Free chapter ¡ Read without an account
3
*RABO YA RANTSE...!!*đš
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*003*
Pillow guda Éaya ya matse a saman Ćirjinshi bai rufa da komai ajikin shi ba, dama haka tsarin shi yake duk sanyi baya rufa idan yana bacci kuma baya sanya riga iya kacin shi dogon wando kaÉai, baccin shi yake cikin nutsuwa sabida yadda gajiya ta zirga zirga ta kashe masa jikin sa damma namijin duniya ne wajan gwagwar mayar rayuwa.
Ammi ta Ćarasa bedroom Éinta bata zauna ba alwala ta Éauro ta fito daga Toilet SadiĆ Yayan Aliyu, Aliyu shike bin sa yana zaune a Garin lagos yana kula da kamfanin ALIYU na lagos,Tare yake zaune da matar shi acan Aunty sakinah da yaran shi guda uku mata, yayi sallama cikin Éakin nata.
Fuskarta a sake ta amsa tana cewa.
"Kaikuma zuwan dare kayi kano kamar korarre"
SadiĆ ya shafa kai yana dariya.
"Hajiya Ammi tamu, to ki fara bani abinci naci sai muyi maganar data kawo ni"
Ammi tayi murmushi.
"Bari nai sallah tukunna sai na ji dakai"
Ta shinfiÉa darduma a nutse take sallar wadda taja lokaci mai tsayi dama Duk sun san yadda sallar Ammi take Éaukar Lokaci SadiĆ har sai da yakai ga yana gyangyaÉi a Ćasan carpet.
Muryar Ammi yaji.
"To sarkin bacci tashi mu fita daga falo sai kaci abincin"
Ta faÉa tana fita daga Éakin SadiĆ ya bita suka zube nan Ćasan carpet.
"Lah Yaya SadiĆ yaushe ka shigo bamu sani ba?"
Cewar sajeeda wadda ta buÉe Ćofar Éakinsu ta fito tana murnar ganin sadiĆ sabida shi mai barkwanci ne da sakewa ba irin Ya Aliyu ba mai tsare gida sam in ya shigo sashin su basa sake wa har sai ya fita.
BuÉe hannunshi yayi yana dariya yana cewa.
"Zo mana autar Ammi ina safnah?"
Da sauri sajeeda ta Ćarasa jikin SadiĆ ya rungumeta suna dariya Muryar Bashir Ce ta karaÉe Falon shima Dariyar yake shigowarshi kenan gidan.
"Babban yaya kaine da tsohon daran nan?"
Bashir ya faÉa yana dariya.
SadiĆ yace.
"Ina naga ta zama mai gida ya kirani Éazu naji muryar shi babu daÉi dama kullum abu a cunkushe babu fuskar far'a"
Bashir dariya ya saki sabida yasan da wa yake yana nufin Ya Aliyu.
Ammi ma dariyar tayi tana cewa.
"Ina ruwan ubana nina rasa wannan rashin far'a na wa ya Éebo"
SadiĆ yayi dariya yace.
"Ammi ke ya gado danni Ammi wani bin in kika Éaure fuska wallahi har tsoron yi miki magana nake"
Gaba Éaya Falon dariya aka saki Ammi ta Éauki Pillow ta jefawa SadiĆ Ya cafe yana dariya Safna ta fito itama Tafiya tai wajan Ya SadiĆ tana Murnar ganin shi dan shi yake iya Éaukar duk sangartar su saÉanin Aliyu da yake cin Ubansu babu sauĆi.
Ammi ce ta miĆe ta nufi kitchen ta haÉowa sadiĆ abinci yana ci ana hira har wajan Sha Éayan dare Bashir ne ya fara miĆewa yayi musu sallama sabida Gobe zasu je Abuja shida Aliyu dan duba wasu motoci da aka kawo sabbi kamfanin Aliyun na can.
Su safna kuwa anga yaya sadiĆ ai sai ma miĆe Ćafa da sukai suna ta zuba masa zance kala kala suna bashi labarin makaranta shi kuma sai jansu yake yana ta sakin far'a Ammi wani irin daÉi take ji aranta gaba Éaya Ć´aĆ´an nata kansu a haÉe yake haka suke in sunga junan su kamar su haÉiye kansu Aliyu ne kaÉai bai da sakin fuska sai dai shi Éin yafi dukkan ĆłaĆ´anta son Ć´an uwanshi Kawai miskilancin sa ne da zafin zuciyarshi yasa ba'a fahimta.
Sai da sadiĆ ya sanya su Safna suka kai Kayan abincin kitchen yasha ruwa sannan yace musu su tafi su kwanta dare yayi.
Sallama sukai masa suka nufi Éakunan kwanan su.
Falon yayi shuru daga sadiĆ sai Ammi ya gyara nutsuwar shi ya kalli Ammi sosai cikin sakewa dan Ammi bata alkunyar Éan fari da SadiĆ gaba Éaya ta sake da Ć´aĆ´anta yadda ba'a zato sabida sune sanyin idaniyarta Sune garkuwa a rayuwarta tun suna Ćananu take gwagwarmaya dasu Sabida suna Ćananu mahaifinsu ya rasu yabar mata su duka duka lokacin SadiĆ baifi shekara goma sha biyar ba Aliyu sha HuÉu dan tsiransu da sadik shekara Éaya ne Salma ce suke da Éan tazara da Aliyu na kusan shekara Biyar ita lokacin tana shekara tara Bashir shekara bakwai Safna shekara huÉu sajeeda shekara Ćaya haka Allah ya Éauki ran mijin nata yabar mata waÉannan Ćananun Ć´aĆ´a wannan tasa ta shaĆu da Ć´aĆ´an nata taja su ajikinta fiye da Ćima.
"Ammi tun safe Aliyu ya kirani a waya wai Mami ta tashi tana ta zubar da Jini haka yace sunje asibiti a gigice hankalina ne yaĆi kwanciya shine na biyo jirgin dare nazo akan wannan batu"
SadiĆ ya faÉa cike da nutsuwa yana fuskantar Ammi wadda ta bada dukkan nutsuwarta a tare dashi.
"Nima bai gaya min ba sai a wajan masu aiki naji, Amman dan shishshigi har Ć´an cikin gidanku sun cika asibitin"
SadiĆ ya kawar da abin da Ammi tace dan har ga Allah baya jin daÉin yadda Ammi take wa Ć´an uwan mahaifin nasu.
"Ammi ni ina ganin kamata yayi kawai Aliyu ya Ćara aure, Dan wannn matsalar tayi yawa"
Ammi ta watsawa SadiĆ wani kallo.
"Haka ya aiko ka waje na kenan? saĆo ya baka?"
SadiĆ ya gigice dan yasan Halin Ammi inta botsare musu.
"Wallahi Ammi ko Éaya kawai dai ni tausayi yake bani ne kinga fa tare akai mana aure dashi yanzu haka Minal shekarun ta goma a duniya kinga shima in da Allah ya bashi da tuni yana da sama da Ć´aĆ´ana"
Ammi ta dube shi.
"SadiĆ zaku ga kamar ina takurawa Babana ne akan Lamarin auren shi, Ko Éaya ni tsorona kada ya auro matar da zata rabamu dashi Na san Baya son Mami ko kaÉan tsananin biyayya ce ta sa ya aureta Ni kuma na haÉa shi da Mami ne sabida Duk tsiya mahaifinmu Éaya da Mahaifiyarta Kaga Mami tamu ce bamu da matsala da ita Kuma auren su zai Ćara Ćarfin zumuncin mu da mahaifiyarta"
SadiĆ ya sunkuyar da kanshi a Ćasa Duk wannan fa ba Masalaha bace A zuciyar shi yake faÉin haka duba da yadda Ammi take Takura Aliyu akan abubuwa da dama ko lokacin auren su ma shi direct daya kawo sakina Ammi bata musa ba Amman shi Aliyu daya kawo wata Najuwa wadda sukai B.U.K tare da ita yace ita zai aura Fafur Ammi ta rufe ido tace bata yarda ya auri Najuwa ba, Haka yace yana son wata Ć´ar nan galadanci itama Ammi taĆi daga haka yay fushi yace shi yama fasa auren kwata kwata katsam Ammi taje gidan Yayarta dake fagge ta kawo masa babbar Ć´arta Mami tace ala dole sai ya aureta Duk da ba wani sonta yake ba amman haka ya auri yarinyar.
"Ammi Wannan fa duk ba Mafita bace, Kowa yana son yayi aure dan ya haihu shima ya sami Éansa na kanshi tunda Mami tana da matsala wajan Éaukar ciki yakamata abar shi ya Ćara aure wataĆil Allah ya bashi rabon a jikin wata"
Ammi ta sunkuyar da kanta Ćasa kafin tace.
"Mami yarinya ce mai ladabi ka duba dukkan Mu babu wanda bata ganin darajar shi, uwa uba mahaifiyarta ma mace ce mai son zumunci, bana son ya auro wadda zata tarwatsa mana gidannan sannan yadda matan nan suke da wankakken ido ba kowacce bace zata aure shi dan Allah wata ma dan dukiyar shi zata aure shi, Muyi addu'a Allah ya bawa mami dan ita ce tamu Kome zata zama agidannan tamu ce ba bare ba"
SadiĆ yabi Ammi da kallo ya kasa fahimtar maganar Ammi kawai yadai fahimci Ammi tana tsoron kada Aliyu ya auro matar da yake sone tazo ta rabasu shiyasa ta aura masa mami sabida tasan baya son mami biyayyace yake mata sannan kuma bayan haka tasan kome mami zata zama ta tace tunda Ć´ar yayarta ce.
Sallama yayi mata ya nufi masaukin shi ya kwanta Cike da tunani kala kala sai da Asubahi suka haÉu da Aliyu a masallaci.
Cikin barkwancin da yake jan Ya sadiĆ dashi dan in kana son kaga Aliyu ya sake sosai to SadiĆ na wajen sabida shaĆuwar da sukai da SadiĆ Aliyu baya Ćoye wa SadiĆ komai nashi kamar yadda Shima sadiĆ Éin baya Éoye masa tun asali basu da abokai awaje su biyu ne aminan juna wanda ko Ammi bata san wani sirrin nasu ba.
"Ah Babban yaya kaine agidan namu?"
Aliyu ya faÉa yana murmushi.
SadiĆ yace.
"Ba dole ka ganni ba tunda kai min waya hankalina bai kwanta ba wallahi yaya mamin?"
Aliyu yayi murmushin gefen baki haka suka jera zuwa sashin Ammi a falo sukai zaman shan baĆin shayi har wajan takwas suna tare da sadiĆ Aliyu ya miĆe yaje yay wanka ya dawo cikin shirin tafiya Bashir ya fito Musa ne ya kaisu airport Bayan sunyi sallama da SadiĆ wanda zai je ya dubo mami sai ya wuce lagos shima..........
AUTA ***