Free chapter · Read without an account

13

by Nana Disoo · LATYFAH IMAM

13


LATYFAH IMAM


  Nana Diso


GIDAN YARI


  Bayyanawa ko labartawa bazai taba baku damar fahimtar yaya wannan gidan yake ba, ina kara tunasarmuku mu bangaren mu bangarene na masu laifi dan haka yakasance hukuncin mu da ladaftarwar da ake mana tafi ta duka wanda suke wannan gidan yari, bazan ce muku wasu basu da katifa ba amma abangaren mu banga mai ita ba, to ina ake maganar katifa ma? Akwai tashin hankular dana gani wanda har yanzu idan natuna sai gabana yafaɗi, tabbas nakula ba'a shigowa da kwaya ko wani abu na bugarwa wannan gida amma kuma abun tsoron danagani shine ganin wasu group na mata suna shaye shaye? Nan nashiga tambayar kaina to a'ina suka samu? Ta'ina aka basu? A she acikinsu wata akaje kotu sharia to bayan sunfito daga kotun sukayi dabara suka karba! Kaicona kaicona shine abunda nake yawan ambata saboda mummun gani da nake yawan yi, wai har acikin wani gidan za'a iya samun mutum mra imani da zai dunga lalata da mata? Kowaccen mu idan kakalleta idan bakayi mata kuka ba to tabbas zaka godewa Allah da yanayin dakai kake ciki. Anacewa rashin ruwa mai kyau zai hanaka samun lafiya? Uhmm shine abunda nake yawan faɗa dan ɗangata agidan kurkune zakaganshi da pure water shima bantaba ganin wanda yasha guda daya ba sai dai naganshi da rabi saboda mutum bayida ikon ya shanye shi shi kadai, shimafa sai dai ƴan uwankane sukazo shine zasu kawo ma. Ku kaddara yadda zakuji idan kukayi kwana daya babu wayar da kukayiwa sabo da'ita yaya.kukeji? Babu masoyanka babu fita babu zuwa inda kaga dama yaya zakuji? Gidane da bazan iya muku bayaninsa ba bazakataba jin daidai ba sai har ka fito daga gidan, Gidane da yake tattare da doka da oda wacce dole ne binta ko kuma kasamu horo mai tsanani idan akace kayi kwasar kashi ko tsinta ko shara wannan babbar ni'ima ce agurina da ayimaka bulallar da za'a a kayyade maka, rashin bin tsari ko abunda akace zaisa ka haɗu da mai horo, a ɗan zamana danayi masu bashi sunfi zuwa gidan yari kamain kaga an danna barawo a bangaren dana fara zama da wahala amma zaka bashine yakawosu, saboda basuda halin biya, akwai matar datacemin akan dubu goma take cikin gidan yari har yanzu watanninta 7 babu wanda ya dubeta kuma batada hanyar bayarwa, ahaka idan ka hadu da gurbatattu dai kuga dabi'ar mutum gaba daya ta canza. Aduk halin da kuke ciki ku godewa Allah kukara godewa Allah, zaman lafiya da kwanciyar hankali yafi komai acikin rayuwar mu.

A bangaren gomnati tana kokarin gurin bamu tallafi da tsaro sosai amma kuma sai kayi tunanin babu wani abu muke samu acikin wannan gida. Tundaga ranar da sir tahir yazo sai ladi ta sassautamin sosai, wani lokaci har abinci take bani aboye bansan dalili ba bankuma taba tambayar ta dan niɗai yanzu ta ƙaina nakeyi. Ina cikin wata iriyar jarabawa da numfashin da nake shaƙama yafi komai wahala gareni, yadda jiri da amai suka aure ne, amma da zarar nasamu abinci sai na warware bansan me isa duk lokacin da anty ladi ke da duty ba bata barina nayi aikin komai, amma dazarar tatafi masu duty sukazo to tabbas sai numfashina yafara gushewa kamin a cillani daƙi arufeni. Satin mukasamu masu ziyara sukazo acikin wannan ayarin akwai fuskokin da nasani sosai amma kuma su basu ganeni ba, akwai dayama da nagani sai anyi mata murmushi sai cewa Tayi sannu Allah yabaki lpya yafiddake, atake hawaye ya wankemin fuska dan ko ban faɗa ba na lura kallon mahaukaciya tayimun, ranar sunkawo mana abubuwa dadama harda maggi da barguna, da darakto yasanar mana nan muka shiga murna muna ihu muna faɗin " Allah saka Allah sassaka mungode." Wasunsu sunfita da kuka sosai wasu kuma sunfita da hawaye. Duk yadda na lallace na jeme akwai waƴanda idan nagani sai na fashe da kuka saboda Lalura suke da'ita dake sassakarsu, akwai masu cancer akwai sugar akwai abubuwa da dama na daga cutuka.


  Sautin kukana ne kitashi aharabar gurin da muke kwashe dattin dake bayan prison din, sosai nake ciƙin damuwa saboda zazzabin da nake fama da'ita yadda na sulale a hankali yasaka anty bandi zubamin bulala na firgita na bude idona nan kuma anty ladi suka shiga taimakamin akayi daƙi dani, ranar nidai sama sama nakejin kowa wannan tsohuwar ɗakin tamu ce zaune a kusa dani tabani ruwanta nasha ashe tanada abinci bansan inda ta samu ba amma kina ganin wannan ƙinsan bana ciƙin gidan yari baniba tabani nasha nan ta bude baƙi tace " ki kula ƴata kada ki illata abunda ke ciƙinki kinga yanzu yafara kwari inaji ma watannin da suka rage miki ƙadan ne." Da hanzari na.ƙalleta nace babah bangane mekike nufi ba?" Murmushi tayi na manya tace yau ince watanninki 7 da sati uku zuwanki gidan ko?" " Eh babah." Anty lady tace to ki kula dan cikine dake har yashiga watannin nan." " Ciki kuma wata 7 wanne irin ciki kuma wannan wacce magana kuke mun? Wallahi banida ciki nifa lukutace ramewa nayi shiyasa kukaga tumbin." Anty ladi ce ta daka min tsawa tana faɗin ke wai bakida hanakali ne? Nace bakida hankali cikine dake kuma dashi kikazo gidannan mijin naki da kika kashe shi yayi miki. " Ranar anga tashin hankali agidan yari dan kuwa duk wata macce dake bangaren mu sai ta tausayamin yadda nasamu wani karfe nashiga duƙan cikina Ina kuka ina banaso natsane cikin wallahi sai dai mu mutu nida cikin natsani duk wani abu da ya danganci zuri'ar mai lema bazan taba haihuwar ciki ba, dakyar akasamu aka kwace abun amma yadda nayiwa ƙaina rauni yasa baccin wahala ya kwasheni!...


********


Tunda amiey takira hamid tagayamasa halin da ɗan uwansa yake ciki shikenan yarasa nutsuwarsa gaba daya, yini yayi yana bincike tare da waya dasu mutanen duk aƙan matsalar aliyu, ko gidan bai dawo ba sai bayan ƙarfe tara na dare, da ya dawoma kasa bacci yayi yashiga yin ibada sosai da gayawa Allah matsalar ahalinsa, ko da yagama sallah anan bacci yayi gaba dashi, da Asuba ma da ya farka kokari yayi tare da sallah da azkar kamin yadawo gida, yanayin sallama a palour ɗin yatarar da mahaifinsa zaune yana aikin acikin system dinsa, har kasa ya durƙusa yana faɗin barka da safiya dady." " Barƙanmu hameed kaceke foam dinnan kuwa?" " dady bancike ba saboda bansamy nutsuwa ba jiya umar da amiey sunƙirani akan Aliyu nashida lpya." A zafafe dady yace " Dan Aliyu bashida lpya shine zakajawomin asarar maƙudan kudi? Yaje yayi shaye shyensa nabanza da wofi kwakwalwarsa ta rikece shine zansaka shi araina so kukeyi ciyon zuciya ya kamani na mutu kenan?. " Wallahi aliyu baya shaye shaye dady Nidai nafi tunanin shafar aljanune." " Jiya mumyn ku tace min har fasa mata ƙai yayi akayi asubuti da'ita. " shiru hameed yayi yana nazari kamin yace " Yanzu dady kuna waya da mumy kullum amma amiey har rasa ɗa tayi bazaka kirata ka rarrasheta ba, yanzuma tana cikin damuwa amma bazaka kira kaji yadda take, da ba haka kake ba, komai halin ammy batada ikon canza kaddarar kowa tunda haka tata kaddarar tazo ka tayata gurin addu'a da kwarin guiwa." " Hamid kasan yadda nakeson uwar taka dakake karewa tunda muka bude wayoyin mu ta dannawa numta blocking kagani ya nunawa ɗan nasa yana ganin yadda kiran yashiga aka kuma katse alamun anyi blocking, to yakakeso nayi ko jiya da suka sanar dani cutar aliyu na kikkira amma still arufe laila ma arufe, ya kukeson nayi ne ita mumy bagashi kullum tana kirana ba abaƙinta naji abunda ke gudana agidan bansan mai ke damun faɗima ba, kuma Allah na ganin kokarina akan kowa ai, wannan wahalar da nakeyi ai duk dan ku nakeyi amma bakwa gani kazo ka titsani akagaba kanamin fitsara akan matata." " kayi hakuri dady bari nashiga ciki."


Kakirani sai faɗa kakeyi hameed menene wai? " haba ammy yazakiyi blocking din dady? Daman tunda mukazo bakuyi waya ba?" " Au tanan yabullo maka? Bai ƙirani ba dai hamid ɗana fa aka kashemin amma yakiramu yaji yaya muke baiyiba." " ke me isa bazaki kirasa ba ammy?" " Wayake kiransa agidan nan umar ma yace basa waya kwatakwata mumynku ma tace basa waya." " Wacce mumyn?" " mumynku dai!" " Ita tacemiki basa waya da dady?" Ko jiyama inaji tana cewa lailah bata samun dadynku, rabonta dashi tunda yatafi. To Allah yasawaka, babu wanda yasan dai halin da ali yake ciki ko?"

Eh babu wnda yasani kasan ya fasawa mumynku kai tace kadataji kada tagani agayawa wani ko da kuwa dadynku ne." Murmushi yayi yace yanzu dai kicire wayar dady daga blocking please! " wanne blocking kuma?" Duba kiga yafaɗa " Garin yaya aka sakamin wanene yasaka?" " Ki kula ammy akwai munafukai kusa dake ki kula sosai yanzu tashi kisaka hijjabinki banaso ko laila ki gayamata inda zakije. " kasan dai bazan fita momynku bata sani ba " " you have to do this ammy kada ki sanarwa kowa tafi daƙin aliyu kina shiga ki nemi tsarin Allah da karfi." Gabanta na faduwa ta nufi bangaren da dakin aliyu yake ko data shiga nan ta tarar da aliyu yana wani irin gurnani cikin murya mai ƙarfi tayi bismillah. " ammy karanta falaki da nasi da karfi da Ayatul-kursiy yanzu zai wadi kokuma yayi bacci." Cikin daga murya tashiga karantawa sai kuma yafara wani irin surutai " Ni bance zan masa komai ba to inbanda an aikoni me zanyi masa ajiƙinsa nifa babu abunda zanmasa fa. " Karkiji tsoro ammy rike hannunsa kutafi." Cikin kaduwar ciki tace " Am afraid hameed." " Karkiji komai babu abunda zaiyimiki kicigaba da ambaton Allah. To ta amsa masa tarike hannun aliyu duk da jiƙinta dake faman rawa kamar mazari sai da suka shiga mota ta fizgi motar tabar gidan. Tana hawa titi wayar mumy tashigo " Ammy ina kika tafi hankalina yatashi yadda kika fizgi motarki danAllah kidinga kula." " wata ƴar kawatace babu lafiya shine fa nafito asubuti ƙinga ma natawo da aliyu yaga likita." " Subhnlhi Allah yabata lpya ku kula danAllah kada aliyu ya cutamiki." " Inshaa Allahu zan kula mumy nace ko zakisa asabe tadanyimun abu mai ruwa ruwa." " To badamuwa bari na sanar da'ita." " Yauwa nagode mumy sannan ta katse wayar. Kiran hameed ne yakara shigowa mumy dawa kike waya lokacin dady fa nake shiga wallahi zai iya saɓamin." " Mumy ce takirani nace mata naje duba ƴar kawata." Murmushi yayi yace yauwa ammy yanzu kun karasa layin mangarorin?" " Eh mun karaso gamu daidai layin." " To tambaye malam mamman." Nan ta tambaya aka nuna mata gidan. " Allah yasa karshen wahalar ce ammy kada kisanarwa kow inshaa Allahu aliyu zai warware kiyita masa addu'a malam mamman indai harkar aljanu ce akazo gurinsa da yardar Allah ta kau" barka da zuwa almajirin gurin suka shiga yimusu ihun da aliyu yashiga yi shiyasa almajirin rirrikeshi ana shiga dashi farfajiyar gidan malam. Hajiya barka da zuwa matarsa tafaɗa. " Ina wunin mu?" " lpyalou ya akaji da lalura? To ubangiji yasa karshen wahalar ce tazo." Da mamaki ammy tace Ameen. Malam mamman ma yazo suka shiga gaisawa. Wannan ne kenan mai larurar? Bismillahi rahamanir rahim! Nan yashiga karanto surorin alkur'ani da yafara a hankali sai yashiga yi da ƙarfi!.

" Wayyo kadaina konamu zamu fita zamu fita, kadaina wayooo kana konamin fuska kana konamin kafa zanfita zanfita."

" Wacece ke?".

aikomu akayi jiƙinsa. "

Ku nawa ne?.

" Mu biyu ne."

" Me Aka aikoshi kuyi masa?" Shiru sukayi basu kara magana ba dan haka malam yashiga karatu sosai yaƙusan mintuna 30 yanayi kamin tayi magana tace " ka konamin miji ka karyamin kafa kuma munce maka zamu fita aikomu akayi mu sakashi yadinga sata nikuma insakashi yadinga hauka har ya haukace!.

" Ta yaya kuka shiga jiƙinsa?"

" Ai shiga jiƙinsa bazaiyi mana wahala ba ɗan baya addu'a sallah ma sai yaga dama yakeyi, ko addu'ar bacci bayayi da addu'ar shiga bandaki, baya komai sai jin wakoki kuma ma aikamin mu akwai wasu aljanun ajikinsa dan dai ka konasu, baya ambaton Allah sai jin wakoki da wasa da sallah kuma ko munfita wasu za'a aiko masa."

Karatu yacigaba dayi har sai da aliyu yayi wata hamma haɗe da atishawa kallonsa malam yayi yace " Malam aliyu."

Zubawa malam ido yayi yana kallonsa. Ammy dataketa kuka yaƙallah yace " Ammy inane nan? Me isa kike kuka ammy me akayi miki."?

" Saurareni malam aliyu zan maka nasiha da ka Kula da ƙanka sosai ta bangaren ibada da ambaton Allah ko da wasa kada kabari zikiri ko ibada ko sallah suna huce muna mantawa acikin duniyar nan munada wasu halittun da bama ganinsu acikinsu suna akwai azzalumai. Nan yabashi magunguna haɗe da yimasa nasiha suka kama hanya suka tafi." Tun ahanya ammy takira hameed tana shimasa albarka. Tabbas ta yarda ita cikakkiyar marainiya ce Amma haihuwa yau tayi mata rana!


*****




Hajiya marsi kinganni nan murna takusan yimun yawa yaro dai ya zube ingayamiki aljanu yakeyi nasan nan da sati daya ya haukace!. " " Kai kawata bakida dama yanzu sai da akayimiki aikin?" " Mijinma na harhada mata sharri agurinsa wayoyinta na karba na dannah masa blocking nasan zafinsa akan haka wallahi sai ayi saki." " gaskiya kawata bakida dama." " hmma akwai abunda nake shiryawa ai danagama zakiji labari mai dadi dan kuwa nasan rabuwa zaiyi da'ita daga ita har ƴaƴan nata babu wani mai addini acikinsu sai shagala da rashin ibada." Kice bazasuyi wahalar asiri ba." Haka malam yace bari zan kiraki.


****


Babban offices ne zaune yake yana juyawa akan kujerarsa yana wata banzar dariya a hankali kuma yajiyo yace " Nagama Nagama da babinka har abada Abdul!!!.saura hamid da sauran yafada yana dariya mai cike da izzah irintasa."


***


ALHAJI AUWALU DOGO

GIDAN ABIEY


Hajiya kubrah kinkira baki sameni ba ina can aiki nakeyi. " Haba nifa nace inata kira baki daga ba, nace yaya alkawarin mu wannan abu da za'a hada antyn maryam bafa nikadai zai amfanar ba har dake! Idan ba zaki Mike tsaye kisan yadda zaki shiga kifita yusufa ya aure kursum kiyi dan baban kursum yazomin da wata maganar banza wai yayansu yace bai taba soyayya da kursum ba, karki manta Anty nina shiga nafita kika aure alhaji auwalu wallahi idan bakiyimun da gaske ƴata tashigo cikin wannan zuri'ar ba to tabbas zanyi duk wacce zan kema ki fita." Cikin Anty ne yaƙada tace " bazamuti haka ba hajiya kubrah kibarni dasu idan sunsan wani abun ai basu san wani ba." " To yanzu naji magana ai sai anjima ina sauraronki.

Innalilahi wannan masifa anty tafaɗa tana barin gurin daƙin ummy tashiga tana mata sallama ummy ta amsa mata da fara'a " Kinganni nan nadawo ummy namanta bangayamiki ba jiyafa mafarkin yayansu nayi wai ya auri kursum amina tanata farinciki da murna acikin mafarki ni wallahi tsorona yanzu kenan kada ma yaje ya auro mana wata yarinyar da bazamuji dadinta ba." " Nima haka nake tunani anty nayi tunanin ko zasu daidaita da kursum din ko?". Murmushi anty tasaki tace " Ashe dai tunanin mu yazo daya daƙe kenan." " To ai yafi masa kowa yasan gidansu amina gidan tarbiya ne, Amma kinga wannan kakartawa ta damu akan a haɗasu da ƴar gidan yayan nan nawa asmah." Gaban anty ne yawaɗi tace " To ummy sai muyita addu'a ALlah yazaba musu abunda yafi Alkhairi." " munatayi."

Baro daƙin anty tayi wani ƙunci yana cika mata zuciya ƴar gidan yayanta na riyadh mai ɗan banzan kudin nan ai wallahi ko hauka zatayi sai ta hana abunnan tabbata tabbijan shikenan ai sai yayan nata yaciga daji da'ita darajar yusuf din ai ƙaruwa zatayi.


******


USA


Inajinka malam yakubu, Nidai nacemusu nasanka kuma kai kaɗaine zaka taimaka musu batare da wasu kudaɗe ba yanzu ma haka kakar yarinyar Kosai takeyi tacemin sun hada dubu dari biyu yanzu harda hamsin! Haka ma lauya daya yaci musu dubu sittin!


Gyara kwanciyarsa yayi yace " Malam yakubu bawai bazan taimaka musu baniba amma ina nan tare da abiey kuma kasan halinsa sarai akan kasuwancin sa, kuma kaga ni Bason yin shari'ar nan nakeyi ba idan bai zama dole na!.


Dan Allah danAnnabi kataimaka musu nan makota nane yarinyar tana cikin jarabawa alhaji yusuf da Allah idan bakai ba ba lallai asamu lauyan da zai iya ja da gidan yaron. " Kana amatsayin ubanane malam, inshaa Allahu zan duba nagani zakajini zuwa gobe." " Allah yasaka da alkhairi.


Daga nan fitowa yayi daga daƙi nana tana class dan haka shinkafa da wanken da yadafa yazuba ya tawo palour nan yaga abiey da alama yanzu yashigo. " mikomin abincin naci wannan turawan suna cazamin kwakwalwa yusuf " " Nima haka abiey yafada yana shafa ƙeyarsa tare da bawa mahaifin nasa abincin yafaraci. " wato kaidai ka.koma ɗan gargajiya yusufa daga wake sai tuwo ko dayake ka huta ai. " abiey danAllah ina neman Alfarma zanje na gabatar da wata shari'a karshen wannan watan sai nadawo." " nimafa alfarma na rokike ka tsaya mugama mu koma daga ƙarshen watan gaba mungama ai sai nana da zamu jira ita sauranta wata 2, maganar shari'a kuma ka wakilta wani yusuf. " To abiey inshaa Allahu zan waƙilta."


*******


GIDAN ALHAJI MAI LEMA


Tunda suka dawo aliyu yake bacci har mumy ma tazo tadade tana tofa masa addu'a kamin taje ta kwanta, Ammy kuwa na shiga daƙi tashiga kiran mijin nata kamar yadda ɗanta yafaɗa mata!.


Assalamu alaikum!!! Dady yafada da alamun bacci amuryarsa.


" Saboda baka sano ɗana ya mutu dayan bashi..." " kiyi hakuri danAllah laifinki ne amma na ƙarbi lefen! Inaso ki biyo jirgi a satinnan kizo ina mararinki ke bakiga hakurin mijin naki ba!. Dariya tayi tace " Nima ina kewarka mijina." " Allah yayi miki albarka ammyn hameed yabaki ladan rashin ɗanki, shikuma aliyu yabasa lafiya!. " Sosai taji dadi aciƙin ranta nan tashiga zuba masa shagwaba yana biye mata daga karshe ma yace nan da 3days zata tawo."


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.