Free chapter · Read without an account

ZAZZAFAR KAUNA 191&200

by Jameelarh Sadiq · DA'IMAN ABADAN ZAZZAFAR KAUNA

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺

    _ZAZZAFAR KAUNA_

*~HOT LOVE AND FATE STORY~*


*BOOK THREE*


_STORY AND WRITING BY_

_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_


_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_


_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! ***_


***


*191-200*


Hunging din shi tayi tight tana wani furzar mai da numfashi a saman gadon baya,a tare suka sauke ajiyar zuciya yana wani lumshe ido a hankali dan bai ga shigowarta ba sai dai yaji unexpected hug kiris ya rage bai yanke da wukar da ke hannunshi ba...zagayowa yayi da ita ta dawo gabanshi yana kureta da ido,rintse idonta tayi tana lafewa a kan kirjinshi tana dan shafawa a hankali tana cewa..."Hubby ga fa abinci can na girka maka." D'ago da kanta yayi yana murmushi yace.."Au ai nasa baki zakiyi ne." Girgiza kai tayi tana cinno baki tace."Uhm!nidai kai na girka mawa fa." Bude idonta tayi tana kamo hannunshi tana jan shi ta nufi hanya da shi,cizewa yayi yana cewa.


"Just indomie nike son ci fa ."


Marairaice fuska tayi tana cewa.."wayyo Allah yanzun Hubbyna yanzun ya kake so nayi da nawa abincin?Dan Allah karda kayi man haka,kazo kaci anjima sai nayi maka indomie din please."


Bai ce komai ba ya bita kamar wani rakumi har bakin dinning ta tsaya tana janyo kujera ta zaunar da shi,zama yayi yana kallon iKon Allah har bai san a wani irin farincikin yake ciki ba wai yau shi ne Zulaihat take taitalawa kamar wani kwai...da kanta ta zuba mashi duk abunda ta san ta girka tana ajiye mashi a gabanshi ta janyo kujera kusa da shi ta zauna.


Had'a ido sukayi ta sakar mashi murmushi tana dibar abincin a cikin spoon ta Kai shatin bakin shi tana cewa.."Yauwa Hubyna Ha." Yanda tayi maganar bai san sanda ya bude bakin ba tana sanya mashi abincin ...dadin da ya Kai mashi ziyara ne har tsakiyar brain din shi ya lumshe ido bai sani ba yana wani kad'a Kai yana mata jinjina da hannu alamu abincin yayi dadi.


Murmushi tayi tana cigaba da bashi sai da ta tabbatar da cikinshi ya cika ta kuma tsiyaya mashi pineapple juice ta bashi sai da ya sanye tas ta sa tissue ta goge mashi bakin tana cewa.


"Hubbyna ya kaji testing din abincin nawa.?"


Shafa cikinshi yayi yana cewa.


"So delicious,kin cika man cika har ya kusa fashewa,na koshi amman dadin abincin yasa na k'asa daina ci." dariya tayi tana cewa.."ko dai na dan k'ara maka Luv.?" Girgiza kai yayi yana kamo kunnenta ya ra'da mata yace.."am full,but anjima zan k'ara ci ,Allah yayi maki albarka." Lumshe Ido tayi tana sakar mashi murmushi itama ta zuba nata abincin zata fara ci..rike hannunta yayi daukota ya maido ta bisa cinyarshi ya fara bata abincin da kan shi bai bar bata abincin ba har sai da ta rike hannunshi ta koshi juice din ya bata ta shaya sanann ya goge mata bakin ta suka dawo parlo.


Kallo ya kunne masu suka cigaba da kallo suna cikin kallo wayarshi ta fara ringing murmushi yayi yana mai daukar wayar ya jingina jikin kujera ya fara cewa..."Amincin Allah ya tabbata a gareki yake tauraruwar zuciya." Wani murmushi mai tsada ya saki yana wani langwabar da murna yana cewa.."afuwan Babe kina raina ,kin san dai ban da kamarki kece rayuwata hasken idanuwana har na kosa gobe tayi nazo naga Kalbina."


Dariya ya fashe da ita yana cewa.."No wallahi ba haka bane Babe na fa ce maki Ina zuwa zan turo manya azo ayi bakin nan kawai a wuce wajen dan zuciya ba zata iya jurar rashin ki ba I swear."


Wani irin makokon bakinciki ya turnike mata zuciya bata san lokacin da ta mike tsaye ba tana nufar wajenshi ko gabanta bata gane ga hawaye da suke zuba kamar an kunna famfo...tana zuwa ta fisge wayar ta k'ara a kunne tana cewa.


"Sannu karuwa matsiyaciya mai bin mazan mutane." Dan shuru tayi bata jira taji ansar da za'a bata ba ta cigaba da cewa.."tun wuri ki fita gonar da ba taki ba ko kuma wallahi nasa ki yi nadama ta har abada,dan mijina yafi karfinki ba sa'anki bane mijina nawane ni d'aya ni Zulaihat Aminu kuma....wallahi ba wata shegiya bayan ni ni ce nan sarauniyar zuciyarshi dan haka idan ma mahauka kike tun wuri kinsan idan ya dace ki baje kayan haukanki."


Tsaki ta buga tana cigaba da cewa.."sakara shashasha wanda bata da class baki san Ina ke maki ciwo ba,in banda bada kai irin naki baki bari shi ya kiraki ke dai kullun sai ke zaki kirashi kin ga hakan ma ya nunun baki da wani matsayi a wajen shi,da ace kina da matsayi a zuciyarshi to kullun shi zai dunga Kiranki ba ke ba wawiya sakarai kin dai ji kunya...ba kunya ki wani kama barin jiki a gaban namiji dan ki samu shiga to nan dai ba'a samu wajen zama ba sai a bi wani sarkin sakarai kawai idiot marar aji da kanmu Kai."


Mtsss ta buga tsaki tana yarda wayar k'asa tana take ta,kuka ta rushe da shi tana take wayar bata damu da tsadar wayar ba dan latest iphone ce ,haka ta kama takata har sai tayi mata watsawatsa.


Sannan ta bar mashi parlorn tana wucewa room dinta tana kuka..da kallo kawai ya bita dan bai tab'a tunanin tana da zuciya irin haka ba,har tsoro tsoro sai da ta bashi bayan ta shige room ta banko kofar bamb da karfi har sai da ya rintse idonshi yana saukewa kan wayarshi da tayi ma pieces ... murmushi kawai ya saki yana d'aga hannunshi sama hawayen farinciki na zubowa a saman fuskarshi yana cewa.


"Alhamdullahi Allah na gode maka da nuna man wanann ranar mai tsada..tabbas wannan mai tsadar gaskece ban tab'a tunanin wannan ranar zata zo man ba Alhmdulh Allah Alhmdulh Allah na gode maka."


Share hawayen yayi yana daukar wayar ya fice gidan, yana fitowa compound yaga Moha tsaye ya rike waya yana kallonshi murmushi ya sakar ma Moha yana cewa..."Ashe dai kana da dubara kala kala Moha.?" Kallonshi Moha yayi sai kuma ya fashe da dariya yana cewa.."Najeeb yau dai nasha zagi,yarinyar ko ta bari nayi magana ma,Ashe haka take da fad'a.?" Dariya kawai Najeeb yake yana cewa.."Ayya Kalbi ko.?" Sai ya kara rushewa da dariya sauke ajiyar zuciya Moha yayi yana cewa.."gaskiya mata a kiyaye su basu da sauki indai akan kishi ne,baka ga wayar rike a hannuna ba?ai ni har yanzun na kasa yarda Zulaihat ce tayi wannan wankin babban bargon ba."


Murmushi kawai yayi yana cewa.."inason wasan nan yana sani farinciki sosai Moha" b'ata fuska Moha yayi yana cewa.."kaga Malan ai wasan ya isa haka tun da ka gane tana sonka sai komai ya wuce ko?a kuma bude sabon babin amarci."


Murmushi yayi yana cewa.."ba yanzun ba sai naji dalilin fasaman waya da tayi ai dan bata fasa banza ba and gobe ma sai na kunna ta dan gayu zan dauka nace zan tafi zance."... hararar wasa Moha yayi mashi yana cewa.."haba Kai kuwa bawan Allah karda ka zak'e mana,karda ka daura ma baiwar Allah hawan jini mana Najeeb Kai daman ba daga baya wajen cucata wallahi."


Dariya yayi yana cewa.."lokacin da taci ubana ka na Ina.?" Shima Moha dariya yayi yana cewa.."nidai na gaya maka gaskiya idan kuma kak'i ji sai na koma bayanta na bata plan." Harararshi yayi yana cewa.."idan ka fasa kaji ko Moha,ko dai baka ji abunda nace ba?cewa nayi fa fasa man wayana tayi."


"Naji mana wace wayar a ciki ta fasa.?"


"Iphone din fa."


Tsaki Moha yayi yana cewa.."ai da sauki tun da ba sumsung dinka ce ta fasa ba dan ma iphone duka baka kashe 60k wajen saka mata screen,inace screen ne ta fasa ba wani ba.?" 


Kallonshi Najeeb yayi yana cewa..."sannu banking,60k din ce duka?okay tun da duka ce ai sai ka biya ni daman ai Kai ka jaman har ta fasa wayar Malan."


Wani kallon Moha yayi mashi yana cewa.."Ashe kuwa zaka dad'e baka gyara waya ba, c'mon Malan idan zaka fiddo kudi ka fiddo ka gyara waya idan kuma kudin basu fidduwa shikenan ai daman ba ita d'aya gare ka ba okay."


Murmushi kawai yayi baice komai ba ya tafiyarshi shi gidanshi,yana shiga ya kashe Komai ya shigewarshi room din shi hankalinshi kwance...ta dad'e tana kuka sai da tayi kukanta mai isarta sanann ta hakura dan taji kanta ya dan fara ciwo kadan kadan, tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka tayi shirin bacci tana jin Ina ma ace gobe Monday da ba abunda zai hanata cima Baby mutunci iya mutunci.


Amman ko yanzun ai bata makara ba tabbas idan har suka shiga school zata yi mata warning mai tsauri ma zata gaya mata ta fita daga harkar mijinta,dan mijinta ba sa'an ta bane kuma mijinta nata ne ita d'aya...zata fidda kunyarta da take ji tayi mata wulakancin da duk duniya ba'a tab'a yi mata irin shi ba,tunda ita bata san kawaici ba duk kawaicin da take mata ta lura a banza to tun da bata san a kauda mata kai ba, zata ta fito mata a mutun ta nuna mata true color din ta tun da haka ta zab'a.


Bayan ta gama shirin ta ta kwanta zuciyarta tana mata zafi,wato bai damu da damuwarta ba kenan?ko a jikinshi ko a kwalar rigarshi kenan?kwafa tayi tana jan bargo tace.."sai na koya maka hankali kaima soon,Wanda ko nan gaba aka kawo maka wata mace aka ce ka kalla ba zaka kalleta ba,ni taka ce Kai d'aya kuma Kai nawa ne ni d'aya wallahi ba wata yarinyar da ta Isa ta shiga tsakanina da Kai,yanda ka koya man sonka ba tare da na fargaba ba haka zaka zauna da ni kuwa ba zaka hadani da ko wace wawiya ba."


Addu'a tayi tana shafawa ta kwanta ta dad'e tana juyejuye kafin bacci yayi awon gaba da ita... karfe hudun dare ta tashi tayi sallah tana kaima Allah kukanta,tana rokan Allah da ya cire ma Najeeb duk wani son yarinya ya k'ara mashi sonta ya sa yaji ba zai iya rayuwa da kowa wace ba sai ita and yasa yaji zai iya rayuwa da ita duk rintsi duk wuya har *ABADAN* ,ta kuma roki Allah ya kauda duk wata fitina da zata shigo masu a gidansu ta riko Allah abubuwa da yawa.


Dan yanzun ta daura d'amarar zaman aure da shi yanzun ta shirya daukar duk wani kalubale da zai bullo mata, yanzun tana jin zata iya yin komai akan shi indai har zai sashi farinciki...ta yarda shi so ba ruwanshi da girman Kai ko kuma miskilanci ajiye su akeyi a gefe ka kula da mijinka ka bashi kula ka taraiyyashi ka nuna mashi *ZAZZAFAR KAUNA* Wanda zata tsaya mashi a zuci Wanda ko fita yayi har ya dawo da tunaninka a ranshi yana kuma sakin murmushi.


Taji zata iya yin duk abunda zai saka Najeeb a farinciki a shirye take ta saukar akan shi..a shirye take tayi mashi duk abunda zata samun fada a zuciyarshi ta shirya ta shirya dan ta yarda *SHI SO NUFIN ALLAH NE* kuma ba ruwanshi da kyau ko dukiya balle kuma wani abu wai jin Kai, masoyi ba'ayi mashi jin kai kulawa kawai yake bukata,bata tashi daga kan darduma ba har sai da aka kira sallar asuba sannan ta tashi tayi sallah ta fara azkar din safe.


Bayan ta gama azkar ta fito parlo lokacin har 6:30 tayi tana fitowa ta tadda shi zaune parlo yana kallon news,a hankali take takawa har ta isa wajenshi ta baya tayi hunging din shi tana sakar mashi hotkiss a pick tana ra'da mashi..."GUD MORNING HUBBYNA" a kunne,baisan lokacin da ya maidota saman cinyarshi ba yana had'a bakinsu waje d'aya ya fara tsotsa ba..ya dad'e yana tsotsar bakinta sannan ya ciro yana kissing din lips dinta a hankali yace.


"Morning too Myluv how was ur night.?"


Murmushi kawai ta sakar mashi tana k'ara kissing din shi kamar tana ra'da tace.."Alhamdullahi sai dai I missing you,bari naje nayi ma mijina breakfast gaya man maikake so na girka maka.?"


Kureta kawai yayi da ido yana kallo can kuma ya ja kumatunta yace.."Na bar maki zabi Myluv komai kika dafa mana zan ci Baby." Murmushi tayi tana sauka daga saman cinyarshi tace.."okay bari naje naga masoyi." Kiss tayi mashi tana barin wajen da kallo ya bita sai murmushi yake.


Maida kallonshi yayi kan tv sai murmushi yake dan yanzun ya fara gane abunda ake fadi sosai a news din...kamatunshi kuwa sai shafasu yake yana wani lumshe ido sai kace wani sabon kamu..(ko da yake ai sabon kamun ne a soyayya ko🤣? Nidai ba ruwana inayi Ina shan coffee ☕).


Natsuwa tayi sosai ta girka mashi indomie da kwai dan ta lura yana son indomie din..bayan ta gama ta soya mashi wata Indomie din da kwai again ta had'a tea din ta mai shegen kamshi da dadin dandano..bayan ta gama ta fito ta jera masu Breakfast din a dining ta dawo gabanshi tana cewa.


"Oga ko a kawo breakfast din anan?naga kamar kana enjoying din kallon."


Murmushi ya sakar mata yana kamota ya zaunar da ita yana shinshinar kamshinta yace.


"Duk yanda kikayi Madam ai kece Ogar."


Dariya kawai tayi tana tashi taje ta dauki breakfast din ta zauna ta fara bashi indomie din..sai da ta bashi ya koshi sannan shima ya bata taci ta koshi ta kwashe kayan ta maida a kitchen tana dawowa ta dan zauna,ganin da gaske yana son labarin kuma ita bata wani gane inda aka dosa sai kawai ta tashi zata je room dinta .


Har ta tashi ya janyota jikinshi yana kissing dinta yace mata..."Ina zaki ki barni nan Myluv.?" Dan cizon kunnanshi tayi kadan tana cewa.."bani some minute Hubbyna yanzun zan dawo."...Dan kad'a Kai yayi sai kuma ya turo baki kamar wani karamin yaro yana cewa.."karfa ki dad'e please Baby idan ba haka ba kallon fice man zai yi a rai." Itama shagwabewa tayi tana wani narke fuska tana cewa.."I promise yanzun zan dawo Babe." Shafa kanta yayi yana cewa.."okay take care love." D'aga mashi kai kawai tayi ta wuce room din ta da kallo ya bita sai da ta shige room dinta sanann ya sauke ajiyar zuciya yana maida kallonshi akan tv din.


Koda ta shiga room dinta wanka ta shiga tayo ta fito ta shirya cikin wata halfgown mai kyau da daukar hankali bayan ta gama shiryawa sai ta dauki wayarta tana kiran Umma.


Sun dade suna waya da Umma sai shagwaba take ma Umma tana cewa tayi missing dinta ita dai ta kusa zuwa gida.. Umma na hanata tana cewa ta dai yi hakuri ba yanzun ba tun da dai ai suna cikin koshin lafiya ai Alhamdullahi itama ai tana lafiya dan haka ta hutar dasu ba sai sunzo ba.


Bayan sun gama maganar sai kuma Umma ta tambayeta fatan suna zuwa gaida iyayen mijinsu nan tace suna zuwa sosai ma,haka danginsu ka suna zuwa sun dade sosai bayan sun gama waya da Umma ta kira Zubaida suka dan yi labari ta kashe wayarta ta Kara gyara kwaliyarta ta fito parlon.


Tun da ta fito kamshinta ya sanar da shi da fitowar tata, murmushi ya saki yana tashi tsaye ya bude mata hannu,shigewa tayi jikinshi tana sakin murmushi tight yayi hunging din ta yana kissing din ta sun dade a haka sanann ya fiddo ta daga jikinshi yana kare mata kallo yace.


"Kinyi kyau sosai Myluv."


K'ara sakar mata wani kiss din yayi yana wani lumshe Ido, kissing din shi tayi tana wani juyawa a gabanshi tace.." naji sosai Hubby.?" Lumshe ido yayi yana cewa.."tsarki ya tabba ga Allah wanda ya hallito wanann hallitar." Dafe zuciya kawai yayi yana wani hura mata kiss.


Dariya ta kama yi tana juyawa a gabanshi sai wata irin tafiya take tana mashi yanga ,shi kuwa ya saki baki da hanci sai kallonta yake yana bayawa sun dad'e a haka sanann ya daukota ya zaunar da ita kusa shi sai wani lalubarta yake suna kallo suna labari a hankali a hankali sai murmushi suke gwanin burgewa.


Sun dad'e a haka sai da lokacin sallah yayi sannan suka tashi suka shiga room din dan yin sallah,wanka yayi yana shirin massalaci sai da ya lek'a room din ta tsaye ya taddata bakin mirror tana gyara fuskarta.


Ta baya ya rungumota yana sakar mata kiss yace.."na tafi sallah sai na dawo." Murmushi tayi tana shafa sajenshi tace.."Allah ya tsare man kai ya kuma dawo man da Kai cikin aminci da koshin lafiya Mijina." 


Hancinta yaja yana cewa.."Amin Babyna take care." D'aga mashi kai tayi tana weaving din shi ya fita da kallo ta bishi har sai da ya fita sannan ta cigaba da abunda take...bayan ta gama sallah ta fita ta fad'a kitchen ta girka masu abinci mai sauki dan tuwo take son girka masu da dare.


Tasan yana son tuwon masara da kuma miyar danyar kubewa,a bakin Yaya Seemarh take ji da yake duk zuwan da zatayi sai ta gaya mata abunda Najeeb din yake so...duk da a lokacin jinta kawai take ba dan tana fahimtatarta ba kuma ba dan zata dauka ba.


Dan a lokacin ita ko ganinshi ba son yi take ba,har mamaki take ashe dai ta rike maganganu ma,har da magunguna duk tana kawo mata sai dai ta boye dan bata ga amfanin su ba.. bayan ta gama sallah taje ta girka masu dambun couscous tayi masu da yaji kayan lambu sanann ta koma ta sake saka kaya tana fitowa.


Tana fitowa yana shigowa da gudu taje ta rungume shi tana manna kanta a wuyanshi ta sakar mashi kiss tana cewa.."welcome back my Hubby "Kara hug dinta yayi yana K'arasa daukarta ya bai aje ta ko Ina ba sai saman three seater yana dariya sun dad'e a haka sanann ta ja shi har dinning tayi serving din shi bayan sun gama cin abincin suka fita compound.


Sosai suka zagaya bayan gidan sai labarin soyayya suke a bakin pool sukayi leading suka zauna baki sai labari kawai suke sai da la'asar tayi suka tashi har parlo ya kawota sannan ya juya dan tafiya yayi sallah.


Bayan ta gama sallar ta shiga kitchen dan fara hidimar daura tuwon daren da take da niyar yi mashi,sosai ta natsu ta fara aikin tuwon sai da ta shafe awa d'aya da rabi sanann ta fito daga kitchen din lokacin ta gama kammala komai har da tamarin juice kuwa da ta had'a mashi maidadin dandano da kamshi .


Murmushi tayi tana kallon Room dinta ganin alamu sun nuna yana ciki,tasan yanzun dai Shirin sallah yake dan mangariba tayi tana shiga tayi wanka tayi sallah,zaunawa tayi tana azkar bata tashi ba har sai da aka kira sallar isha'i sannan ta tashi tayi sallah ta fara shiryawa.


Bayan ta gama shiryawa cikin minisiket da riga iyakar cibiyarta sannan ta gyara gashinta yayi kyau ya kwanta yayi lub gwanin burgewa kuwa.. kitchen taje ta dauko cup ta had'a wani magani da Madara ta sha da dai wasu magunguna kawai dai ta sha kawai tana fitowa parlo dan ganin ya dawo daga sallar tana fitowa ta tsaya tayi turus tana kallonshi..gayu yaci ya shirya cikin wata arniyar shadda fara ba kamaramin kyau yayi ba sai zuba kamshi yake sai kace wani ango kallonshi tayi tana dan murmushi tace.


"Sai Ina Hubby.?"


Agogo ya kalla yana sakar mata murmushi sai kuma yayi kissing din goshinta yace..."zani zance ko Baby." Girgiza kai tayi tana cewa.."ban gane ba,zance kuma?wajen wa.?" Dan hunging dinta yayi yana cewa.."Kalbi mana Babyna Wanda zata auran mana." Wani irin kallo take mashi tana ja da baya baya can kuma ta je ta kulle kofar parlon tana kallonshi tace...



_Wai ta ina matsalar take ne?nace ta ina matsalar take?sunan kawai kina mace Amman kin rako mata anya kuwa?Nace anya kuwa?ba abun da kika iya sai gulma da saka ido aikin kenan😏,ke dai baki san gyaran jiki ba,baki iya girki ba,baki san iya magana mai daɗi ga Oga,baki san kwaliya ba,baki san kumshi da kitso ba balle gyaran gashi anya kuwa?yar shagwabar nan da yar yangar nan gami da kishishina duk wala baki iya ba🤔,a haka kike so karda ayi maki kishiya baki iya komai ba?komai ina nufin komai fa anya kuwa yar'uwa🌚 nidai babu ruwana idan kin gyara kanki idan baki gyara ba kanki dan haka na bude mana online class idan zamu ringa yin lecture kullum akan duk abubuwan da sillafo mana dan kawo gyara_


_Idan kina bukatar shiga wannan class din zaki yi register ne akan 2k only,Amman zanyi discount daga yau 23 zuwa farkon sabon watan nan na October in shaa Allah zaki turo 1k dan samu ki kasance a wannan group mai take MACE 'YAR KWALISA_


_Zaki biya kudinki ta wannan account number 8160508316 Jamila Bello Abubakar opay bank ko kuma 0777512438 Jamila Abubakar Bello access Bank sai kiyi man magana ta wanann NUMBER *** da shedar biyan ki_



*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi 300 1GB*


*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din 8160508316 Jamila Bello Abubakar Opay bank,*** for call or whatsapp*


Share✓

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.