeji?" Girgiza kai tayi dakyar ta buɗe baki tana jin yadda muryarta ke wani harɗewa jin yadda harshenta yayi mata wani irin nauyi, a hankali ta zare hannunta cikin nasa hannunsa “Daman maganar birthday party ɗinka ne, gida baza'a barni ba Fu'ad." Ta faɗa da wani yanayi a muryarta tana ganin yadda ya zuba mata fusatattun idanunsa "Kice min Wasa kike Amaah?" Ɗaga kai ta shigayi hawaye na cika idonta "Wallahi baza'a barni ba Fu'ad kasan ka'idar gidanmu." Kallonta yake sama da kasa kafin ya lashe busassun lips ɗinsa "Daga ranar da kika ƙi attending birthday party ɗina daga ranar munyi breakup a tsakanin mu." A wani irin firgice Amaah ke kallon Fu'ad bakinta na rawa bata taɓa tunanin zai yanke hukunci kalar wannan ba “A saboda wannan zaka yanke alaqar dake tsakaninmu Fu'ad? Da gaske zaka iya rayuwa babu ni?" Ta faɗa tuni hawaye suka fara forming cikin fiskarta, samun kanta tayi da ɓalle marfin motar ta fice daga motar, lokaci ɗaya hanyar hostel ta nufa da sauri Fu'ad ya kwantar da kansa cikin seat ɗin motar yana ƙoƙarin control ɗin anger dinsa. Yana son Amaah dikko da dukkan zuciya da ruhi ta yadda baki zai iya furtawa ba, amma ya take neman ta wulakanta masa soyayya a gaban friends ɗinsa? Rai a ɓace ya tada mota a fusace yabar cikin makaranta dan gwara yaje ya nemi wani abun da zai sha ya bugar masa da wannan bakin yanayin da Amaah dikko ta bar masa lokaci ɗaya.
Ganin yadda Amaah ta faɗo dakin yasa tasan sunyi halin nasu tasan Fu'ad shine babban weakness ɗin Amaah dikko ta kuma tabbata yadda take haukan sonsa baya mata wannan kalar son, dan yana da wasu yammatan a gefe sannan kalar su Fu'ad ba irin na macce ɗaya bane, ta zubawa Amaah ido wacce ke famar zubar hawaye "To me kuma ya haɗo ku?"
"Daga kawai nace bazan je birthday ɗinsa ba wai sai dai mu rabu, ban taɓa tunanin Fu'ad zai iya faɗa min haka ba Rufy?" Amaah ta faɗa muryarta na wani irin shaking. Rufy ta taɓe baki "Kema dai kin san halinsa ba hankali ne da Fu'ad ba kuma kin san zai iya, kawai shawarar da zan baki kiyi ƙoƙari kije koda na awa ɗaya ne." kwanciya Amaah tayi akan bed ɗin Rufy tana ta tunanin inda zata fara.
#ASMY B ALIYU
#BA(Secret Relationship)
#Amaah Dikko
#Fu'ad
#Rufy