Free chapter · Read without an account

Page 6

by Ameera Adam · SHU'UMAR MASARAUTA 1

*SHU'UMAR MASARAUTA*



    ©AMEERA ADAM


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.


 SHAFI NA SHIDA


  Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta zauna a gefen gado, wani irin gumi ya fara tsattsafo mata.


 "Binciken da nake kan yi dangane da abin da kike ɗauke da shi a cikin cikinki, na shafe tsawon kwanaki ina bincike har yau na gagara sanin mene ne a ciki. Kullin duhu nake mai ɗauke da rashin alkairi, duhu ne mai ɗauke da tururi da ke ƙone duk wani makusancinsa. Ba ke kaɗai ba ni kaina ina da burin sanin me za ki haifa domin amfanar gobena. Ina buƙatar Magaji a halwar tsafina Umaima."


 A razane ta ɗago tana kallonsa, "Ban gane kalamanka ba Bamaguje, me ye alaƙar abin da yake cikina da gadon halwar tsafinka?" Bamaguje ya saki murmushi. "Wannan sirrintaccan sirri ne tsakanina da mahaifiyarki, ba alaƙar abin cikinki ya kamata ki tamabaya ba. Amma mu jirayi lokacin kin san ko ba daɗe ko ba jima akwai lokacin da ya za ta ɗakin ƙanwa."


 Sallamar Baiwa Salame ta katse Fulani Umaima daga duniyar taunanin abin da suka tattauna da Boka Bamaguje. Ba ta amsa mata ba don haka Baiwar ta koma, Fulani Umaima ta miƙe ta ci gaba da kaiwa da kawowa damuwa cunkushe a zuciyarta. Kamar wacce aka tsokara haka ta miƙe ta ƙarasa ta ɗauko akwatin sirrinta, ta ɗauko littafin da Bamaguje ya bata. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe shafin da ta tsaya da karatu.

  

Na jima a tsugunne gaban Uwar Bayi ina tsammanin kalamanta har sai da na fara yanke ƙauna da samun abin da nake buƙata, ba zato na ji muryarta a tsakiyar kaina.


 "Hidaya labarinki cike yake da almara, al'ajabi da ban mamaki. A tsammanina ni ce mace ta farko da na fara tozali da ke a cikin masarautar nan, ban sani ba ke 'yar cikinta ce ko akasin haka. Abu ɗaya na sani watarana na tafi isar da saƙon Fulani Hauwa na gan ki tsaye a jikin bishiyar kukar da ke bayan ɗakunan Bayi kina rusa kuka, gudun kada na yi latti a aiken da aka yi mini ya sa sai da na kai na dawo har lokacin ba ki daina kuka ba. Da yake a ranar an shigo da sababbin Bayi sai na yi tsammanin 'yar ɗaya daga cikinsu ce yawo ya kawo ta nan take kuka ta gaza gane hanya wurin mahaifiyarta. Sai na riƙe miki hannu muka wuce sashen Bayi na ƙaraci cigiya babu wanda yace 'yarsa ce, to da yake a cikin Bayin da aka kawo akwai wasu mata biyu da suka rasu sai na yi tsammanin mahaifiyarki na ɗaya daga cikinsu. Amma daga baya sai na ga 'yan uwansu suna cewa sam ba tare da su aka kawo ki ba, wannan dalilin ya sa kika ci gaba da zama a sashen Bayi ba tare da iyaye ba."


 Kalama Uwar Bayi suka zo ƙarshe a daidai lokacin da ni kuma bakin ƙomar idaniyata ta ɓalle, sai da na yi kukana mai isata na dube ta. "Haka zan ƙare rayuwata ba tare da sanin makomata ba."


 Uwar Bayi ta wara hannuwa. "Abin da na sani kaɗai na sanar da ke, idan Allah ya sa akwai rabo sai ki gansu ko a nan gaba ne." Yau ita ce rana ta farko da na ji daddaɗan kalamai daga bakin wani daga cikin Bayin da nake mu'amala da su, don haka na ƙirƙiri murmushin da bai kai zuci ba na furta. "Shi kenan ina godiya Uwar Bayi da wannan bayanin naki." Babu wanda ya sake tanka mini haka na tashi jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da wuƙa na koma mazaunina na farko na zauna ina jin zuciyata babu daɗi. Ina jin su suka ci gaba da hirarsu sai dai ko kaɗan ba na fuskantar koda kalma ɗaya, zuciyata ta yi nisan kiwo a fannin tunani da na gagara janyo ta balle ta gane in da hirarsu ta dosa.


 Wani farin tsoho mai ɗauke da farin gemu na gani yana tunkaro ni, tsananin kammanin da muke yi da shi ya sa na tsaya cak ina kallonsa. Tun da na zo duniya ban taɓa ganin mai kamceceniya da ni ba, ban yi tsammanin ya kusance ni ba don haka na ji hannuwansa a cikin nawa. 


"Kada ki damu da sai kin san wace ce ke, kina da kowa kuma wannan masarautarki ce gadonki ce halak malak, sai dai ina mai ta'ajibin sanar da ke har duniya ta tashi ba za ki ga mahaifiyarki ba. Ni ne mahaifinki! Ni ne mahafinki!! Ni ne mahaifinki!!!"


 Firgigit na farka daga mafarkin da nake yi, na juya ina kallon yadda mutane ke baccinsu hankali kwance. Mamaki ya kama ni, cikin damuwa na furta.


 "Ya aka yi ka zama mahaifina? Kuma me ya sa kuka guje ni." Kamar alamara na ji an furta mini.


 "Ba mu guje ki ba, mun kawo ki karagarki ne don ki karɓi abarki."


 Waige-waige na fara yi don ganin mai tanka mini a cikin tsohon daren nan, har na yunƙura zan tashi sai na ji tsoro ya mamaye ni, ba shiri na koma na zauna bacci ya ƙaurace mini. A lokacin da bacci ya fara fisga ta na ji Uwar bayi tana tashinmu cikin hargowa da masifa kamar yadda ta saba duk asubar fari.


  A haka na ci gaba da gudanar da rayuwa cikin rashin daɗi, rashin 'yanci da ƙangin bauta. Mu Bayi ba mu da wani gata ba musan ci mai kyau da sha mai kyau ba, ana cikin haka watarana saƙo ya iso gare mu ana san Uwar bayi ta sake zaɓen Bayi ta kai sashen Fulani Hauwa kulu, haka kawai na ji gabana yana tsananin faɗuwa. Aka saka mu muka yi layi cikin tsautsayi ƙaddara ta yarfo mini hannunta, Uwar Bayi ta zaɓa har da ni a cikin mutane ukun da Fulani Hauwa take buƙatar ƙari.Tun da nake rayuwa a cikin Masarautar ban taɓa shiga sashen Fulani ba, hasali ma ban taɓa tozali da ita ba, sakamakon rashin imanin da nake jin ana faɗa game da ita. Wannan ta sa nake takatsantsan a kan abin da zai sa na kai kaina sashenta. Tun da muka dumfari hanyar sashen Fulani nake jin jikina yana yi mini wani irin zafi, hayaniya na fara ji sama-sama a kaina ga wani kiɗan tambura da nake ji yana tashi a tsakiyar kunnuwana. Sai dai yadda na lura ni kaɗai nake jin waɗannan baƙin al'amuran da ke yi wa duniyana dirar mikiya.


Take gumi ya fara keto mini sakamakon yadda nake jin zafin na ratsani kamar wacca aka tsire a tukubar tsire. A babban ƙofar rumfar (Falo) Fulani Hauwa na coge, sakamakon yadda nake jin ana fisgata. Hayaniyar da nake ji ta fara rikiɗa zuwa muryar da nake jin tamkar na taɓa sanin mamallakiyar muryar. 


"Barka da zuwa Sarauniya." 

Na ji an furta. Waige na fara yi amma ban ga kowa ba, na riƙa jin busar sarewa a tsakar kaina ba tare da na ga masu yi mini ba. Ina nan tsaye na ji Uwar Bayi na faɗin.


 "Ku yi hanzari kada ku fusata Fulani kuke tafe laƙai-laƙai kamar marasa laka a jiki." Da sauri na ci gaba da tafiya har muka ƙarasa babban rufar Fulani da ta ƙayatu da kayan alatu kala-kala. Kaina na ji ya yi girma wata irin ƙasaita, isa da tsantsar izzar mulki na ratsa ni, da ƙyar nake taku cikin ƙasaita. Uwar Bayi da sauran Bayin da muka taho tare suka tsaya cak a bakin wata mashinfiɗa wacce bayi suke tsayawa idan sun shiga wurin Fulani Hauwa kulu. Ban kalle su ba na zarce kan ƙasaitacciyar karagar da ke cikin falon, na zauna ina kallon su Uwar Bayi ɗaiɗai. Da zamana na ji wani abu ɗau! Yana zagaye ƙoƙon kaina. Uwar Bayi kusan mutuwar tsaye ta yi ganin ɗanyan aikin da na aikata, bakinta na rawa ta furta mini.


 "Hidaya...hankalinki ɗaya kuwa? Kin san a fadar wacce kike?" 


"Ya kamata ki gyara linzamin harshenki, idan ba haka ba sai na sa an datse shi nan take. Wannan fadata ce..." Ashar ɗin da Fulani Hauwa kulu ta saki ya katse kalamaina, na dube ta cikin tsadaddiyar shigarta ina ƙare mata kallo.


 "Uban waye ya halatta wa wannan ƙasƙantaciyyar zama a karagata?" Cikin isa da ƙasaita na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, kamar ba zan amsa ba na ɗago ina kallonta a wulaƙance. "Wannan karagar iyaye da kakannina ce don haka ki gyara kalamanki."


 Na lura da razani a saman fuskarta, ɗan yatsanta na rawa ta nuna ni. "Ta tabbata ke ce Hidaya ko?" Na jingina da jikin kujerar na furta. "Ba tsammani ba ne ni ce Gimbiya Hidaya." Wata gwauruwar ajiyar zuciya na ji ta sauke. "Tabbas da alama tarihi zai kuma maimaita kansa. 


"Tarihi tuni ya sake maimaita kansa tun da gani na wanzu a gabanki." 


 Fulani Umaima ta rufe littafin tana jin kanta na sarawa don a kullin labarin Hidaya ƙara hargitsa kwanyarta yake. Ta wurga shi cikin akwatinta tana sakin tsaki a fili don ba ta jin za ta sake ci gaba da karanta wannan rikitaccan labarin.


  Komawar su Yaya Halima Masarautarsu da kwana ɗaya labari ya dawo wa Fulani Babba na sabuwar lalurar da ta afka wa Yaya Halima na kurumcewa da makanta, hankalin Fulani Babba ba ƙaramim tashi ya yi ba. Da yake jego take yi babu damar ta tafi dubiya haka ta zauna ta ci kukanta a cikin ɗaki, ta sake ayyanawa zuciyarta ko da wasa ba za ta sanarwa da mahaifiyarta halin da take ciki ba don kar damuwa ta yi mata yawa.


 BAYAN SHEKARA GOMA


   Tafe suke a cikin wani baƙin ƙasurgumin daji mai matuƙar hatsarin gaske, su kansu sukan yi takatsantsan wurin shiga irin waɗannan dajijjikan sakamakon miyagun hallitu da iskokin da ke cikinsa.


 "Mai gado wai ni kam kin taho mini da baƙar bakata?" Umaru ya faɗa yana sake leƙen wani koren maciji da ke saƙale da wata koriyar bishiya. "A'a Malam tsakani da Allah ni kam na manta ka san sai da na ce idan za mu fito ka tuna mini." Da sauri ya ciro wata ƙanƙanuwar kwari da baka daga cikin ƙugunsa, bai cika harbi da ita ba don haka ya so Mai gado ta taho mata da farar bakar wurinta. Ya kalli macijin haɗe da matsa wata laya da ke saƙale a wuyansa, ya sakar wa macijin harbi nan take ya tsire shi wani koren ruwa mai kauri ya fara fita daga jikinsa. Yana shirin miƙa hannu ya ciro kibiyar daga can gefensu suka fara jiyo numfarfashi, Mai gado da sauri ta fara matsawa don tabbatar da zarginta.


 "Wash wayyo! Ku taimaka mini, ku kawo mini ɗauki tsafi zai taimake ku. Tsafi zai shiga lamarinku, ku taimaka mini kada na mutu idan na mutu tsafi zai yi fushi da ku." Gaban Mai gado ya faɗi ganin wata matashiyar mace mai tsohon ciki tsugunne babu kaya a jikinta, ƙugunta ne kaɗai ɗaure da ganye sai saman ƙirjinta. Kanta da wani irin cukurkuɗaɗɗan gashi ya zubo har ƙirjinta.


 "Malam zo ka ga." 


"Kada ki taɓa komai Mai gado, har yanzu ba ki gama sanin sharrin daji ba. Wannan ba kamar sauran dajijjika ba ne, ki yi takatsantsan." Yana ƙarasawa idanunsa suka yi tozali da matar, ta galabaita da alama naƙuda take duba da yadda jikinta ya ɓaci kace-kace. Mai gado ji ta yi ba za ta iya daurewa ba don haka ta ƙarasa ta ruƙo ta tana faɗin. 


"Baiwar Allah me ya kawo ki naƙuda cikin dokar dajin nan?" Wani irin nishi suka ji ta yi cikin galabaita da fita hayyaci tana faɗin. 


"Tsafi, tsafi ka dafa mini. Abin bauta ka tserar da jinina ko ɗon ta gagara magautana, tsafi ka taimaka mini." Rufe bakinta babu jimawa suka ji ta ƙwalla ƙara nan take ta haifo jaririyar 'yarta mai tsananin kama da ita. Mai gado na shirin taɓa jaririyar da sauri matar ta dakatar da ita, ta hanyar ture hannunta tana girgiza mata kai.


 "Zuri'ar RUMZU daban take da sauran al'umma, idan muka haihu tashin farko jinin wata al'umma ba ta isa ta taɓa mana 'ya'ya ba har sai mun gama da 'ya'yanmu ake taɓa mana su. Idan ba haka ba yanzu za ki mutu, abin bauta zai hallaka ki." Mai gado ta ɗan zaro idanu cikin tsananin mamaki. Umaru da ya juya bayansa ya jinjina kai yana taɓe baki.


 Hannu ta sa a ƙugunta ta ciro wata ƙaramar baƙar aska ta yanke wa jaririyar cibiya, ta sa wata siririyar fata ta ɗaure cibiyar tamau. Hannunta ta saka ta lakuto jinin da ke fita daga ƙasanta ta shafa a saman goshin jaririyar lokaci ɗaya jaririyar ta tsanyare da wani irin matsanancin kuka, jinin da ta lakata mata a goshi ya shiga wata irin tafarfasa a kan goshin jaririyar. Wani irin baƙin jini ya fara zuba daga cikin hancin jaririyar, kunnuwanta da ƙasanta. Mai gado tana tsaye tana kallon abin da matar take yi cikin al'ajabi da tsananin mamaki har sai da tsoro ya fara kamata. Ganin jinin ya zarce ƙa'ida ya sa matar ta saka bakinta ta zuƙo shi sannan ta fesar a gefe, take ciyawar wurin ta ƙone ƙurmus. Ta jima tana zuƙe jinin jikin jaririyar tana ɗiban jinin gabanta tana zubawa a goshinta, idan ya tafasa sai ya shige jikin jaririyar.


Sai da matar ta gama ta ɗago ta dubi Mai gado cikin karyewar zuciyata tana faɗin, "Ban san ku su waye ba, amma na tabbata daga yanayinku ku masu karamci ne kuma tsafi zai shiga lamuranku ya dafa muku..."


 Da sauri Umaru ya waigo ya katse ta. "Baiwar Allah mu ba mu dogara da tsafi da sihiri ba, mun dai dogara da Ubangijin sammai da ƙassai." Jinjina kai ta yi tana murmushi ta furta.


 "Koma da wa kuka dogara ban damu da na sani ba, zan bar muku amanar 'yata domin na san dangina ba za su bar ni ba mutuwa zan yi, don na hangi tsinin mashin tsafin da Mahaifina ya wurgo min, idan ban damƙa muku ita ba tabbas har ita za su hallaka mu. Ba a nan doron ƙasa ba, ko ƙarƙashin ƙasa na nutse matuƙar ina numfashin na tabbata zuri'ata ta Rumzu ba za su bar ni ba." A firgice suke kallonta. 


"Wace ce ke? Mutum ce ko aljan?" Mai gado ta wurga mata tambaya a tsorace.


"Sanin matsayin hallitata ba shi ne mafita ba, domin a yanzu ba lallai ya amfane ku da komai ba. Ga amana zan bar muku ku dubi darajar abin bautarku ku riƙe ta amana, na so a sanya mata suna HAIZAT amma dalilin mahaifinta ya nunke nawa don haka ya ce mini ya fi son a saka mata sunan JAWAHIR, ban san ma'anar sunan ba don ba ya daga cikin sunan zuri'ata. Sai dai na tabbata wannan sunan zai amfane ta zuwa nan gaba, idan ta isa zama budurwa ku ɗauke zuwa bakin kowacce irin bishiyar kuka akwai ajiyar da mahaifinta ya taɓa yi wanda ita za ta tono gadon da zai bayyanar da ita jininsa ce da hannunta. Wannan jaririyar ita za ta sanar da ku asalin wace ce ni har zuwa zuri'ata ta Rumzu, tun daga zubin hallita har zuwa tushenta. Na san dangina da bibiya, kafiya da matsanancin ruƙo duk rintsi kada ku bayyana ba kune asalin iyayenta ba matuƙar za ku shiga baƙon wuri ko al'umma, wataƙila ta iya tsira da rayuwarta daga kaidinsu." Tana gama maganar ta ɗora jaririyar a kan saman wani ƙaton gidan tururuwa, ta damƙi ƙasar gidan tururuwar tana runtse idanunta haɗe da furta waɗansu irin kalaman tsafi da su Mai gado ba su taɓa ji ba, tana gamawa ta shafa a jikin jaririyar gabaɗaya, take jinin da ke saman goshin jaririyar ya ɓace ɓat. Ta sunkuya saitin kunnen jaririyar tana yi mata raɗa, lokaci ɗaya jaririyar ta yi shiru tamkar wacce take sauraron kalaman mahaifiyarta. Wani irin jini ne ya ɓalle wa mahaifiyarta amma duk da haka cike da ƙwarin gwiwa da dakiyar zuciya ta ɗauki jaririyar ta fara takawa har zuwa bakin ramin kwarmin bishiyar kukar da ke gefenta ta ɗora jaririya a ciki, ta saka hannu ta dafa saman goshinta nan take suka ga ta fara wata irin jijjiga, idanunta suka firfito numfashinta ya ɗauke rai ya yi halinsa.


 Daga Umaru har Mai gado kusan mutuwar tsaye suka yi saboda al'ajabi don tun da suke a duniya ba su taɓa ganin makamancin irin wannan lamarin ya faru a gabansu ba. Mai gado ce ta iya motsawa ta ƙarasa ta ɗauki jaririyar da mamaki ta kalli Umaru jin jikin jaririyar ya yi wani irin sanyi kamar ƙanƙara.


 "Malam yanzu ya zamu yi da wannan gawar?" Ajiyar zuciya ya sauke yana shirin yin magana suka ga gawar matar na matsawa haɗe da nutsewa cikin bishiyar kukar da take jigine a jikinta. Cikin tsoro suka ja da baya suna kallo, kafin wani lokaci babu gawar babu alamarta ta nutsa cikin bishiyar kukar sai shatin jinin da ke manne a jikin bishiyar. 


Jiki na karkarwa Mai gado ta ajiye jaririyar a ƙasa tana ja da baya ta furta. "Mai gida Allah ya sani ba zan iya riƙon wannan abin ba, domin ba na ko tantama mahaifiyar yarinyar aljana ce ita kanta yarinyar dubi irin siddabarun da mahaifiyarta ta yi mata kafin ta mutu." Cike da gamsuwa Umaru ya ɗago zai yi mata magana, gabansa ne ya yanke ya faɗi sakamakon mugun gamon da ƙwayar idonsa ta yi. Da sauri ya ja hannun Mai gado suka faɗi can gefe haɗe da kurma ihun neman taimako.



_Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚

  ***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.