Free chapter · Read without an account
Part 3
~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~
Daga Alƙalamin
_*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
_Littafin na kuɗi ne nomal ~N~ 300 ne vip ~N~ 500 ne_
Domin ƙarin bayani ku neme ni a wannan number 👇🏻
🥏+966577675904.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Shafi na uku (3)
Saurin taro ta Abdul ya yi ya kamo hannayenta kafin ta isa ƙasa, ɗaura ta ya yi akan kujera a hargitse yake kallon yadda take jan numfashi, ya kwanto da ita jikinsa ganin Mommy ta nufi ɗakinta. Ƙagara ya yi Mommy ta fito duk daƙiƙa ɗaya in ta ja numfashi ba ta iya janyowa ta shaƙa sai mimmkiwa take a jikinsa, kanta ya shiga shafawa Grandma na tsaye a kansu sai kiran Mom take ta yi sauri. Ita kuwa Mommy maganin take nema a ɗaki, amma kiɗimewar da ta yi yasa ta kasa ganinsa a gaban ta a aje, sai da ta kusan minti goma Allah ya ba ta ikon gani ta ɗauko da sauri ta fito har tana haɗawa da ɗan gudu.
Saurin amsa Abdul ya yi ya buɗe maganin ya kai bakinta gabaɗaya ta soma sakin jiki, jin maganin a bakinta ta yi ƙoƙarin shaƙa da ɗan kuzarin da ya rage mata, ƙara ɗago kanta ya yi wannan karon da kanta ta riƙe gwalbar maganin ta ƙara shaƙa numfashinta ya soma kai-kawo. Grandma da ke tsaye ta matso ta ƙara tallabo ta ta zauna ta ɗaura kanta a kan cinyarta, shi ko Abdul ya ƙara shaƙa mata maganin ta kuma shaƙa sai gata ta buɗe idanu.
Sannu suka shiga jera mata ta yi lamo a cinyar Grandma tana kallon su dan ta kasa cewa da su komai. Cikinta ta riƙe ta yunƙura ta tashi zaune jin yadda yake mata wani irin kukan yunwa, Abdul ya cire mata ɗankwali yana kallon ta cikin tausayawa ya ma kasa ce mata komai, zuciyarsa sai bugawa take da auari-sauri har sai da ya kai hannu ya dafe saitin zuciyar.
Mommy ta sauke numfashi ta ce "Ina ne yake miki ciwo yanzu?"
Girgiza kai ta yi kawai abin da Abdul ya tsana kenan a mata magana ta girgiza kai ko ta gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa, hakan yasa ya koma ya zauna sannan ya ce "Mommy na faɗa miki ki mayar da ƴar aikin nan a kawo miki mai hankali amma kin ƙiya gani kike kamar bana son ta ne, kalli ki ga ta kunna wa mutune turaren wuta a gida bayan kuma saboda Baby ba a yin hayaƙi a gidan nan. Yanzu da gida ba kowa sai dai in kwanan ta ya ƙare ta mutu." Ya faɗa yana jin kamar ya je ya rufe Laraba da duka.
Haƙuri kawai Mommy ta ba shi har ta samu Abir ta dawo nomal sannan ta zauna ita ma ta ce "Ka fiya ɗaukan zafi Babana me ye haka? Ni na ce mata take yi mana turaren wuta tun lokacin suka ɓata, zan sanar da ita ta daina yanzu." Tana gama faɗin haka ta miƙe ta shiga kitchen ɗin inda ta samu Laraba na kuka, da sauri ta isa wajan ta ta ce "Laraba lafiya kike kuka?"
Ɗago kai ta yi idanunta sun yi jajur ta ce "Hajiya don Allah karki koreni aradu na saba da ku, kuma kin ga yanzu ban san wani gida za a kaini ba in kika koreni, saboda na je wani gida inda 'yan gidan halinsu ɗaya da wannan babban ɗan naki har dukana suke in suka kira ni ban zo da wuri ba. Ki yi haƙuri mai ne na ɗaura shi ne na tafi kai abinci kafin na dawo ya yi zafi sosai, to da na dawo na zuba a wani kwanan sai na zuba wa kwanon ruwa shi ne ya cika kitchen ɗin da hayaƙi har ya je palon." Tana maganar tana ɗaura zane kafin ta kai kalma ɗaya sai ya warware, abin sai ya ba wa Mommy dariya ta murmusa ta ce "Ba komai Laraba ai ke kamar 'yata kike ba zan kore ki ba kin ji, kuma daga yau karki kunna turaren wuta a gidan nan 'yata ba ta da lafiya in ta shaƙi hayaƙi numfashinta ƙoƙarin barin jikinta yake."
"Alkur'anin Allah ko da wasa ba zan yi ba Hajiya, na gode Allah ya saka miki kina da kirki." Ta faɗa tana murmushi.
Ita ma Mommy murmishin ta yi dan ɗabi'un Laraba na birge ta, kayan abinci ta haɗa da kanta ta dubi Laraba ta ce "Idan na ce ki shirya abinci a kan denning wannan teburin na bakin ƙofa a nan za ki dinga jera abinci idan kin gama, sunan shi haka duk wanda ya ce ki kawo abinci denning to nan za ki kawo."
Ita dai Laraba sai to take cewa har Mommy ta gama magana ta fito ta rufe mata ƙofar..
Tarar ta ya yi ya amshi kayan abincin ya aje a gaban Abir ya ɗago ya kalle ta, itama kallon na shi ta yi ganin yadda duk ya kiɗime akan tashin ciwonta, kawar kai fege ya yi ya zauna sannan ya ce "Baby za ki iya cin abincin? "
Shagwaɓe fuska ta yi kamar za ta sa kuka ta ce "Yaya na ƙoshi ma da abincin, a ba ni maganin ciwon jiki na sha." Ta faɗa ba wai dan ba ta jin wuyar ba, ciwon jikin nata ne ya rinjayi yunwar shi ya sa ta ji duk ko'ina na jikinta ciwo yake.
"A a sai dai na kaiki Asibiti da na gama cin abinci, in kuma mu tafi in na dawo sai na ci to?" Ya faɗa yana zuba mata idanuwansa masu ƙara masa ƙwarjini.
Jin wani irin zogi da ƙafarta take yi yasa ta ɓare baki kamar wata yarinya ta saki kuka ta ce "Ni ka tashi ka kaini in mun dawo sai ka ci."
Babu muso ya miƙe tare da cewa "Oya tashi muje kar ki kafa min kuka da Magaribar nan."
Ganin fita za su yi Mommy ta tsayar da su ta haɗo mata tea ta ce ta sha kafin su tafi, tana turo baki ta amshi tea ɗin ta soma sha tana yatsine fuska kamar tana cin sabulu sai hawaye take ita ala dole an matsa mata sai ta sha.
Grandma ta kawar da kai ta ce "Ni Hauwa'u ban taɓa ganin sangartacciya irin wannan mai jiki a bushen ba, tashi ku tafi karki tara mana jama'a."
Tashi ta yi tana mitar Grandma tana ce mata mai jiki a bushe, shi kuma ya goya mata baya yana faɗin "Yo Grandma ai irin jikinki ne Baby ta ɗauko, shi ne kike kushe ta." Ya yi maganar yana kama hannun Abir suka wuce daga palon.
Grandma ta watsa musu daƙuwa ta shiga zagin Abdul, "koɗaɗɗan mazan koɗaɗɗan wofi, za ka ci butar ubanka tun da har kake haɗa ni da wannan shashashar yarinyar da kuka sangarta ta ta kasa gane ta girma, ni ba ƴar banza ba ce da zan tsaya ina kula ka mu taru mu lalace."
Dariya Laraba ta yi tana daga bakin ƙofar kitchen sai cin karas take abin ta ta ce "Inna Wallahi kina da abin dariya wannan ai he ki sa mutum ya yi ciwon ciki, Alkur'an haka Innar Babana take sai masifa." Ta ƙarashe maganar tana ƙarasowa palon.. Sai da ta zauna sannan Grandma ta ce "Ke na ci ƙundun uwaki Laraba, ni kike ce wa ina masifa?"
Sunkuyar da kai ta yi ƙasa sai kuma ta yi saurin kama ƙafafuwan Grandma ta soma matsa mata jin tana sauke mata ruwan zagi, ai kuwa Grandma ta yi shuru tana lumshe idanu jin yadda Laraba ke matsa mata ƙafa gwanin daɗi.
"Allah ya miki albarka Laraba ta bawa."
Washe baki Laraba ta yi jin ana sa mata albarka..
Suna isa Asibiti ana kiran Sallar isha'i, hakan yasa Abdul cewa "Baby muje ciki kafin a gama duba ki na dawo daga Sallah. "
Ɓata fuska ta yi ta ɗago za ta masa magana suka haɗa idanu ta yi saurin kawar da kanta, ɗaure fuska ya yi ya ce "To meye na wani haɗe rai bayan Asibitin ba baƙuwar ki ba ce?"
Cuno baki gaba ta yi tana matso hawayen dole ta ce "Yaya ni tsoro nake ji don Allah karka tafi ka barni a nan, ka bari in mun je gida sai mu yi kawai. Wancan lokacin ma ai daga kawoni Asibitin da ka yi ba ku sake ganina ba." Ta ƙarashe maganar ta na ƙara matso hawaye suka zuba kan kincinta, ji take ba za ta iya zama ko da na sakan ɗaya ne babu shi a kusa da ita ba.
Bai ce da ita komai ba ya fito ya zagayo ya buɗe mata ta fito, ciki suka nifa inda daret suka nufi wata ƙofa, suna isa Abdul ya kwankwasa ƙofar aka ba su izinin shiga suka sa kai ciki.
Da Sallama suka shiga inda suka samu Doctor zaune yana duba wasu takardu, ɗago da kai ya yi sai kuma ya riƙe baki cike da mamaki ya ce "A a wa nake gani kamar Mr Abdul Maitama da Ƙanwarsa?"
Murmushin gefen baki Abdul ya yi ya ce "Mu ne dai ni da Ƙanwata."
Wajan zama ya nuna musu suka zauna ya ba shi hannu suka gaisa sannan ya kuma cewa "Kai amma na yi farin cikin ganin Abir, 'yan kidnapping ɗin da suka sace ta ne suka sako ta ko jami'an tsaro suka kwato ta?"
Hade fuska Abdul ya yi jin ya soma jero musu tambaya daga zuwan su ya ce "Kai fa kana da matsala Hashim ya daga zuwan mu za ka tsare mu da tambaya?" Ya faɗa yana hararar shi.
Sanin halin Abdul ya sa Doctor Hashim ya canza maganar, ganin zai ɓata musu lokaci yasa Abdul cewa "Ka kira a duba ta ta ji ciwo ne."
"Kawai ka bari ni duba ta mana."
Wani irin kallo Abdul ya watso masa kamar zai kai masa duka ya rufe shi da masifa "Ko da wasa na kawo Baby Asibiti ka bari wani ƙato ya taɓa koda yatsar hannunta ne sai na karya masa muƙa-muƙi, Ƙanwar tawa za ka ce wai na bari ka duba ta?"
Ganin ya harzuƙa yasa Doctor Hashim yin dariya ya ce "Mayar da wuƙaƙen dama tsokanar ka nake." Tsaki ya ja yana harɗe hannayensa bisa ƙirji. Ita kuwa lamso ta yi lakwas a gefen shi tana bin su da kallo har suka gama ba ta ce musu uffan ba.
Waya ya ɗauka ya kira wata Nurse ya ce ta zo sannan ya kashe. Ba a fi minti ɗaya ba sai ga ta ta shigo tare da rusunawa ta ce "Sir gani."
Nuna mata Abir ya yi ya ce ta je ta duba ta, cikin girmamawa ta amsa sannan ta ce Abir ta tashi su tafi a duba ta. Har sun juya ta fisge hannunta ta dawo wajan shi tana yin raurau da idanu, ganin haka yasa ya kamo ta ya zaunar murya a ƙasa ya ce "What happening my Babyn Yaya?"
Hawayen da ta matso su tun a mota ne suka ƙara cika mata idanu, ganin ba za ta yi magana ba sai ya sa hannu ya goge mata hawayen cikin nuna kularsa a kanta ya ce "Baby ba fa komai za a miki ba ki je."
Sai a lokacin ta buɗe baki cikin rawar murya ta ce 'Ya... Ya... Ni dai kar ka tafi ka barni." Kumatunta ya shafo ya mikar da ita tsaye ya ce "Salla kawai zan yi." Ya faɗa yana kallon ta cikin idanu.. Ba dan ta so ta bi bayan Nurse ɗin suak nufi ƙofar fita Abdul ya dakatar da su ta hanya kiran sunanta suka waigo a tare, ya ce "Ki kula da ita zan je na yi Sallah minti goma zan dawo."
OK ta ce sannan suka wuce, suna fita shi da Doctor Hashim suka fita zuwa Masallaci..
Bayan an gama duba jikinta an tabbatar ba ta samu targaɗe ba ciwo ne kawai waje ke mata, hakan yasa suka rubuta mata wani pharmacy na maganin zafin take shafa wa a wajan..
Minti 20 cif Abdul bai dawo ba hakan yasa Abir ce wa Nurse za ta je mota ta jira shi kawai, ba dan ta so ba ta fita. A hanya suka haɗu da shi suka wuce mota sai gida...
Suna tafiya a hanya danger ta tsayar da su, kamar an ce ta kalli gefe ta gan shi tsaye a bakin hanya yana son wucewa, sai ya tafo kamar zai wuce sai kuma ya dawo baya a guje yana dariya. Zuge madubi ta yi ta leƙo da kanta ai kuwa suka haɗa idanu, wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta har sai da ta dafe ƙirji tana ƙura masa idanu, ji ta yi tana son masa magana amma kuma bakinta ya mata nauyi ta kasa furta ko da kalma ɗaya ce ga shi ba ta san sunan shi ba bare ta kira shi. Rufe idanunta ta yi ta buɗe sai ta ga wayam ba kowa a wajan, ƙara leƙowa ta yi ko za ta gan shi amma ba shi ba alamar sa haka ta dawo ta zauna tana mamakin ganin shi a wannan wajan.
Danger na ba da hannu suka wuce Abdul ya juyo ya kalle ta ya ce "Baby are you OK?"
Kai kawai ta ɗaga masa zuciyarta na ƙara tausayin shi da halin da yake ciki, ba ta san wani irin yanayi take ji ba game da wannan Mahaukacin da ya ceci rayuwarta...
Tsaye yake a cikin palo ya juya baya waya kare a kunnen shi sai faɗa yake kamar zai ari baki.
"Amma Wallahi Goje ka bani mamaki, yanzu ashe yarinya ƙwaya ɗaya tal ta gagare ku har ta samu hanyar da ta gudu ta kuɓuce daga hannunku? Mun yi da ku cewa yau ne ranar da zan je na aiwatar da aikina a kanta amma sakacin ku yasa ta gudu."
Daga cikin wayar aka shiga ba shi haƙuri.
"Sorry Oga Wallahi yarinyar nan gudun bala'i ne da ita, duk da hannayenta a ɗaure suke amma ba ka ga yadda ta dinga gudu ba kamar barbela. A labarin da Dagus ya bani ya ce wani Mahaukaci ne ya cece ta daga wajan su."
"Dalla yi min shuru suna ƙarti majiya ƙarfin har wani Mahaukaci zai gagare su, to na ba ku nan da sati ɗaya duk inda yarinyar nan ta shiga ku kawo min ita nan."
"Dama Oga ai lefin ka ne, kai ka ce mu bar mata wannan maganin da yake wajan ta, sannan ka ce kar mu kunna sigari a inda take dan ba ka so ciwon ta ya tashi kana so ka same ta garau, yanzu ga shi ta fe ce."
"To na dai faɗa muku ku nemo mafita in ba haka ba za ku ga mai zan yi a kanku." Yana gama faɗin haka ya cillar da wayar kan kujera ya nufi wata ƙofa.....
_*Maman Nusaiba*_