Free chapter · Read without an account
29
by Nabeeha Aminu · TSANANI
57/58
***
Tace "ina kwana Yaya Saifuddeen!
Saifuddeen kallon ta yayi da sauri saboda jin yadda ta kira sunan, zai iya rantsewa tunda aka aife sa bai tab'a jin wanda ya iya kiran sunan yadda yaji ta fad'a ba, tsikan jikin sane duk ya tashi ya lumshe idonsa yana jin wani abu na fusgan sa wanda shi kansa ya kasa gane meye, bud'e idon sa yayi ya zuba Mata ya kasa amsa gaisuwan ta sai kallon da yaketa binta dashi, Amna jin bai amsa ba saita zaci baiji bane ta d'ago kanta danta sake gaishe shi karaf idon su ya sark'e cikin na juna dakyar ta iya janye nata tana jin fad'uwan gaban ta yana dad'a tsanan ta murya na rawa ta sake cewa "ina kwana Yaya Saifuddeen"
Tasowa yayi yazo ya tsuguna a gaban ta ganin haka yasa Abbas tashi ya futa ya basu waje yana addu'an Allah yasawa Addan sa k'arfin gwuiwa da na zuciya kar wannan shed'anin mutumin yayi nasara akanta dan tun ganin farko daya masa yaji kwata kwata bai kwanta masa arai ba, Saifu yana ganin futan Abbas ya sake matsowa kusa da ita har nunfashin sa yana sauk'a a fuskan ta ya kama hanun ta duka biyu yana murzawa a hankali ya kafeta da Ido ganin fuskan ta bai nuna halamun tana jin dad'in sak'on da yake aika Mata ba yasa ya sake hanun yana k'ok'arin jawota jikin sa tayi saurin janyewa daga kusa dashi tana cewa "Yaya Saifuddeen bana son wannan kusan cin a tsakani na dakai, ka fad'a mun abunda ya kawo ka wajen mu da asuban nan, dan na matsu naga nabar gidan"
Nunfashi mai zafi ya furzar a bakin sa yana mamakin wai yau shine a gaban mace tana fad'a masa bak'ar magana yake iya jurewa kuma har zuciyar sa baiji zafi ba, kallon ta yayi yaga yadda take yatsina fuska kaman taga kashi ko wani abun kyama, murmushi yayi a zuciyar sa yace duk ranan da kika shiga hanu na zan fanshe duka abunda kika mun, a fili kuwa yace "nazo sheda miki gobe zamu bar k'asan nan ne, idan akwai abunda kuke buk'ata ku sanar dani tun yanzu basai lokaci ya k'ure ba"
Murmushin takaici tayi tace "jiya baka fahinci abunda na fad'a maka ba kenan?
Yace "y'an Mata kenan baki san waye Saifuddeen ba shiyasa kike k'ok'arin maimaita abunda kika fad'a jiya, inaso ki sani tun ina yaro ba'a mun magana biyu, da abunda kunne yaji na farko nake amfani dan haka baki isa ki canja mun magana ba ko kuma ki canja ni a yadda nake, ya zamo dole ki bini mu tafi gobe wannan umurni ne ba shawara ba" ya tashi cikin fushi zai futa muryan ta ya tsinta tana cewa "kaman yadda baka san waye niba haka nima ban damu nasan waye kaiba, da farko ni nace zan bika kuma na fasa binka dan haka baka isa kamun dole ba, wai meyasa mutane sukeso su mayar dani baiwa mara y'anci ne? Ni kenan rayuwa ta a cikin TSANANI akeso ya k'are? Hakan bazai tab'a yiyuwa ba dole na karb'a wa kaina y'anci aduk inda nake da duk wanda na zauna, kayi hak'uri ban kasance cikin mutane masu sab'a alk'awarin ba saidan, kawia naga hakan bai dace ba, ba irin tarbiyyan da ma'aifina ya k'are rayuwar sa wajen bamu ba kenan, idan kuma ka dage sai kayi mun dole ko kuma ka nuna mun k'arfin Arzikin da kuke dashi tabbas yau d'in nan zan kashe kaina saidai ka tafi da gawa na" ta k'arasa maganan tana kuka maicin rai da zuma zuciyar mai sauraron ta.
Kallon ta yayi yace "karki rainawa kanki hankali domin bazan tab'a yarda ba karuwanci kika futoyi ba, domin duk y'ar arziki bazata tab'a barin iyayen ta ta futo titi tana kwana ba, dan haka ya zamo miki dole ki bini ko kinaso ko baki so saikin bini, kuma k'anin kin da kikace zai bimu yanzu na fasa dake kad'e zan tafi, kisawa ranki zaki kasance dani a shinfud'a na harsai ranan dana gaji dan kaina na koroki Nigeria, gargad'i na k'arshe karki kuskura ki sake mun musu ko gardama aduk abunda zance inba haka ba zan futo miki da real colour d'ina, dan naga ke bak'uwa ce a bariki bakisan waye Saifuddeen ba" yana gama maganan ya juya ya futa a gidan, Abbas ganin ya futo a fusace ya shiga motan sa yabar gidan yasa ya shiga d'akin da gudu, ganin ta tana kuka ba k'aramun d'aga masa hankali yayi ba yaje ya tsuguna a gaban ta yace "meyace miki Adda Amna? Yak'i amincewa ne?
Rungume sa tayi cikin kuka tace "mugudu a gidan nan Abbas yace dole saiya tafi dani ya lalata rayuwa ta dan Allah mugudu kar kace mun saiya dawo mu futa da izinin sa" kama hanun ta yayi yace "mu tafi saidai bansan hanyan da zamu bi mubar unguwar nan ba, kinga bamu kula ba lokacin da yake shigo damu"
Tace karka damu da wannan idan muka futa zamu samu hanya" gyara zaman hijabin ta tayi ta d'auki rawanin ta suka futo da gudu, saidai abun takaici get d'in gidan arufe yake sunyi sunyi su bud'e sun kasa, tsuguna sukayi a wajen suka saka kuka duk dauriyan Abbas amma wannan karan ya kasa rik'e kukan, ya kama hanun ta suka koma d'akin yana kuka yace "kiyi shuru Adda Amna insha Allahu Allah bazai bashi nasara akanki ba, muyita addu'a har Allah ya sanyaya mishi zuciyar sa" batace mishi komai ba sai kukan data cigaba dayi, shima tayata yayi tayi.
Saifu tunda ya futa ya kasa tafiya saboda suyan da zuciyar sa take masa dawowa gidan yayi a zuciyar sa yana cewa ya zama dole na nunawa yarinyan nan ba'a mun jayayya, dole kota k'arfi na nuna Mata jarumta na ta inda gaba ko ance tamun musu bazata iya ba.
Jin karan mota halamun ya dawo yasa suka d'ago cikin tsoro suna kallon hanyan shigowa d'akin, banko k'ofan d'akin yayi ya shigo kaman namijin kumurci ya kalli Abbas yace "bamu waje" tashi yayi ya futa zuciyar sa tana tsinkewa, yana futa ya fara cire belt d'in wandon sa yana nufo kanta, ganin haka yasa jikin ta ya fara b'ari ta kasa koda bashi hak'uri, tace daka mun abunda kake shirin aikatawa gwanda na kashe kaina, tayi saurin warware rawanin hanun ta, ta ciro wuk'an ta saita cikin ta dashi tace "Yaya Saifuddeen kana dad'a kusanto ni zan kashe kaina idan kana tunanin wasa ne kazo ka gani"
A razane ya juyo ya kalleta jin ta ambaci zata kashe kanta zuwa yanzu ya yarda zuciyar sa ta kamu da sonta, danji yayi idan ra kashe kanta bazai iya rayuwa ba kuma yanayin ta ya nuna zata iya aikata abunda ta fad'a, mayar da belt d'insa yayi yace "ki mayar da wuk'an muyi magana"
Tace bazan mayar ba harsai kamun alk'awarin bazaka mun komai ba!
Yace "namiki rantsuwa da Allah bazan miki komai ba" jin haka yasa ta ajiye wukan ta tsuguna agun ta saki kuka mai ban tausayi, zuwa yayi ya tsuguna a gaban ta yace "naji nafasa tafiya dake amma ki sani bazan sake barin ki ki koma rayuwar bariki ba, saidai idan kin yarda zaki zauna a k'ark'ashin kulawa na, zan barki a Nigeria a hanun aboki na zai kula dake kaman ni koma nace fiye dani, zai nema miki gurbin karatu amma idan naji kinbi wani bani ba wallahi sansa a kashe ki"
Kallon sa tayi batasan lokacin da murmushi ya sub'uce Mata ba tace "nagode Allah ya k'ara girma na amince duk lokacin dakaji labarin ina tare da wani ka yanke duk hukuncin da ya dace a kaina, amma bani kad'e zaka nemawa gurbin karatu ba harda Abbas d'ina, domin shine farin cikin rayuwa ta shi kad'e nake kallo naji dad'i tunda Baffan mu yabar duniya"
Karo na farko kenan da yaji wani ya bashi tausayi saurin tashi yayi domin yaji yanayin sa ya fara canjawa ganin idan ya cigaba da zama kusa da ita komai zai iya faruwa ya kalleta daga tsayan da yake yace "k'unci abnici jiya kafin ku kwanta?
Kai ta girgiza masa tace "bamu ci ba" Ido ya zaro yace meya hana ku ci?
Kai tsaye ba tare data kalle sa ba tace "saboda tunanin kana neman ruguza mun rayuwa ta"
Dariya maganan ta ya bashi cikin dariya yace "na fasa ruguza miki rayuwar yanzu ki tashi kije ki nema muku abunda zaku ci nasan ba bread da eggs a gidan bazan je na nemo muku " bai jira amsan taba ya futa Abbas ya gani yana zaune a k'ofan d'akin ya had'a kai da gwuiwa daga gani kuka yakeyi ya d'ago sa yace kukan mai kakeyi aboki na?
Share hawayen sa yayi yace "naga duk wanda yakeso ya taimaki Adda na akwai wani abu a ransa, dan Allah ka dubi maraicin mu karka cutar da rayuwan mu bamu da kowa a duniyan nan sai Allah, idan bazaka iya taimakon mu saboda Allah ba ka barmu mu tafi duniya fad'i ne da ita zamu had'u da mai taimako mu a gaba"
Shafa kansa Saifuddeen yayi yace ka shiga ciki yanzu zan dawo sai muyi maganan" saida ya tabbatar Abbas ya shiga falon kafin yaje ya shiga motan sa ya futa yana jin wani iri a zuciyar sa, a duba duk shaguna yayi basu futo ba yana dawowa ya ga wani runfan mai shayi ya tsaya yace ya soya masa kwai guda ishirin da bread manya guda biyu, kud'in ya fad'a masa shi kuma ya koma mota yana jiran ya gama, baifi minti goma ba mai shayin ya kawo masa, ya karb'a ya tada motan yabar wajen.
Abbas yana shiga yaga Amna tana murmushi ya k'araso kusa da ita yace "ya amince bazai tafi damu ba? Murmushin ta, ta fad'ad'a tace "eh ya amince Abbas kuma yace zai nema mana gurbin karatu ni dakai anan, amma yace zaibar amanan mu a hanun abokin sa"
Abbas yace "Alhamdulillah Allah mungode maka da kake kawo mana mafuta a rayuwar mu aduk lokacin da abubawa suka kwacib'e mana, suna magana ya shigo bakin sa d'auke da sallamah, ajiye musu laidan hanun sa yayi yaje kitchen ya dafa ruwan zafi ya juye a fulas ya d'auko kofi Lipton da sugar ya jera musu a gaban su yace "idan kuna buk'atan wani abu ki kirani a waya, da number dana kira ki jiya, duk wanda ya kira karki d'auka idan ba ni bane, zanje amma zan dawo anjima na sanar daku yadda mukayi da aboki na.
Ta mishi godiya ya futa, yana futa suka fara karyawa suna dad'a godewa Ubangijin mu, Abbas yace Allah yasa ba wayo yayi mana ba"
Tace "zaiyi wuya idan wayo ya mana amma bari muga dawowan sa muji dame zaizo"
Saifuddeen yana futa.............
***