Free chapter · Read without an account
2
qallonsa ta tsaya tanayi da mamaki a fuskarta haka tana yimasa wani irin qallon tsana ,magana takeso tayi ta qasa .lokaci daya taji ya fisgota ya wani hade rai .baiyi magana ba
Sai taga ya haɗe bakinta da nasa sauqar wani Abu takeji acikin ba'kinta Wanda ta qasa tantance minene .
qazantar bakinsa takeji kokarin fisgar kanta takeyi ta qasa haka amai takeji sosae bbu musu ta hadiye narkakken tuwon shinkafan da khaleepha ya zuba mata acikin baki saida ya tabbatar ya wuce a makoshita yyi saurin turata da qarfi. qaro na farko a Rayuwarsa da ya hada bakinsa da na wata ya'h macce.
Amai taji yazo mata bbu musu ta durku'she anan ta shiga yin Aman tamkar Ranta zai fita.
Idan zaki iya ki fiddo da cikin duka Lailah maska!"
Kowane fanni bazaki iya Jadani ba.nafi karfinki !
Ya qarasa maganar cike da gadara gamida ficewa daga kitchen din ,
Kusan cin qaro sukayi da Hajja ganin lailah zube a qasa tana Amai tamqar ranta zai fita idonta na akan khaleepha tana binsa da qallon tuhuma .
Ta gefenta ya Ra'ba zai wuce ,tayi saurin dakatar dashi."
dawo nan khaleepha mekayi mata?"
Hajja ta tambayesa gamida tsaresa da ido .batareda khaleepha ya amsawa Hajja ba ya cigaba da tafia .
"Auh tafia xakayi Dan uwarka ina magana?'
Hajja tayi maganar a Dan tsawace!"
Shaye da to'ka khaleepha ya Juyo yana qallonta .kinga abunda ke ha'dani dake Hajja kidaina zagarmin uwa!"
"Baki wangalau hajja ke qallonsa na zageka ko zaka Rama.?"
Karama nace Abubakar!
baice komai ba ya Juya yafice daga kitchen din Ransa a ba'ce...
Yarasa mai xaiyi Wanda zuri'ar maska zasu tsani lailah gaba day'a kamar Yarda ya tsaneta.
Hajja zata riqa ta tayi saurin ture hnnun Hajja .haka lokaci daya ta saki kuka ,Lallashinta Hajja keyi ganin haka lailah ta qara lafewa ajikin hajja ."
Meyayi maki?"
Kanta ke ciwo haka tana Jin bakinta ba dai dai ba.
Tana Jin kazantar bakin khaleepha maska .
Wai yau ita Lailah Maska ke hada baki da khaleepha Maska,tayi Alkawarin Ramawa .
Ta kowace irin hnya ce.
Hajja ta riqata zuwa parlor Amra kawae CE a falon .tana zaune tana qallon tashar zee word.
Murya mujaheed maska ta tsinkaya a tsakiyar falon yana kwala mata kira .kwance take akan soofa idonta a lumshe har yanzu batajin ta dai -dai ."
Kan hannun kujerar da lailah ke kwance Anan ya zauna ."matashin saurayine Wanda baxai wuce shekara Ashirin da Biyar ba A dunia."
qallo daya zakayi masa zakasan sun hada Jini da khaleepha maska.sae dai shi Mujaheed fari ne tas.Haka bai kai Jikin khaleepha maska ba .
Bai kuma kai tsayinsa ba."
Yyinda khaleepha maska black beauty ne yana da tsawo haka yana da Jiki.mujaheed maska Kullum fuskarsa farin ciki ne da Annashuwa acikinta mai haba-haba da mutane ,mai son qa'nnensa sabanin khaleepha maska.'yarda yake ba'ki haka fuskarsa take bbu fara'a akanta.miskilanci da shegen girman kai."Amma a hka bbu Wanda uwarsa keso fiye da shi..
"Hajja meya samu Swt sis ne?''
Yawancin lokutta haka Jaheed maska ke kiran lailah.
Yyi maganr cikin fuskar damuwa."yooh itada wannan mugun ne Wanda bbu Allah azuciyarsa.
Da mamaki mujaheed ke fa'din Yaushe yah khaleepha yazo zaria?''
Dazun nan mana .bu'de idonta tayi tana qa'llon mujaheed ,Wanda shima idonsa na qanta.
Kuka yasaki ko?
" mujaheed yyi maganar murya a qarye ,Laylah batace komae ba.
Ta tashi zaune sosae ,wasu lokutta tana Dan kyale khaleepha ne sabida mujaheed .Dan duk cikin zuriar maska mujaheed ne Wanda tafi kusanci dashi.
"Wannan qaron kuma meya hadaku?mujaheed yyi maganar Ransa a Dan ha'de .yanajin yarda wani sashe na zuciarsa kejin haushin yayan na'sa ." da wanine keyiwa laylah haka ,da yanzu yakai qarshensa.
Ya tsine fuska Lailah tayi ,Yah mufita zan sha ice cream."tayi maganar gamida tu'ro masa baki.Hajja ta qaraso falon riqe da tea cup ta miqawa lailah.ya tsine fuska tayi ,
Ta qalli hajja a tausashe tace na qoshi Hajja fita zamuyi da Yah mujaheed .A masifance Hajja ta dire cup tea.din tana ban bamin fa'da kada Allah yasa kisha cikin ki banawa ba.
Anan Hajja ta wucesu tana banbamin fa'da .mujaheed ya qa'lli Laylah wadda tabi ta ha'de rai .Dan ware idonsa yyi akanta."
Hey babe!"
Kin fasa fitar ne?
Yyi maganar cikin wani irin yanayi .shikawae yasan meyakeji idan yana tareda Laylah maska.
doguwar Abaya baka kawae ta aza asaman kayanta mai maba'llai Ajikinta .
Sai black veil na abayar wadda tayi Rolling kanta dashi ,tun daga kan stairs mujaheed yake qallonta .
Baya gajia da qallon Laylah maska komae nata mai kyau ne.
"Jerawa sukayi sukafice daga cikin falon gidan .Amra CE ta fito kitchen da gudu tana fa'din Yah Laylah kizomin da nawa.
Juyowa mujaheed yyi yana wurgawa Amra din mugun qallo ,kafin yace wandda kuka fito tare yakai ki shan ice cream mana.
dan turo baki Amra tayi ,tana fadin Yayah mujaheed ni bakai naceba.
Yah Laylah nace !"
girgiza kai Laylah tayi taja hnnun Mujaheed tana fadawa Amra zata siyomata.
Yaya bani najamu mana.bbu musu ya cilla mata car key ta cafke ,
Idon khaleepha maska na Kansu wanda ke zaune Acikin fararen kujeron dake cikin balcony din.
Wya yakeyi amma hankalinshi na kansu.
Haka kawae yaji Ransa ya baci ganin yarda Laylah ke wasa da mujaheed hardasu kya'lkyalar daria Sai yaga a yau tafi ko yaushe kyau.
Samun kansa yyi da saita camera yashiga daukarta pics."Wanda zuciyarsa ke basa umurnin yin haka.akan idonsa suka fice daga cikin get din gidan.
Yayah Ice cream din nan da ddi kamar yarda yanayin nan yake da ddi ,
Yayah mujaheed inason yanayin damina yafi kowane irin yanayi ddi.
Lokaci ɗaya lailah ta hade rai ganin yarda mujaheed din hnkalinsa baya ma kanta.
"Yaya mana."
Tayi maganr a shagwabe gamida cinno masa dan qaramin bakinta mai daukeda kyawawan pink Lip's. Dan ware idonsa yyi akanta yana fadin Lailah mana.
Yyi kwaikwayon muryarta murya can ciki.
" shin wai minene damuwar ?.gaba day'a kabi ka canja fa'damin minene?
Kaga wannan karon bazan kyaleka ba.bazan saurareka ba.
Akwae abunda kake bo'yemin ta qarasa maganr shaye da to'ka.
Sanyi nakeji Laylah maska."
Yyi maganr can cikin maqoshinsa ,ware idonta tayi tana murmushi tana fa'din bbu sanyi Yaya .
Yanayin nan yana da ddi kaji yarda iskan Allah ke kadamu kaji wani irin kamshi na damina.
Ta fa'da tana lumshe idonta kafin ta bu'desu a hnkali ,gamida saukesu akan Mujaheed maska."Wanda ya zuba mata narkakkun idanunsa masu wani irin yanayi.
"Baka da lfy Yaya .
Ga idonka nan ya nuna tashi mutafi Asibiti laylah tayi maganar tana qoqarin miqewa tsaye ,
Kamota yyi ya zaunar daita.
Lfia ta qlau fa.
To minene?"
"Gobe zan koma Cyprus.
Har yaushe ka dawo Yaya sabida Allah ko sati hu'du bakayi ba.ta qarasa maganr tamkar zata fashe masa da kuka.
Na fada maki hutun baida yawa .Am so sorry!"
Ya fa'da yana qoqarin kai hnnunsa akan ka'fadarta tayi saurin buge hnnun nasa ,bakada kirki yah mujaheed ka Rabu dani ."
Zaka koma skull shine sai yanzu zaka sanar dani.?
Tayi maganar tana fashe masa da kuka .da gaske laylah maska hawaye takeyi kuka takeyi dan zai ko'ma skull.
duk wannan tashin hnakalin na minene? "Dan kawae Mujaheed maska zai ko'ma makaranta laylah ke zubar hawaye.
To oya share hawayenki kiji." Bbu musu ta fara share hawayen yana qallon fuskanta Wanda har ya fara canjawa.
"Bazan komaba.
Zanje na fadawa Baban Kaduna.bana iya karatu a Cyprus adawo dani Nigeria .Nigeria ma a garin Zari'a shikenan?"
Yyi maganr yana qallonta bata rai tayi haka kawae saika datse karatun da kayi Rabi cikinsa sabida ni yah mujaheed! "
da yanzu Ina karatu a Cyprus da ku'llum muna tare amma wannan mugun ya soke tafiar ya zuga Abban maska.an hanani tafia!"tayi maganar rai abace!
"dan murmushi mujaheed yayi yayah khaleepha fane ko?''
Batareda ta amsa saba take fa'din gobene birthday party din Meela ,ya zanyi yayah?"
Kowa da boy friend dinsa zai shiga wurin .ni kuma bani da *Saurayi Yayah mujaheed*!"
Nazata tare zamu tafi Yaya.
Yarda tayi maganar sai tabasa daria.da gaske laylah maska bata da Saurayi duk wannan kyawon nata?"yayi tambayr cikin wani irin yanayi da bazai fassaru ba!"
"Kaima ka sani Yaya !
Ya zanyi .
Saiki fasa zuwa.
Ware masa manyyan idonta tayi.
Abun kunya ne yayah mujaheed kasan kuwa ya matsayin Meela yake a wurina?"
"She is my Best Friend in the whole world. Bazataji ddi ba.yayah!
Wannan zuwa partyn ba addini bane Laylah ki hkura dashi.plss muje gida Kaina ke ciwo.
Yyi maganr gamida dafe kan nasa.
da gaske sanyi yakeji suna shiga mota ,jacket dinsa ya ya Daura a saman farar shaddarsa.haka ya takure kansa wuri day'a Ac.n ma da suke sha kashesa duka tayi.
Bbu yarda lailah batayi ba akan sutafi Asibiti.amma yaqi dole suka dau hnyar komawa gida.
Haka zakaja mota har Kaduna ?" Bakada lfy kabari sai gobe nan gidan Hajjan maskane ko ka manta.?
Lailah tayi magana cikin fuskar damuwa.
Baya iya magana zuciarsa ke dokawa."sanyi yakeji sosae amma bazai iya kwana Zari'a ba.
da kyar yake fadin inada abubuawan da zanyi a yau shiyasa .gobe Jirgin qarfe 12:@m zanbi .batareda lailah ta qara magana ba.ta bude back sit ta saka Ice cream din Amra.
Ga ice cream din Amra nan nasan zaiyi melting kafin ka kai."idan ka kai mata sai ta qara sawa a fridge ka gaisheda su Mami da Hajia.
da haka ta Rufe ko'far gamida matsawa gefe ,tana maganar ne batareda ta qallesa ba.
Haka yana nufin fushi tayi ,fitowa yyi daga motar.
Ya qaraso gabanta hnnunta na dama ya riqa yana fa'din haka zan tafi kina fushi dani."?
Yyi maganar a qarye."
Batareda tayi magana ba.ta danyi hugging dinsa,
Tana fa'din I love you.Allah ya kiyaye hanya bata jira mai zaice ba.
Ta zare Jikinta cikin nasa tabar wurin da gudu.
*****
Kaduna.
Cire kayan Jikinsa yyi gamida dannna su acikin washing machine. "Har lokacin Jikinsa qamshin Turaren Laylah maska yakeyi.
Baita ba ha'da Jikinsa daita ba." Amma yau shine da hada baki da Yarinyar da yakeyiwa tsanar da baisan adadin taba.
Fadawa yyi akan bed gamida lumshe idonsa ,haka yakejin bakinsa tamkar Wanda yasha swt.baisan mai yakaisa hada bakinsa danata ba?
Baisan waya aikesa ba!"
Barci yakeso yyi da gaske barci yakeji .....Amma kowane Juyi da zaiyi Laylah.
Maska ke manne aransa.
Tsoki ya buga a qaro na farko tamkar Wanda aka tsakura ya miqe tsaye gamida daukar brown jallabiyar sa ya saka.haka ya xura Bed shoes nasa yyi part din mamin sa.
#ASMY B ALIYU
#lailah Khalifa
#maska family
#love ,hate and destiny
#family And reletionship