Free chapter · Read without an account
56
by Nabeeha Aminu · TSANANI
111/112
***
Amna gidan Mommy aka wuce da ita, y'an uwan Baffa sun nunawa mata karanci sosai, dan gaba d'ayan su sunzo, Goggo ma tazo da ya'yan ta duka, Larai ce kawai batazo ba itama dan batasan da bikin bane, Goggo Adda Lantana D'ahare da Maree bud'e baki sukayi suna kallon gidan Mommy, tsoro ne ya kamasu dukan su sai suka fara tunanin kodai gidan yankan kai aka kawo su, basu sake tsurewa ba saida aka shiga falon Mommy dasu, Goggo batasan lokacin da ta saki ihu ba saboda sanyin AC dataji yana shiga jikin ta, mutanen falon sukayo kanta suna tambayan ta lafiya, dan a zaton su wani abun ne ya rik'e ta.
Cikin kuka tace "aradun Allah ba cutar da Amna mu kazoyi ba, munzo tayata murnan auran tane, dan Allah kuyi hak'uri ku barmu da ranmu, baza mu sake dawowa ba"
Matan Baffa Sule ne ta fara Mata masifa da yare duk da itama a tsorace take, juyiwa tayi ta kalle mutanen da suke kansu tace "kuyi hak'uri kunsan a riga muke kuma bamu tab'a shigowa gari ba sai wannan karan, shiyasa sanyin dataji ya tsorata ta" dariya mutanen falon suka farayi Mommy tace "su shiga d'akin da yake cikin falon zatasa a kashe musu AC, Goggo jiki na b'ari ta tashi suka shiga d'akin, wajen cin abinci ma saida tayi k'auyanci tace baza suci irin wannan abincin ba, k'arshe tuwo miyan kuka aka dafa musu sukaci, Amna tana d'akin da aka sata tare da y'an uwan Zainab kwata kwata batasan wainan da ake toyawa a falo ba
Washe gari Mommy ta turo mai makeup ta tsantsara Mata kwalliya, idan ka ganta baza kace itace Amnan riga ba, k'arfe hud'u aka fara gabatar da Liyafa, taron ya had'a manyan mutane da k'usosin gwammati, k'arfe shida aka tashi daga taro, bayan sallan isha Daddy da Mommy suka had'a su suka musu nasiha mai ratsa zuciya, godiya Ammar yayita musu, Amna kan ba bakin magana sai kuka takeyi dakyar Mommy ta lallashe ta tayi shuru, kafin ta d'auke ta da kanta ta kaita gidan ta da yake Madina questers, bayan futan Mommy ta d'ago Ido tana kallon gidan ta, gida ne daya amsa sunan sa gida, dan tun daga k'ofar gidan zakasan an kashe wa ginin kud'i bana wasa ba, falon takebi da kallo idon ta yana tsiyayan hawaye, dan ba k'aramun b'arnan kud'i Abbah yayi a falon ba, an nuna Mata gata iya gata wanda koda ma'aifin tane iya abunda zai Mata kenan, tashi tayi a hankali ta haura sama raba Ido ta tsayayi dan batasan wanne ne bedroom d'inta ba, d'akuna ne guda biyar a sama ko wanne da key a jikin sa, tana tsaye taji an rungume ta ta baya, da k'arfi tace "innalillahi wa'inna ilaihin raju'un, yayi saurin juyo da ita ya had'e bakin su waje d'aya, Amna jin abunda bata tab'a jiba a rayuwar ta ba yasa ta nutsuwa tana karb'an sak'on sa ganin yana shirin rasa control d'insa daga rarrashi, yasa ya raba jikin sa da nata dukan su suka koma gefe suna mayar da nunfashi, suna had'a Ido ya sakar mata murmushi mai sanyi, ta sunkuyar da kanta tana murmushi k'asa k'asa kaman mai tsoron kar wani ya ganta, hanun ta yaja suka wuce d'akin farko, saida ya zaunar da ita a bakin gado kafin ya shiga toilet yayi wanka tare da d'auro alola, umurni ya Mata da taje ta d'auro alola, ba musu ta shiga tayi alola ta futo, wajen dataga ya shinfud'a dadduma ta nufa ta d'auki hijabin da tagani akai ta saka har zata tada salla taga shigowan sa, gaba da ita kad'an ya tsaya ya jasu sallah raka'a biyu, suna idarwa ya juyo ya kama goshin ta yace "Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira majabaltaha alaihi, wa a'uzu bika min sharriha washarrima jabaltaha alaihi"
"Ya Allah ina rok'on ka alherin ta da alherin daka d'abi'antar da ita a kansa, kuma ina neman tsarin ka daga sharrin ta da sharrin daka d'abi'antar da ita akansa." Kafin yayita karanto Mata duk addu'o'in dayazo bakin sa, tambayoyi ya Mata dangane da addini taba shi amsa, kafin ya d'auko musu kaji da fresh milk d'in daya shigo musu dashi, a hankali yake bata harta k'oshi, kafin ya barta shima yaci,tattare wajen yayi yakai kitchen ya dawo ya cire jallabiyan jikin sa yasa na bacci yace "sweet Amna tashi muje mu kwanta, d'ago kanta tayi ta sauk'e shi akan kwantaccen gashin k'irjin sa, tsikan jikin tane taji ya tashi yarrrrrrr da sauri ta rufe ido da tafin hanun ta, d'agota yayi yana murmushi ya zuge zip d'in rigan ta, a hankali cikin nutsuwa ya cire Mata kayan jikin ta ya saka Mata na bacci, duk abunda yakeyi idon sa yana rufe saida ya kwantar da ita ya lullub'eta da bargo kafin ya bud'e idon sa, shiga bargon yayi ya kwanta tare da jawota jikin sa, bacci yaso suyi amma daya rufe idonsa sai yaji tsikan jikin sa ya tashi, idan ya tuna da laushi fatan jikin ta sai yaji kaciyan sa yana mishi rad'ad'i, abun har mamaki yake bashi na canjawan da yana yin sa yayi yau d'aya, shafa jikin ta ya farayi cikin nutsuwa yana kissing d'in duk inda bakin sa yakai, hanu ya d'aura akan na shanun ta, ji yayi kaman yana shafa auduga tsaban laushi da taushin sa, lumshe Ido yayi yana sauk'e Mata nunfashi a fuskan ta, lakaci guda ya nemi nutsuwar sa ya rasa, Amna ganin yana Mata abu da zafi zafi yasa ta saka mishi kuka, cak ya tsaya da abunda yakeyi yana kallon fuskan ta duk da a duhu suke hakan bai hanashi k'are Mata kallo ba, dakyar ya iya had'a kalmomin bakin sa yace "Amna maiyasa zaki dakatar da dani? Bayan wannan abun bashi bane karon ki na farko ballan tana nace tsoro ne ya sakaki kuka, dan Allah ki barni na futar da abunda ya taru mun a marana na tsawon shekara talatin da uku" janye jikin ta tayi daga nashi tace "Ammar kenan bansan kallon karuwa kake mun ba har yanzu, amma karka manta da abunda ubangiji ya fad'a "bad women are for bad men ands bad men are for bad women and good woman are for good men and good men are for good woman, kasan bazaka tab'a zamowa mutumin kirki ka auri fasika ba, idan ko kallon fasika kake mun tabbas ya tabbata kaima fas....sai kuma tayi shuru ta juya masa baya tare da sake kuka mai ratsa zuciyar masoyi, matsowa yayi kusa da ita ya had'e jikin su wajen d'aya yace "Amna dan Allah kiyi hak'uri ban fad'a haka danna b'ata mana daren mu na yau ba, wallahi ko a gidan karuwai aka aife ki ina sonki haka, ballan tana keda aka aifeki ta hanyan sunna kikayi rayuwa a tsarkakekken waje, taya zan miki gori, ki gafarce ni wannan kalman bazata sake futowa daga baki na ba" gyara Mata kwanciya yayi akan kirjin sa kafin ya sake rufe su dakyau a haka bacci ya d'auke su, da asuba shiya fara tashi saida yayi alola kafin ya tasheta yace taje tayi alola shi zai wuce masallaci, tashi tayi taje ta d'auro alola ta gabatar da salla harta idar da azzakar bai dawo ba, hakan yasa ta gyara gidan duk da ba wani datti yayi ba, abun karyawa taso musu sai tayi tunanin ai ba kayan abinci a gidan, d'aki ta koma tayi wanka ta shafa mae tasa less sky blue ba k'aramun karb'an jikin ta yayi ba, batayi wani kwalliya ba amma idan ka ganta kaima kanka saita birgeka, yana shigowa da fuskan ta ya fara arba, hamdala yayi tayi wa ubangijin daya halicce wannan suran, k'arfe takwas Mommy ta aiko musu da abun karyawa, k'arfe goma kuma su Goggo sukazo Mata sallama, Goggo dataga gidan Amna kasa danne hassadan ta tayi ta saka kuka tace "abunda kullun nakema ya'yana fata yau shine tare dake Amna, lallai Allah ba azzalumin bawan sa bane saidai bawa ya zalincin kansa, Amna ki yafe mun abunda na miki a Riga, yanzu na gane duk d'an gata d'an banza ne, gashi keda na takurawa rayuwar ki daga k'arshe Allah ya d'aukaka darajan ki, su kuma su D'ahare dana nuna musu so ga saka makon son inata girb'a a kwarya na"
Amna ta matso ta rungume ta tace "ki daina fad'an haka Goggo kowani bawa da kike gani da nashi kalan jarabawan fatan mu dai Allah ya bamu ikon cin jarabawan rayuwar mu" basu wani jimaba suka Mata sallamah suka tafi"
Bayan futan su ya futo ya d'aura ta akan cinyan sa duk yadda taso ta sauk'a suci abinci k'i yayi dole haka suka karya tana kan cinyan sa, kullun saiyayi yunk'urin saduwa da ita saita saka mishi kuka, yau suna kwance yace "Amna yaushe zaki bani hakki na?
Tura kanta tayi cikin k'irjin sa tace "sai ranan dana k'addamar da makarantan Tilde da ake ginawa"
Murmushi yayi yace "angama komai dama jibi nakeso muje ki k'addamar dashi, amma wani suna kikeso asawa school d'in?
Shuru tayi tana tunani can tace "Baffa Salihu memorials school" waya Ammar yayi wa masu gina school d'in ya fad'a musu sunan da zasu rubuta mishi a gaban school d'in, itama ta kira Abbas ta sheda masa jibi zasuje Tilde su had'u a Riga"
Yau tun asuba ta tashi ta had'a musu abun breakfast suna gama karyawa suka d'auki hanyan Tilde mutan rigan ba k'aramun murnan ganin su sukayi ba, inda aka damk'a wa Baffa Sule ragaman makaranta, tare da iban Malame, dama Ammar ya bada kwangilan d'inka uniform, kuma suna zuwa suka samu har angama, da hanun ta tarabawa yara uniform d'in da littafe, kuma tace koyarwa kyauta har su gama"
Gidan Baffan su taje taga har angama ginin data bayar su Goggo an baje a ciki anacin arziki, jari ta bata tacewa su Maree da D'ahare ku futar da mijin aure zan muku kayan d'aki, gidan Baffa Sule ma Ammar yasa an zubar an masa ginin zamani, ba k'aramun farin ciki tayi ba da karan da Ammar ya Mata ta sake tabbatar da shi masoyin tane na gaskiya, bakin ruwa sukaje suna k'arewa wajen kallo, Amna ji take kaman ta dawo wajen ta cigaba da rayuwar ta dan Allah ya gani tafi son rayuwar rigan su fiye dana cikin gari da take yanzu, sallama sukama Rigan suka futo har zasu wuce school d'in su tace "Ammar dan Allah mu shiga na gaishe da headmaster" bai Mata musu ba suka shiga office d'insa suka wuce direct suna shiga suka tarar dashi a zaune yayi nisa cikin tunani, Abbas ne yayi ta mishi Sallama tare da buga table d'in, d'ago kansa dazaiyi ya sauk'e sa akan Amna, kallo d'aya ya Mata ya gane ta dan inda ya kwallafa ransa akanta duk canjawan da tayi bazai tab'a mantawa da ita ba yace "Amna Abbas kune?
Amna tace "mune Malam, zamu wuce ne mukace bari muzo mu gaishe ka"
Baki ya washe yace "aiko nagode dama akwai maganan da najima nakeso nayi dake"
Amna tace "Allah sarki gashi kuma sauri nakeyi dan tare muke da mijina"
K'irji ya dafe yace "yanzu Amna amana ta kikaci kikaje kikayi aure?
Ammar ya dube sa rai b'ace yace "kai badda haukan ka wannan tayi maka kalan Matan da zaka nema? Kafin yayi magana yace "ku wuce mu tafi" Amna ta kallesa tace "nagode da gudumawar da kaba rayuwar mu, Allah ya k'addara saduwar mu" suka fuce a office d'in, headmaster ji yayi kaman zaiyi hauka tsaban bak'in ciki, yaci kukan sa daga k'arshe ya hak'ura, dan shi yafi kowa asara a rayuwa ba kaciya ba Amna, dan yanzu kwata kwata kaciyan sa bata tashi"
Suna futowa Abbas ya d'auki hanyan Birnin kudu dan yanzu yana da motan sa da doctor Mansur ya siya masa, su kuma su Amna suka d'auki hanyan Bauchi, bayan sun huta da daddare Ammar yaje da kwad'ayin zai kusance ta amma tak'i fur, haka ya hak'ura bai sake neman ta ba, yanzu har tsawan wata uku da auran su.
Malama Aisha yau ta tashi da zazzab'i mai zafi, Abdallah duk ya kud'ime ya kira doctor Mansur ya sheda masa Aisha bata da lafiya yace ya kawota asibitin sa ya dubata, suna zuwa suka samu Zainab a office d'in ya d'aura Mata ruwa, Malama Aisha tayi kanta da sauri tana cewa Aunty Zainab baki da lafiya shine koki fad'a mun?
Murmushi tayi tace "je a dubaki kizo na baki labari"
Doctor Mansur dubata yayi tare da Mata text result na futowa yaga cikine da ita, a take ya Mata scanned yaga cikin harya shiga wata hud'u, wato ranan da aka kawota ranan Abdallah ya wurga kwallan sa cikin ragan ta, murmushi da Abdallah ya gani akan fuskan sa yasa cikin b'acin rai yace "kufa matsalan ku kenan sai akawo muku mara lafiya tsaban rashin imani ku tsaya kuna mishi murmushi"
Dariya doctor Mansur yayi kafin yace "kuka kakeso nayi Abdallah? Abun farin ciki nagani shiyasa nafarayi tun kafin na sanar dakai, na takaice maka Matan ka tana d'auke da cikin wata uku da sati biyu"
Zainab da Aisha sukace ciki fa kace doctor?
Yace "tabbas ciki ne daku dukan ku biyun" a take suka farama juna kallon kallo "Malama Aisha tace "Aunty Zainab lokacin da mukaje asibiti da Baba akace mun bana aihuwa, ke kuma naji kaman a labarin ki kince mana Umar yaba da ma'aifan ki wa k'ungiyan su?
Zainab tace "nima haka yace mun amma da doctor ya dubani yace ma'aifa na tana nan gashi harna d'auki ciki, ke kuma inaga shine baya aihuwa suka juya ya koma kanki, yanzu sai muma Allah godiya da wannan kyautan daya mana, sannan mu du'ufa addu'an Allah ya rabamu da cikin lafiya" Zainab kasa hak'uri tayi saida ta kira iyayen su ta sheda musu suna da ciki, suma ba k'aramun farin ciki sukayi ba dajin batun cikin...............
***
Mmn Ashfaq