Free chapter · Read without an account
006
A yaune zasu koma gombe, yana daga waje yana jiran ta, sanye take cikin bakar doguwar rigar Abaya egyptian , tayi rolling da gyallen kayan,jikin nan nata yayi fresh sai sheki yake , duk da cewar ita ɗin ba fara bace amma baza a kira ta baƙa ba, ba tayi wani make up mai yawa ba powder da gazal sai lip glow ta shafa a fuskarra amma hakan bai hana round cute face ɗinta bayyana tsantsar kyawun da take da shi ba.
Wani mayateccen kallo yake binta dashi wanda kana gani zaka gane na zallar sha'awace. Mai wuyar fassarawa ni da kaina saida na ƙara kallon ta acikin sati ɗayan nan Zee ta canza kamar ba ita ba ta koma zee diamond ɗin sai walwali take , duk da ba tayi wani ƙiba sai dai ta ɗan cika sabida cimar da ta samu mai kyau taci mai kyau ta sha mai kyau ba kamar yadda ta saba sai afi sati ba a ɗaura tukunya a gidan su ba, Alhaji yusuf da ya lura da halin rashi da kuma rashin sabo da kayan kwaɗayi da bata saba dashi ba nama,kifi,shawarma,ice cream,youghurt da dai sauran su babu dare babu rana yake saya mata su duk a dabarun sa ta saki jiki da shi ya kuwa yi narasa(Talauci mugun ciwo ne ya Allah ka raba mu dashi amin).
Ganin irin kallon da yake mata sai taji kunya ya rufe ta kasa sake jikin ta sai da tazo r)dab dashi tace "Alhaji wannan kallon fa?"
Ɗan shafa fuskar sayayi da babu ko ɗigon gashi yace "Zee diamond ɗina wallahi gani nayi kin ƙara kyau fiye da yadda kike a da sai naji kamar a fasa tafiyar nan."
"Alhaji kenan ai duk ɗaya ko a gomben ma zamu haɗu ni yanzu hankali na ya karkata ya koma kan baba tun sanda Nussy ta haɗani da Mama a waya tace min ya farka ban kuma ji daga garesu ba"
"Kar ki damu insha Allah ma yaji sauki zuwa yanzu, amma muna komawa zaku ƙaura ko?" ya tambaye ta.
Ɗan jim tayi "Sai dai in na koma duk yadda mukayi da mama zan sanar da kai idan mun shirya"
"Shirin me zakuyi bayan duk an tanadar muku da komai? Ai ina ga kayan jikin ku kaɗai zaku fito dashi"
"Toh Alhaji duk yadda kace haka za'a yi"
Riko hannun ta yayi yana mata wani irin shu'umar murmushi "muje ko flight ɗin mu zai ɗaga nan da 30 minutes" a baya suka zauna shi da ita yayin da driver ɗinsa ya ja motar , isawowar su ke da wuya aka fara kiran sunaye ana boarding, nan da nan suka shige tana zaune a gefen shi hannun su a cikin na juna jirgin su ya ɗaga.
Mama
Zaune hannunta rike yake da kofi tana bawa baba koko yana kurba a hankali kana ganin sa zaka gane yana jin jiki "Ya...... isa na...... koshi" ya faɗa a rarrabe da muryar mara lafiya ya ɗan gyara zaman sa haɗe da kawar da kansa gefe, tana jin haka ta ɗage kofin ta kwankwaɗe kokon da ya ji madara da sugar sai da ta shanye tass kana ta ajiye kofin, wani irin kallo yake mata wanda yafi kama da kallon tuhuma "Malam lafiya kake min irin wannan kallon ko akwai wani abinda kake so ne?"
"Ɗazu na tambaye ki baki ce dani komai ba" ya karisa maganar kamar numfashinsa zai ɗauke da alama yana jin jiki abinka da zuciya "wace tambaya kenan malam?" ta maida masa tambayar tana tsare shi da idanu.
"Ina zainab?"
Sai da taji wani abu mai kama da tsoro cike da iya naɗe tabarmar kunya tace "Wai malam sau nawa kake so na faɗa maka cewar ta samu aiki, aikatau take yanzu da ba don aikin da take yi ɗin nan ba yanzu da ana irga kwanakin ka a ƙasa, to sayar da zainab din zanyi ne kam ko kuma mene ne na kasa gane manufar ka?" ta hayyake shi da masifa Allah sarki bawan Allah rasa abin faɗi yayi ya koma ya kwanta gwanin ba tausayi, ganin ya kwanta sai ta ɗauki kofin da yasha kokon ta sa ruwa a ciki ta mike da niyar ta fita waje ta wanko "Naga tunda na farka ban ganta bane shi yasa na damu" ya faɗa dai dai sanda tasa hannu zata buɗe kofar chak ta tsaya haɗe da jiyowa tana kallon sa.
"Zata dawo ai , na fada maka zata dawo yanzu da zama tayi anan da wani labari ake yanzu ba wannan ba haba mutum sai shegen naci baka da lafiyar ma baza ka bar mutum ya huta ba......"
"Ayya mama kiyi masa a hankali mana , ɗaga muryar da kike yi sai ya haifar masa da ciwon kai"
"Kutumar ubanka ɗan iskan yaro, sai naci ubanka ina magana kana samin tsumman bakin ka shege mai idon mage"
Siiit Ibrahim yayi bai kuma cewa kala ba ,girgiza kai baba yayi sai ganin hawaye sukayi yana gangaro wa daga idanun sa da sassarfa Ibrahim ya nufi gadon yana faɗin "Sannu baba jikin ne? Ko a kira likita? Ina ne yake maka ciwo?" jin baba bai amsa ba hayi hanyar fita da sauri baba ya riko hannun sa " Yi zaman ka kaji babu abinda ke damina"
Yana sakar masa murmushi.
Mtswww Taja wani dogon tsaki "Sai kuyi ai " ta faɗa irin ko a jikina ɗin nan tayi ficewar ta.
"Ibrahim!! Baba ya kira sunan sa "Na'am Baba" ya amsa cike da tausayin mahaifin nasu
"Ina ƴar uwar ka? Ka faɗa min gaskiya kar kamin ƙarya"
"Wallahi baba ban san inda take ba, ni kaina na kai sati ban sa aunty zainab a idanuna ba, amma na tambayi mama tace min aikatau take wallahu a'alam."
Girgiza kai yayi alamun ya fahimta, zama Ibrahim yayi yana tunanin inda ƴar uwar sa ta shiga duk da kananun shekarun sa amma hakan bai hana ya gane cewar akwai abinda mama take boyewa ba.
Audu
Zaune yake a shagon yaga giftawar mota BMW idan dai ba idanun sa karya suka masa ba zainab ya gani zaune aciki, baiyi ƙasa a gwiwa ba ya ɗauki makullin mashin ɗinsa yabi bayan motar, isowar sa yayi dai dai da sanda take ɗaga masa hannu wanda ke jaan motar ya gani shima yana ɗaga mata hannu, yayi wa motar key ya bar kofar gidan, zainab da bata lura da Audu dake tsaye yana kallon ta ba ta nufi hanyar Shiga gida, hannun ta rike yake da Akwatinta ɗayar hannun kuma handbag ɗinta ne da wayar ta "Zainab" ya kira sunan ta cike da mamaki, chak ta tsaya haɗe da juyowa ganin audu a tsaye gabanta yasa kirjinta bugawa daaam, sauka akan mashin ɗin yayi ya karaso dab da ita baki a buɗe yake kallon ta dubaga irin canzawa da tayi kamar ba ita ba shin murna zaiyi ko kuka? Sannan wane ne wannan da ya ajiye ta a mota tambayar da yake wa kansa kenan "Ya Audu ina wuni?" ta gaishe sa kai a ƙasa bata so ya ganta ba, gaishe shi da tayin ne ya dawo da shi daga tunanin da ya lula.
"Lafiya lau Zainab ina kika shiga ne? Kimanin sati biyu kenan rabon da na sanya ki a idanuna duk hankali a tashe yake ina kika Shiga ne?" ya jero mata tambayar.
Kallon sa kawai take ta kasa ce dashi kala sai ma ƙara sunar da kai da tayi ƙasa. "kinyi shiru zainab? Naje duba Baba mama tace min kinje kauye, kuma naga wannan mutumin...." sai ya ɗanyi shiru yana kallonta "Wane ne shi?"
"Umm Eh....eh kauye naje yanzu dawowata ma"
"To wane ne wanda ya ajiye ki?"
Shiru tayi ta rasa amsar da zata bashi tunda mama tayi ƙaryan kauye taje , wannan kuma fa wa zata ce masa tunda yasan komai akanta yasan basu da da kowa wanda zasu nuna suce dangin sune, shi ko tsaye yayi yana kallon ta sai a yanzu ne ma ya lura da akwati da kuma handbag ɗin da ke hannunta ko ba a faɗa mishi ba yasan zasuyi tsada ai kiwa bai yi mamaki ba sai da ya ga iphone 14 ɗin dake hannun ta sabuwa gal, idanun sa ta bi don ganin abinda yake kallo , ganin wayar hanun ta yake kallo hakan yasa ta ɗan tsorata haɗe da waro idanu wanda yake nuna cewar Tabbas akwai abinda take nunawa ilai kuwa ya ɗago idanun sa sukayi ido huɗu dashi tayi saurin kawar da idanunta daga cikin nashi, duk alamun rashin gaskiya sun bayyana a tattare da ita.
"Zainab....." ya kira sunanta jiki a sanyaye ɗan ɗago idanun ta tayi ta kalle shi "wayar waye wannan a hannun ki?" sanin bata da abin cewa ta kauda zancen da "zanje nayi wanka naje na duba baba"
Bata tsaya jin me tace ba ta shige ciki da sauri.
Baki a tsagale ya tsaya kallon kofar gidan kamar tana gun yafi mintuna 10 a tsaye ya kasa ɗaga ko da ƴar yatsar hannun sa ne, ya rasa tunanin me ma zaiyi ɗaya shi sai bayan da tafi ne ma yake hango irin canzawar da tayi gaba ki ɗaya,jiki a sanyaye ya juya ya hau kan mashin ɗinasa ya mata key,bai tsaya bata lokaci ba ya koma shagon sa.
Zainab
Tana shiga gida ɗakinta ta ta nufa a tsakiyar ɗakin ta dire akwati da kuma hand bag ɗin nata, wani nauyayyen ajiyar Zuciya ta sauke haɗe da dafe kirjin ta "Na Shiga Uku" shine abinda ta faɗa kuka ta fashe dashi wanda ko da ace kashe ta za'ayi baza ta ce ga dalilin kukan nata ba abubuwa ne suka taru suka mata yawa , sai da tayi mai isar ta kana ta fita Waje bokitin wanka ta ɗauko ta nufi randa haɗe da ɗebo ruwa ta cika bokitin sai taji wani iri, a ƴan kwanakin da tayi da Alhaji Yusuf a hotel sai da ta shige ban ɗaki ta kunna shower Ko me ta tuna sai naga ta girgiza kai kawai tayi ta shige ban ɗaki. Tunawa da tayi da shower gels ɗinta masu ƙamshi da tsada tayi wanda Alhaji Yusuf ya saya mata da sauri ta fito ta shige ɗakinta haɗe da buɗe akwatin ta dauko guda ɗaya ta koma ban ɗakin ,a gaggauce tayi wankan ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa A shape ready made ne duk yana cikin kayan da Alhajin natan ya saya mata ,sky blue ne atamfar sai akayi wasu flowers da army green a jiki zanin yayi matukar kyau kuma ya amshi jikin ta, ko powder bata shafa ba ta ɗauki perfumes har kala uku ta fesa ko wanne a jikinta, mayafi green ta yafa, jakar ta kawai da waya ta ɗauka ta fice daga gidan.
Audu
Kasa zama yayi a shagon nasa duk ya fita hayyacin sa tunani kala kala yake da kuma tarin tambayoyin da yake so mata sune suke masa yawo a kwanyar sa , mikewa yayi yace da yaron shagon nasa ya kula sa shagon zai Shiga ya dan kwanta kansa ke masa ciwo, da "Toh oga Allah ya ƙara sauki" ya amsa, Audu kuwa baice dashi kala ba ya shige gida, umma na ganin sa tace "Abdullahi lafiya kuwa ya na ganka haka?"
"Kaina ke ciwo" ya bata amsa yana kokarin shiga ɗakinsa dake chan gefe "Toh Allah ya sauwaka wai dama yanzu nake so na aiki salima ta ƙira ka muje mu duba funitures ɗin nan kaga bikin na ta karatowa"
"In ba damuwa Umma ki bari gobe mu je"
"Yau da gobe ai duk ɗayane ba damuwa ka samu kasha magani"
"To umma" yayi shigewar sa ɗaki ,ɗan jim tayi tana kallon kofar ɗakin nasa tabe baki tayi haɗe da "Allah ya kyauta"
Zainab
Tana fita a gidan tayi sa'a wani mai napep ya ajiye wasu mata, yana fakawa a gaban ta ,ta shige haɗe da faɗin "Medical centre"
"Toh hajiya."
Ya tada mashin ɗin suka bar unguwar a hanya tace dashi ya tsaya zata sai fruits,kankan, lemo,apple, ayaba ta saya dawaya,wani shago na provisions ta gani ta nufi shagon maltina,faro ,peak milk ta saya ko wannen su katon da taimakon mai napep ɗin ta sa a baya suka kama hanya, ta kofar emergency suka shiga asibitin.
"Don Allah ka taimaka min mu shiga dasu ciki"
"Toh hajiya" ya shiga ɗiban kayan, kasantuwar suna dayawa ga nauyin sai da suka bawa secuirity ajiyar wasu kayan tana gaba yana biye da ita har suka isa dakin da baba yake.
Tun daga nesa ta hango mama tana zaune a kofar ɗakin tana shan rake girgiza kai tayi "mama dai ba a raba ta da ciye-ciye" ta ayyana hakan a ranta, gefen ta kuma Ibrahim ne zaune yayi tagumi yana kallo wuri guda hakan sai yasa taji babu daɗi a ganinta ai yanzu basu da wata matsala dama rashin lafiyan babane sai kuma rashin abinci "Toh kodai jikin baban ne?" ta tambayi kanta cike da farga da sauri sauri ta karasa inda suke tana faɗin "Mama" zumbur ta mike daga ita har Ibrahim ɗin.
"Adda kece?" ya tambaya yana mai murmushi wanda yake nuna yaji daɗin ganin nata da yay yi.
Murmushi ta masa tace "Eh nice Ibro"
"Adda ina kika je?" ya kuma jefa mata wata tambayar.
"Zaka fara Halin naka ai dan jarida,idan bakayi min shiru anan ba sai na fasa maka baki"
Zainab tace "Na dawo kuma" ta ayyana hakan a ranta a bayyane kuwa cewa tayi "Baza ka karbeni ba ka tsaya kana tsare ni da tambayoyi?"
Kamar dama jira yake ya karbi ledan da ke hannun ta ya shige ɗakin ya dawo ya karbi na hannun mai napep, 2k ta cire a jakarta ta mika wa mai napep ɗin "Ga wannan nagode....". Ta maida kallonta ga Ibrahim tace "Ka bishi akwai sauran kayan da suka rage.
Mai napep yasa hannu ya karba kamar zai duka mata yayi gaba Ibrahim na biye dashi.
"Zainab ƴar baba kece kika canza kikayi kyau haka? Lallai Alhaji ya iya kiwo" ta faɗa tana kai raken bakin ta "Uhmn" kawai zainab tace kana ta ɗaura da faɗin "Mama ya jikin baba?"
"Da sauki yana barci"
Ibrahim na dawowa ya dire kayan a ɗakin ya fito "Adda ina kika shiga ne dan Allah baba sai tambayar ki yake ranar har kuka yayi"
"Toh ishesshe yanzun nan na maka magana amma baka ji bako? Idan ma tambayar ta zakayi ka bari ta zauna ta dan huta mana ka tsare ta da tambayoyi sai ka ce ka aiketa"
Mama ta faɗa kamar zata kifa masa mari.
Girgiza kai tayi tace "Mama ki barshi dan Allah." shafo kansa tayi tace "Baban ya fara magana ne?"
"Eh amma tun ranar nan da ya tamabayi ina kike bai kuma magana ba amma likita yace ba damuwa zai fara magana da kyau ,ko a lokacin chan ma da ya fara maganar muryar sa bata fita da sosai"
Maida kallon ta tayi ga mama "Mama ya jikin nasan ne da fatan babu wata matsala?" ta tambaya kamar zatayi kuka.
"Gashi kinji ai daga bakin magananne, ya labarin alhajin ne?" ta tambaya tana mai tsare ta da idanu.
"Wani alhaji kuma mama?" Ibrahim ya tambayi mama.
"Kai kaci gidan ku ɗan iska shege"
"Haba mama dan Allah ki daina zagin sa haka kar ki manta fa ke uwa ce haba dan Allah"
Washe baki mama tayi "Toh Ibrahim ɗin ne sai da haka ƴar albarka baya jin gari"
Mamakine yasa Ibrahim buɗe baki wai yau addarsa ce tayiwa mama magana bata zage ta ba har take ce mata ƴar albarka eh lallai da wata a ƙasa.
"Yanzu duk ba wannan ba mu shiga na duba shi nayi kewar sosai Wallahi" tayi gaba,Ibrahim na kokarin binta a baya mama tayi saurin jawo shi rankwashin sa tayi har sau biyu haɗe da kama kunnen sa ta murɗa ƴar karamar ƙara ya saki, sakin kunnen nasa tayi ta buge masa baki "Zanyi maganin ka mara mutun bakin nan zan yake shi na dafa maka ka ci" ta karashe tana mai jan bakin haɗe da murɗawa, yaji zafi sosai hakan yasa ya fara matsar kwalla.
Tsaye tayi tana kallon Baba dake kwance yana barci tun daga inda take tsaye take hango yadda Numfashin sa yake hawa yana sauka sam numfashin ba a dai dai yake ba, matsar Kwalla take tana shessheka murmushi ta kuma yi ganin jikin nasa yayi kyau kamar bashi ba ramar nan duk babu ita, ta shagala da kallon sa tana murmushi.
Zungurin ta mama tayi haɗe da faɗin "me kuma na kuka? Ke da ya kamata kiyi farin ciki?"
"Ni kaina ban san kukan nan na farin ciki ne ko na bakin ci ba ne ba ,ni dai nasan bazai rasa na saba da abinda na aikata na samu kuɗin aikin da aka masa ba kuma....."
"Dallah yimin shiru wawayi kawai so kike mai kunnen zomon nan yaji komai ko? Ya fara tambayar nan nasa kamar ɗan jarida in ya fara magana chachacha kamar aku" ta karashe tana kallon Ibrahim da shima ita ɗin yake kallo.
"Zanci uban kane shege idan baka daina kallona ba" ta harareshi , yayi maza ya bar ɗakin.
Ajjyar Zuciya ta sauke tana girgiza kai "mama dai baza ta canza ba" ta ayyana hakan a ranta.
Kujerar plastic dake ɗakin ta janyo haɗe da zama ta riko hannun baba tana kallon yanda kirjinsa yake hawa yana sauka murza hannun nasa tayi a hankali "Allah ubangiji ya baka lafiya baba ya kuma tashi kafaɗun ka" ta furta haɗe da ɗan sa kanta a bakin gadon.
Tabe baki mama tayi , ledojin da ta shigo da su ta fara buɗe wa ta buɗe wannan ta buɗe wanchan duk abinda idanun ta ya gani kuwa sai ta kai baki.Ana cikin haka baba ya fara buɗe idanun sa a hankali har ya buɗe su duka ya sauke su akan zainab, kamar a mafarki ya ke kallon ta rufe idanun sa yayi ya kuma buɗe su ya tabbatar dacewar ita din ce dagaske rawa bakin sa ya fara yi yana son ƙiran sunan ta amma ya kasa, rike hannun nasa ta yi da iya ƙarfin ta kamar za'a kwace mata shi "Baba ka farka? Ya jikin naka? Kana bukatar wani abu ne?" ta jero masa tambayoyin nan haɗe da zuba masa na mujiya.
Baba kallon ta yake shima yana son tambayar ta inda ta Shiga na tsawon kwanaki amma hakan ya gagara , kallon yake sosai yana ganin chanji a tattare da ita kama daga yanayin fatar jikin ta da kuma suturar dake jikin ta, rintse idanun sa yayi yana jin wani irin yanayi wanda shi kansa bazai ce na mene ne ba amma tabbas yana zargin wani abu, a hankali ta soma hango hawayena kwaranya a idunan sa dake a rintse "Baba me ya same ka? Ina ne yake maka ciwo? Bari na ƙira likita" ta karashe a ruɗe haɗe da mikewa ji tayi ya riko hannun ta girgiza mata kai yayi alamun kar taje , ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta fahimci kallon na mene ne yake mata yasa ta zauna haɗe da faɗin "Baba kayi hakuri ban samu na zauna a tare dakai ba , aikatau na samu nake yi da safe sannan na samu shara-share a wani company Allah ya taimake ni suka bani kuɗin aiki na shekara ɗaya dashi na biya kuɗin aikin, ka kwantar da hankalin ka baba don ka warke da wuri bazan taba aikata abinda zan sa kaji kunya ba insha Allah, na ɗauka ma mama ta sanar da kai komai" ta faɗa tana mai tsare mama dake ta faman cin apple da iduna sai da ta kuma gutsira tace "Ai a makaryaciya ya ɗauke ni na sanar dashi amma bai yarda da magana ta ba."
Ibrahim da tun ɗazu ya shigo yayi tsaye yana kallon su yace "Amma Adda mama fa cewa tayi......" ai kuwa bai kai karshen zancen nasa ba mama tayi surin buge bakin sa saurin haɗiye sauran zance nasa yayi ba shiri, murmushi baba yayi wanda ake cewa ya fi kuka ciwo yana ji a jikin sa akwai abinda suke boye masa , takaicin sa ɗaya shine kar ta ɗaura mishi ƴa a turba mara kyau, amma ko ma mene ne yana fatan ya zo da sauki kuma zai zuba musu idanu.
BAYAN SATI ƊAYA
Zainab wasan ƴar buya take da Audu bata bari su haɗu duk inda tasan zata iya haɗuwa dashi to kaucewa take, idan kuwa sun haɗu sai ta nemi wani uzurin ta kauce masa ko da wasa bata bari sunyi magana ba,shi kuma so yake su zanta, yana da tarin tambayoyi da yake so ta bashi amsarta amma hakan ya gagara , baya ga haka duk ta daina kula shi yana son sanin dalilin sauyin na ta a gare shi.
Likita ne ya shigo da sallama bayan ya gama ƴan dube-duben sa sannan yayi rubuta magani mikawa zainab yayi "Ga wannan magunan da za'a saya masa ne ki tabbata an saya sannan a rika bashi a kan kari gudun kar a samu matsala idan kuma ba a bashi a kan Lokaci ba aikin mu zai iya lalace wa Allah ma ya tsare ya ƙara mishi lafiya, sannan na sallame ku zaku iya tafiya."
"Toh Dr mun gode sosai Allah ya saka da alhairi" ya amsa da ameen. Likita na fita ta mike hade da faɗin "mama bari naje pharmacy na karbo maganin sai mu zo wuce"
"Nifa bani da kuɗin sayan wani magana yawwa"
Murmushin takaici Zainab tayi "Ai dama ba cewa nayi ki bani kuɗi ba ina da su"
Washe baki tayi haɗe da faɗin "Yauwa ƴar albarka sai kin dawo....." ta maiida kallon ta ga ibrahim "Toh CCTV sai ka tashi mu haɗa kayan kan ta dawo ko? Ka tsaya kana ta kallon mutane kamar sabon maye"
Ba musu ya fara tattara kayayyakin, Baba na daga kwance yana ji kuma yana ganin abinda suke amma babu bakin magana,girgiza kai tayi ta yi ficewar ta.
Billing point ta nufa haɗe da basu prescription ɗin haɗe da mika musu ATM card ɗinta , bayan sun cira ne ta karba ta wuce GOPD Pharmacy, bayan ta karbi maganun ta nufi hanyar ɗakin da baba yake "Allah mai iko wai yau ace ni zainab ina da kuɗi kusan Million biyar a banki na? nawa? mallaki na ? hmm a baya naira biyar gagara ta take, alhamdulillah Allah nagode maka." ta ayyana hakan a ranta.
Daga bayan ta taji ance "Kin gama wasar buyan naki?"
_______________
Millhart ce
Ƴar Terawa