Free chapter · Read without an account
Part 4
~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~
Daga Alƙalamin
_*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_
_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_
Littafin na kuɗi ne nomal ~N~ 300 ne vip ~N~ 500. Ga masu buƙatar Littafin ki neme ni ta wannan number.
_🥏+966577675904_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Shafi na (4)
Tallah !! Tallah !!
Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , Rai daya janzaki, yau na sake dawowa domin muku Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji.
Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa.
RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal.
Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal
Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (*** ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.
Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank
Turo shaidar biya akan wannan *** sai najiku.
Tun da Abir ta dawo Asibiti shiga ɗakinta babu abin da take sai kuka da hasaso abubuwan da ta gani a wannan ɓakin gida, sosai tsoro da tashin hankali yake kawo wa zuciyarta ziyara yadda suke azabtar da mutane kamar ba su da zuciya a ƙirjinsu. Dan ita a yadda take ganin suna aikata mugun lefin nan tunani take ko an cire musu zuciyoyinsu daga cikin ƙirji ne? , ai ko da wataran ba su ji tausayin mutum in za su cutar da shi ba to fa wata rana za su ji tausayin mutum inda da kawai zuciyar a gangar jikinsu.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da zama a bakin gado tana dafe kanta jin yadda yake sara mata kamar zai rabe gida biyu, lumshe idanu ta yi zuciyarta na mata zafi in ta tuna alƙawarin da ta ɗauka. Jin ciwon kan na ƙaruwa yasa ta sauke hannayenta daga kan ta kalli ledar maganin da ta yi wulli da ita, tun da dai ta ji sauƙin ciwon jikinta ba ta waiwayi ledar ba har lokacin shan na safe ya wuce ga na yamma ya zo shi ma ba ta sha ba, a hankali ta ɗan muskuta ta janyo ledar maganin ta ɓalli ƙwaya biyu ta zuba a baki, gorar ruwan da ke kusa da ita ta ɗauka sai ta ga ba ruwa a ciki. Miƙewa ta yi ta isa gaban ƴar ƙaramar freezer dake gaba da gadonta ta buɗe ta ɗauko gorar ruwa mai mugun sanyi. Jin yadda ruwan ya yi sanyi har ba ta san lokacin da ta haɗiye yawu ba , dan ita ma'abociyar son ruwan sanyi ce indai ruwa ba sanyi to fa ba za ta sha shi ba duk ƙishirwar da take ji sai dai ta haƙura. Ko Makaranta za ta je sai ta cika wata gora mai girma ta zuba ƙanƙanra mai yawa a cikin ruwan dan kar ma ya huce, kaɗan daga cikin halinta da yake bai wa Abdul takaice, ya yi faɗan har ya gaji ya barta ga kafiya akan abu indai ta ce sai ta yi abu to ba mai hanata yi sai dai a zuba mata ido kawai.
Gorar ta kafa a baki ta sha maganin, sai da ta kusa shanye ruwan dake gorar sannan ta janye tana mayar da numfashi jin yadda sanyin ruwan ke ratsa ta. Komawa ta yi kan gadon ta zauna ta laliba kan gadon da zimmar janyo wayarta ta ji wayam, dafe goshi ta yi tunawa da wayar na can a hannun waɗanda suka sace ta, dafe kai ta yi tana mai jin zafin rasa wayarta ta.
Kwankwasa ƙofar aka yi ta ɗago da kai tana kallon ƙofar, sai da ta ji an kuma bugawa sannan ta ce "Shigo."
Shigowa Mommy ta yi Laraba na biye da ita, a ƙasa ta aje trey abincin tare sosa kai tana buga kan nata alamar ƙwarƙwata ta dame ta da cizo, ganin Abir yasa ta durƙusa har ƙasa tana washe baki ta ce "Madam sannu da hutawa, Alkur'anin Allah kina kama da wata mace da muka gani a TV gidan Sule a ƙauyenmu."
Murmushi Abir ta yi jin yadda Laraba ke rattaɓo bayani, ganin kuma ba ta daina susar ƙwarƙwatar ba ya sa ta miƙe ta shige toilet, can sai ga ta ta fito hannunta ɗauke da shampoon kai ta miƙa wa Laraba ta ce "Laraba kike ko?"
Da sauri Laraba ta ce " E Madam sunana Laraba amma sunan da aka yanka min rago da shi Shafa'atu ne, Innarmu ce take wani kirana da Laraba wai ni ce mace ta farko a wajan ta shi ya sa take min kara, ni kuma hauhi nake ji kawai dai kar na ce bana son sunan ta ce na mata rahin kunya." Ta ƙarashe maganar tana ɗaure fuska kamar tana gaban Innarta ta.
Murmushi ta yi ta dawo bakin gadon ta zauna sannan ta ce "To ki yi haƙuri da hakan, wannan idan kika tashi da safe ki shiga banɗaki ki wanke kanki da shi, haka in dare ya yi ki dinga wanke kan kafin ki kwanta. "
Godiya ta dinga jero mata tana washe baki ita ma za ta wanke kai da sabulun 'yan gayu sannan ta fita.
Zama suka yi a bakin gadon Mommy ta ce "Abir Grandma fa na jiran ki a waje sun ce za su yi magana da ke akan lamarin nan."
Dam ta ji gabanta ya faɗi ta zaro idanu tare da dafe ƙirji tana kallon Mommy, ita da ta yi alƙawarin ba za ta faɗi komai ba ya za ta yi da wannan meeting ɗin da aka shirya saboda maganar? Idan kuma ta faɗa ɗin kenan ta ƙarya alƙawari? Sannan za su iya aiwatar da abin da suka faɗa mata in ta faɗi wani abu game da wannan ɓakin gidan?. Tambayoyi ne suka dinga ziyartar masarrafarta ɗaya bayan ɗaya hakan yasa ta runtse idanu tana neman hanyar da za ta rusa wannan meeting ɗin, buɗe idanuwanta ta yi wanda suke cike da rauni da kuma tsananin tsoron abin da zai biyo baya ta dubi Mommy ta ce "Mommy to me ake so na yi bayan kuma ba na jin daɗin jikina?"
Karantar yanayin da ta shiga saboda maganar yasa Mommy ta ji gabanta ya bada ras! Tana tunanin kar dai abin da take tunani game da 'yarta ta tilo ne ya faru da ita? Girgiza kai ta yi tana kawar da wannan mummunan tunanin ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita tana jaddada mata ta yi ta fito.. shuru ta yi tana juya maganar da ke cikin zuciyarta, dafe kai ta yi gabaɗaya ji take kamar ta fasa ihu dan ba ta son taron nan, a sanyaye ta tashi daga kan gadon ta cire rigar da ke jikinta ta saka riga da sket, kwamtaccan gashinta mai santsi yana sheƙi ya bayayna, warware bakkilar ta yi ta sake ɗaurewa. Sanin halin Yayan nata yasa ta ɗauko hijabi har ƙasa ta saka tana kumbura baki ba dan ta so ba ta fita cikin mutuwar jiki da raunin zuciya hadi da tausayin kanta ta isa palon.
Dukkan su sun hallara a palon Abba da Daddy kowanne da matarsa, sai Mommy dake kusa da Grandma Abdul na gefen ta, sauran 'yan gidan duk suna ƙasa kan capet zaune suna jiran fitowar ta. Waje ta samu a kusa da ƙafar Grandma ta zauna kanta a ƙasa ta ce "Abba gani."
Gyara zama Abba ya yi cikin nutsuwa ya soma tambayarta.
"Mamana su waye suka sace ki? Kuma da suka ɗauke ki me suka miki a can ɗin ke da Ibrahim? Sannan ina shi Ibrahim ɗin yake?"
Wani irin raunataccan kuka ne ya kubce mata wanda ta yi iya kar bakin ƙoƙarin ganin ba ta yi kukan ba amma hakan ya custura sai ta ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Kuka take sosai babu wanda ya hana ta kuma babu wanda ya rarrashe ta har sai ta yi mai isarta sannan ta tsagaita kuka tana shashsheka tare da ɗago da kanta, idanuwanta da suka tashi daga farare suka koma jajur ta kai tafukan hannayenta ta rufe fuska ta kuma sakin wani kukan abin da ya tayar wa da su Abba hankali.
Cikin kiɗima Abba ya ce "Z... Zo nan Mamana."
Da rarrafe ta ƙaraso inda Abba ke zaune ya nuna mata gefen shi, zama ta yi tana ci gaba da kukan tana murza idanu. Hannu yasa ya kwanto da kanta kan ciyarsa ya shiga shafa kanta zuciyarsa na bugawa, kukan da take duk ya tada masa hankali so yake ya ji shin ina ɗan'uwansa yake?
Bayan ta lafa kuka ne Mami ta taɓa baki tana turo da ɗaurin ɗankwalinta gaban goshi ta harari Abir, gabaɗaya ta tsani yarinyar daga ita har mahaifiyarta ganin yadda kowa na family su yake so da ƙaunar su. Duk wanda ya zo gidan to a part ɗinta zai sauka komai sai ita , hakan yasa Mami ta tsane ta fiye kima kwata-kwata ba ta so ta ɗaga ido ta gan su a gidan. Tsaki ta ja cikin tsantsar tsana ta ce " Tsuww! Mu kun wani zo kun tara mu kamar wasu masu ɗaukan darasi a aji, ita kuma ta ɓare wa mutane baki tana kuka kamar a kanta aka fara kidnapping, ke kuka baya miki wahala ne?." Ta ƙarashe maganar tana kuma jan wani tsakin..
Jin haka yasa Mommy ta ce "Abir ki faɗa musu abin ya faru da ke, sannan ki faɗa ina Abbanki yake?"
Tashi ta yi zaune ta sunkuyar da kanta ƙasa ta soma musu bayanin da ta san in ta yi ba za su aikata mummunan ƙudirin da suka ɗauka a kanta ba.
"Abba ni ai na ɗauka Abie ya tafi Niger ne wajan kasuwancinsa, kenan bai dawo ba?"
Wata irin zufa ce ta shiga tsastsafo wa Abba, Daddy, Mommy, Grandma, Abdul. Cikin tashin hankali Abba ya ce "Mamana ki faɗa mana duk abin da kika gani dan mu tun da kuka yi tafiyar nan ba mu taɓa jin labarin ku ba, mun yi cigiyar har mun gaji da nema mun fauwala wa Ubangiji."
Jinjina kai ta yi ta goge hawayen da ya silalo daga kwarmin idanuwanta sannan ta ce" Ni fa Abba ban san komai ba, kawai zan iya tuna cewa ni da Abie muna mota daga wata ruga da na raka shi ya sayo shanu. To muna cikin tafiya ne mun zo tsakiyar wani jeji wasu maza suka dinga saukowa daga kan bishiya suna nuna mu da bindiga. Suka ce mu ba su kuɗin hannunmu Abie duk ya rikice ya fito da kuɗinsa dake aljihu ya ba su, amma ba su haƙura ba suka ce sai sun bincike motarmu ko akwai wani abu mun ɓoye. A bayan motar Abie suka ɗauko wata jaka mai girma wadda shaƙe take da kuɗin da ya ɗauko daren ranar da za mu yi tafiya daga banki, ya ce min zai sa hannun jari ne a wani company dake nan Yola, shi ne suka ɗauko kuɗin suka buɗe suka ga tabbas kuɗi ne a ciki. Abie ya roƙe su da su bar mu mu tafi tun da sun ɗauki kuɗin, amma suka ce sam ba za mu tafi ba ƙarshe ma wani a cikin su ya harbi Abie a ƙafa ganin haka yasa na kurma ihu neman taimako amma ba mai ji na. Kafin na kuma na biyu ni ma suka buga min wani abu a kaina, tun daga nan ban san komai ba sai shekaranjiya na farka na ganni a ɗaure. Ganin mai gadina yana bacci yasa na yunƙura da ƙyar na tashi tsaye saboda sun ɗaure min hannu ta baya bakina ma sun manna min gam, a hankali na samu na gudu daga gidan ina Addu'ar kar su ganni ashe sun gannin suka biyoni." Nan ta basu labarin yadda Mahaukaci ya ceci rayuwarta a lokacin da suke neman keta mata mutumci, tana dasa aya a maganarta ta fashe da kuka wiwi tare da faɗa wa jikin Abba..
Salati duk suka ɗauka masu kuka na yi masu tagumi na yi, Abba da Daddy su kan su sai da suka zubar da hawaye.
Abir ta ɗago ta ce "Abba kenan kuna nufin Abiena bai zo gida ba?"
Da ƙyar ya saita kan shi ya ce "Ki yi haƙuri Mamana tabbas bai zo gida ba, sai dai mu yi addu'a Allah ya kubuto shi daga mugun hannun da yake ciki, zan sa Abdul ya sanar da abokan aikinsa dawowar ki gida su ƙara tsananta bincike ko za aci sa'a mu san halin da yake ciki."
Hankalin Abir ya ƙara tashi fiye da wanda take ciki, wani irin zafi take jin zuciyarta na mata wanda har yawun dake cikin bakinta ya ƙafe. Da gudu ta tashi ta bar palo ta nufi ɗakinta jiki na rawa, Abdul ya bi bayanta Mami ta raka shi da harara aka yi sa'a Mommy ta ɗago ta ga kallon da Mami ke yi wa Abdul, girgiza kai kawai ta yi ta rafka tagumi.
Shin a ina mijinta yake? Yana raye ko yana mace?
Tambayar da ba ta da mai ba ta amsa, ta numfasa tana zubar da hawayen tausayin ƴarta da rashin sanin halin da mijinta yake ciki..
Sharce hawaye Grandma ta yi duk jikinta sai rawa yake, da ƙyar ta iya saita kanta ta dube su ta ce "Salmanu ka faɗa wa Abdullahi ya ƙara tsananta bincike su kwato min shi daga hannunsu." Ta yi maganar tana kuma goge hawaye.
Abba ya ce kowa ya tashi ya tafi ya rage daga Abba sai Daddy sai Mommy sai Grandma, ya gyara zama ya ce "Inna ki kwantar da hankalinki, in sha Allah Yaya Ibrahim zai fito ya dawo gida lafiya."
"Kayya! Kana ji fa wannan bushashiyar ta ce an harbe shi a ƙafa, yanzu ba mu san a wani hali yake ciki ba. Gardama ce irin da Ibrahimu na faɗa masa ya daina fita shi kaɗai batare da masu tsaron lafiyarsa ba, amma fir ya ƙi su bi shi rabon wannan ƙaddarar ne za ta faru da shi, ni dai don Allah ka ƙara jadadda wa Abdullahi su nemo min inda yake." Ta ƙarashe maganar tana face majina.
Haka ya shiga kwantar mata da hankali shi da Daddy, ita ma Mommy suna kwantar mata hankali, ita kuma ta ce in sha Allah zai dawo gida. Ta faɗi haka ne dan kar ta nuna damuwarta a fili Grandma ta fita shiga tashin hankali..
Ko da ta shiga ɗaki kan gado ta faɗa tana rera kukan kaddarorin da suka faruwa da ita, yanzu kenan ba a san inda Abie ɗinta yake? Tsagaita kukan ta yi jin an rufo ƙofar, harɗe hannayensa ya yi ya tsaya daga bakin ƙofar yana bin ta da wani irin kallo, tausayinta ya mamaye masa zuciya duk ta bi ta firgice ga ta ita dama ba wani jiki ba duk ƙashin jikinta ya firfito, takowa ya yi a nutse ya iso bakin gadon ya tsaya.. Ɗago kai ta yi ta kalle shi idanunta na tsiyayar da hawaye, hannu ya buɗe mata ta tashi da sauri ta faɗa jikinsa tana shashshekar kuka, juyawa ya yi ya zauna a bakin gadon tana maƙale a jikinsa ya shiga shafa bayanta har yanzu ya kasa ce mata komai. Sai da ya ji ta daina kukan ya ɗago fuskarta da ta yi sharkaf da hawaye ya sa hannu ya shiga goge mata, cikin kasalalliyar murya ya ce "Baby am so sorry kin ji."
Lamo ta yi a faffaɗan ƙirjinsa tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri, dogon numfashi ta ja ta ƙara rungume shi tana saɓa baki. Ƙura mata idanu ya yi yana shafa gashin kanta, ganin tana mutsu-mutsu ya miƙo bakinsa saitin kunnenta ya shiga yi mata ƙira'ar suratul baƙara cikin daddadar muryarsa, lumshe idanu ta yi tana jin yadda sautin muryasa ke ratsa ko'ina na jikinta har bacci ya kwashe ta.. Sai da ya tabbatar baccin ta ya yi nisa sannan ya zame mata hijabin ya kwantar da ita, bargo ya jamyo ya rufe ta tare da ƙara tofe ta da addu'a sannan ya miƙe tsaye, ya jima a tsaye yana kallon yadda take sauke numfashi sannan ya fita..
Daren ranar haka Mommy, , Abba, Daddy, Abdul, Grandma, da sauran su wasu na gidan ba wanda ya runtsa. Ita ka Abir ta samu bace duk da tana yi tana farkawa..
Washegari Abir tana cikin shiryawa Fatima ta shigo ɗakin, cikin sanyin jiki ta ce" Anty Abir wai Yaya Salim ya ce ki je ya kaiki Asibitin."
Ba ta juyo ta kalle ta ba ta kuma amsa mata ba har sai da ta gama saka ɗankunne sannan ta juyo ta ce "Ki ce masa ina nan zuwa."
Ganin ba ta zauna yasa ba Fatima ta riƙe baki ta ce "Anty juyo na ga kwalliyar mana."
Juyowa ta yi tare da aro murmushin yaƙe ta ɗaura bisa fuskarta, ta saka mayafi da takalmi haɗi da jaka duk tana kallon ta sannan ta ce "To tashi mu tafi."
Ba muso ta tashi suka jera a tare suka fito zuwa palo, inda suka samu Mommy ita ma na shirin barin palon jikinta sanye da hijabi.
"A a! Mommy ina kuma za ki je?" Cewar Abir tana ƙare mata kallo.
"Gidan Baba Malam zan je na duba shi da jiki, ba shi da lafiya tun kwana uku da suka wuce kuma na sanar da shi Allah ya kubto da ke." Ta faɗa tana yin gaba. OK kawai Abir ta faɗa ba ta kuma cewa komai ba har Mommy ta fita a palon. Juyowa ta yi za ta yi wa Fatima magana sai ta ga wayam ba kowa, taɓe baki ta yi ta nufi part ɗin Umma wajan Salim. Har ta kusa ficewa a palon ko me ta tuna sai ta dawo ta nufi ɗakin Grandma, tura ƙofar ta yi bakinta ɗauke da sallama.
Sallamar tata ce ta maƙale sakamakon ganin Fatima da ta yi a durkushe a gaban drower Grandma ta fito da kayan ciki waje, sosai abin ya mata mamaki.
A razane Fatima ta yi saurin kai kallon ta bakin ƙofar nan-da-nan tsoro ya cika mata zuciya ganin kallon da Abir ke mata. Cikin in'ina ta ce " Am dama da...
Ɗaga mata hannu ta yi kafin ta yi magana ta tari numfashinta ta ce "Grandma ce ta ce na gyara mata kayanta duk sun hargice, to shi ya sa ma kika ga na bar ki a palo na shigo ɗakin." Ta faɗa tana ƙifƙifta idanu.
"Ok to ina Grandma ɗin?" Ta tambaye ta cike da tuhuma dan ita a iya rayuwarta ba ta taɓa ganin Grandma ta sa Fatima aikin ɗakinta ba.
"Sun tafi Station ita da Abba da Yaya Abdul ta ce da ita zai je ba za ta bari a barta ba sai an tafi da ita, shi ne Abba ya ce Abdul ya kai su."
"Ok." Iya abin da ta iya faɗa ta tsaya tana mata kallon ita fa take jira, ganin haka yasa Fatima durƙusawa cikin hanzari da kuzarinta ta ɗauke kayan da ta fito da su wanda suke a wanke a goge tsaf ta jera a drower. Ganin ta gama Abir ta juya ta fita hakan ya ba wa Fatima damar ɗauko ambulan ɗin da ta ɗauko tun farkon buɗe drower, rigarta ta ɗaga ta soka ta a mara ta yi saurin barin ɗakin tana murmushi..
Salim da ya gaji da jira ya kira Abir ya ce yana harabar gidan ta yi maza ta fito, ta amsa da to ta fita ta same shi a mota suka bar gidan..
Shagon sayar da waya suka fara zuwa suka taya waya ta sa yi iPhone sannan suka isa Asibiti...
Suna zuwa Salim ya aje ta ya ce in an gama mata ta kira shi zai je su gaisa da abokin shi ta amsa da to. Ba ta wani ɗauki lokaci ba ta amshi maganin da ta saba amsa duk ƙarshen wata na asma ta fito.
Ta daɗe tana jiran Salim bai zo ba ta buɗe sabuwar wayarta ta saka sim ta kira shi ya ce ga shi nan zuwa amma shuru, wayar ta shiga tana dudduba cikin ta sako ya shigo wayar abin da ya ba ta mamaki matuƙa, saboda sim ɗin nata special number ce ba kowa ya san tana da number ba. Buɗe sakon ta yi ta soma karantawa.
_"Wato ke mai kunnan ƙashi ce ko? Kin yi alƙawari amma kika karya kin manta sharadin mu da ke?"_
Da sauri ta miƙe tsaye ta nufi hanyar fita daga Asibitin saboda kiɗimewa ba ta san ta fita daga Asibitin gabaɗaya ba sai da ta ji ƙaran motoci na wucewa ta gane ta fito a waje take. Waige-waige ta dinga yi hagu da dama ai kuwa ta ga wasu maza biyu na kallon ta, da gudu ta nufi hanyar komawa cikin Asibitin sai ji ta yi ta yi karo da wani abu ta faɗi Tim!....
Littafin nan dai na kuɗi ne my sister.
_Taku har kullum Maman Nusaiba ce_