Free chapter · Read without an account
01
*2023.*
#PaidBook.
__________________________________
BISMILLAHIR-RAHMANIR RAHIM. dukkan yabo ya tabbata ga Allah (S.W.T), ina gode masa, ina neman agajinsa da gudunmawarsa da taimakonsa. Salati da sallama da ɗaukaka da daraja, su tabbata a bisa manzonmu Annabi Muhammadu (S.A.W), cikamakin Annabawa shugaban mazanni, wanda Allah ya aiko domin ya zama rahma ga al'umma. Ina roƙon ya Maliku da ya ba ni ikon rubuta abin da zai amfanar da alumma, ya hane ni rubuta abin da zai ruguza al'umma, Ya Hayyu Ya Qayyum yanda na fara lafiya kasa in gama lafiya._ __________________________________
Ga masoyana kuma makaranta littafaina, ba ni da bakin godiya gare ku, ba zan gajiya da yi muku addu'a da godiya ba bisa goyan bayan da ku ke ba ni, Allah ya faranta muku ya yafe muku zunubanku, yasa ku gama da duniya lafiya, masu fuskantar ƙalubale a dalilin jinkirin aure ubangiji yasa hakan ya zama alkhairi babba a gareku, haka masu fuskantar ƙalubale a zamantakewar aure Allah ya gyara lamura...A wannan karon dai tafiyar ta dabance, kusa kuɗi ku siya, ba zaku yi nadamar siya da karantawa ba, a nuna min son so...har kullum ƙofa a buɗe take domin karɓar saƙonninku._ _______________________________
All rights reserved. No part of this book may be reproduced or transmitted in any form without seeking permission from the writter. This novel is a work of fiction, Names, characters, business, places, events, and incidents, are either the products of the author's imagination or used in a fictitious manner. Any resemblance to actual persons, living or dead, or actual events is purely coincidental. A person who commits an act of piracy, is liable on conviction to life imprisonment and a fine of not more than N50,000,000...So becareful of copying any part of this story._* ©Copyright2023 Halima.hz
_________________________________ SHIMFIƊA.
_A wasu lokutan da bamu tsammaci rikicewar al'amura ba, sai ya zamana al'amuran sun runcaɓe mana babu zato babu tsammani. rayuwa kan canja tayi juyayi da mutum, wasu ta juya da su duniyar rikicewa, firgicewa da tashin hankali har mutum kanji tamkar shi kaɗai aka tsana, yayin da a gefen wasu juyin rayuwa kansa su mance da baƙin ciki, haushi, da damuwa, su dulmiya a jin daɗin rayuwa. babu abin da bai da farko, babu abin da bai da asali, haka babu abin da bai da tushe, kazalika babu abin da bai da ƙarshe, sai dai yarda da Allah kan tafiyar da komai cikin daidaito._ _kamar dai yanda darasi ya ke a matsayin koyarwa da miƙa saƙo, hakan yasa a yau zan rubuta labarin rayuwarmu, sunana Sa'ida Salman, kuma wannan shi ne labarin ƘAYAR RUWA..._ ________________________________
(1)
Kwance na ke akan makeken italian royal bed a cikin tamfatsetsen ɗakin barcina. Wayata ƙirar S22 na gefena ina sauraren karatun alqur'ani mai girma, cikin ƙira'ar Muhmood Hosary, idanuwana a lumshe suke tamkar mai bacci, sanyin acn da ke busawa na bin dukkan ƙofofin gashin jikina, yayin da gefe guda hancina yake shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren wutar da na kunna a burner, wanda ba ya ko ƙaurin kamawa saboda irin salon yanda nake bi wajen ƙona shi.
Sanye na ke cikin doguwar rigar material mara nauyi, rigar na ɗaya daga cikin sutturun da nake so sosai a kayana. Material ɗin ba wai mai tsada ba ne, fuskata fayau babu kwalliya ko ɗiso, sai hakan ya ƙara fito da ramar fuskata. Gaba ɗaya yau ɗin jina nake yi kamar mara lafiya, kuma kaman an yi min mutuwa, sai dai babu ko ɗaya a ciki, tun safe dai da na tashi bakina babu ɗanɗanon komai, ga tsananin faɗuwar gaba na damuna.
Hakan yasa tun lokacin nake ta addu'oi da tasbihi, kuma karatun ƙur'anin da na kunna ina saurare ina bi shi yake ɗebe min kewa, to amma dai duk da hakan ina ji a jikina cewar akwai wani babban al'amari da zai girgiza duniyata nan kusa, ina jin kamar nan kusan zata zamar min ƙarshen komai na rayuwata ne.
Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi, na juya kwanciyar da na yi inda a yanzu na ke fuskantar bakin ƙofar shigowa, cikin zuciyata ina roƙon ubangiji da yasa komai zai faru ya zama alkhairi, ya kuma ba ni ikon cinye kowacce kalar jarabawa da iya ɗaukan ƙaddara.
Zoben azurfar da ke hannuna na ke ta kallo ina jin wani abu mai girman gaske na tsarga min, yayin da tunanin wasu shekaru yasa fuskata ƙwacewa da murmushi mai faɗi, murmushin da za'a kira shi da na yaƙe.
Wayata na ɗauka don duba lokaci, ƙarfe biyar da mintina na yamma ya nuna min, zaune na miƙe da mamakin gudun lokacin a cikin raina na furta "Har biyar? Lallai duniya na gudu, Allah kasa mu cika da imani".
Da azama na zuro ƙafafuna ƙasa ina gyara ɗaurin ɗan kwalina, ji na ke kamar zan faɗi saboda rashin ƙwarin jiki, kaman wadda ta sha zawo ya zabgar da ita a yini ɗaya.
Na tsaya gaban tafkeken madubin ɗakin, ina ɗaukar tissue in shiga goge kwantsar ciki, saboda ciwon idon da na ke fama da shi daga shekaran jiya zuwa yau.
Na tsaya kallon kaina a cikin madubin, lallai in har akwai rayuwa da shekaru to tabbas akwai sauyi, gaba ɗayana kamar ba ni ba, kallo ɗaya da zaka min ba sai ka ƙara na biyu ba, zaka ga zallar ƙuruciyar da ke kan fuskata, wanda zai bayyana maka cewar shekaruna ba su da yawa. Sai dai kuma in har ka yi min farin sani a baya, to a yanzu zaka ce na sauya, ba wai sauyi na ɗabi'a da halayya ba, a'a sauyi na halittar jiki.
A baya ni ɗin ƴar duma duma ce mai kyawun dirin jiki tubarakallah, saɓanin yanzu da ko'ina a jikina ƙashi da jijiyoyi ne suke magana, ido kuwa ramar da ta fito da shi waje yanda kasan na mujiya, gefen kumatuna duk ya zurma ciki, shi kansa uban hasken da nayi ba na lafiya ba ne.
Albarkatun ƙirjina su kansu sun kwanta, ka rantse da Allah na taɓa shayarwa. Bayan ƙirjina na daga abin da mijina ke so, yake kuma ɗaukar hankalinsa, amma ina yanzu ko kaɗan basa burge shi. Duk na canja na zama wata babu kyan gani, kai baka ce mai tashen ƙuruciya ba, shekaru ashirin da uku ba a duniya.
Lokaci guda idona ya cika da tarin ruwan hawaye, sai dai ba su sami nasarar zubowa ba, cikin yanayi na bala'in tausayin kaina na sunkuyar da kaina ƙasa, ina jin wani dunƙulallan abu na tsaya min a maƙogoro yaƙi wucewa, hakan sai ya zama famin ciwo a gare ni, wanda da zan samu in korashi da yawun bakina, ko kuma ya wuce da kansa wataƙila da na sami sassauci.
Cikin ƙarfin halin da na saba na ɗago kaina ina mayar da tarin ƙwallar da ta cika min ido, ɗakin kawai na ke bi da kallo, ko a iyaka shi aka bar bawa rayuwa ya ishe shi jin daɗi da more rayuwa, ya manta da dukkan damuwa a duniyarsa, ballantana kuma ace rayuwa kake yi a cikin tamfatsesen gidan nan da yake sai kace a ƙasashen turawa.
Lumtsum na ke a cikin daula, duk wanda ya zo gidana ba ya son tafiya, iya dukiya dai an narkata wajen ginin gidan, zaka rantse da Allah ba duniyar da talakawa ke rayuwa ba ne, idan ba Allah ya soka da rahma ba sheɗan sai ya shagaltar da kai da yin ibada.
Sau tari ƙawayena da ƴan uwana kan ce min ke kam Sa'ida kin more, ba ki da saurin baƙin ciki da takaicin duniya domin Allah ya kashe ya ba ki, arziƙi ta ko'ina, kalli gidan da kike ciki kamar ba za'a mutu ba, irin motocin da ake fita da ke a cikinsu zamansu kaɗai yasa ki yi ƙiba ki fresh, abinci kullum da nama, ke kam ba ki da sauran damuwa.
Ba su san da cewa ba anan take ba wai abin da yawa mutuwa taje kasuwa, sai da kwanciyar hankali ake jin daɗin. MAI ƊAKI dai shi ya san inda ke masa yoyo, sunan wani novel da na taɓa karantawa na Nana Haleema.
Na kalla madubin da ke gabana da kyau, na sauke doguwar ajiyar zuciya tare da yin murmushi mai ciwo, ina mamakin masu faɗa min irin wannan zantukan, ban sani ba ko iyaka daular da Allah ya ajiye ni a ciki kawai suke kallo, shiyasa ba su taɓa lura da cewar akwai ƙalubale mai wahala a gefe ba, bana jin daɗin gidan, bana farin ciki sam, sun ka kasa ganin irin lalacewar da na yi, sun ka kasa fahimtar gwara ma rayuwata ta baya akan ta yanzu, sun ka kasa fahimtar ina da buƙatar taimakonsu.
Suna ganin cewa zan iya yi musu komai, tunda suna kiran wannan ƙaton gidan da gidan Sa'ida, ba su san cewar babu abin da zan iya ba, domin ba ni da komai, tunda komai ɗin da su ke kallo ba mallakina ba ne, ba taƙamata ba ne. Ƙwarai kuɗi da rai da lafiya rahma ne, kuɗi komai ne bayan lafiya, babu abin da ya fi ace yau kafi ƙarfin komai, ace yau kai ne kake ɗauka ka bayar ba wai a ɗauka a baka ba, ka ci mai kyau ka sha mai kyau, ka kwanta a mai kyau, kasa sutturu masu kyau da tsada, ka hau jirgi ka keta hazo zuwa in da kake so, ka ɗiba ka kashe babu mai ƙayyade maka, ka yi mu'amala da mutanen da su ka fika, duk saboda kana da kuɗi.
To amma me? Duk da irin tarin dukiyar da kake da ita, da irin daular da kake rayuwa a ciki, muddin babu kwanciyar hankali, to babu farin ciki da jin daɗinta. Ni a wurina gwara in rayu cikin talauci, akan ace ga tarin dukiyar amma babu zaman lafiya, babu kwanciyar hankali, balle na sami natsuwar zuciya.
Na sake sauke ajiyar zuciya mai nauyi a karo na uku, murmushin da yafi kuka ciwo na yi ina girgiza kaina, wanda ni ɗaya na san ma'anarsa. Abu ɗaya na barwa kaina sani shi ne, kowanne matakin nasara ba'a hawansa sai da ƙalubale, kuma komai na duniya fararre ne ƙararre, kuma dogaro ga Allah jari, babu kuma mai yi sai Allah.
Muddin akwai yau, gobe da jibi, to komai zai shuɗe ya zama tarihi.
Ɗaurin ɗankwalin da ke kaina na gyara, turare na ɗauka oil na shafa, sannan cikin sanyin jiki da mutuwarsa na fita a ɗakin, ina jin ƙafafuna tamkar a ƙanƙara. Cikin sauri da rashin jin daɗi a raina, da ban ankarewa tafiyar lokaci ba na fita, na san duk inda Hubbi yake yanzu yana kan hanyar dawowarsa gida, wataƙila ma ya dawo ban sani ba, tun da ƴan kwanakin nan bana sanin dawowarsa, in ba zaman parlo na yi ba, kamar yadda ba zan san fitarsa ba.
Ga shi ko abinci ban ɗora ba sakacin da ban taɓa yi ba, abincin da idan na yi ma ba'a masa cin kirki, ko kuma a barni da kayana, amma duk hakan ba zai sa in daina ba, zan ta ƙoƙarin sauke nauyin da ke kaina na dafawa, tun da an siyo an ajiye.
Ina fitowa daga bedroom ko ƙasa ban sauka ba don gani nake zan ƙara ɓata lokaci ne. Kitchen ɗin sama na wuce kai tsaye, babu ɓata lokaci na buɗe fridge na ɗauko gwangwanin bama da nake zuba dafaffen kayan miya a ciki, ni kam ba ruwana da wahalar jajjage ko markaɗe kullum, da ya jido uban kayan miya na ke markaɗesu in dafa in juye a kwalabe.
Ina aiki ina ta muraja'a. A ƙanƙanin lokaci na kammala dafa taliya jallof sai tashin ƙamshin busassan kifi take yi, da ƙamshin kayan lambu, na juyeta cikin tsadadden kular abincin da Hubbi ya zo da su last week daga dubai, wanda na ji Hamida na faɗin kuɗinsu ya kai dubu ɗari biyu. Bayan nan na ɗauko bilenda na haɗa lemun abarba na juye shi cikin jug. Da kammalawata na kwashi komai na kai parlon Hubbi da ke nan sama na jera akan table, na gyara ɗakin ko'ina ya ɗauki ƙamshi sannan na fito na kulle.
Da na leƙa parking lot ta window banga motar da ya fita da ita ba na san bai dawo ba, hakan yasa na yi komai a nutse, sai dai kuma cike na ke da mamakin rashin dawowar tasa da wuri yau, tun da duk inda ƙarfe biyar da rabi take ya dawo gida, da ya ci abinci zai kwanta sai an kira magrib zai fita masallaci, ba zai dawo ba sai bayan isha'i.
In da nake jin daɗi kenan, Allah bai bani miji mai son zaman majlisa ba, yafi ganewa zaman gidansa. Duk da yanzu na kan yi fargabar dawowar tasa, duba da bama wanyewa lafiya da shi.
Ɗakina na koma na yi sabon wanka, na fito na shirya cikin riga da skirt na atamfa, ɗinkin ya yi matuƙar amsar jikina, skirt ɗin ya fito da cikakken ƙuguna, musamman hips ɗina wanda shi ne abu mafi ɗaukar hankali a jikina bayan baiwar madaidaitan ƙirji.
Na bar ɗakin ina ta baza ƙamshi, duk da halin da na san ina ciki yanzu a rayuwar aurena, hakan ba shi ke hana ni gyara jiki, in ci kwalliya in isa ga mijina ba, ba kuma shi zai sa na waje ya shigo in bari ya gane ina cikin matsala ba, domin na iya sirrinta zaman aurena.
In da sabo na fara jure halin ko in kulawar mijina yanzu, hakan yana damuna, amma na kan nuna masa bai dame ni ba, balle hakan ya ƙara ingiza shi, ban taɓa fasa hidimta masa ba, shi kansa ya san ina da mugun haƙuri, don idan wata ce tuni anji kansu, ƙila ma tuni an tunguɗe igiyar auren.
A halin yanzu banda burin da ya wuci mu zauna mu fahimci juna da shi, ya karanta min kuskurena in gyara, domin har ga Allah bana jin daɗin irin zaman da muke yi. Auren soyayya muka yi ba auren ƙiyayya ba, kuma tsawon shekara takwas da aurenmu, bamu taɓa zaman da za'a ce don mun sami saɓani, zamu shafe sama da kwanaki babu ruwan wani da wani ba, har ta kai ga muna raba makwanci.
Yaƙi bani damar magana da shi, ni kuma iyakar sanina ban masa wani laifi ba, haka dangisa ma, ban san matsalar da ta gifta a tsakaninmu ba, da kowa ke nuna min ƙiyayya ƙuru ƙuru. Ta kai ta kawo har shayin shiga cikinsu na ke yi. Don sun dinga min kallon banza kenan ana jajja baya da ni kamar wata jaɓa.
Sai in shiga taro ma in fita babu wacce zamu yi magana da ita, in ka cire gaisuwa ta sallama da zata haɗa mu. Kuma abin da yake matuƙar ɗaure min kai, duk wannan matsaltsalun cikin ƴan watanni ne, watanni ba masu yawa ba, komai ya canja, da can komai lafiya tsakanina da su, har ina ganin tamkar duk matan duniya babu wadda ta yi dacen dangin miji irina.
Saboda suna nuna min so da ƙaunar kamar za su cinye ni. Miji kuwa ai sai son barka, a ko ina zan bugi ƙirji in ce nafi kowacce mace sa'a, sai dai banda yanzu, yanzu kam ɗaya na ke da wadda aka yiwa auren ƙiyayya, miji ke neman yin galaba akanta ya kassara rayuwarta.
A yanzu haka so nake na samu wani in karanta masa halin da nake ciki ko na ɗan ji sanyi cikin raina, kun san idan mutum na cikin damuwa, ko ya ya idan ya amayar da ita, ya kan ɗan ji sauƙin ciwon da ke zuciyarsa.
To ni ta ɓangarena gaba ɗaya na rasa wa ya kamata na yi maganar da shi. Ban isa ba! Na yi kaɗan in ce zan tunkari ƙawa da zancen matsalar zamantakewar aurena, kai ban ma ni da shaƙiƙiyar ƙawa ta sirri.
Mahaifiyata kuma bana so na tunkareta da magana makamanciyar wannan, ba don komai ba sai don gudun shigarta damuwa, tun da a ko yaushe burinta ta ji na ce mata lafiya muke babu wata matsala.
Haka a kullum nasiharta a kaina in ta haƙuri, in guji kai ƙorafi domin hakan na ƙara taɓarɓare zamantakewar ma'aurata. Sannan ba ni da Ƴar uwa mace balle in zauna mu zanta da ita, ta ba ni shawarar samun mafita.
Sai Yayyu maza da Allah ya ba ni har huɗu, su kam bana jin ma zan yi kuskuren musu wannan maganar.
Kun san an ce mai ɗaki shi ya san inda ke masa yoyo, idan zan kira su in kwana dubu ina faɗa musu matsalar da ke faruwa, ba za su taɓa yarda ba, idan ma sun yarda ba za su goya min baya ba.
Idan ace dai matsalar daga ni ne, to nan za su yi saurin cafewa har a iya samun mai zuwa har gidana ya naɗa min na jaki, amma batun wai in faɗa musu laifin Hubbi ne, tabbas ruwan ashariya sai na sha na ƙoshi, ba kuma wai don basa sona ba ne. A'a! suna mugun sona, tun ma da na zama ni ɗaya ce mace a cikinsu, kuma suna matuƙar tausaya min, amma batun dai su goyi baya ga laifin mijina zance ne.
Gwarama ranar da Ya Imam ya zo duba ni, ya ga duk na bushe ya zauna ya yi min nasihohi masu ratsa jiki, akan zaman duniyar gaba ɗayanta ƴar haƙuri ce. Bai bani damar buɗe masa cikina ba, ya dai ta min nasiha tare da kalaman kwantar da hankali, kafin ya tafi.
Abbana kuwa zafi ne da shi, ina fara faɗa masa zai sa azo a ɗauke ni, ko kuma yace in kwaso kayana in taho gida, duk ranar da mijin ya san darajata ya zo ya bada haƙuri in koma, ko kuma mu rabu har abada.
Ni kuma ko kusa bana son abin da zai ja igiyar aurena ta sami tangarɗa, ina cikin matan da za su iya shanye kowanne kalar baƙin cikin gidan aure akan dai a sake su. Kun ji wani rashin sanin ciwon kai a wurina ko.
Allah ya gani tun kafin aure na ke tsoron saki, tabbas ina tsoron a sakeni. Za ku tambaye ni dalili ko? To ba ni ɗaya ba, kowacce mace ma bata so a saketa, babu macen da ke son igiyar aurenta ta mutu, sai dole.
Shiyasa idan kun duba, duk yadda mace ta so a saketa, namiji na furta mata, jikinta ya ke sanyi, ta ji dama komai bai faru ba, duk da cewa ba kowa ba, domin akwai auren da irin cutarwar da ke cikinsa, gwara rabuwar auren kawai.
Ni fa wani waje daban ma ban so in ji aure ya mutu bare a kaina, abun da na yarda da shi kawai babu wani ƙunci da ke dawwama, komai zai shuɗe, kuma ubangiji zai warware min kowacce matsala.
Tun barowata sama har na sakko ƙasa kiran lambar Hubbi na ke yi bata shiga.
Amma fa zuwa yanzu da akai magriba hankalina ya kai ƙololuwar tashi, ga dai shi ba wai dare ne yayi ba, to amma ban saba ba, tun aurenmu sau ɗaya ya taɓa kaiwa bayan isha'i a waje, shima kuma dalilin hatsarin da ya samu ne.
Shiyasa ko yanzu nake ta jin kaman da akwai wata matsalar, sai dai ina ta kore mugun saƙe saƙen da zuciya ke min.
Na yafa mayafi na fita, mai gadi na hango ni ya taso da sauri ganin na fito a furgice, gabana ya russina yana tambayar lafiya, da ƙyar na daure na haɗiye tashin hankalina na ce masa.
"Tun da Hubbi ya fita bai dawo ba ne?".
Mamakin tambayar tawa ya bayyana ƙarara a irin kallon da yake min, na san mamakin bai wuci ace ni da za'a tambayi fita da dawowar mijina ba, amma ni ce ke tambayar.
Cikin girmamawa yace da ni,"Hajiya ai bai jima da fita masallaci ba, amma dai da mota ya fita ina ga ba masallacin nan kusa ya tsaya ba".
Wani ɓacin rai na ji ya ziyarci zuciyata, na kawar na ce,"ok".
Abin da na iya faɗa kenan na wuce na bar wajen, don idan nace zanyi doguwar magana tabbas sai ta sarƙe da kukan da nake dannewa. Ni kasa sabawa da wannan canjin, ba zan iya da wannan sabuwar zamantakewar mara armashi da rashin daɗi ba.
Ina komawa ciki na shiga bedroom nasa na ƙasa, ya daɗe da dawowa tabbas, daga yanayin yanda ɗakin ya nuna. Abin da ya bani mamaki matuƙa shine sabon ƙamshin turaren da ban san da shi ba.
Turarensa ɗaya na sani a duniya, wanda tun kafin mu yi aure da na taɓa basa kyautarsa shikenan ya riƙe shi bai taɓa canjawa ba. Sai a yau, kuma yanzu da nake ganin sabuwar kwalba akan madubi, bayan ga waccen kwalbar bata ƙare ba.
Ɗakin na bi da kallo, idona ya kai kan warm coolers ɗin da ke ƙasa guda uku, wani abu na ji ya soke ni kaman sukar mashi. Ƙafafuna na rawa na isa gabansu da sauri na buɗe, ƙamshin lafiyayyan abincin ciki ya doki hancina, babu tantama abincin wata ƙwararriyar chef ɗin ne.
Kuma yanayin coolers ɗin zai tabbatar maka daga gidan girma suka fito.
Na ɗauke gani na daga kai, ina kallon kan gadon da kayansa ke zube waɗanda ya cire. Sai na ji kamar ana jana zuwa bakin wadrobe, jikina duk na rawa na buɗe ɓangaren da jallabiyunsa su ke, kaf guda ashirin da yake da su, suna nan ciki rataye a hanger, babu ɗaya da ya saka ya wuce masallaci kamar yadda ya saba.
Lokaci ɗaya na ji yawun bakina ya bushe gaba ɗaya, cikin rasa makamar abin yi na rarumi wayata na shiga kiran lambarsa, farko not available su ka ce min, na biyo kuma ringing ɗin bai je ko'ina ba aka danna user busy.
Na kalli agogo na ga lokacin sallar isha'i ya wuce, hakan yasa na ƙara danna kiran, amma har sau huɗu abu guda ake faɗa min user busy, ni kuma ƙara kiran nake ta yi.
Zuciya da bata da ƙashi tuni ta fara ƙissima min tunanin wasu lamura, har tana haska min hoton hakan a cikin idanuwana, babu shiri na rumtse ido gam ina girgiza kaina, ban san lokaci da na sami mazauni a gefen gadon ba ina damƙe zanin gado, wani abu ya soki ƙirjina, cikin raina faɗi na ke ina ƙara maimaitawa, ba yadda za a yi Hubbi yayi min abin da zuciyata ke rayawa.
Ko da komai ya canja, shi ba zai taɓa sauyawa daga mutumin kirki ba, nagartaccen namiji mai wuyar samu, ba ɗan kuka na aura ba. Duk tsanani Hubbi ba zai taɓa juya min baya ba, ba zai taɓa cin zarafina ta irin wannan hanyar ba.
Matsayin da nake da shi a zuciyarsa ya wuci gaban ya ci mutuncina ta irin haka, yana tsanin sona na sani, kowa kuma shaida ne.
Aka ce ba'a shaidar namiji ko? Na san kuma kun yi mamakin yaƙinin da na ke da shi akan mijina ko, da shaidar da na masa na ba zai taɓa cin amanata ya juya min baya ba.
Hmmm ku dai ku biyo ni kawai, za ku sha labari.
Kaman daga sama na jiyo ana kwaɗa sallama a parlo, na miƙe da sauri ina saita natsuwata na fita da sassarfa.
Na fita ne cike da zumuɗi, in fita in ci karo da Hubbi nah, a asalin Hubbin da mu ka yi aure cike da so da ƙauna, gami da kwanciyar hankali a zamantakewarmu.
Sai dai me! Ina isa falo gabana ya faɗi ras sakamakon tozalin da na yi, duk sai na daburce ina neman rasa ina zanyi kuma mai ya kamata inyi.
Yayar Hubbi ce ta zo Maijidda wadda muke cewa Yaya, daga ƙanne har ƴaƴa da ƴan uwa kowa Yaya yake ce mata. Ita ce babbar su wadda ta zamar musu tamkar uwa, kowa na sonta haka kuma kowa na tsoronta.
Sai abin da tace ayi haka kuma idan ta faɗa ta zauna, ko mahaifiyarsu bata fiya yanke hukunci ba sai dai ta bata wuƙa da nama. Haka duk abin da za a yi sai da shawararta, ba'a taɓa yin abu ba tare da masaniyarta ba. Don ana girmamata sosai da yi mata biyayya, kuma itama tana mutunta kowa, ba zan ce bata da kirki ba idan na faɗi haka na zalunceta.
Macece mai ƙaunar nata, duk abin da ta tattaro na ƴan uwanta ne, burinta ta ga kowa cikin farin ciki, haka kuma kowa ya tashi kai kukansa ita yake kaiwa, kowa Yaya komai Yaya.
Amma fa tana da zafi, bata ɗaukar raini, idan ta tashi faɗanta da masifarta shafar kowa yake yi, shisa kowa ke kiyaye abin da zai haɗosa da ita. Kaf cikin matan ƙannenta tafi sona, babu ya ni a wurinta, ba wai don su ɗin bata son su ba, a'a nima albarkacin tsananin soyayyar da take ma Hubbi ne yasa na zama ta gaban goshinta.
Don Facalolina har kishi su ke da ni, saboda yadda Yaya ta ɗauke ni kamar jininta.
Irin yadda take nan nan da ni kamar ƴarta Shatu wacce muke sa'anni, amma duk wannan tarin soyayyar tata da kulawarta gare ni, sun rushe cikin ƴan watanni, halinta da ɗabi'unta sun sauya, ban san laifin me na mata ba, haka kawai ta ɗora dukkan fushinta da karan tsanarta a kaina.
Ko bikin da aka yi watan da ya wuce cewa ta yi kowa ya zauna ya huta ni a tattara min duka ayyuka, haka na zama saniyar bare a wannan bikin.
Na yi ta fama da uban wanke wanken kwanukan taron biki, shara kuwa har sai da na ranƙwafa saboda mugun riƙewar da bayana ya yi.
Da an tashi rabon abincin zata kira sunana ta yarfo min zagi tace in ɗauka in bi mutane in raba musu, ban da damar zama ko na sakanni, hatta kashin ƴaƴa da wankan yaran baƙin kunya duk nice.
Ta mayar ni kaman wata jaɓa, na sha baƙin ciki da takaici a bikin nan, har sai da na dinƙa jin kaman in gudu gidanmu.
Su kan su ƴan bikin sai da suka dinga tausaya min, wasu na cewa ya kamata a barni in huta, in huta tunda surukan gidan gamu nan fal, to amma ban isa ba, zaman hutawata daidai yake da zaman hutu a gidan iyayena tun da har Yaya na fushi da ni.
Za ku ji haushina ko? Ku ce kamar ban san darajar kaina da ƴancina ba ko. Ba haka ba ne, wallahi tsananin haƙuri ne da ni, ga shi ba ni da baki, ban iya rigima ba sam. Amma tabbas ina jin ciwon abin da ake yi min. Kawai ban san ta yadda zan ɗauki matakin ba ne, saboda ina tsoron abin da ka iya zuwa ya dawo.
Kun ga fa ko a yanzu mugun tsoron Yaya nake yi, Wallahi a baya da zarar ta ganni take washe baki ta buɗe min hannaye in tafi jikinta ta rungume ni.
Amma yanzu har gwara naga hukuma su ce kama ni su ka zo yi akan ganinta, ganin ma kuma ace a gidana. Hakan na zamar min babbar fargaba da tashin hankali.
Kuma idan ta zo ɗin, har ta bar gidana bana samun natsuwa da kwanciyar hankali, saboda ban san me za a je a ƙulla min ba. _________________________________ _Sabon salo, sabon zubi, sabuwar shimfiɗa kuma sabuwar tafiya, saboda haka ku ɗaura ɗamara domin tafiyar mai zafi ce...tabbas tafiyar doguwa ce me ƙunshe da tarin darussa, tafiyar da ta juya matakin rayuwar wasu mutanen..._ ku yi ƙoƙarin mallakar abu mai inganci, masu iya magana su ka ce siyan na gari mai da kuɗi gida, saboda haka na ke cewa kar ku ji ɗarr ɗin saka kuɗi ku mallaki littafin ƘAYAR RUWA.
#Halima.hz
Dm ***
#2023