Free chapter · Read without an account

22

by Nabeeha Aminu · TSANANI

43/44






***




Suje suyi karuwanci kaman yadda uwar su tayi ta aifesu, k'ofa a bud'e take zasu iya tafi, dan kinsan d'an nagada yafi d'an na koya, nifa Goggo aradu na tsani nazo garin nan na bud'e Ido naga yaran nan a cikin gidan mu, tunda aka aifeni ban tab'a ganin wanda ya rik'e shegu ba saike, kema d'in rashin zuciya ne irin naki, tunda Baffa ya mutu aida kin korasu inda suka futo"


Amna cikin tashin hankali tace "Goggo dan Allah kice abunda Adda Lantana take fad'a k'arya ne, kice kece kika aifi mu ba wata can ba, Goggo ke kikafi dacewa da zama uwa a garemu, nasan bani da uwar data wuce ki a duniyan nan, Goggo tunda na bud'e idona ke kad'e nake gani a matsayin uwata dan Allah kice ba daidai ta fad'a ba" ganin Goggo tayi shuru yasa taje kusa da ita tafara girgiza ta tana cewa dan Allah Goggo kiyi magana kice mun kece" ta k'arasa maganan cikin matsanancin kuka.


Goggo hankad'e ta tayi taje zata fad'i Abbas ya tare ta yana watsawa Goggo mungun kallo.


Goggo ta nunasu da yatsa tace "ku bud'e kunnen ku dakyau kujini yau zan fad'awa ko wannen ku asalin sa, gyara zaman ta tayi dakyau ta dubesu a wulak'ance kafin tace "watarana ina bakin murhu ina tuk'a tuwon dare Baffa ya shigo gidan hankalin sa a tashe da jinjiran a hanun sa, na tashi ina mishi kallon tuhuma kafin nace "a ina kasamu jinjira Salihu?


D'ago Idon sa da yayi jajazur yayi ya zuba mun yace "y'ata ce, Zulai ina neman alfarma a wajen ki, yau kwanan ki goma da aihuwa dan Allah ki had'a ta da D'ahare ki shayar"


Ashar na d'ura kafin nace "haba Salihu ina zaman zamana kazo mun da jinjira sabon aihuwa kace mun na shayar, gaskiya bazan iya ba domin y'a d'ayan ma dakyar nake iya shayar da ita, to dama kake cewa na shayar da ita y'ar waye?


Kai tsaye ya sake maimaita mun kalman sa na farko yace "y'ata ce idan kumma ban isa na kawo jini na gidan nan a rik'e mun ba saiki fad'a"


Duk da naga cikin b'acin rai yake maganan, hakan bai hanani tashi na shak'e wuyan sa ba nace wato ha'inta na kakeyi ban sani ba, Salihu aure kayi baka sanar dani ba"


Buge hanuna yayi yace "baki kai wanda zan b'oye Mata dan zanyi aure ba, wannan y'ar da kike gani ta futo ne daga tsatsan wanda take sona nake sonta, dan haka ya zamo dole na rik'e ta a gidan nan"


Ni kuma nace ko mutanen duniyan nan zai had'a a kaina bazan shayar dake ba, muna cikin sa'insa k'anin sa Sule ya shigo gidan, futa naga sunyi sunata tattaunawa can suka shigo Baffa Sule ya tsuguna a gaba na yana rok'o na akan na yarda na rik'e ki, ni kuma nak'i ba yadda baiyi ba ganin bazan amince ba yacewa Baffan ku ya bashi ke zai kaishi wajen mai d'akin sa, shi kuma dayake yana da taurin kan tsiya yak'i amincewa, tun ranan yake kula dake har kika girma shine cinki shan ki wanke kashin ki wankan ki duka shi yake wannan d'awainiyan dake har kika girma kika farayi da kanki, lokacin da kika cika shekara biyar ya sake zuwa mun da wani sabon jinjiri nanne yaka tashin hankali a wajena dan bud'a wa idona garin barkono nayi nace banga wanda ya isa yasa yaron ya zauna mun a gida ba, ba k'aramun tashin hankali mukayi ba dayake kanshi kaman na mutanen farko ne yak'i bin abunda nace, ke dashi kukayi ta rainon Abbas, kuma daliln haka yasa muka raba shin fud'a bamai shiga hark'an kowa harya koma ga ubangiji, dan nace idan bai futar mun da shegun yara a gidana ba bazan tab'a bashi had'in kaiba, shi kuma ya gwammace ya hak'ura da kusanta na ya rik'e ku, yanzu kinji asalin ki ke shegiya ce dan ciki yake zuwa yama wata can ni kuma dayake ya mayar dani bola saiya kawo mun yaran yace na rik'e, ki godewa Allah dana cigaba da rik'e ku bayan mutuwan sa, dan danaso muku mugunta koran ku zanyi tunda wanda yayi cikin kun yabar duniyan, yanzu ma nabaku daga yau zuwa jibi ku tattara kubar mun gida na dan d'an shege bayi da gado ehe.


Amna da zuwa yanzu zuciyar ta ya bushe ba d'igon hawaye a Idon ta sai tarin tsanan Goggo da ya'yan ta, ta dubeta tace "a ina ma'aifiya ta dana Abbas suke?


Goggo tayi shewa kafin tace dana san inda suke ance muku zan rik'e kune, kuma da uwar taku tana sonku ai bazata k'i shayar daku ba, kawai kuma kuje ku bud'e gidan karuwai dan kusamu kuna aifan ya'yan da zaku na watsarwa kaman yadda uwa tayi"


Lantana tace "Goggo ban tab'a tunanin baki da wayo ba sai yau taya zaki koresu da wuri bayan idan sun tafi bakida masu miki bautan aiki da tallan nono, koso kike ki bautar da ya'yan ki na cikin ki wanda kika aifesu ta hanyan aure?


Goggo tace "gaskiya Lantana kinyi tunani maikyau dan kin hango mun abunda na kasa hango wa kaina, shiyasa aihuwan d'a mai hankali da hangen nesa yake da dad'i, nafasa koran ku ya zama dole ku zauna kumun bauta nida y'aya na, dama Baffan ku ne ya hanani fad'a muku tushen ku dama tuntuni, saboda yace duk lokacin dayaji nace fad'a muku asalin ku ko na fad'awa ma wani ku shegu ne kuma bani na aife kuba a bakin aure na, hakan yasa na rufe baki na dan abun kunya ne na koma gida nace mijina ya sake ni saboda shegun yara, to yanzu kuma nice da mulkin komai dan haka na fasa koran ku yanzu sai nan gaba tukunna"


Amna zatayi magana Abbas yayi saurin rufe Mata baki ya tashi ya kama hanun ta ya Mata halamu da Ido su futa, shiya fara futa kafin tabi bayan sa, d'akin su suka tafi suka zauna kowa da irin tunanin da yakeyi a zuciyar sa, Goggo da Lantana ne sukazo suka lab'e domin jin abunda zasuce, sunkai awa d'aya suna lab'e amma basuji sunyi magana ba, Lantana tace "anya yaran nan suna ciki kuwa? Goggo tace "nima abunda nake tunani kenan amma mu shiga mugani, d'akin suka shiga bako sallama ganin su kowa yayi tagumi Lantana ta kwashe da dariya tace "na jima ina rok'on Allah ya nuna mun wannan ranan, ranan da zan ganki kina cikin bak'in ciki da tashin hankali da rashin mafuta a rayuwar ki, sai gashi ba'aje ko inaba nagani, Amna idan akwai wanda na tsana a rayuwa ta kece, bansan meyasa ba ganin ki yakan k'aramun bak'in ciki a rayuwa ta, kisani indai na cika y'ar halak bazan tab'a bari kiji dad'in rayuwar ki a rigan nan ba"


Goggo tayi saurin amshe maganan da cewa "Lantana ai kece cikekkiyar y'ar halak wanda aka aifeta ta hanyan da Allah yace yanzu muje d'aki ki fad'a mun kalan uk'uban dazan gana musu kafin ki tafi dan na sanki akwai basira" futa sukayi hanun su sark'e dana juna suna dariya kaman k'awayen juna.


Amna girgiza kai kawai tayi amma har yanzu idonta ya kasa zubar da hawaye sai wani k'unan bak'in ciki da takeji a zuciyar ta dan da zata samu daman yin kuka daba k'aramun dad'i zataji ba sai yanzu tasan kuka ma rahma ne, suna zaune a wajen har dare yayi kowa yayi bacci, amma badda su dukan su bamai jin ko d'igon bacci a idon sa, ruwa ne ya b'alle kaman da bakin kwarya, ga d'akin su ba rufi akansa ruwan yayita sauk'a, Abbas tashi yayi ya futa ya tsaya a filin gidan yanata kallo ruwa na sauk'a akansa, Amna ganin shurun sa yayi yawa yasa ta biyo bayan sa tana futowa ta gansa a tsaye a yanata kalle kalle, k'araso wa tayi ta dafa sa tace "kayi hak'uri kanina insha Allahu watarana zamuji dad'in rayuwa, kuma nasan ma'aifiyar mu bata guje mu haka kawai ba tare da kwankwaran dalili ba, sannan kuma Baffa bai tab'a bari munyi kukan uwa ba, a koda yaushe yana k'ok'ari yaga ya dawo uwa a gare mu, kazo mu koma kasamu kayi bacci kaga dare ya raba nasan yanzu k'arfe ukun dare yayi, ta rik'e hanun sa ta juya akan zasu tafi taga ya tirje a wajen juyowa tayi da sauri ta kalle sa taga ba ita yake kallo ba tace "Abbas bazaka iyama abunda na fad'a ba biyayya?


Kai ya girgiza Mata idon sa yana zubar da hawaye dan tunda aka fara maganan sai yanzu ya samu daman yin kuka, gaban shi tazo da sauri ta rungume sa tace "karka mun haka Abbas rashin kukan ka shi yake k'ara mun k'arfin gwuiwa, Abbas ina da rauni akanka, idan naga kana kuka nima zanyi" tana magana tana kuka d'ago Ido yayi ya kalle cikin muryan kuka yace "Adda Amna ba kukan rashin sanin ma'aifiya ta nakeyi ba, akan mema zanyi kuka dan bansan ta ba akan mai zanyi kuka akan Matan data yar dani tun ina tsumma alhalin tasan ubana bayi da nonon dazai shayar dani? Bani da uwa a duniyan nan data wuce ki domin tun ina jinjiri ke nasani a matsayin uwata, nagodewa Allah dayasa muna da uba, kuma muka tashi a hanun sa, kawai ina kukan rashin rama miki bak'an maganan da sukeyi ne, amma nayi alk'awarin rama miki duk daran dad'ewa, dan Allah kimun izini na shiga duniya neman ilimi da dukiya"


A razane ta kalle sa tace "Abbas yanzu zaka iya rayuwa ba tare dani ba? Zaka iya tafiya ka barni na zauna bani da mai d'auke mun kewa? Bata bashi daman bata amsa ba ta cigaba da cewa ya Allah ka karb'a rayuwa ta kafin zuwan ranan da Abbas zai tafi ya barni" rungume ta yayi yana kuka yace "dan Allah karki sake irin wannan addu'an, Adda Amna bazan iya rayuwa a cikin gidan nan ba yanzu"


Tace "kayi hak'uri da safe muje mu samu Baffa Sule mu mishi bayanin abunda Goggo ta fad'a mana ko shi yasan inda iyayen mu Mata suke"


Murmushi mai ciwo yayi yace "Adda Amna nifa bani da uwar data wuce ki dan Allah karki sake mun maganan wata uwa bayan ke, amma bazan hanaki neman Maman kiba, nikam ina tare da nawa dan kece uwata Baffa ubana, dan Allah Adda Amna kimun alfarman d'aya!


Tace "wani irin alfarman kakeso na maka?


Tsugunawa yayi a gaban ta ya rungume k'afan ta yana kuka maicin rai dakyar ya iya cewa "dan Allah Adda Amna ki amince mubar rigan nan mu tafi gidan Malama Aisha kafin muga mai hali zaiyi nasan idan na cigaba da zama anan zan iya had'iye zuciya ta na mutu, dan bazan iya juran ganin abunda suke miki ba, idan kuma kinfi son rayuwar su fiye dani shikenan saimu cigaba da zama ana"


Tsugunawa tayi itama suka rungume juna suna kuka maicin rai tasan idan bata amince suka tafi ba zai iyayin abunda ya fad'a, kuma idan tayi sanadiyar mutuwan k'anin ta meye riban ta, sannan kuma tasan batama Baffa adalci ba, ta shafa kansa tace "Abbas inaso kasani bamu da gidan daya wuce gidan uban mu, duk inda muka shiga a duniyan nan sai sun goranta mana muna zaman cin alfarman sune, nan kuma saidai amana gorin bata hanyan aure aka aife mu ba, na amince mubar rigan nan na wani lokaci domin zuciyar ka tayi sanyi, saidai idan ka yarda a gidan Malama Aisha zamu zauna har zuwa lokacin da Allah zai kawo mana k'arshen wannan abun"


Yace "na amince muje gidan ta, kuma barin mu nan shine k'arshen wahalan mu insha Allahu" ya mik'e ya rik'e hanun ta yace mu tafi kawai basai kin koma ciki ba"


Tace "ka jirani anan akwai abunda zanyi, kuma inaso na naje na d'auki ko abu d'aya ne a d'akin domin tunawa da Baffan mu" bata jira jin abunda zaice ba tashige d'akin tana shiga ta d'auko wani d'an k'aramun k'aho da wuk'a na Baffa ta nad'e a cikin rawanin sa, kafin ta d'aga wani k'aton dutsen da yake d'akin ta d'auki ledan da take tara kud'in da take samu agun Sama'ila da Ilu, futowa tayi tace "Abbas muje bakin kogi muyi bankwana dashi" bai Mata musu ba sukaje suka zauna a bakin kogin hawaye na zuba a domin ta, tunawa tayi da Baffan ta, dan wani lokacin idan ya dawo daga kiwo da wuri zai rik'e hanun su, su zauna a bakin ruwan yayita basu labarin abun al'ajabi da yake faruwa a duniya, saurin kawar da tunanin tayi domin bata son tuna maganan ko d'aya da Baffa yake fad'a Mata, tashi tayi tana kallon sansanin su, bukkoki ne zagaye da kogin, duk wanda yazo wajen saiya bashi sha'awa, dan wajene mai dad'in zama mutanen wajen basu da damuwan komai, kowa hark'an gaban sa yakeyi, kusan Goggo ne da mutanen gidan su suka futa daban a rigan, ganin kukan ta yak'i tsayawa yasa Abbas tashi ya kama hanun ta yace "kiyi hak'uri komai zai wuce da yardan Allah, watarana sai munzo mun gina babban gida a wajen nan mun cigaba da rayuwar mu mai dad'i da soyayyan al'umman wajen, ban futar a raina ba watarana saimun kawo wa rigan nan cigaba, ki tashi mu futa da sunan Allah, nasan zamu dawo da ikon Allah kodan mu cimma burin mu" rik'e hanun ta yayi suka fara tafiya cikin daran, Amna sai juyawa takeyi tana kallon garin, dan harga Allah bata k'aunan abunda zai rabata da rigan Baffan ta, k'arfe biyar da rabi suka isa cikin gari, lokacin ruwa ya ya tsaya sanyin asuba ya huro ga jikin su a jik'e, runfan shagon Sama'ila sukaje suka zauna, suna zama aka kira sallan asuba, Abbas yace bazanje masallaci nayi sallah zan taho miki da ruwa kema kiyi, ta d'aga masa kai ya tafi masallaci.


Abbas yana tafiya taji an dafa ta tabaya ta juyo dan ganin wanda ya dafa ta, suna Ido biyu da mutumin ta zare idon ta tace..........







***






Mmn Ashfaq

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.