Free chapter · Read without an account
3
"Ke ce ajalinsa Jamila?" maimaita maganar take cikin zuzutawa! tare da rike bakinta tana nuna al'amarin ya girmama! Kawu Sammani ya kalleshi rai a 'bace ya ce."Ali ka dawo ko? wai shin don Allah mai yake damunka ne? mai yasa baka kaunar zaman lafiya muddin kana gari shikkenan bamu da nutsuwa, na tabbatar da cewa; laifin ka ne, domin dai Jamila ba za ta yi wannan furucin ba sai da 'kwakkwaran dalili, wai shin mai yasa kuke nema ku tona mana asiri! me yasa kuke kokarin lalata mana zumuncin mu" Cikin rashin jin dadin al'amarin ya kai 'karshen maganarsa.
Hawaye na zuba a saman fuskata na ce" Wallahi ba laifi na bane asali ma tunda ya dawo ban kula shi ba, kawai saboda nayi maganar ya tashi daga shimfid'ata shikkenan ya hau zagi na, ya ma'kure mini wuya a jikin bango tare da cire blet kamar yanda ya saba zai doke yana fadin sai ya illata mini rayuwa, shine fa Tokar ta juya maganar a kaina."
Kawu Sammani ransa ya sake 'baci! ya kalli mahaifiyarsa dake zaune tana fadin 'karya nake maganar da nayi ya ce." Tokar don Allah ki daina haddasa fitina a tsakaninsu, da Ali da Jamila duk naki ne, mai zai sanya kina goyan bayansa yana cin zarafin yarinyar nan, bana jin dadin wannan al'amarin ko kadan wallahi."
Girgiza kanta tayi da cewar" 'Karya take duk maganar da ta fada muku sharri tayi masa ita da bakinta tayi furucin itace ajalinsa."
Baba Hama mahaifiyarsa ta ce." Nima na ji da kunne na saboda haka dole hukuma ta shiga cikin al'amarin nan wallahi." Kawu Sammani ya buga mata tsawa tare da cewa" Rufe mini baki shashashar banza da wofi duk waye ya 'bata yaron idan bake ba." Shiru tayi ranta a 'bace ta bar gurin. Ya kalleshi fuskarsa a murtuke! ya ce." Ka bata hakuri a gabana ko kuma ranka ya 'baci! ba zan lamunci wannan rashin kirkin ba."
Jin furucin mahaifinsa sai hankalinsa ya tashi! hak'uri yana nufin shi zai bata hakuri? to me ya yi mata wanda har za a k'askantar dashi irin haka! lokaci guda ya burkice! 'kwayoyin idanuwansa sukayi jawur! wani abu mai nauyi ya tokare masa a wuya! yana tsaye! kamar wanda aka dasa a gurin ya gagara bin umarnin mahaifin nasa, wanda ni kuma a lokacin ji nake kamar na taka rawa saboda farinciki, gaskiya naji dadin hukuncin da Kawu Sammani ya yanke masa.
Tsawa! mai karfi ya buga masa da fadin" Ba za ka yi abinda na umarce ka ba?"
Tokar ta ce" Sammani kabi a hankali mana, wai shin da Jamila da Ali waye babba ne?"
Ya ce." Duk ba wannan maganar ba Tokar ina sane da irin rashin arzikin da yaron nan yake yi, ya addabi yarinyar nan, ya hana ta sakat! ke kuma kina daure masa gindi saboda yana siyo miki nama da kifi! ita kuwa Jamila duk hidimar da take miki ba ki duba ba, kiyi hakuri da furuci na Tokar dole ki gyara idan ba haka ba, Allah zai tuhume ki ranar lahira domin dai Jamila amana ce a hannunki."
Jikinta ne ya yi sanyi sai ta sunkuyar da kanta tana cigaba da tsotsar k'ashin hannunta!
Kallonsa ya yi a karo na uku ya ce." Ban isa ba ko?" Kansa ya girgiza yana huci! ya ce." Kiyi hakuri!" da saurin gaske ya bar gurin don har sai da ya taka mini kafa da kambos din dake 'kafasa.
Ranar kwanan farinciki nayi dalilin abinda ya faru! kuma na samu sau'ki daga gurin Tokar ban sani ba ko nasihar Kawu Sammani ce take d'awainiya da ita domin yini tayi jikinta a sanyaye sai hannunka mai sanda take yi mini akan abubuwan da suke faruwa tsakanina dashi, na ce" Tokar wallahi babu ruwana da Bahago mutu'kar bai shiga hurumi na ba, ya yi rayuwarsa nayi tawa tunda babu wanda ya isa ya kori wani a tsakaninmu."
Ta ce."Ai jini daya ba wasa bane Jamila, Ali dan uwanki ne, kuma komai abinki ya girme ki tunda ya riga ki shakar iskar duniya, saboda haka ko yaya ne ki bashi girmansa.
Dariya maganar ta bani, na bude baki kenan zanyi magana ya shigo gidan cikin shigar 'kananun kaya kamar koda yaushe rigar data matse masa jiki da wando iya gwiwa mai tarin aljihunai. f-cap a kansa kafarsa sanye da kambos mai igiyoyi sai wasu shegun sarkoki a wuyansa al'amarin nasa dai sai gyaran Allah kamar ba dan musulmai ba.
Hanci na toshe saboda na tsani warin sigari ita ce kuma a hannunsa yana busawa! babu ruwansa a gaban kowa sha yake saboda rashin tarbiya.
Ta ce" Tun safe nake cigiyarka ina ka shiga ne?" Hayakin dake bakinsa ya feso mini a fuskata! ya kuma tsira mini jajayen idanuwansa masu girman gaske! kallonta nayi raina a masifar 'bace! Ta ce." Yi hakuri akan wanda ki ke yi." Ta kalleshi da fadin." Mai yasa kake neman tashin hankali ne?" shiru ya yi mata hankalinsa gabad'aya yana kaina, tunda naga haka sai nayi niyyar barin dakin, na san ba alheri ne ya shigo dashi ba, tashi nayi domin fita babu zato! ya sanya mini k'afarsa na fad'i a jikinsa! ya hankad'e ni na zube a kasa kafin ma na yun'kura! ya cimma ni, ya fara hauri na da takalmin kafarsa yana kaiwa fuskata duka! Tokar ta rarrafo tana rike 'kafarsa tare da fashewa da kuka! " Ali wace irin zuciya gare ka ne? na d'auka jiya akayi muku sulhu mai zai sanya kuma kazo kana dukanta."
Na ce" Tokar ki 'kyaleshi ya kashe ni mana ai d'an-daba ne d'an-ta'adda." Bakina ya kaiwa duka! da kafarsa a take kuwa jini ya fara zuba can naji turmin ha'kori na yana girgid'i! kukan kura nayi na tashi tsaye na kai hannu zan zabgawa fuskarsa mari! ya murd'e ni! bango ya matse ni ya cigaba da bugu na! kuka nake sosai ina zagin sa tare da kokarin kwace kaina. "Jama'a wai menene yake faruwa ne tun daga soro nake ji ihu! da kururuwa! Anti Hamida ce take wannan maganar lokacin da ta shigo dakin, nan taga abinda yake faruwa, salati tayi cikin tashin hankali tazo tana k'wace ni daga hannunsa da fadin." Idan ka kasheta wallahi sai munyi shari'a da kai! mara mutunci kawai!" Ya fita daga dakin yana numfarfashi! sai yanzu ya samu sassauci a zuciyarsa dalili jiya kwanan zaune ya yi in banda haya'ki babu abinda yake busawa! ya ji takaici abinda mahaifinsa ya yi masa shiyasa ya yanke shawarar ladabar da ita domin bata kai matsayin da zai 'kaskanta da kansa ba.
Rungume ta nayi sosai ina wani irin kuka! Na ce."Anti Hamida rayuwata yake nema! baya 'kaunata kullum kokarinsa ya za'ayi ya sabauta ni, bani da inda yafi nan, amma ina ganin dole zan tattara kaya na na tafi can gurin mahaifiyata domin na gaji da wannan lamari Bahago rayuwata yake nema!" cikin gurshe'ken kuka ta kai karshen maganar. Tokar ta dinga share hawaye! da alama itama abin ya girgizata, wai shin wannan wace irin k'iyayya ce yaran sukewa junansu?
Anti Hamida murya na rawa ta ce." Babu inda zakije Jamila, kamar yanda ki ka fada cewa baki da inda yafi nan hakane mune 'yan uwanki kuma gatanki dole ayi wa tufkar hanci domin ba zamu zuba ido wannan al'amari yana faruwa ba"
Tokar na fyace! hanci ta ce." Hamida anya kuwa yara nan ba jifansu akayi ba? wannan abun yana bani tsoro wallahi, kiga irin dukan da yake mata kamar wanda aka aiko shi.
Ta ce."Tokar kema fa kina da hannu a cikin faruwar wannan lamari, domin icce tun yana danye ake tankwara shi, ke kuma tun fil'azal ba kya k'aunar 'bacin ran yaron nan komai ya yi daidai ne a gurinki, ya lalace ya zama d'an iska baya jin maganar kowa ya zama baragurbi a cikinmu saboda haka ni da kaina zan shigewa yarinyar nan gaba domin a kwatar mata hakkinta kada kuma a k'ure hak'urin Kawu 'Danlami abin ya yi yawa gaskiya."
Ta ce." To dai kada ki manta da Ali da Jamila duk babu bare a cikinsu, kuma idan salsala za'a bi Ali ne makusancinki domin ke kika saki nono ki ka bashi don haka ki bi komai a hankali."
Ranta a 'bace Ta ce." Yo ai ni gwara Jamila sau dubu a gurina tunda duk rintsi tana jin maganata tana kuma jin maganar iyayenta, shi kuwa fa ai na riga na sallamashi tunda babu wanda ya isa ya fada masa ya ji."
Ta ce." Itama fa tana yi masa abubuwa marasa kyau! tana kiransa da mazinaci dan shaye-shaye d'andaba! da dai sauran kalmomin da ba su dace ba."
Cikin takaici ta ce." Ai ba 'karya tayi ba Tokar Bahago bashi da kirki duk abinda Jamila ta lissafo a kansa yana aikatawa idan hakan ke b'ata masa rai sai ya gyara!
Tokar ta kama kuka tana tana ta goge majinar da take ta tsiyayowa a dakalin hancinta. Ita dai ta tsani a jingina masa mugun abu bayan kuma ta san duk abinda aka fad'a a kansa gaskiya ne.
"Jamila ki yi hakuri kinji ko ki tashi ki shirya kayanki mu je can gidana ki huta kafin mu san ya za'ay....Kafin ta karasa maganar Tokar ta katse ta da fad'in." Hamida baki isa ba kinyi kad'an!" duk muka zuba mata ido muna kallonta.
Ta cigaba da cewa" Aure ne kawai zai raba ni da Jamila ko mutuwa ke baki isa ba saboda haka ba zataje ko'ina ba ni bana son munafurci da neman gindin zama."
Anti Hamida tayi dariya tana kallonta ta ce." To ai kisa na ga za'ayi a gabanki baki dauki mataki ba, shiyasa na yanke shawarar dauketa daga gidan, idan ya daina ganinta shikkenan sai ku sakata ku wala!"
Tsaki! mai tsayi taja ta ce." Ni dai na fada miki baki isa ba, idan kuma kina so ran mahaifinki ya 'baci akan wannan lamari shikkenan ki tafi da ita d'in."
Ta ce." Ba zan so hakan ba gani nayi lamarin yana kara tsananta shiyasa na yanke wannan hukuncin amma don Allah ku d'auki mataki akan wannan abu idan ba so akeyi yarinyar nan ta hadu da larura ba"
Ta ce." Ke dai baki isa ki shiga tsakaninsu ba duk gulma da munafurcinki don haka sahun ki a likkafa ki tashi ki tafi gidanki bana son neman guri."
Na ce."Anti Hamida yi mata shiru don Allah! kar ki sake magana, in sha Allahu cikin satin nan zan zo na kwana biyu a gidanki."
Ta ce." To godiya nake k'anwata bari na tashi na tafi dama gidan biki zan je na ce bari na shigo na gaisa da Tokar sai kuma na riski wannan tashin hankalin."
Na ce" Bikin Humaira ko ? ai tun sassafe Baba Hama ta tafi ita kuma Baba Iyami ta tafi aiki shiyasa ki ka ji gidan shiru, nima abinyi nake nema wallahi domin na gaji da zaman banza." Tana kokarin tashi tsaye Ta ce." Kada ki damu idan na dauki adashin da nake zan baki dubu goma sai kiyi shawarar sana'ar da zakiyi."
Cikin farinciki na rungume ta ina ta godiya Tokar sai ta'be bakinta take yi tana hararar mu.
Dubu biyu ta d:auko cikin jakarta ta ajiye mata a gabanta da fadin " Tokar gashin ki sayi goro." Abin mamaki! sai ta fara washe baki, tayi sauri ta dauki kudin tasa a k'arkashin fillo. Muka kalli junanmu dariya ta kufce mini da sauri na dauki hijab na fita tsakar gida ina dariya da mamakin abinda ya faru, itafa Tokar duk mai bata kudi ko wani abun duniya shine mutum a gurinta, kuma yanzu nan za'ayi magana da ita ta gaskiya amma anjima kad'an sai ta ce 'karya ne, mussaman idan kana yi mata ihsani to ba ta da gwani wanda ya fi ka.