Free chapter · Read without an account
06
*MR & MRS MAIDOKI*
©AzizatHamza2023
06
***
"Dr Mansur maganan yaran nan, akwai alamun sulhu?"
Abbie yayi maganar bayan sun gaisa da Dr Mansur.
Ya damu matuƙa akan auren Adam da Bilkisu dake rawa. Ba kuma dan komai ba sai saboda matsalolin da zai iya shafar 'ya'yansu. Dan broken homes yana shafan mental health na yara, one way or the other.
"Ambassador ka san aure baya ginuwa da I Love You kaɗai. Na yi magana da su duka jiya and abinda na lura shi ne, they still love each other, amma gaskiya they have poor communication a aurensu. Kuma wannan tun farkon aurensu ne har ya girma yanzu ya jawo wasu matsalolin. Babu trust, babu respect a tsakaninsu"
"Dr Mansur Wallahi bana son maganan divorce ɗin nan. Dan Allah ka taimaka musu su samu su resolving matsalolinsu"
"Well, akwai wani special method da nake recommending wa mutane irinsu. 70% idan couples sun yi wannan zaman zaka ga sun resolving matsalolinsu da kansu"
"Tell me, in dai za a samu zaman lafiya ai sai a gwada"
"Adam da Bilkisu suna buƙatar chanja environment"
"Ko zan tura su England, ina da gida a chan"
Dr Mansur ya yi dariya yace " Alhaji Imran ai ba irin wannan environment nake magana akai ba. Za su zauna ne a inda basu taɓa zama ba, a inda basu san kowa ba"
"Ina zuwa" ya ɗauko wani file ya miƙa wa Abbie "Ga terms and conditions na irin zaman da za su yi. Akwai slot uku a ƙasa idan sun shirya tafiya. Ina da slot a Bauchi, Jigawa da kuma Taraba"
Abbie ya karanta bayanan a tsanake ya ɗago yace " this is good, amma ba zan iya yanke hukunci ba sai na yi magana da Alhaji Salihu"
"Ba matsala idan sun shirya sai ka min magana"
Daga wajen Dr Mansur Abbie kai tsaye gidan Alhaji Salihu ya wuce.
Ya samu Alhajin ma na shirin fita dan haka ya dakatar da fitan suka koma cikin gida.
Bayan sun gama gaisawa Abbie ya bashi takardar da Dr Mansur ya bashi.
Alhaji ya karɓa ya ce "gashi ba glass ɗina a kusa, amma bari mu ga"
Sama -sama ya karanta takardar ya miƙa masa yace "Imrana ka faɗa min abinda aka rubuta kawai, abubuwanku sai ku"
Abbie ya ɗan yi dariya yace "Alhaji idon ya fara tafiya kenan"
"Kan ma ya tafi ai, idan ba takardar kuɗi bace ai ba abinda zan gane"
Dukkansu suka yi dariya. Alhaji Salihu ya yi karatu amma degree kawai ya yi kusan shekaru arba'in da biyar da suka wuce, daga nan ya faɗa kasuwanci. Ya bar masu boko da bokonsu
Abbie ya masa bayanin abinda Dr Mansur ya faɗa.
"Har wata shida? Wannan abun zai yiwu kuwa. Ya Babangida zai yi da kamfaninsa?"
"To akwai wannan ma. Amma ina ga ko babu Babangida kamfani zai tafi da kansa tunda akwai management system a ƙasa"
Alhaji yace "Haka ne. Gara su tafi su je su sake koyon darasin rayuwa"
Abbie yace "to yanzu ina za a tura su?"
"Ina ga Bauchin ma ya yi"
"To Allah yasa mu dace"
Alhaji ya ce " komai zai zo ya wuce, lokaci ne"
Abbie yace "Hakane"
***
Duk wani information da kuma shirye-shiryen da ake yi Abbie yana faɗawa Alhaji kuma a hankali da ya ƙara fahimtar yadda abin zai tafi sai ya ji abin ya burge shi sosai.
Duk da dai ya yarda da hankalin ɗan nasa amma gaskiya ba zai iya bada shaidar bai aikata abinda matarsa ke tuhumarsa ba, musamman da ya ji batun rabonsu da mu'amalar aure kusan shekara. Ko shi da tsufanshi yana da lafiyar da shekara ya yi yawa ace bai samu nitsuwa da iyali ba.
Duk abinda ake shiryawa babu wanda ya faɗawa Adam da Bie. Bari aka yi sai komai ya kankama tukunna a faɗa musu.
Cikin sati biyu aka gama duk wani shiri da za a yi. Sai a lokacin Abbie da Alhaji suka yi zama da Adam da Bie wanda a yanzu sun koma kaman kowa zaman kansa yake a gidan. Basa magana, kowa harkan gabansa yake.
Adam ne ma ke ƙoƙarin yiwa Bie magana amma ita kam ta koma tamkar kurmiya. Ta riga ta yi alƙawarin ba zata sake masa magana ba idan ya gaji zai saketa. Idan kuma ya ƙi lokaci kawai take jira da za ta bashi zaɓin ko dai ya bata takardarta ko kuma ta je kotu ta karɓo. Aure kam an gama shi.
Bie ce ta fara cewa ba fa zai yiwu ba lokacin da Abbie ya yi bayanin irin hukuncin da suka yanke.
"Abbie this is not fair, maimakon ka sa baki Adam ya sake ni shine kuke maganar mu zauna tare for 6 months a wani gari. Abbie kana so na yi kisan kai ne"
"Zauna" ya nuna mata inda ta tashi.
"Abbie, Abbie ni 'yarka ce, wannan zalunci ne"
"Ya isa" ya ɗaga mata hannu
Ta kalli Alhaji tace " Baba yanzu zaka iya barin Munnirah ta auri mazinaci?"
Adam ya zaro idanu cike da kunya.
"Bilkisu!"
"Abbie ka barni in yi magana. Na san bani da ilimi sosai akan musulunci, amma na san ZINA da aure babban laifi ne da ya deserving kisa. Ina da shaidar Adam yayi zina da Labiba"
Ta fito da wayarta ta miƙawa Baba dan shine bai taɓa ganin hoton ba.
"Kin san shaidar zina kuwa?. Kin san matakan da aka tsara kafin a karɓi shaidar zina?"
Abbie yai sauri ya karɓe wayar a hannun Alhaji ya ce " wannan ba shaida bace da Allah ya faɗa. Wannan ba shine shaidar da za ki zargi mijinki da zina ba"
Ya sa hannu ya deleting hoton.
"Kar ki sake fito da wannan. Kar ki sake zargin mijinki da irin wannan"
"Ni dai ba zan zauna da shi ba. Babu garin da zan je in yi zaman wata shida da mutumin dana tsana ba"
Duk abinda ake Adam bai ce uffan ba. Sai zufa yake haɗawa. Duk da dai hoton kiss ne amma abin kunya ne Baba da Abbie su ga wannan hoton.
Abbie ke ta masifa yana faɗin dole ne Bilkisu ta yi abinda ya ce. Itama Bilkisu na faɗin ba zata yi ba.
Alhaji yai shiru bai ce komai ba. Ganin Abbie na ta faɗa sai yace " Imrana ɗan dakata"
Abbie yayi shiru yana huci.
"Babangida"
Adam ya ɗago kansa ya kalli Alhaji cike da kunya.
"Bilkisu"
"Na'am" ta amsa tana kallon cikin idanunsa.
"Umurni zan bayar ba zaɓi ba. Ku shirya zuwa Bauchi ranan Asabat mai zuwa. Idan kuma ni da Imrana bamu isa da ku ba sai ku kama gabanku. Duk abinda kuka yi ku sani wasu iyayen kuka samu ba mu ba. Wannan kenan"
Bie da Adam suka kalli juna.
"Ke kuma" ya nuna Bilkisu da yatsa.
Duk irin soyayyar da gatan da ya bawa 'ya'yansa babu wacce ta isa ko ya isa ya yi magana karangatsau babu taunawa a gabansa.
"Yau ya zamo na ƙarshe da zaki sake musayar magana da mahaifinki babu girmamawa. Kina jina"
"Na ji" Bie ta amsa rai a ɓace
"Maza ki tsugunna ki bawa mahaifinki haƙuri. Ni ba zan yarda da tarbiyyan Bature a gidana ba. Mahaifi mutum ne mai daraja"
Bie ta ɓata fuska kaman za ta yi kuka. Ta tsani yadda Alhaji ke yin magana da isa da taƙama. Shi yasa ko lokacin da suke zaman lafiya da Adam ma take kaffa-kaffa da shi. In ba ya zama dole ba bata son zuwa inda yake.
Ta sauka daga kan kujera ta tsugunna ta ce "Abbie, i'm sorry"
Har zuciyarsa Abbie ya ji daɗin abinda Alhaji ya yi. Har ƙwalla sai da suka taru a idanunsa.
"Bana son maganar 'yan boko. Ki nemi gafarar mahaifinki na ce ba Sorry ba"
Kaman ta fasa ihu. Shi yasa tun farko bata shiri da Local Alhajin nan.
"Abbie ka yafe min" ta faɗa tana cursing Adam a zuciyarta dan shine ya jawo komai.
Abbie yace " tashi na yafe. Je ki wajen Babanki ki nemi yafiyarsa"
Ta sake tashi ta je wajen Alhaji ta tsugunna shima ta ce ya yafe mata.
Alhaji yace "Allah ya gyara tsakaninku"
Abbie ne yace Amin dan ita bata amsa ba.
Adam ma bayan Bilkisu ta dawo ta zauna shima ya tsugunna a gaban su Abbie ya basu haƙuri tareda alƙawarin cewa za su yi duk abinda suka ce.
Abbie sai murmushi yake. Duk da bokonsa da kuma zaman ƙasar turai da yayi bai yarda da maganar reni ba. Ya sani yadda aka sakalta Bilkisu tun tana ƙarama shi jawo har ta kai wannan shekarun bata dena wasu abubuwan ba
Suna zuwa gida Bie ta fara sparking.
"Adam ka je ka gaya musu ni ba zan je Bauchi ba. Ba zan iya zaman minti biyar da kai ba balle zaman wata shida"
Adam ya kalleta a fusace. Me take nufi bayan ta san umurni aka basu ba zaɓi ba.
"Kana jina. Ka fi kusa da Alhajinku ka same shi ka gaya masa wannan zama ba zai yiwu ba"
"Look, na san darajan iyaye idan ke baki sani ba. Kuma ina son rabuwa da iyayena lafiya"
"Iyayen da suka supporting zinar da ɗansu ke yi kam iyaye za a kira su ko..."
"Ya ishe ki!" Adam ya daka mata tsawa
Ya nunata da yatsa " duk maganar da zaki yi ya tsaya a kaina. Kada ki kuskura ki sake cin mutuncin iyayena. Ba kuma Baba kaɗai nake nufi ba duk wanda yake da matsayin babba a cikin gidanmu ba zan lamunci ki ci mutuncinsu ba."
"Na sani ni mai laifi ne, amma wannan bai baki damar da zaki zagi iyayena ko ki musu rashin kunya ba. Na yi kuskure da na dinga shiru a baya da kike hakan, amma yanzu kam zan ɗau mataki..."
Yadda yake maganar da masifa sai da ta sha jinin jikinta. This is the first time a shekaru goma na aurensu da ta ke ganin Adam na masifa irin wannan.
Ko lokacin da aka sake video na shooting ɗin nan bai yi masifa kamar wannan ba. A yadda yake masifa idan ta yi tari ma zai iya dukanta. That's how mad he is.
Yana gama masifan ya haura sama ko sauraren me za ta ce bai yi ba.
**
Sai da lokacin tafiyar tasu ta ƙarato Bilkisu ta tabbatar zaman da aka ce zasu yi ba mai yiwuwa bane. Su zauna tare wata shida ba tareda sun dawo gida ba. Sannan banda kayan sawa ba abinda zasu ɗauka.
Ta san kamfaninta zai iya surviving ba tareda ita ba amma kuma ita ce zuciyar AdBie. Sannan yaranta fa. Wata shida zata yi bata gansu ba.
Babu wanda ma ya goyi bayan ƙorafinta na a canja hukunci. Hatta Ya Jamal cewa yayi ta yi haƙuri ta bi maganar Abbie.
Ana ranan Asabat zasu tafi Bauchi amma ba abinda ta shirya. Ko MD ɗinta na AdBie bata faɗa masa zata yi tafiyan wata shida ba.
Ranar Laraba Dr Mansur ya kirasu.
Sai da ta zo za ta shiga motarta motar ta ƙi tashi. Ta daki steering tana faɗin shit!
Ta fito daga motar dan bata san me ya samu motar ba. Maigadi ta fara ƙwalawa kira a daidai lokacin Adam ya fito. Shigarsa na AdBie design ne irin kayan da ta sa. Me yasa zasu yi shiga iri ɗaya yau of all days. Yanzu idan suka je gaban Dr Mansur a haka sai ya ɗauka sun fara shiri ne bayan jiya da dare ma da hawaye ta kwanta.
"Ki zo ki shiga mu tafi"
"Ka barshi zai duba motar yanzu"
Suka haɗa ido ta kauda kai.
"Malam Ɗalha ka koma bakin gate ka buɗe min ƙofa"
Maigadi yace to ya wuce da sauri. Dama shi ba makanike ba mi zai iya yiwa motar. Idan ya ce bai iya ba Hajiyar masifa za ta yi shi yasa yai karambanin fara taɓa motar.
Adam ya shige motarsa ya bar Bie tsaye.
Ta ja tsaki ta buga ƙafa ta je ta ɗau bag ɗinta a cikin motarta ta je ta shiga motar Adam.
Lokacin da suka isa wajen Dr Mansur wani booklet ya bawa kowannensu ya ce duk bayan wata ɗaya a zaman da zasu yi akwai tambayar da zasu amsa a ciki. Tambayoyi shida ne a ciki kowanne tambaya zasu amsa ne bayan sun yi zaman wata ɗaya.
Ranan Alhamis Abbie ya kira Bie. Zama ne na shi da iyalensa dake Abuja. Qaseem na ƙasar waje da matarsa amma Ya Jamal ya zo da matarsa Hauwa.
Batun dai tafiyar Bie da Adam ne.
Bayan dogon bayani ya faɗa musu dokokin tafiyar dan haka ya bada umurnin bai yarda wani nasa ya turawa Bie kuɗi ko abun buƙata ba.
"Abbie sai kace wanda zamu je desert. Ba za ma a kai haka ba ina da kuɗin da zan iya settling bills ɗina"
Abbie yace " that's because daga yau baki da access da kuɗin"
"Ban gane ba. Abbie kuɗina nake magana fa, ba kuɗin wani ba"
"Daga nan zuwa wata shida ba zaki iya cire kuɗi ko tura kuɗi ba. Na sa an yi freezing account ɗin"
"Abbie you're joking right"
"Idan kun je can sai ku nemi sana'ar da zaku yi ku ci abinci"
Dariya Bie ta kwashe da shi dan yanzu maganar tafiyar nan ya fara dawowa kamar shirin film. Gaskiya wannan shirin Adam ne saboda ta dogara da shi ta dinga tambayarsa komai. Wannan kuma ba a isa ba, ko da suke zaman lafiya ma bata tambayarsa kuɗi sai dai shi ya bata dan ra'ayinsa. Balle yanzu da ta ke da miliyoyin kuɗi halaliyarta.
"Abbie ku ce kawai prison zamu je"
" tsakani da Allah babu adalci a wannan tafiyar. So kuke na yafewa Adam abinda ya min kuma ba zan yafe ba"
"Bilkisu" ya kira sunanta da sigar rarrashi
"Babu Uban da zai so auren 'yarsa ya mutu ana zaune lafiya. Na sani Babangida is not perfect, kema kuma haka. Idan kika duba good side ɗinsa sai ki yafe masa a inda ya gaza"
"Abbie it's not possible. I'm hurt. Idan na tuna komai ji nake ƙirjina zai fashe. Da gaske ba zan iya sake zaman daɗi da Adam ba. It's over"
Abbie shima ya ji tausayinta. Har ga Allah maganar da suka yi da Dr Mansur dama idan har suka yi zaman wata shida ba a samu sulhu ba to rabuwan zai fi alkhairi. Wannan yasa ma ya kawo maganar a freezing account ɗinsu duka saboda su je su fara sabuwar rayuwa. Wani lokaci arziƙi ma wata dama ce na kowa zai iya yin abinda ya ke so.
"Baby ina son ki sosai. Ba zan so na saka ki yin abinda zai cutar da ke ba. I want the best for you. Bari ki ji"
Ta goge hawayenta ta ƙura masa idanu.
"In har kika bi dokokin wannan tafiyar kuma bayan wata shida ba ki ji za ki iya cigaba da zama da Adam ba, na miki alƙawarin ni da kaina zan karɓo miki takardarki a wajen Babangida"
"Abbie da gaske?"
"I promise"
Nadeem yace " ni dai na san da cikin ƙanwar Adnan za a dawo"
"Allah ya kiyaye. Ya Nadeem ka dena min mugun fata"
Hauwa matar Ya Jamal tace " nima na yi Amin da wannan addu'ar"
Bie ta fara masifa, Abbie ya ce su dena tsokanarta su yi musu addu'an alkhairi kawai.
Bayan ta koma gida ta zauna ta fara tunanin ya za a yi ta yi zaman wata shida da Adam. Gaskiya akwai wahala. Ko a nan ma da suke kwana ɗaki daban ɗan haɗuwa da suke a falo ko a waje tana jin ɓacin rai balle kuma su je wajen da bata da masaniyar wani irin gida ne, ko tana da separate ɗaki ko kuma bata da shi. In har babu to sai dai Adam ya koma zaman falo ita ta kwana a ɗaki dan babu yadda za a yi ta sharing ɗaki da Adam ko kuma ma ta haɗa gado da shi.
Sai a lokacin ta kira Manager ta ta ce masa tana da meeting da shi gobe.
Da dare Adam ya shigo gidan tana zaune a falo tana jiransa. Ta yi ƙoƙarin kiransa amma numbarsa bata shiga.
"Adam ka ɗauko mana Anwar da Adnan. I want to see my children"
Yadda ta yi maganar ta bashi tausayi. Duk da dai wani lokaci suna zuwa nan ɗin amma yanzu sun fi zama a can family house.
"Dare yayi, gobe zan kawo su"
"Adam ance wata shida zamu yi. Please ka je ka ɗauko su"
Shima jikinsa yayi sanyi. Bai ma kawo maganar yaransu ba dan yana can yana fafutukar yadda kamfaninsa za ta running ba tareda shi ba har tsawon wata shida ne. Ya san yaransa suna hannu mai kyau amma wata shida ba tareda ya sa 'ya'yansa a ido ba babu daɗi. Ba dan makarantansu ba ai sai yace ayi tafiyar da su. To amma...
Fita yayi ya shiga mota ya wuce gidansu duk da kuwa tara ne da rabi na dare.
A wajen Hajiya su ke dan haka sashenta ya wuce. Ya samu Adnan yayi bacci Anwar kuma na kallo.
"Hajiya zan kaisu gida su yi sallama da Mommynsu"
"Babangida dare bai yi ba, da ka bari gobe da safe ai"
"Asabat ne tafiyar Hajiya. Ba lokaci"
Hajiya tace " to shikenan"
Ya shiga ɗaki ya ɗau Adnan a kafaɗarsa ya riƙe hannun Anwar suka fita.
Bai taɓa ganin Bie ta damu da yaran nan irin na daren ba. Kafin su isa gida Adnan ya tashi a bacci suna isa gida shi ta fara karɓa tana faɗin my baby boy.
"My love let's go upstairs" ta kama hannun Anwar.
A ɗakinta yaran suka kwana ta rungumi 'ya'yanta tana jin wani tsoro. Tana son yaranta duk da Nanny Asabe ke musu komai. Bata da lokaci ne kawai amma time to time tana kaisu shan ice cream ko amusement parks. In Allah ya yarda idan suka dawo za ta dinga basu lokacinta sosai.
A baya idan Adam na musu homework ita tana instagram tana replying comments. Yanzu kam tunda idan ta rabu da Adam a wajenta yaran zasu zauna ita za ta dinga duba homework ɗinsu...
**
Irin zaman da Abbie yayi da iyalensa haka Alhaji Salihu ya tara duk iyalinsa dake Abuja ya musu bayanin hukuncin da aka yanke da kuma haɗin kansu daya ke buƙata.
Sun san halin Alhaji sarai dan haka babu wanda yayi gigin maganan hukuncin bai yi ba kowa kuma ya ɗau alƙawarin ba zai taimaka musu da ƙwandala ba.
Mutanen Zaria ma an isar musu da saƙo kuma sun yi alƙawarin bin dokar da Alhaji ya sa.
Daren Jummu'ah sai ga Abbie da Alhaji a gidansu . Nanny Asabe ce ta je ta yiwa Bie magana. Tana kwance da yaran tana musu karatu.
Kayan bacci ne a jikinta. Ta shiga neman Abaya.
"Mommy ga shi" Anwar ya miƙa mata hijabin da ta yi sallar Isha da shi ɗazu.
Ta sauko ƙasa ta samu Adam har ya fito.
Ta zauna ta gaishe su. Duk da kuwa da rana ma sun gaisa da Abbie.
"Gobe za a zo a kaiku inda zaku zauna. Fatanmu shine ku sulhunta tsakaninku kafin zaman ya ƙare"
Adam ya amsa da Amin.
Bie kuwa a zuciyarta cewa ta yi su gama zaman dole su dawo kowa yayi hanyarsa ba.
Abbie ya fito da bundle ɗin kuɗi a Aljihunsa ya miƙawa Adam. Adam ya karɓa yana tunanin kuɗin mene ne.
Alhaji yace "wannan dubu ɗari kenan, ku ɗauke shi a matsayin jari na wata shida. Ku yi amfani da karatun da kuka yi da kuma baiwar da Allah ya baku ku sarrafa shi yadda zai isheku zuwa wata shida"
Bie ta waro ido waje dan bata gane me #100k zai musu a wata shida ba. Ko ita wannan kuɗin ba zai isheta a wata ɗaya bama balle kuma wata shida.
Abbie ya ƙara da cewa " bama buƙatar ku kiramu sai idan akwai babban dalili. Zamu riƙa kiranku sau ɗaya a wata saboda mu san halin da kuke ciki sannan ku yi magana da 'ya'yanku"
Har suka gama maganarsu Bie bata ji a ranta zaman nan zai zo da daɗi ba. Irin waɗannan dokoki ko prison za su je albarka.
Suka musu nasiha akan haƙuri da kuma yiwa juna uzuri kafin suka tafi.
***
"Adam are you sure ba ƙauye za a kaimu ba. Ka masa magana ko ya manta hanya ne"
Bie ta faɗa ganin tafiyar ta ƙi ƙarewa. Har gida wata mota blue sharan ta zo ɗaukarsu. Abbie ya zo da safen har da Nadeem da ke ta tsokanarsu.
Abbie ya nuna musu wanda ya zo tareda Direban a matsayin wanda zai rakasu gidan da aka kama musu a can Bauchi.
Akwatuna biyu manya na kaya da wata jaka Bilkisu ta ɗauka shi kuma Adam jaka ce guda ɗaya.
Ta rungume Anwar da Adnan tana jin kewarsu. Motherhood love ɗinta ne ya motsa har da guntun hawayenta.
"Bye bye Mommy" Adnan ƙaramin ɗanta ya faɗa yana ɗaga musu hannu lokacin da za ta shiga mota.
It breaks her heart ta ji kamar ta fasa tafiyar. A lokuta da dama Adnan zai zo jikinta wasa ta tura shi wajen Nanny Asabe.
Sai yanzu ta lura Adnan ɗinta ya saɓe. Da can ƙato ne sosai dan yafi Anwar jiki, ga shi acici kamar Ubansa.
"Malam anya bamu bar garin Bauchi a baya ba. Sai ƙauyuka muke shiga"
Bie ta kasa haƙuri ta tambayi wanda aka ce zai kaisu gidan da zasu zauna.
Ɗanladi kamar yadda Abbie ya faɗa musu sunansa ya ɗan juyo da kansa ya ce " Hajiya ai mun wuce garin Bauchi tuntuni, Gaɗau muka nufa yanzu"
"Gaɗau" ta furta sunan tana kallon Adam da ya yi kamar bai san me ake faɗa ba.
"Estate ne, ko sunan Lodge ?"
Ɗanladi ya kwashe da dariya da alama idan ya kaisu gidan da aka kama musu ba zata zauna ba.
"Hajiya ai Gaɗau ɗaya daga cikin Lokal Gamman ɗin Bauchi ne"
"A Local Government zamu zauna ba a Capital ɗinsu ba"
Ta kalli Adam tace "Adam ƙauye su Abbie suka tura mu. This is crazy"
Adam yace "Idan ƙauyen ne ba mutane ke zama a ƙauyen ba"
Ta ɗauko wayarta ta fara kiran numbar Abbie amma ba network.
Sun isa garin Gaɗau da yammaci kusan ƙarfe shida ta goce.
Motar ta kaisu har ƙofan gidan da za su zauna.
Bie sai girgiza kai take. Babu yadda za a yi ta zauna a nan.
Motar ta tsaya suka firfito.
"Malam Adam ga gidan nan mun iso"
Bie ta tsaya ta riƙe ƙugu tana ƙarewa gidan kallo.
"Ko a mafarki ba zata iya zama a gidan nan ba"
Ɗanladi ya ce "mu shiga na nuna muku ɗakin"
Bie ta ɗauko waya ta kira Abbie.
"Abbie ƙauye fa aka kaimu. Abbie i thought a cikin Bauchi zamu zauna."
Amsar da Abbie ya bata ya sa ta yi baya kaman zata faɗi
"Abbie i can't do this again. Ba zan iya ba. Ka ga gate ɗin gidan kamar gidan marayu. Abbie baka faɗa min zaman ƙauye zamu yi ba. I didn't agree to this"
Tana can tana ƙorafi Adam da Ɗanladi suka fara shigar da kaya cikin gidan. Adam ma ya yi mamakin inda aka kawo su amma kuma bai raina ba dan ya san a hakan wannan ɗin ya fi wajen wasu.
Kuma shi ba baƙon zama a gidaje irin wannan bane.
Aka gama shigar da kaya Bie bata shigo ba. Tana gama waya da Abbie ta kira Ammie ta saka mata kuka. Ammie dama ba ta ɗaukan shirme ta ce mata maganinta kenan. Ta zauna a gidan ta ji yadda mutanen da basu da gata irin nata ke ji.
Ta kira Ya Jamal ta sake masa kuka. Yana tare da matarsa dan haka bai iya cewa komai ba yace mata zai je Masallaci zai kirata anjima. Bie na jin matarsa na faɗin Daddyn Zahira da wa kake magana ya yi sauri ya kashe wayar. Ya bar Bie da buɗe baki.
Adam ne ya ƙaraso wajenta ya ce "mu shiga ciki"
"Adam this is crazy. Ba zan iya zama a nan ba. Ka nema mana hotel"
"Dare yayi mu shiga ciki, please"
"Malam ba hotel mai kyau da zamu iya kamawa" Bie ta tambayi Ɗanladi daya fito daga gidan
"Hajiya nan aka ce na kawo ku kuma na gama nawa aikin. Idan akwai abinda kuke buƙata gobe da safe zan dawo"
Ya shige cikin mota suka ƙara wuta.
Bata da zaɓi dole ta bi bayan Adam suka shiga gidan.
Ɗakin da suka nufa shine na biyu a ɓangaren hagu. Adam ya buɗe ya shiga ta bi bayan shi tana taɓe baki.
Akwatunanta a tsakiyar ɗakin, can gefe dungun ɗakin kuma wata katifa ce daidai kwanciyar mutum biyu idan ba su da jiki. Sabuwa ce kam dan da leda a jikinta. Ta taɓe baki tana ganin ikon Allah. Ko sadaka aka bawa Abbie ita ba zai sa a kawota kurkukun nan ba.
"Adam Maidoki ba zan iya zama a nan ba fa. Zuwa gobe ka nema mana inda zamu zauna, this place is prison"
"Na ji" Adam ya kunna fankar ɗakin saboda ɗakin akwai zafi.
Bie ta buɗe ƙofar kitchen da ke ta gefen ɗakin. Wani baƙin ɗaki ta gani ba komai a ciki sai sabon 3kg gas da wata tukunya irin ta student a samanta, da alama sabuwa ce dan akwai leda a jiki. Wai wannan lungun ne kitchen? ta sake faɗin This is crazy.
Ta buɗe ɗaya ɗakin wanda take tunanin nan ne banɗaki. "Adammm" ta kira shi da ƙarfi.
Ya sake zip ɗin jakarsa da ya ke son buɗewa ya ce " mene ne?"
"Adam wannan ne banɗakin?"
"Nan ne mana" ya riga ya gani kuma ya san dole zata yi magana. Toilet ɗin na tsugunno ne bana zama ba.
"Adam ba fa zai yiwu ba. Ta ya su Abbie zasu yi tunanin zamu zauna a irin wannan Prison ɗin har na 6 months. Wannan hauka ne. Ko Nanny Asabe ba zata iya zama a nan ba"
"Kin gani dai da idonki akwai ɗakunan wasu a gidan. Mutane ke zama a gidan kamar ki"
"Adam na san wannan plan ɗinka ne. To Wallahi ba zai yiwu ba. Zan koma Abuja gobe"
"Allah ya kaimu"
Tana tsaye ya fara aiki ya ɗau tsintsiya ya fara share ɗakin. Ɗanladi ya musu sharan ɗaki, dake ɗakin leda ne akwai ɗan ƙasa ƙasa saboda ɗazu da suka shigo da kaya basu cire takalmansu ba.
Da ya gama ya shiga banɗaki ya ɗau bokitin dake ciki ya fita dan ya samo musu ruwa.
Bie ta zauna gefen katifar tana ta ƙoƙarin kiran nambobin Abbie amma basa shiga. Ƙila ma blocking ɗinta ya yi. Ga shi ta san halin Alhajinsu Adam ba ya ɗaukan ƙorafi balle ta kira shi.
Tana zaune Adam ya shigo da ruwa a bokiti ya je ya kwara a banɗakin sauran ya kora toilet da shi. Daya gama ya sake fita ya ɗebo wani.
Kusan kaf dangin Abbie na kusa da shi da ta san Abbie na jin maganarsu sai da ta kira wasu basu ɗauka ba, wasu kuwa cewa suka yi hukuncin da Abbien ya ɗauka daidai ne.
Adam kam babu ruwansa. Zuwa ya yi ya watsa ruwa saboda ya rage gajiyar tafiya. Ya fito ya saka jallabiya ya ce mata zai je ya nemo abinda zasu ci.
Jikinta ƙaiƙayi yake ga gajiyar tafiya amma ƙyanƙyamin banɗakin da kuma rashin ruwan zafi yasa ta zauna a haka tana tunanin yadda za a yi su zauna a wannan kurkukun har wata shida. Ba zai ma yiwu ba, idan ba za a canja musu gida ba ko su koma cikin Bauchi to ta haƙura da zaman sulhun.
Sai kuma ta tuna gargaɗin Alhaji. Idan suka ƙi zaman sulhun nan to su nemi wasu iyayen ba su ba. Alhaji yana da influence akan Abbie dan haka zai iya sa Abbie ya yi fushi da ita har ya fita a lamarinta.
Duk da zata iya riƙe kanta but idan ta bar gidan Adam kuma Abbie ya hanata zama a gidansa zaman kanta zata yi kenan?. Su Anwar da Adnan fa?.
Bayan kusan awa ɗaya sai ga Adam ya dawo ɗauke da ledoji.
Take away na abinci ne sai goran ruwa da fanta.
"Ga abinci"
Ta kalli kayan da ya kawo ta kauda kai.
Ruwan goran ta ɗauka ta sha. Fitsari ta ke ji dan haka ta yi ta maza ta shiga banɗakin ta yi fitsari ta yi tsarki da ruwan gora. Ta sake fitowa ta ɗau ɗaya goran ta shiga ta yi alwala da shi.
Adam na ganinta bai ce komai ba dan ruwan guda huɗu ya siyo kuma ta yi amfani da biyu.
Abinci yake ci yana lissafin yadda zasu yi da kuɗin da aka basu. Akwai yadda za a yi ya assessing kuɗin dake ɗayan account ɗinsa amma tunda ya yiwa Alhaji alƙawarin da abunda aka basu kaɗai zasu yi amfani shi yasa ba zai taɓa wancan kuɗin ba.
Bie ta zo za ta yi Sallah ya nuna mata fuskar alƙibla dake ɗakin. Thank God Nanny Asabe ta saka mata sallaya cikin kayan da ta shirya mata
Data idar da sallan ta ɗau take away pack ɗin daya bar mata dan yunwa take ji sosai. Jollof rice ne da nama yanka biyu. Ta kai abincin baki sai ga shi ta tufar.
"Adam miye wannan?"
"Ba zaka iya siya mana abinci mai kyau ba"
Ya kora fantarsa ya shareta.
"And kasan bana shan fanta me yasa ka siyo?"
Ita kaɗai ta gama maganarta. Dan uffan bai ce mata ba.
Fantan kawai ta sha ta kwanta lokacin Adam ya shimfiɗa musu bedsheet daya siyo tareda abincin.
Barci gagarar Bilkisu El-Sayed ya yi. Gadon ya musu kaɗan gashi da ta ɗan yi motsi sai ledar katifar yai ƙara. Ga jikinta da ya ke ƙaiƙayi. Ta cire kayan jikinta ta sa kayan bacci amma bai taimaka ba dan wanka take buƙata.
"Allah ya isa na Adam Maidoki. Duk laifinka ne"
Bai ce mata komai ba ya juya fiskarsa ya cigaba da kwanciyarsa.
Ta cigaba da danna waya har sai da cajin wayar ya ƙare wayar ta mutu.
Bacci kam babu a idon Bie. Kusan ƙarfe ɗayan dare baccin gajiya ya fizgeta.
Wajajen ukun dare wani gurnani ya tasheta.
"Ohh! Umm! Ahh! Ahhhhh! Papa James you get am, continue dey knack oooo... ewoooooooo, chim ooooo"
Bie ta rufe kunnenta. Wannan wasu irin neighbors ne haka suna abu kamar mahaukata.
Nishin mijin da surutun matar ya shiga kan Bie ya hanata bacci. Ji tayi kamar ta je ta watsa musu ruwan zafi.
Ta shiga bubbuga Adam.
"Mene ne?" Ya tambaya da muryan bacci
"Ka je ka musu magana, suna damun mu"
Adam ya sa kunne ya ji nishin maƙotan nasu ya ja tsaki.
"Ka je ka musu magana please"
"Na je na ce musu me?"
"I don't know"
"Idan kina da abin faɗa kya iya zuwa da kanki ki same su" ya juya ya cigaba da baccinsa.
"Adam, Adam"
Ta jawo filo ta danne kunnenta tana tsine musu. 'Yan iska sai kace sun fi kowa iyawa, sun bi sun dami mutane...