Free chapter · Read without an account

7

by Asmy b Aliyu · ABUUTURAB



kusan karfe goma da Rabi na dare yana baiwa Noor tea Sai shagawaba take zuba masa shikuma Sai tarairayarta yakeyi wayarsa dake Ajey agefe tafara Ring.nainah!"................lokaci daya Noor ta kurawa screen din wyar ido nan take kuma ta hade Rai ,

Tayi saurin dakatar da Abutturab dake kokarin kai spoon abakinta .shima hade rai yyi yana kallonta ,meya faru kuma?"

Nainah!"

Ta basa Amsa simple in short! "Sae akayi yaya ?" Turo baki tayi gatanan tana kiran ka awaya ni gaskiyya ka cire lambarta a wyarka ,

Ta karasa mganar cike da yarinta gamida turo baki.

Har lokacin kuma baa daina nacin kiran ba,Afusace ya da'ga wayar maimakon yaji muryarta tamkar yarda ya zata, sae yaji sabanin haka.

"Wat !".... Ya fada da qarfi yana miqewa tsaye okey okey!ganinan zuwa ,

Kallon noor yyi gaba daya baya cikin natsuwarsa.

" my chaculaty!"

Harde hannayenta tayi akan kirjinta haka tasha toka sosae batareda ta Amsa ba,

Bbu shiri Abutturab ya russuna agabanta gamida kamo hannayenta,

Ni nake maki mgana kike shareni ko?"haka aka koya maki a islamiyyar Ku?hawaye yaga sun fara Rolling akan fuskarta ,

Kuka kuma?"mezakaje kayi a wurinta?"ta fada cikin kuka "bana son katafi wurinta I don't like her!"

I so much hate her!"

Sakin baki hambal yyi yana kallonta lokaci daya ya hade rai ,waye ya fada maki wurinta zani?"

Mum dinsu mamdud che bbu lfy shine xamu kaita hospital, yana maganar zuciyarsa na dokawa.

Qaro na farko da yafara yimata karya.

Oya share hawayen idanunki ,mutafi na rakaki wurin Aunty kafin na dawo.

"Zan bika!".....

Hade rai yyi tareda fa'din." Dare yyi haka kurum kitafi maza na kallonki keda bakida lfy!"

Kara fashewa tayi da kuka !

Nidai ban yarda ba!"Noor ni abokin wasan kine ?"zaki tsaya musu dani?yyi mganar cikin tsawa."da alamr ransa ya fara baci.

bata kulasa ba tafita dakin da gudu tsoki yaja ,ya cire jallabiyar jikinsa ya saka kananan kaya.

Part din Aunty ya nufa knocking yyi ,aka basa izinin shigowa.

"Kallonsa kurum Aunty keyi ,

Tana shan daman man fura acikin wani dan qaramin bowl .

Sai ina ?" Ina kuma Noor?"Aunty tajefo masa tambayar lokaci daya,

daurewa yyi yace tana daki tasamu barci fita zanyi .

Aunty bata kara mgana ba tamasa Allah ya kiyaye da haka ya Juya yyi ficewarsa ko dakin Noor bai kallaba ,da alamr ta bata masa rai.

*

Nainah!..."

Zaune take kan motar ta kwalbar beer CE a hannunta, yyin da driven ta ke dan nesa daita yana kallonta hango Abutturab da yyi yasa yaji hnkalinsa ya kwanta,

Kafin ya karaso ya qarasa garesa kallo daya zakayiwa madu driver kasan a tsorace yake ,

Yallabai !"dama da.....kasa karasawa yyi da hannu ya shiga nuna masa nainah ,Karasawa yyi gaf daita gabansa yaji ya fadi lokaci daya dama wannan yarinyar yar shaye -shaye CE?"

Bin wurin ya shigayi da kallo tabbas nan gidan giya ne!"Afusace ya Juya kan madu yana binsa da wani matsiyacin kallo ,meyasa ka kawota a irin wannan wurin?"

Wlhi idan ban kawota ba zata iya korata ,tsoki Abutturab ya buga afausace yashiga fa'din ."ko kasan duk zunubin da ta aikata Dana ka kamisho aciki?"ya zanyi yallabai ,Aunty nainah batada mutunci."Abutturab bai kara sauraren driver ba ya nufeta Afusace ,ya fisge kwalbar veer din ya watseta a kasa.

Lokaci daya ta ka'llesa tana langabar da kanta Sai kawai ta fashe da kuka cike da shagwaba take fa'din meyasa ka fasamin?"kallonta kurum yakeyi Sai yaga ta qara kyau!"

Ki rufemin baki!"

Yyi mganar cikin daka mata tsawa!"

Hannunta duka biyu tasa ta toshe kunnuwanta ,

A hnkali ta sauko daga kan motar .

Baya tayi zata fadi yyi saurin tarota ajikinsa ,umurni yyiwa madu driver akan ya bude masa back side ,cikin bin umurni ya bude masa .ya sakata ya shige front side madu driver yaja motar sukabar wurin .ga mamakin Abutturab Sai yaga yabi titin maska Road !"ina zaka kaimu ?"ae yallabai idan Hajia tana cikin wannan yanayin agidanta take kwana dake maska Road!"shuru Abutturab yyi bai kara cewa komae ba amma kallo daya xakayi masa kasan Ransa abace yake......

 

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.