Free chapter 路 Read without an account
Episode 1
*馃拫KURKUKUN 茦ADDARA馃拫*
*Boss Bature 鉁嶏笍*
_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon fa蓷akarwa da kuma ilmantarwa harma da nisha蓷antarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba.鉁嶏笍_
Gargar蓷i
_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a ha蓷a mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini ha茩茩ina!馃憣_
*E1*
Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana ba da sauti tik-tik-tik. Sakamakon dare da ya tsala don time din karfe 蓷aya da rabi na dare, wayar da ke ajiye saman bed side drawer 茩irar Samsung Galaxy ta soma ruri da 茩arfin gaske. A lokacin ya yi nisa a cikin barcin nasa, kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa. A kira na hu蓷u ne, sautin ya daki dodon kunnansa, a firgice ya farka yana faman ambaton sunan Allah, jikinsa na sanye da singlet da gajeran wando fari, a茩alla ya kai shekaru 40 a duniya. A launin fata kuwa wankan tarwa蓷a ne, da 茩yar yake iya ware manyan idanuwansa a kan katafaren gadonsa kafin a hankali ya mayar da 茩wayar idonsa kan agogon bangon, tafin hannunsa ya kai tare da shafa fuskarsa cikin sanyin murya ya ambaci sunanta, "Angel!"
Kafin ya zame hannunsa daga kan fuskarsa wani kiran ya sake shigowa wayarsa a hanzarce ya mika hannu saman drawer 蓷in ya 蓷auki wayar, cike da mamakin wane ne yake kiran shi a irin wannan lokaci? Anya kuwa Lafiya?
Lokacin da ya kalli screen 蓷in wayar sunan Aminina ne ya bayyana, ajiyar zuciya ya 蓷an sauke tare da 蓷aga kiran ya manna wayar a kunnansa tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sautin harbin bindugu. A gigice ya furta, "Aminina!" Kafin Ya 茩arasa rufe bakinsa, muryar Aminin nasa ta katse masa hanzari, a ru蓷e yake fa蓷in,"Na ba ni na lalace, shikenan tawa ta 茩are."
A firgice ya dakatar da shi, "Ka nutsu ka yi mini bayanin me yake faruwa ne?"
"Sun kama ni ina yi musu le茩en asiri, yanzu haka sun biyo motata, na san kashe ni za su yi, kai ma kuma ba za su 茩yale ka ba. ba zan so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi ba, don Allah na roke ka, ka gudu kai da Angel, ba na fatan laifina ya shafe ka Abokina. Bayanan sirrin da na 蓷auka a wurinsu, yana a cikin memory 蓷ina, ita ka蓷ai ce hujjar da asirinsu zai tonu..." Bai kai 茩arshen maganar ba, 蓷if ya ji kiran ya katse.
A gigice yake kwa蓷a masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar wayar ta katse, sake kiran layin nasa ya yi cikin sa'a aka 蓷aga kiran, abin da bai ta6a tsammani ba, sautin kururuwa ya ji a cikin kunnansa mai matu茩ar razanarwa, wata kausasshiyar murya ya jiyo tana magana ta cikin wayar, "Idan kana son sanin meke faruwa, ka kalli screen din wayarka." Jiki na rawa ya 蓷ago da wayar yana kallon screen 蓷in yayin da suka canza kiran zuwa Video Call.
Saboda tsabar firgita, a ru蓷e ya diro daga saman gadon, Idanuwansa sun firfiro waje tamkar 茩wayar idon za ta fa蓷o kasa. Ba komai ne yasa shi firgita ba, face motar Amininsa dake ci da wuta, akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar, wuta sai cin naman jikinsa take yi. Wata irin zufa ce ta wanke masa fuskarsa, a ki蓷ime ya shiga furta, "No, no!" Duk ya firgice, rejecting call din suka yi.
Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far masa, ba arzi茩i ya zube gefen gadon ya zaune yayin da jikinsa ke kyarma sosai, ku san minti goma shabiyar baya a cikin hayyacinsa, ya rasa ma me yake yi masa da蓷i duniyar nan.
Yana cikin wannan halin ha'ula'in, muryar amininsa ta soma dawo masa a cikin kunnansa, "Ka gudu kai da Angel ba na so laifina ya shafe ku." Tabbas kuwa za su dawo kansa ne, domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa, ba komai ya fi ji ba face 拼arsa 蓷aya tilo da ya mallaka wato Angel.
A matu茩ar ru蓷e ya mi茩e, ko jallabiya bai zura a jikinsa ba, iya key 蓷in motarsa ya 蓷auko saboda tsabar ru蓷u wardrobe ya dosa zai bu蓷e a matsayin kofar dakin, har sai da kansa ya bugu tukunna ya ankare, ya nufi ainihin 茩ofar, da sauri-sauri ya fito daga bedroom 蓷insa da ke a downstairs ya nufi cikin babban falon, kai tsaye Upstairs Ya haye. A ki蓷ime yake tattaka staircases din benen, bai nufi ko'ina ba sai 蓷akin Angel, bugu 蓷aya ya yi ma 茩ofar ta bu蓷e, ko'ina duhu, kunna hasken 蓷akin ya yi, nan take haske ya gauraye ko'ina, wurga kwayar idonsa ya yi kan Angel da ke 茩unshe cikin lallausan bargo, a hanzarce ya 茩arasa shiga 蓷akin, tare da hawa saman gadon yana kwala mata kira, "Angel, Angle my daughter!Azeezaty!" Babu alamun za ta farka, a hautsine ya cakume ta ya saba ta saman kafa蓷arsa. Da sauri ya fito daga bedroom din nata, ya sauko downstairs, kai tsaye ya fito waje wurin da motocinsu suke, 蓷aya daga cikinsu ya bu蓷e 茩irar Range Rover, back seat ya bu蓷e ya kwantar da Angel tukunna ya bu蓷e driver seat ya shige ciki, a gaggauce ya yi wa motar key, a daidai bakin gate ya tsayar da motar, a hanzarce ya fito ya bu蓷e gate 蓷in, kafin ya koma cikin motar ya fusgeta da gudun gaske. Fitar motarsa ke da wuya, wasu dan茩ara-dan茩aran motoci kusan su shida suka nufo shantalelen titin da zai sada ka da gidansa da alama sun hango motarsa hakan yasa suka bi bayan motar da wani irin matsiyacin gudu. Hankalinsa ba 茩aramin tashi ya yi ba, saboda ya hangi motocin da ke biye da motarsa ta cikin mirror 蓷in motar, hakan yasa shi 茩ara gudun motar. La66ansa na kyarma yake ambaton La'ila'ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! Shi kansa bai san inda zai dosa ba, driving kawai yake yi a makance, shesshe茩ar kukan Angel ce ta fara dawo dashi cikin hayyacinshi, da alama ta farka sakamakon gudun ceton ran da yake yi da su, yasa kanta ya dinga buguwa jikin motar, har hancinta ya fashe jini ya soma zuba.
A ru蓷e take furta,"Daddy...What's happening, where are u going in this darkness night?"
Karamar yarinya ce da ba za ta wuce 11 years a duniya ba, maganarta ma da茩yar take fita saboda halin da take ciki, hawaye ne suka wanke masa fuska yana mai dana-sanin yin aikin jarida fiye da tunanin mai tunanin, saboda shi ne silar shigar shi cikin wannan tashin hankali.
"Angel am really sorry! Na cuci rayuwarki, a yau daddynki ba zai iya ceton ki ba, Angel ba zan jure rashin ki ba, ba zan so laifina ya shafe ki ba." Yana magana cikin kuka, tafin hannunta ta sanya ta dafe hancinta dake bleeding, jini duk ya 6ata fuskarta, cikin shasshe茩ar kuka ta kuma cewa, "Dad! My nose is bleeding, zan mutu, gaba蓷aya ya rikice ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa ya ji da蓷i. Bai san amsar da zai ba ta ba, iya sorry kawai yake iya furta mata.
Har yanzu motocin nan na biye da motarsu, lokacin da ya fara jin saukar alburushin bindiga a bayan motar a gigice ya karya kwana ya fa蓷a wani kurmin daji, mai duhun gaske, shi kansa bai san ina zai dosa ba, ga manya-manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar, a ru蓷e ya yi parking 蓷in motar ya fito ya zagaya ta back seat din motar jiki na kyarma ya zura hannu ya 蓷auko Angel, daga ita sai rigar barci a jikinta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, da gudun gaske yayi cikin dajin da ita yayin da take sa6e a saman kafa蓷arshi. Hasken motarsa ne da ya bari a kunne yake haskaka masa gabansa, yana cikin gudun nan ba tare da ya ankara ba, ya 蓷aura kafarsa saman wani 茩arfe mai tsatsa, wanda ke a tsire cikin 茩asa, kaifinsa tamkar na wu茩a, zuruf karfen ya shiga ta cikin tafin 茩afar ya 6ulo ta sama, wani irin ra蓷a蓷in azaba ne ya kai masa ziyara, tsikar jikinsa duk ta tashi, tuni jini ya wanke 茩afarsa, sam ya kasa motsawa daga tsayen da yake a hankali ya shiga furta, "Innalallahi wa'inna ilaihir raji'un." Cikin kyarma yake ambaton hakan, muryar Angel ce ta katse shi, "Dad let's go home, nan fa daji ne, akwai kura da zagi za su cinye mu. Daddy ko dai mafarki muke yi ne?" Ta yi tambayar still tana shasshe茩ar kuka.
Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, "Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne." Hannayenta ta sanya tare da zagayo da su ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa, "Daddy, to mu tashi daga mafarkin, Angel tsoro take ji." Tamkar ya fashe mata da kuka haka yake ji,
A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin da ya fisgi 茩afarsa ba, ya 蓷ago da ita daga jikin 茩arfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan 茩afar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya 茩wammace ta mutu a cikin ruwan da ta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu 蓷igon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su 茩ona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin Angel sai kuka take yi, sautin motocin miyagun da suka biyo shi ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, Allah Sarki yana ji yana gani haka ya 蓷aga Angel sama ya yi wurgi da ita, tsulundum ta fa蓷a cikin tafkeken ruwan mai zurfin gaske yana jiyo sautin kururuwarta.
Ba 茩aramin tashin hankali ba ne zai sa uba ya yi silar mutuwar 蓷iyarsa.
Saboda tsabar kuka jikinsa har jijjiga yake yi, duk ya ji ya tsani kansa. Don tuni ya fitar da rai da rayuwa a cikin duniyar nan, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi, jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin wani irin jiri ne ya soma kwasar shi, nan take ya yanke jiki ya fa蓷i a mace.
A daidai lokacin suka 茩araso da motocinsu, bayan sun yi parking sun kewaye shi, wasu gabza-gabzan samari ne suka fito, 茩irar Samudawa, ba茩ake wulik! Babu 蓷igon imani a kan fuskokinsu, sun yi shigar bakaken kaya da alama bodyguards ne, a tare suka bu蓷e wa iyayen gidan nasu murfin motocin don su fito.
Abin ban mamaki, manyan mutanane dattawa, suna sanye cikin shiga ta mutunci wato shigar Hausawa, shadda har da malun-malun kai ka ce mutanen arzi茩i ne. Koda fitowar su, ba su dora idonsu a kan komai ba sai a kan gawar Taj dake yashe cikin ciyayi.
Guntun tsaki 蓷aya daga cikinsu ya ja, "Mala'ika ya riga mu 蓷aukar ransa, ba haka na so ba."
Na gefensa ya ce, "Ban so ya yi salahar mutuwa irin wannan ba, amma duk da haka ba mu makaro ba, tun a nan za mu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun Munkar da Nakir."
Tuntsirewa suka yi da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma suka 蓷aure fuskokinsu. 茒aya daga cikin manyan mutanen ne ya juya tare da kallan 蓷aya daga cikin miyagun da suka zo da su, cike da ba da umarni ya ce, "Mi茩o mini galon 蓷in fetur tare da lighter." A hanzarce wanda ya yi wa magana ya nufi motocinsu.
"Maganin masu kunnen kashi ke nan, an gaya musu shiga gonarmu abu ne mai sau茩i." Bai kai 茩arshen maganar ba, aka mi茩o masa galon din fetur yasa hannu ya kar6a, cire murfin ya yi tare da zazzage masa fetur 蓷in a jikin rigarsa, sharkaf suka wanke shi.
Dalilin da yasa za mu 茩ona shi, saboda gudun mu bar wata hujja da zai sa a zarge mu.
Ba su 茩yasta lighter 蓷in ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya 茩yasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin 茩an茩anin lokaci, wutar tacinye shi 茩urmus
For whatsapp馃憞
*****
*****
_*Boss Bature馃拫 鉁嶏笍*_