Free chapter · Read without an account
Page 4
*SHU'UMAR MASARAUTA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.
*Masarautar Zazzau ta sauya zuwa Masarautar Huddam.*
SHAFI NA HUƊU
Wani irin kallo Fulani Umaima ta watsa wa Bamaguje, shi ma ya yi ƙuri yana kallon ta da daƙwa-daƙwan idanunsa jawur kamar sabon barkono, ta katse shirun da ce wa. "Ka na nufin Baiwata Maimuna ce Takawa zai kusance ta? A saboda wanne dalili kuma ba ka ganin tamkar na miƙa kai a kan hanyar da asirina zai tonu?" Bamaguje ya girgiza mata kai. "Matuƙar ina numfashi kullin za ki kasance lulluɓe cikin bargon rufin asirin da babu wani mai numfashi ya isa ya yaye miki shi, dalilin da ya sa na ce ki aiwatar da wannan aikin matuƙar Sarki Abdul'aziz ya kusanci Maimuna ta gaba da baya za ki sha gaban kowa. Wane na mai faɗa a ji a cikin ƙasar Huddam?"
"Sarki Abdul-aziz." Umaima ta amsa masa.
"Ki saurare ni da kyau. Ba akwai wata baƙar rijiya mai baƙin murfi a turakar Mai martaba ba wacce suke kallon juna ita da tsohon shuri mai tsohon tarihi?" Umaima ta gyaɗa masa kai. "Mai martaba na gama mu'amala da ita ki tabbatar kin ɗebi najasar jikinsu sai ki shafa ta akan saman murfin take murfin zai buɗe, ki zura Maimuna cikin rijiya ki koma gefe su zuba ido zai koma ya rufe kamar yadda yake da farko. Maruƙar kika aiwatar da komai yadda ya kamata za ki sha gaban duk wata hallita da ke cikin ƙasar Huddam, kwarjini da tsoronki zai mamaye zuƙatansu ta yadda kina faɗar maganar za a aiwatar miki. Sai dai akwai sharaɗi duk ranar da aka fito da Maimuna daga cikin wannan rijiyar wannan asirin ya karye, amma kuma abu ne da kamar wuya gurguwa da auren nesa domin yanzu haka rabon da a buɗe rijiyar yau kimanin shekara ɗari da hamsin kenan." Umaima ta sauke ajiyar zuciya. "
Duk wannan ban ɗauke shi abu mai wahala ba, shin ya za a yi na wuce da Maimuna har turakar Takawa ba tare da wani ya gan ni ba, kuma na sa shi ya yi mu'amala da ita?"
"Umaima a kullin kin fi son a yi miki ciki a yi miki goyo, za ki saka hannu ki ƙwaƙwalo ƙwayar idonta ki jefa a cikin wancen sihirtaccan ruwan, yadda za ta makance ta daina gani haka za ki ci karenki babu babbaka ba tare da wani ya kawo miki cikas ba. Kuma daga wannan lokacin hatta uwar da ta kawo ta duniya ba za ta sake tambayarta ba, yadda matacce ke mantawa da rayuwar baya haka duk wanda ya santa zai manta da shafinta." Umaima ta yi masa jinjina da hannu. "Na gode sosai Bamaguje faɗi kowanne irin tukwici kake buƙata." Bamaguje ya saki murmushi, "Ki je Umaima zan fanshi aikina a cikin masarautarku." Umaima na gama sauraronsa ta miƙe ta ƙarasa gaban Maimuna da ke zaune kamar butum-butumi, ƙaramar wuƙa ta saka ta ƙwaƙwalo idanunta ta watsa cikin wani koren ruwa kamar yadda Bamaguje ya faɗa mata. Ta koma gabansa ta yi masa sallama da faɗin duk abin da ake ciki za ta sake ziyartarsa. Ta rungume littafin a jikinta hannunta ɗaya riƙe da Maimuna na biye da ita kamar raƙumi da akala. Duk wani abu da take gudanarwa na siddabaru sai da ta gudanar babu jimawa sai ga su a cikin ɗakinta a tsaye. Kai tsaye uwar ɗakinta ta wuce da Maimanuna ta buɗe wani akwatinta na ƙarfe da take ajiyar abubuwanta na sirri ta ajiye littafin, sannan ta koma falo ta zauna tana ta zuba murmushi don gani take ƙiris ya rage haƙonta ya kai ga cim ma ruwa.
Bayan fitar Fulani Umaima daga sashen Fulani babba, Jakadiya da kanta ta ɗan tattara wurin. Ta leƙa madafa tana tambayar su Baraka ko ruwan zafin ya tafasa, a daidai lokacin ta same su sun fara kwashe ruwan. Bayan an zuba aka kai banɗakin Fulani babba, shi kuma jaririn Jakadiya ta zauna ta sulle shi tas. Sai da gari ya waye tangararan sanna Jakadiya ta ɗauki Yarima ta wuce da shi turakar Mai martaba. Farinciki fal fuskarsa ya karɓi jaririn yana jin son shi a zuciyarsa don ya jima yana mafarkin samu ɗa namiji. Huɗuba ya yi masa da suna Abubakar sannan ya ba wa Jakadiya ta mayar da shi, Jakadiya na mayar da shi Fulani ta rungume jaririnta suka kwanta bacci. Jakadiya da kanta ta sanar da Baiwa Zainaba a kan duk wanda ya zo mata barka a ce masa tana hutawa. Sai a lokacin ita ma Jakadiya ta wuce can sashensu na Bayi ta samu ta yada haƙarƙarinta don ta yi ramuwar baccin daren da ba ta yi ba.
Fulani Umaima tun da ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye don burinta bai wuce ta ga ta aiwatar da abin da Bamaguje ya umarce ta ba. A yadda ta jingine Baiwa Maimuna a haka ta same ta a bayan ƙofa, bayan ta idar da sallar asuba ta riƙo hannun Maimuna tana faɗin, "Wuce mu je sashen Mai martaba." Babu musu Maimuna ta fara tafiya tana biye da Fulani. Duk da ta aminta ɗari bisa ɗari da hatsabibancin Bamaguje, a lokacin da ta fita harabar da Bayi suke kai wa da kawowa sai da gabanta ya faɗi, jikinta ya ɗauki rawa tana tsoron kada su ankara da Maimuna wacce take tafe da ƙwaƙwulallun idanuwa asirinta ya tonu. Amma ga mamakinta duk wurin da ta gifta sai dai Bayi su riƙa zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa. Cike da izza, ɗagawa, faɗin rai da alfari Fulani Umaima ta ci gaba da taku ɗaiɗai tana kallonsu a banzace ba tare da ta amsa ba ta wuce. Ba su yi mamaki ba domin ba wannan ne karo na farko da ta saba yi musu haka, wulaƙanci da tozarta na ƙasa da ita kamar a jininta yake don haka kowannensu ya sake shiga taitayinsa. Lokacin da ta isa sashen Sarki Abdul-aziz shiru ta ji wanda hakan ya alamta mata baya nan, can gefen gadon sa ta zaunar da Maimuna sannan ta fara jiyo motsi daga jikin windonsa. Tana leƙawa ta hango Takawa a cikin lambun shaƙatawarsa zaune a kujera a gefensa ɗawisu ne da ƙananan tsuntsaye suke ta kaiwa da kawowa. Har ta nufi ƙofar da za ta sada ta da lambun ta tuna ba ta ɗauko sihirtaccen turarenta, da sauri ta fice don kar Sarki Abdul'aziz ya dawo ba tare da ta kammala shirinta ba. Da fitarta ba a ɗauki minti biyar ba Sarki Abdul'aziz ya taso kai tsaye ya nufo cikin turakarsa, gabansa ya ji ya yanke ya faɗi ƙwarin gwiwar da ke tattare da shi ta tarwatse. A razane yake bin kan gadonsa da kallo, sakamakon ƙwaɗayin idanunsa da suka hango masa abin da ba yi tsammani ba.
Fulani Umaima na zuwa ta wuce ta zaro akwatinta da ke ƙarƙashin gado, ta buɗe ta da niyyar ɗaukon turaren amma zuciyarta ta fara kwaɗaita mata son sanin abin da yake ƙunshe a cikin littafin da Bamaguje ya damƙa mata. Ta sake tuna matuƙar ta rasa karatunsa a wannan ranar sai dai ta bari zuwa wani makon mai zuwa. Ɗaukan littafin ta yi ta koma gefen gado ta zauna, za ta sa hannu ta buɗe ta tashi da sauri ta je ta saka kuba a ƙofarta ta rufe sannan ta sake komawa ta buɗe shafin farko daga cikin littafin, ƙwayar idonta ta sauka a kan jimlar farko da aka yi rubutunta da ajami.
BAN SAN KAINA BA
Da mamaki ta sake furtawa da bakinta, "Ban san kaina ba! Me hakan yake nufi?" Duk harsashen kwanyarta ta gagara lalubo mata amsar tambayarta don haka ta sake mayar da kanta ta ci gaba da karatun.
Ban san mizanin tubalin ginin da ya dace na jingine rayuwata ba, balle na san kaina da abin da rayuwata ta ƙunsa, abu ɗaya na sani ban san kaina ba. Ban san wace ce ni ba domin kuwa wata hallita ce ke sarrafa zuciya da ruhin gangar jikina. Ban san asalina ba ballantana na binciki dangina, hasali ma kusan duk wani Bawa ko Baiwa da za ka gani a cikin masararutar Kabbab kusan kowa akwai tushe da asalin yankin da ya fito, nawa asalin ya yi rauni dalilin da ya sa ko a cikin Bayi na kasance ƙasƙantacciyar baiwa. Wacce take fuskantar tsangwama, kyara da duk wani nau'in cin zarafi saboda babu mutum ɗaya da zan kalla da sunan dangina. Har ya zame mana jiki a kowacce rana idan rana ta take muna karkasuwa ɓangare-ɓangare domin gudanar da ayyuka daban-daban. Ni da su Dije muna ɓangaren bangon yamma muna sirfen geron da za a yi wa su Fulani fura da shi, a lokacin rana ta take sosai daga bayana na ji an saka hannu an dafa kafaɗata wacce na ke kai taɓarya ina yin surfe da ita. A hankali na waiga ƙwayar idona ta sauka a kansa, cike da fargaba da sake waro idanuna haɗe da tattaɓa gefen fuskarsa don tabbatar da ƙwayar idona ba yaudarata take ba. Tun ban fi shekara biyar a duniya ba nake mafarkinsa ba dare babu rana, domin a duk lokacin da zan yada haƙarƙarina gangar jikina ta samu hutu bacci ya yi awon gaba da ni sai na yi mafarki da wannan hallitar. "Ki taya ni murna da farinciki domin na samu 'yancina, na zama kamar kowa mai ɗauke da rayuwar gashin kai. Na yi miki alƙawarin sai na karɓo miki karagarki, a kullin Kaka na sake jadadda mini mu tabbatar da mun ba wa alƙawari muhimmanci kuma mun cika shi, wannan zai dawo da ƙima da martabar ahalinmu, wacce zuri'armu ta tarwatse silar cin amanar da aka yi mana." Kalamansa suka mamaye masarrafar jina, mamakina ya ninku dalilin ganin ƙwalla na zuba daga ƙwayar idonsa.
"Ke Hidaya kar ki raina wa kanki hankali, kina nufin mu za mu ci gaba da surfen kina can kina kalle-kalle banza da wofi? Wallahi kika bari muka surfe na cikin turmin nan sai dai ki surfe wannan kwano ukun ke kaɗai." Kalaman Safare suka katse ni, da sauri na waiga wurinsu kowaccensu ta sakar mini harara kamar idanunsu zai faɗo. A zuciyata na furta. "Ko dai su Safare ba sa ganin wannan saurayin?" Daga bayana na ji ya sake taɓo ni. "Ba za su taɓa ganina ba, saboda wasu muhimman abubuwa. Ke ma akwai dalilin da ya sa kike rayuwa a cikin Masarautar nan har kike mu'amala da su. Ki ci gaba da haƙuri kin san idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi." Yana gama furta mini waɗannan kalaman na neme shi na rasa. Wata irin azaba ta riyarci ƙafata sakamakon wurgo mini taɓarya da su Safare suka yi, na sunkuya cike da azaba ina matsa ƙafata. "Ga shi nan ki yi ki surfa ragowar, kuma kin fi kowa sanin halin Uwar tuwo matuƙar aka gama surfen aka bar ki a baya za ki yaba wa aya zaƙinta."
Idanuwana na kai kan ƙwaryar da ke cike da gero har kusan kwano uku, tausayin irin wuyar sirfen da zan sha ya mamaye ni. Dole ƙanwar na ƙi, na sunkuya na ɗauko taɓarya kafin na ɗago na ji saukar bulala a tsakiyar bayana, azaba ta sa na wurgar da taɓaryar ina ihu haɗe da soshe-soshe. Ragowar mutanen da ke wurin babu wanda ya motsa ballentana na saka ran wani daga cikinsu zai kawo mini ɗauki, sai da Uwar tuwo ta gaji da dukana don kanta sannan ta nuna ni da murtukekiyar dorina.
"Ki yi gaggawar ƙarasa surfen gabanki idan ba haka ba wallahi sai na sa Balele ya kai ki ɗakin duhu, shegiyar yarinya da idanu kamar na ƙwanƙwamai." Tun ba ta ƙarasa zagina ba na suri taɓaryar da a tsaye ta kusan tsayina, jiki na karkarwa na fara daka cike da tashin hankali. Ganin haka ya sa Uwar tuwo ta yi gaba tana buga wa sauran Bayin da ke tsaitsaye tsawa, da tafiyarta babu jimawa waɗansu zaratan samari biyu suka kewaye ni.
"Shugaba wannan ba aikinki ba ne." Mamaki ya lulluɓe ni domin ko a mafarki ban taɓa cin karo da su ba, haka kuma suturun jikinsu bai yi kama da kayanmu na bayi ba. Na sake mamakin kalamansu da suke kirana da shugaba. Tsaye na yi ina bin bayan Uwar tuwo da kallo samakon har lokacin ina hango ta sai da ta ɗan yi nisa da ni, takaicin dukan da ta yi mini ya mamaye ni na fara ayyana da ina da hali sai na karɓi doriyar hannunta na zane ta ita ma ta ji irin abin da muke ji. Ihun da na ji Uwar tuwo na yi ne ya dawo da ni hayyacina, na kai ƙwayar idona wurin cikin mamaki nake bin ta da kallo. Kamar yadda na ayyana haka Uwar tuwo ke tsalle tana ihu, hatta ni da nake nesa da ita haka na riƙa jiyo sautin saukar dukan da ake yi mata.Ta jima cikin wannan halin sannan ta faɗa gefe ɗaya tana sauke ajiyar zuciya, kamar wacce aka ce na waiga ina juyawa wurin turmin na yi tozali da abin da ya daskarar da ni. Gabaɗaya geron da ke wurin an surfe shi an dake mini tas, tsoro ya mamaye ni da ganin wannan lamarin. Duk da ba sabon abu bane a wurina na ji kalamai daga cikin zuciya, amma a wannan karon na razana, "Kada ki tsoro ta Shugaba domin firgici ba hali ko ɗabi'ar ahalinku ba ne." Jin haka ya ƙara mini ƙwarin gwiwa na ɗauki ƙatuwar ƙwaryar na ɗora ta a kaina da ƙyar, kafin na ƙarasa wurin da Uwar tuwo ke kwance tuni Bayi suka taimaka mata aka kai ta can ɓangarenmu na Bayi. Kallo ɗaya za ka yi wa Bayin da ke wurin ka fahimci kowa ya sha jinin jikinsa, don babu hayani tsit wurin ya yi kamar an yi mutuwa.
Kamar kullin idan kowannenmu ya dawo daga sashen da yake yi wa hidima, mukan taru a sashenmu na Bayi. Zaune muke gabaɗaya a tsakar gida, wasu daga cikinmu na zaune kusa da yayyansu suna wasa. Waɗanda suke da ƙanƙarta shekaru kamar nawa da ba su wuce sha uku ba suna kwance a jikin iyayensu, idanuwana suka ciko da ƙwalla sakamakon ganin ni kaɗai ce wari ɗaya ba ni da makusanci. Ko da ba ni da iyaye ya kamata wasu su tausaya mini su ƙaunace ni kamar yadda na ga wasu Bayin da aka samo marasa iyaye ake kula da su, me ya sa na kasance mai baƙin jini kowa ba ya ƙaunata?" Ba zato daga gefen kunnuwana na ji an furta mini.
"Ke kike da kowa Hidaya! Kada ki karaya domin lokacin na nan da za ki tabbatar da haka." Abin ka da mai shirin kuka an jefe shi da kashi awaki nan take hawaye ya fara kai-kawo a ƙwayar idona. Jiki a sanyaye na miƙa zuwa gaban Jakadiya na tsugunna, da mamaki gabaɗaya suka juyo suna kallona. Ban damu da irin ƙalubalen da zan fuskanta ba, babban burina bai wuce ni ma na san wace ce ba.
"Lafiya kika zo kika saka ni a gaba kamar tsohuwar mayya?" Gabana na dakan lugude na tattaro kalaman bakina da na guntso na fesa mata. "Don Allah Jakadiya su waye iyayena?" Kamar haɗin baki haka na ji sun tuntsire da dariya, sai da suka yi mai isar su sannan Jakadiya ta nuna wurin da Uwar Bayi ke zaune. "Akwai tarin bayanai dangane da samuwarki, ki tafi wurin Uwar Bayi za ta warware miki zare da abawa." Cike da ƙwarin gwiwa na miƙe cikin sassarfa na isa gaban Uwar Bayi, na baje tagwayen kunnuwana ina sauraron makoma da tushena.
Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta kai hannu ta rufe shafin littafin ba don ta gaji da karatun wannan hargitsattsan labarin mai cike da rikitar da kwanyar mai karatu ba. Mayar da littafin ta yi cikin akwatinta sannan ta ɗauko turaren da take amfani da shi a duk lokacin da za su yi wata mu'amala da Mai martaba. A cikinta ta soke shi sannan ta rufe ɗakinta ta fice kai tsaye ta wuce sashen sarki Abdul'aziz, haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa ba tare da ta san dalili. Babban tashin hankalinta bai wuce kada laƙanin jikin Takawa ya wargaza mata shiryayyan shirin ta a kan Maimuna ba.
_Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚
***.